Showing 132001 words to 135000 words out of 271643 words
Chapter 45 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
sabo da mutane domin wayeyen mutum ne da ya iya jan mutane jiki.
“Kin ga mun fita kina kuka yanzu mun dawo kina dariya”
Ta sake yin murmushi mai sautin, har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleshi.
“Zaka kira kin Sulem? Ko mu je?”
“Inda yake?”
Ta daga kai.
“Toh ai kin ga ni ban ga Sulem din ba balle na san yadda fuskarsa take ba, kuma ban san masaukinsa ba, labarinsa kawai aka ba ni, kuma babu number sa a nan ban san number shi ba”
“Ka sani”
Ta fada da kamar shagwaba tana son dawo masa da kukan, a iya gaskiyar take fadar ya nemo mata Sulem ko ya kira mata shi, bata gama wayewa da abubuwan garin ba dan haka ba san idan baka da number mutum baka iya kiransa ko kuma shi idan ba shi da number ka ba zai iya kiranka ba, ita dai tana ganin ana waya a kara waya a kunne a ji magana, kuma a iya saninta garinsu idan ana neman mutum ba shi wahalar ganewa.
“Idan ina da number shi me zai hana na ki kira miki shi? Ba ni da number shi”
“Kana da”
Idonta har ya fara zubar da hawaye. Matsawa yayi kusa da ita ya ciro wayar ta shi ya mika mata.
“Idan kina da mumber shi saka a kira shi”
Ta kalli wayar ita dai tana jin ana cewa numbers kuma ana nuna mata su a makaranta, does that mean kowa yana da number shi kenan, sai ta kama ring din dake wuyanta, ta duba S ne a jiki tunanin ya bata cewar number Sulem dinta kenan.
“Na shi alphabet ne, ka saka S”
Jabir be san lokacin da dariya ta subuce masa ba.
“Ba haka ba ne, ita number kira ai tana da yawa ba kadan ba ce balle ace daya, kuma kin ga number dabam alphabet dabam na daya ba ne”
“Ka kira haka nan”
“Ko na kira ba zai yi ba look here kin ga babu inda S take a nan duk numbers ne”
Ya nuna mata wayarsa, sai ta taba 5.
“Gata nan, ita ce ta canja ka kira haka nan zai yi”
Ya fita gurin ya shiga gurin kira ya nuna mata numbers din mutane.
“Kin ga yadda numbers suke kowa da kalar tasa kuma suna da yawa”
“Ka saka 5 da yawa”
“5 dabam S da am ba a banbance muku ba a makaranta? Kuma 5 din har guda nawa zan saka?”
“Da yawa”
“Okay”
Ya saka 5 din kusan guda ashiri sannan ya kira ya saka mata a speaker, ta ji ana the number you try to call is not exist, sai ta fashe da kuka.
“Ka cika da yawa, ka saka kamar na su”
Ya rage ya saka daidai ya sake kira the same thing.
“Idan mun shiga ki ce Ummi ta kira shi ni wayata ta lalace bata kira kin ce ai abun da take cewa”
“Okay, ni meye number na?”
Gudun rigimarta ya saka dole ya bata number.
“2”
Ta share hawaynta da rigar jikinta sannan ta shiga falon, shi kuma ya juya ya shiga motar daman yana da gurin zuwa bata bari sun tafi ba tace ya kawo ta gida.
43
Idonta be sauka a ko'ina sai akan Tea da ta bari dazun, kamin ta kalli dinning room tunawa da a nan ta bar Maleek a lokacin da suka fita, ba ta yi zaton Ummi ta dawo ba dan haka bata haura sama ba sai ta zauna a kasan kujerun da suke nan ta bude wani chocolate din tana ci, tana daf da cinyewa zomonta ya zo gurinta da gudu ya fara shinshina jikinta. Tana ganin haka ta tashi ta shiga Kitchen ta kunna tap ta wanke hannunta sannan ta dauki cup ta aje ta zuba ruwan zafi ta saka Lipton kamar yadda ta ga Ummi tana mata, sugar da sauran kayan hada tea da suke kitchen din sun mata tsawo domin suna a cikin cabinets ne, ita kuma ba wani tsayi ne da ita sosai ba idan ma zata ce ta dauko sai idan zata hau wani abun ne, dan haka ta dauko ta dawo dinning ta aje cup din ta bude sugar ta saka fiye da cube din da Ummi take saka mata sannan ta dauki daya ta kai baki tana tsotsawa, daki-daki ta bi har ta hada wa kanta tea ta dauko ta fito dinning area din ta dawo falo ta zauna, tana busawa saboda ya rage zafi.
“Idan Ummi ta dawo zamu ce ta kira Sulem ko?”
Baby rabbit dinta take tambaya da yarenta tana shafa kansa.
“Zill na baka labari? A can garin mu ina da bera da yawa a dakina, kuma ina da zakaru, kuma ina da Eid, na san yanzu ya manta ni, ko kuma yana jin haushin guduwa da na yi shiyasa ba zai zo ba na yi kewarshi sosai”
Shi dai zomon ya zauna a jikimta shiru sai saurarenta yake kamar fahimtar abun da take fada.
“Yanzu ni da kai Ummi ce mamanmu ko? Ko kuma ni ce mamanka kai ni kuma Ummi ce mamata”
Ta dauki tea zata kai baki sai ta kalli stairs Maleek dake tsaye rike da key ta gani tsaye yana kallonta. Babu annuri a fuskarta ba kuma fushi yake ba, rashin walwala ne irin ba wanda ke cikin tsananin damuwa domin idanuwanta sun nuna haka as well as fuskarsa. Aje cup din ta yi ta mike tsaye tana kallonsa a zatonta fada zai mata saboda fitar da Jabir yayi da ita, a kokarin ta na kare kanta ta duka ta dauki ledarta da cup din ta nufi inda ta saba boya ta zauna tana sauraren ta ji ko binyo ta zai yi. Shi kam bata ita yake ba, a zahiri ita yake kallo amman a badini tunaninsa da hankalinsa suna gurin damuwarsa ne. Ganin be wuce ba ya saka ta sake lekowa sai ta ganshi tsaye har yanzu inda ta tashi yake kallo sai dai wannan karon ta ga abin da ya daga mata hankali, hawaye ta gani a idonsa, saurin boyewa ta yi gabanta ba faduwa. Tana jin saukowarsa ta takure guri daya ta yi zaton gurinta zai zo, sai ta ji shuru hakan ya saka ta sake lekawa ta ga baya gurin, fitowa ta yi gaba daya, ganinsa ta yi zaune akan kujera ya cije ya cije baki yana kallon wani gurin dabam.
“Ya Maleek”
Yesmin ta kira shi be amsa mata ba be kuma juyo ba, sai yayi saurin tashi ya fice daga falon ba tare da ya bari ta ga hawayensa ba. Waira ta kalleta ba wani sabo ta yi da ita ba dan haka bata ce mata komai ba ta koma ta zauna a inda ta saba boya ta dauki tea ta rike da hannu biyu kamar yadda ta saba yi ta shanye duka. Sannan ta sake fasa wata ledar chocolate din ta fara ci tana yi tana lashe hannu, sai da ta gama sannan ta fito rike da cup din ta nufi kitchen jin motsi ya saka ta boye sai ta fara lekawa ta ga Yesmin ce ke kokarin kunna gas sannan ta shiga ta aje cup din ta wanke hannunta, bata san rike sunan Yesmin ba, dan haka ya saka ta matsa kusa da ita ta taba rigarta.
“Zaki kira min Sulem”
“Waye kuma Sulem?”
“Wanda ya zo, ko ki kira Ummi”
“Ummi tana dakinta, shi kuma Sulem ban san shi ba”
Tana jin haka ta yi saurin fita kitchen din ta nufi stairs da gudu ta fada dakin Ummi sai ta tarar da Ummi a bathroom.
“Ummi... Ummi”
Ta kira sunanta daga bathroom din Ummi ta amsa muryarta a shake.
“Na'am Baby Waira gani na fitowa”
Gurin kofar Bathroom din Waira taje ta tsaya har sai da Ummi ta fito, sai ta rumgume ta tana murnar ganinta ita dai idan Ummi bata cikin gidan bata da natsuwa da kwanciyar hankali duk sai ta ji kamar bata da kowa a duniya ta zama marainiya.
“Oyoyo Yata i miss you”
“Ummi baki tafi da ni ba”
Waira ta fada tana kallon idonta dake kumbure har bata oya bude da kyau.
“Waira ko dan kin ji ina ce miki Baby? Ke fa ba yar karamar yarinya ba ce da zan rika yawo da ke, daman can ai ba fita nake da ke ba, dan haka ki daina cewar ma ban tafi dake ba”
“Ummi idonki ya dahu”
Ummi ta yi dariya tana murza idon.
“Ciwo yake”
“Kuma Ha Maleek yayi kuka”
“A ina kika gani? Maybe saboda Nimra bata da lafiya ne, kin san tana asibiti ko?”
Ta daga kai, Ummi ta sake ta ta nufi wayarta dake cikin jaka tana ringing, bude jakar ta yi ta dauko wayar number one of ma su kula da gate din ta ne yake kiranta.
“Wa'alaikussalam”
“Hajiya an wuni lafiya?”
“Lafiya kalau”
“Na kira wayar Alhaji be daga ba shiyasa na kira wayarki, wani ne ya zo da mota yana son ya shigo ciki, na ce wa yake son ganin wai Zahra”
“Waye shi?”
“Bari na tambaye sunanshi”
Tana jin lokacin da yake ta tambayarsa ya sunansa amman yaki yayi magana.
“Musa bar shi ya shigo na gane shi”
“Toh Hajiya”
Ta aje wayar ta nufo falo Waira ta biyo bayanta. Yesmin dake zaune ta dago tana kallon Ummi wadda ta zauna kan kujera idonta na kan kofar falon, juyawa Yesmin ta yi ta kalli kofar sannan ta juyo ta kalleta.
“Ummi lafiya”
Ummi ta daga mata hannu alamar ta dakata. Da wani irin karfi aka murda kofar falon aka turota, daga Ummi har Yesmin da Waira sai da suka mike tsaye suna kallon Ameer da ya shigo falon fuska babu annuri, kai tsaye ya nufo inda Ummi take domin ba kallo kayan alatu suka kawo shi ba balle ya tsaya bata lokaci. Tsaye yayi a gabanta kamar without any rest yana mata wani irin kallo da ya fi kama da tsana. Waira ta saki baki tana kallon Ameer da mugun mamaki shi kam ko ganinta be yi ba domin baya ganin kowa a falon sai Ummi kadai daman zuwan nata ne. Yarfar da hannu ta fara yi tana son ta tuna sunansa ta kasa amman tabbas ta gane shi, abun ka da mai son mutane ta ga wanda ta sani sai jin yayi an shiga tsakanin shi da Ummi an rumgumeshi da karfi. Yana kokarin saka hannu ya ture kowaye ta dago kai shi kuma ya sauke nasa kan kasa dan ganin wanda ya yi masa wannan kasadar. Murmushi take masa mai sauti hakoranta a washe, lokaci daya ya gane wacece ita, ya tuna inda ya fara ganinta, alakarta da gidan ta tuna masa cewar ita ce yarinyar da ya saka a motar Nimra, daman Nimra ta fada masa yarinyar tana gidansu, a yanzu ya gane duk ganin da yake mata a gidan take. Yesmin ta fisgeta ta jefar da karfi kan kujera.
“Baki da hankali daga ganin mutum zaki tashi ki rumgume shi?”
“I know him i know him”
“Idan kika taba shi sai na kusa kasheki. Kai.. Ya zaka shigo cikin falo ka nufi uwar masu gida kai tsaye ko baka da hankali”
Ta fada tana kallonsa kamar yadda yake kallonta cikin bacin rai, shigarsa da yanayinsa be yi mata kama da mahaukaci ba, balle ta ji tsoronsa kama yayi mata da marasa tarbiya yan tijara.
“Yesmin stay out of this please, Ameer me kake so?”
Ummi ta fada sai ya dawo da dubansa gareta.
“Shaida abun da zai saka na yarda da abun da kika fada”
“Ribar nawa zan ci idan na yi maka karya? Na san wannan abun zai iya kai ni gidan yari idan har karya ne, to akan me zan yi haka? Ina da yaya mata kuma Allah ya ba ni mata idan ba ni da hujja ba zan yi haka ba, idan aka auna jinina da naka na tabbatar results daya zai ba da, ba dukiyar Mr Bashir nake kwadayi ba nima Allah ya rufa min asirin da zan iya yin komai... Amman jira ni ina zuwa”
Ta nufi stairs da sauri dakinta ta fara shiga ta bude wardrobe dinta, sai da ta fara kokarin sauke akwatin sannan ta tuna Maleek ya dauki jakar, da sauri ta fito dakinta ta shiga dakin Maleek akan gadonsa ta tararda jakar wasu takardun a watse wasu kuma be taba su ba, wadanda be taba din ba ta dauka tana dubawa har ta kai ga evidence din da take son nunawa Ameer ya sauko da sauri ta iso inda yake ta mika masa. Kallon envelop din yayi ya kasa mika hannu ya karba, kamar wanda aka cewa makomarsa ce a ciki.
“Shaidata tana nan, kuma ka tambaye duk abun da kake so zan amsa maka...”
Cikin nauyin jiki tana zuciya ya karba ya bude, takardar yarjejeniya ya fara cin karo da ita kalar wadda Hajiya Jamila ta bashi, abun da ke rubuce a can shi ne a rubuce a nan babu banbanci har kwanan wata. Daga kasan takardar kuma hoton mahaifinsa ne da ya kara gasgata masa cewar tabbas shi ba ďan Mr Bashir ba ne. Domin kamanin dake jikinsa da fuskarsa su ne a jikin hoton banbancin wannan hoto ne da ya dade shi kuma yana a tsaye ne a zahiri. Zubewa yayi kasa guiyoyinsa ya fashe da kuka ya rumgume hoton a kirjinsa.
“Me yasa zaki yi haka? Me na yi miki?”
Dukawa ta yi tana kuka
“Baka min komai ba Ameer, ban aikata hakan saboda son zuciya ba”
Ta mika hannu zata taba shi sai ya daka mata tsawa da zai da ta zabura.
“Don't touch me”
“I won't i won't”
Ta rike hannayenta da sauri.
“I'm sorry Ameer na san ban kyauta ba, amman ban aikata hakan da nufin bana son ka ba dole ce ta saka”
“Da kina so na, da baki siyar da ni ba tun farko, kuma da baki bari na rayu a gurin wani da yake amsa sunan Ubana ba, da soyayyaa bata barki kin kai wannan lokacin ba tare da ni a kusa da ke ba”
“Wallahi soyayyar ka bata bar ni na samu farinciki da kwanciyar hankali ba, a kullum da kai nake wuni na kwana a zuciya, ina tunani a wane hali dana yake ciki”
“Ni ba ďanki ba ne, you have never been my mother and you will never be, kin san abun dariyar? A kullum sai na yi ma mahaifiyata a addu'a, saboda Daddy ya fada min cewar ta mutu, kuma haka zan cigaba da yin addu'ar har a yanzu, domin har yanzu uwata a mace take, ta tafi kenan ba zata taba dawowa ba, ki bayyana gaskiya a yanzu saboda ki sake ruguza rayuwata, me yasa ba ki bar ni na cigaba da kallon mutumen da ya tsaya min a matsayin Ubana ba?”
“Saboda ina son na farantawa kowa kamin na mutu, na tafi ana yabawa ba a bini da bakar addu'a ba, ina son an roki gafarar kowa Ameer?”
“Har da mahaifina? Ba zaki taba samun wannan damar ba, ba zan taba yafe miki ba, kuma ba zan taba kallonki a matsayin uwata ba..”
“Mahaifinka yana kaunata Ameer, da ace yana raye da baka isa ka fada min wata magana marar dadi ba, ban aikata hakan dan bata ran kowa ba, idona a rufe lokacin bana ganin kowa sai mahaifinka rayuwarsa kawai nake son na ceto”
“Yana kaunarki, amman ke baki kaunar ďansa baki son jininsa, shiyasa kika zabi rabuwa da shi, why me? Miyasa baki siyar da Maleek ba?”
Kamar daga sama suka ji muryar Abiey yana amsa tambayar da Ameer yayi.
“Saboda Maleek ubansa mai arziki ne, Ameer kuma an siyar da cikinsa ne saboda a nemawa Ubansa magani”
Duk kallonsa suka yi, Ameer ya ji ina ma be zo duniya ba, da be ga wannan bakar ranar ba a rayuwarsa. Ya girgiza kai ya kalli Ummi yana murmushi.
“Na gane, tsiya kike gudu, shiyasa da kika samu wani mijin kika watsar da ni, kika tara wasu iyalin? Toh miyasa yanzu kika ruguza tawa rayuwar? Da ace da kika haife ni kashe ni kika yi da na huta ganin wannan ranar, kin cutar da ni ba ki cancanci a kira ki uwa ba, na ga soyayya da kauna daga gurin wadanda ba jinina ba, ya kike son na yi rayuwa a yanzu? Farincikin da nake ne yake kona miki rai?”
Ummi ta kasa cewa komai sai kuka take, ya mike tsaye rike da takardun ya nufi kofa har ta ya kusa fita ya juyo hawaye na masa zuba cikin ihu ya ce.
“Kin san zafin da ďa yake ji idan uwarsa bata sonsa? Da ma gidan marayu suka hai ni, siyarwar ita ta fi min zafi...”
Ya juya ya fice, kai kawai take iya girgiza masa domin kuka ya ci karfinta ta yarda bata ko iya magana. Abiey ya rikota ya nufo inda take ya rikata.
“Ya isa haka, and this is the last zuwan da yaron nan zai yi a gidan nan, domin ba zan dauki ya shigo har cikin gidana ya fadawa matata magana marar dadi ba”
Ummi ta kwanto jikin Abiey tana kuka ta dafe zuciyarta, Yesmin ma kuka take duk da kasancewar a yanzu ne ta fahimci abun da yake faruwa, Waira ma kuka take tana kallon Ummi.
“Me yasa bana da tunani, me yasa ban yi tunanin zuwan irin wannan ranar ba Abiey? Ameer zai iya shiga wani hali, ba zai yafe min ba na shiga uku..”
Shi ne abun da ta iya furta tana kuka sosai kamar zata rusa ďakin.
“Zai yafe miki amman ba a nan kusa ba, dole sai kin jure kin zama jajirtacciya, and i promise you zan yi iya kokarin da zan yi na gyara mun gyara duk wani abu da kika bata”
Ta runtse ido tana girgiza kai, zuciyarta na wani irin zafi kamar an watsa mata tafasasshen talge a ciki.
____________________
Allah sarki Ameer 😭 ni dai duk ya fi ba ni tausayi, taya kana rayuwa da iyayenka rana daya ace ba iyayenka ba ne. Wayyo Allah, ku dauke zancen jindadi ko da wahala ake sha a tare wannan kallon da kake musu a matsayin iyaye canja shi ne abu ne mai wahala, and the most painful part yana zaton uwarsa ta mutu ashe tana raye a kusa da shi........
Ni daman can team DEEN ce yanzu ma ina bangaren ďansa AMEER, gaskiya Zahra baki kyauta mana ba 🥺😏
𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 𝐧𝐚 𝐦𝐮𝐤𝐮 𝐛𝐚𝐫𝐤𝐚 𝐝𝐚 𝐒𝐚𝐥𝐥𝐚𝐡.
𝐅𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐤𝐮𝐧 𝐲𝐢 𝐒𝐚𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐥𝐚𝐟𝐢𝐲𝐚, 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐲𝐚 𝐦𝐚𝐢𝐦𝐚𝐢𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐲𝐚 𝐤𝐚𝐫𝐛𝐢 𝐢𝐛𝐚𝐝𝐮.