Showing 243001 words to 246000 words out of 271643 words

Chapter 82 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

Ameer ba, duk wanda take so shi za a aura mata, but for now ni na ja jiki already na yi magana da Ameer jiya na fada masa ba zan iya jayyaya da dan'uwana akan mace ba, duba abun da ya faru ya so kashe kansa saboda kawai ya ji cewar an daura aurena da ita, da ya mutu ya Ummi zata ji, kuma ni ma hakan ba zai min dadi ba, zan iya rasa Nuwaira ko kuma shi ya rasa ta amman ba zan sake samun dan'uwa ba”

“Ka yi tunani mai kyau Maleek shiyasa a kullum nake alfahari da kai, kuma bana shakkar nuna ka a ko'ina, ko yau na mutu na san ban bar mugun baya ba, zaka kula da kanenka kuma zaka yi abun da ya kamata, Allah ya zaba maka abun da ya fi zama alheri a rayuwarka Maleek”

“Ameen Abiey Thank you, about Ummi kuma na ga jikinta yayi tsanani yau fiye da ko yaushe and na yi magana da ita tace min ta yarda zata je asibitin a dubata”

“Already mun fara magana da Dr akan ciwonta saboda kai na ga abubuwa da yawa a gabanka kuma ga matsalolin da suka tunkaromu a yanzu, saurin da nake yanzu ma daukarta zan mu muje asibitin idan ka kare abun da kake sai ka same mu”

“Okay sai na zo”

Ya nufi kitchen ya dauki kwandon da aka aje da kayan abinci da kuma flask, Abiey kuma ya nufi upstairs. Tafiyar minti goma sha biyar ta ya iso Asibitin Skylines, duk yadda ya so ya fara isa dakin da Nuwaira take hakan be faru ba a dole sai da ya fara zuwa office dinsa ya duba wasu abubuwa sannan ya fito ya nufi inda take. A hankali ya tura kofar dakin ya shiga tana ganinsa ta sauko daga kan gadon da sauri ta nufo kofa kamar zata zo ta tarbe shi.

“Ina zaki je?”

“Bana son nan, na farka ni kadai a dakin kuma a waje ban san kowa ba”

Tana maganar idonta na cika da kwalla.

“Toh cinye ki za'ayi? Muka shiga garinku ma muka fito lafiya balle kuma nan? Muje ki zauna”

Kamar tace masa a a sai kuma ta ji ba zata iya musa like always dan haka ta koma ta zauna tana taba hannun nata gurin da aka saka mata drip. Zaunawa yayi a saman gadon yana kallonta

“Kina jin wani abu yanzu?”

Ta girgiza kai.

“Fever din ya sauka?”

Ta daga kai. Be sake ce mata komai ba ya mike tsaye ya bude abincin ya fara zuba mata, sai da ya gama hada mata tea sannan ya juyo ya kalleta.

“Kin wanke baki?”

Ta girgiza kai.

“Aa na dauka gida zamu tafi sai na wanke a can ina son na ga Ummi”

“Sai na tabbatar saukin jikinki tukuna, Ummi ma asibiti zata tafi”

“Waye ba lafiya? Ita”

“Eh kanta zata kai tare da Abiey daga nan ma can zan je, Ameer ma yana asibiti ya samu accident jiya amman da sauki sosai musamnan ma yau na ga sauki a tare da shi”

A take hankalinta ya tashi jin cewar mutumen da ta sani yayi hatsari, kuma Ummi ma tana asibiti.

“Ina son na duba su”

“Zamu fara duba jikinki tukuna, idan mun ga da sauki sai ki koma gida”

Ta mike tsaye domin tabbatar masa bata jin komai a yanzu.

“Kalli”

Samun kansa yayi da murmushi yana kallonta kamar ba zai dauke ido ba.

“Ba daga nan ba ne, zauna ki yi breakfast”

Ta bude masa hakoranta, alamar bata wanke ba.

“Bari na fita waje na samo miki brush, kin yi Sallah?”

“Eh har na jika hannun mai ciwo ma”

“Good”

Ya dauki wani plate ya rufe abincin da ya zuba, ya juya ya fita da kafa ya taka har wajen asibitin domin saninsa akwai wani karamin super market dake kusa da asibitin, ya shiga ciki ya siyo mata brush da toothpaste ya riko chocolate da biscuit sannan ya dawo cikin asibitin. Wannan karok ko da ya shigo ya samu wani likitan na dubata tare da Nurses. Likitan ya bawa Maleek hannu suka gaisa

“Yanzu Karima take ce min yarinyar nan kanwarka ce na ce mata ban ga kama ba, kuma da na duba sai na sunan mahaifinku daya”

Nuwaira ta kalli Maleek shi ma ya kalleta sai yayi murmushi.

“Kanwata ce, mutane suna yawan fadar bama da kama ai”

“Na gani ai, sam ba ku da kama gaskiya”

“I can take care of her za ku iya duba wasu patient din”

“Mun gama ma, Allah ya bada lafiya”

“Ameen”

Ya amsa sannan ya karasa gurin gadon ya bude ledar ya bude brush din ya zuba mata man wanke baki ya mika mata. Sai ta saka hannu ta karba ta sauka saman gadon ta nufi bandakin, bata jima ba ta fito ta zauna Maleek ya mika mata plate din indomie da kwai ta karba ta kura ido, tsawonta zamanta a gidan bata taba gwada cin indomie ba ko taliya, ta kan ci shimkafa ne kawai.

“Ba zan iya cin wannan mai zare zare ba”

“Baki san sunanta ba?”

“Indo”

“Indomie”

Ya gyara mata sannan ya karba ya mika mata mata tea da ya sake hadawa wannan kam babu musu ta karba ta soma sha, ya bude dayar kular ya zuba mata plantain da ya hada mata da chocolate din da ya siyo mata. Sai da ta ci ta yi fam sannan ya dauki sannan ya shiga dubata.

“Bana son Allura Ya Maleek akwai”

“An taba miki ne?”

“Eh lokacin da aka kai ni asibitin farko, kamin Sulem ya zo shi ne kawai baya min allu shiyasa nake son shi”

“Kowa kike kina so, kina son Ameer kina son Sulem kina son Mahmood sai kuma wa?”

Ta sauke kanta kasa.

“Duk mai min kirki ina sonsa, shiyasa nake son Ummi sosai”

“Ameer fa?”

“Shi ma ina sonshi”

“Shi ma yana sonki sosai, ya dauka auren gaske aka daura mana hakan ya kusan jefa shi a matsala shi ne silar hatsarin da yayi ma a jiya”

Ita ce bata ce masa komai ba har ya fasa wasu tables da suke gurin ya bata ya cire mata cannula sake hannunta ya saka mata kada.

“Ki fara koyar cin irin abinci da muke ci fiye da da baya, domin a yanzu kin dawo da zama a nan Ummi da Abiey sun zama iyayenki mu kuma mun zama yan'uwanki and i promise you za mu baki kulawar da ya kamata za mu nuna miki soyayya fiye da baya, a yanzu ne zaki gane kina da yan'uwa ba kamar baya ba”

Ya daga kanta sama ya duba wuyanta har yanzu akwai shatin yatsu da kuma akaifa da kana ganinta ka san bata mutum ba ce a wuyanta.

“Still yana miki ciwo?”

“Eh shi kadai ne yake min ciwo”

“Shi ma zai daina, za a rika miki addu'a a gurin kuma idan mu tafi gida akwai maganin da zan baki sai ki rika shafawa”

Da kai ta amsa masa. Sannan ya fice daga dakin cikin asibitin ya shiga yayi wasu ayukan ya dauki awa biyu sannan ya dawo dakin, be bari ta dauki komai ba tun daga kulolin abincin da ya kawo har filo da carpet din da Namra ta zo da shi. Yana gaba rike da kayan abinci wata daga cikin ma'aikatan asibitin na bayansu dauke da kayan, da kansa ya bude mata front seat ta shiga ta zauna ya bude baya aka saka kayan sannan ya shiga bangarensa ya ja motar suka dauki hanyar gida. Yana tukin yana kallonta ba tare da ta san yana yi ba domin hankalinta yana wani gurin dabam ba a tare da shi ba, shi dai ya san yayi sadaukarwa ga dan'uwansa ne kawai saboda tunani da ganin hakan ne maslaha, sai dai a kasan zuciyarsa ya san yana jin wani abu mai rikitarwa da kasa shi cikin wani yanayi a duk lokacin da yake kusa da Nuwaira, tun a lokacin da aljanar take tare da shi balle kuma a yanzu da abun yake zsfafa masa fiye da baya, domin ya zama cikaken namiji mai cikaken iko.

“Me kike tunani?”

Ya tambayeta a daidai lokacin da ya faka motarsa harabar gidan, kamar wadda ta farko daga bachi haka ta juyo ta kalleshi.

“Komai yayi min kamar mafarki, baka lura da haka ba? Mun shiga mun fito lafiya kuma abubuwa da yawa da nake tunanin za su faru ba su faru ba”

“Haka ne kin ssmu sauyi rayuwa a yanzu, sai cigaba da addu'a kuma ki kara rike addininki da kyau”

Ya bude motar ya fita tana kokarin bude bangarenta ta ji ya bude mata. Sai da ta kalleshi sannan ta fito ya daga kai ta karewa gidan kallo, tana ganin komai kamar ba gaske ba, sam bata saka ran dawowa a gidan ta cigaba da rayuwa ba, kusan duk abin da ya faru bata saka tsammani ba.

“Na gode Ya Maleek ka yi min abun da ban tana mafarki ba, ka tsaya min a lokacin da nake jin tsoro lokacin da garina da kuma jama'ata suka so cutar da ni, ka jefa kanka cikin hatsari duk saboda ni, ban san da me zan saka maka ba kai da Ummi kun gama yi min komai”

Murmushi kawai yayi ya ciro wayarsa ya amsa kiran da Ameer yake masa.

“Mun fito daga asibitin ai, jikimta da sauki gata nan na dawo da ita gida ma”

Ya juya ya rufe motar.

“No ba sai ka zo ba, zan direba ya kawo ta saboda ni zan tafi gurin Ummi”

After ya gama ya kalleta.

“Ki shiga ciki ai kin san dakinki idan kin huta kin canja kaya ki fito a duk lokacin da kika shirya zan yi magana da direba ya kai ki asibiti ki duba Ameer ya damu yana son ganinki”

Mamaki ya cika yau shi da kansa yake cewa zata tafi gurin Ameer? Har ya yake fada mata Ameer ya damu da rashin ganinta.

“Ameer?”

“Yeah”

Yana fadar hakan ya wuce gaba ya barta a gurin tsaye da mamaki, cikin falon ya shiga ya saka Hanne ta fito ta kwashe kayan da suke cikin motar, Nuwaira kamar kazar da kwai ya fashewa haka ta shigo cikin falon.

“You can go in, da alama gidan babu kowa sai Hanne, but please you should be careful ba zan ce ban yarda da Ameer ba a yanzu ba, amman na san so babu abun da ba shi sawa, karki yarda wani ya taba jikinta sai muharraminki kuma as i told you muharamminki na nufin mijinki, kannenki ko yayanki wanda uwa ko uba suka haifa, ko kuma kuka sha nono daya, ko kuma yan uwan mahaifiyarki ko mahaifinki, ni da Ameer da Mahmood duka ba mu da wannan ikon a yanzu so ki cula da kanki”

Yana gama fadar hakan ya nufi kofar fita falon zuciyarsa na masa mugun zafi, ya san yayi yankan kaddara ya naukar abun da ba shi da tabbacin zai iya ko akasin haka a yanzu, yes be taba furta yana son Nuwaira ba kuma ba shi da tabbaci idan abin da yake ji a kirjinsa da zuciyarsa so ne ko kuma kokarin karewa kawai kamar yadda yayi ikirari da farko. Cikin motarsa ya zauna ya kasa tuka motar kuma ya kasa fadawa direba ko daya cewar Nuwaira zata fita su kaita idan ta bukaci haka, a duk lokacin da ya tuna Ameer zai kebe da ita sai ya ji wani irin abu na fisgarsa, a yanzu dai ya shirya da dan'uwansa kuma baya fatan wani abu ya sake shiga tsakaninsu domin ya ga canji a rayuwar Ameer sosai ba kamar baya ba, a yanzu zai iya masa shaidar mutumen kwarai amman duk da haka zuciyarsa bata natsu ya kebe da Nuwaira ba.

Duk wani dauki da take na son dawowa gidan da kuma samun abun da zamu iya kira da yanci ya ragu saboda ta tararda Ummi bata cikin gidan, idan kuma ta tuna da kalar ciwon Ummi sai hankalinta ya tashi, a lokacin dakinta sai ta nemi farkom gadon ta zauna ba tare da ta yi komai ba, tunanin auren da aka daura musu da Maleek ya tsaya mata a rai, rashin lafiyar Ummi ma wani abu ne dake dauke mata jindadi. Mikewa ta yi tsaye a hankali ta isa gurin windows din dakinta ta daga curtains din ta bude windows din tana kallon Motar Maleek dake harabar gidan har lokacin, shi ma saitin windows din dakinta yake kallo kamar ya san zata leko ya ganta.

“Ya Allah make it easy for me, me nake ji now? Me na aikata why yanzu nake jin kamar ba zan iya numfashi idan bata kusa da ni ba?”

Shi dai kam mamakin kansa yake domin be tabbatar son Nuwaira yake ba ko akasin haka, abun da yake ji a kirjinza so ne ko kuma sabo ne da shakuwa. Sai da yayi da gaske sannan ya iya jan motarsa ya fice daga gida. Sai da ya daina hango motarsa sannan murmushi ya cika fuskarta ta kai hannu ta tana kirjinta dake cikin hijab wani abu take mai bugewar da saka farinciki na rabarta wani kalar abu ne dake kokarin rayuwa a tsakanin kirjinta da zuciyarta, wani kalar abu ne da bata taba jin irinsa ba, wani irin bugawa zuciyarta take da karfi kamar zata fasa kirjinta ta fito numfashinta har nauyi yake. Wani abu take ji mai kamar nishadi tuna abun da Maleek yayi a gaban Sarkinsu da kuma irin yadda Sarkinsu ya nuna yana tsoronsa, a yanzu kan ta yarda Maleek taba dake da duk mazan da ta hadu da su, a yanzu yana burgeta fiye da kowa, jarumtarsa da tsayarwa da yayi a gaban matsafan garinsu ya nemi aurenta abun a jinjina masa ne. Har ta cire tufafin jikinta ta yi wanka murmushi ne a fuskarta tunanin abubuwan da Maleek yayi ya rika ruhuta, ya hana ta tunanin komai sai shi, ciki har da aikin da ya taya ta, sai a yanzu daure mata idon da yayi yake bata dariya. Wasu tsofin tufafi da ta bari a dakin a lokacin da zata tafi su ta dauka ta saka domin bata da wasu tufafin da suka yi saura a dakin yanzu tofafin da ke motar Maleek bata san inda aka aje su ba. Bata samu hijab ko daya ba dan haka ta shiga dakin Ummi ta dauki mayafin abayarta ta rufe kanta ta fito ta sauko kasa. Hanne ta gaisheta ta mata barka da dawowa Nuwaira ta amsa cikin far'a da sakewa domin tana cikin nishadin zuciya. Waje ta fito ta zauna a kujerun da Maleek ya saba zama make herself comfortable tana jin kamar shi ne yake zaune kusa da ita. Although direban zai zo da kansa ya same ta a gurin ne ya dauko mata ya kai ta, sai ta ga sabanin haka domin babu wanda ya zo ya ce mata ta taso su tafi, haka ta yi da zama a gurin har rana ta fara yi, ana hada hadar fara Sallah azahar motar Mahmood ta kunno kai cikin gidan, ko fitowa motar be yi ba ya sauke farin gilashin motar ya mika hannunsa ya bude mata front seat.

“Ta so Nuwaira”

Da hannu yayi kiranta sai ta taso da saurinta ta nufi motar ta shiga ta rufe.

“Ummi tana son ganinki amman zamu fara zuwa ki duba Ameer”

Bata ce komai ba, shi ma be sake ce mata ba har suka bar gidan. Ta kunsa labari a ranta kala kala da zatawa Ameer idan sun isa na jarumtar da Maleek yayi dan haka ta fita motar da kuzarinta bayan sun isa asibiti. Mahmood yayi mata jagoranci suka shiga cikin asibitin, shi ya bude mata kofa ta shiga shi kuma ya juya ya koma yana fadin.

“Idan kun gaisa ki fito ina jiranki gurin motar”

“Okay toh”

Ta amsa har sau biyu saura da turanci, sannan ta shiga cikin dakin, bata saba sallama ba dan haka bata gwada yi a nan ba, sai dai ta gaishe da kanwar mahaifinsa Bahijja da ta samu a dakin, sai kuma Humairah da kusan wannan ne gani na hudu da ta yi mata. Ameer ya sauko da kafafuwansa daga saman gadon yana kallonta murmushin dake fuskarsa kamar zai rikide ya zama mutum tsabar farinciki da shaukin ganin Nuwaira, gaba daya sai ya ji kamar babu ciwo a tare da shi.

“Mama bari mu ba su guri”

Humairah ta fada tana kallon Mahaifiyarta Bahijja, a take ta tashi tsaye suka fice tare da Humairah, Ameer na ganin haka ya cira kafarsa mai ciwo ya dan taka cikin karfin halin da ya saba yana son mika hannu ya riko hannun Nuwaira, domin to him rike hannun mace or hugging dinta is nothing to him ko da kawarsa ce balle kuma wanda yake so, even a yanzu ya canja but baya jin zai iya rike kansa daga taba hannun Nuwaira ko hugging dinta musamman ma a yanzu. Ganin yana kokarin rikota ya saka ta dan ja baya tana masa kallon tausayi ganin rauni a tare da shi.

“Ya Maleek yace na daina bari wanda ba muharrami ba yana taba ni”

Yayi murmushi.

“I just want to touch you, i miss you so much ji nake kamar shekara kika yi baki kusa, karki damu kin kusa zama tawa ni kadai na kusa zama muharraminci halak malak, bana tunanin zan iya dauka lokaci baki kusa da ni Nuwaira we will gate married soon”

Daga tausayi dake fuskarta ta koma mamaki.

“Daman ana iya a addinin nan namiji biyu zai iya auren mace daya?”

Wannan karon dariya yayi kamar ba marari lafiya ba.

“No auren da aka daura muku da Maleek ba auren gaske ba ne irin na addininmu, a yanzu ne dai za a daura miki aure na gaskiya a tare da ni”

“Ya Maleek fa?”

“Shi ai ba mijinki ba ne, and he won't be, you're mine forever and ever come here”

Ya mika mata hannunss yana murmushi wani irin farinciki marar misaltuwa yana cika ransa. A take mamakin dake fuskarta ya gushe zuwa wani abu mai yanayi da damuwa, ta kasa karasa inda yake sai ma juyawa da ta yi da fice daga dakin ta kasa amsa kiran da yake mata.
One Month Later...

Dakinsa ya fito yana gyara rigarsa ya isa bakin kofar da Nuwaira take ya murda kofar a hankali ya tura, ganin babu kowa ya saka ya shiga cikin dakin ya kwankwasa bathroom ya saurara ko zai ji motsin ruwa ko kuma ayi magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login