Showing 165001 words to 168000 words out of 271643 words
Chapter 56 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
hira da Waira.
“Kin manta school bag dinki shiyasa na kawo miki”
“Thank you”
Waira ta fada sannan ta kalli Ummi.
“Ummi zan saka shi”
Ummi ta daga mata kai, ya kalli Ummi.
“Sai da safe”
Ya dauke kai ya nufi kofar fita, Waira ta bi bayansa sai ya tsaya ta iso ya kama hannunta suka fice daga falon. Daman to him rike hannun mace ba wani big problem ba ne, ita kuma ba haramci ba ne a addininta. Sai da ya fice sannan Ummi ta lumshe ido tana murmushin dake dauke da hawaye, she never thought abun zai zo kusa kusa kamar haka. Saboda ita ne or saboda Waira ne?
Saboda da Waira ne.
Ta bawa kanta amsa, tana bude idon zuciyarta na raya mata, abun da idanuwanta suka kasa gani tuntuni. Maleek ya wuceta gabanta kamar zai tashi sama ya aje mug din hannunsa kan dinning, sai a lokacin hankalinta ya dawo kansa.
“Maleek ba ku gaisa da Ameer ba, yau ya shigo gidan nan lafiya kalau kamar ba shi ba it's not wonderful?”
Maleek ya kasa cewa komai, ya sani matukar ya bude baki da zimmar magana abun da zai fito bakinsa ba zai yi ma Ummi dadi ba, and ba zai iya fada mata magana marar dadi ba saboda uwarsa ce. Kujerar dinning yaja ya zauna yana da girgiza kafarsa da alama kufular ta kai masa matuka. Farinciki ya saka Ummi barin falon ta nufi bangaren Abiey domin labarta masa abun da yake faruwa shi da yayarsa tsohuwar likita mai zaman kanta wato Dr Zainab. Tafiyar da Ummi ta yi ba karamin dadi yayi ma Maleek ba, daman so yake ya horar da Waira irin horon da ko kallon Ameer ba zata sake sha'awar yi ba. Ya mike tsaye da zimmar leka windows ya ga abun da take sai gata ta turo kofar falon ta shigo hannunta cike da dollars, tun da take a rayuwa a gidan bata taba rika kudi ba, bata san yadda suke ba, ba a taba bata ance je ki kashe shi ba, bata taba gwada siyen wani abu ba. Komai yi mata ake ko a school da sa'aninta suke siyen abubuwa da kudi be taba damunta tace zata siya ba, saboda sanin da da ta yi ba lallai ta iya cin abun da suke ci ba. Tana karewa falon kallon ta ga babu Ummi a ciki sai ta tsaya cak tana kallon Maleek gabanta ya hau faduwa da mugun karfi, ba dan yanzu da ta dawo falon ta ga Maleek ba, ba zata iya tuna yana zaune a falon ba, domin daukin ganin Ameer ya mantar a ita wani Maleek ma.
“Karaso mana”
Ya fada yana wani kashe ido dake tabbatar mata ba karamin duka zata sha ba idan ya ta shiga hannunsa. A gurin ta zubar da kudi ta har ta nufi stairs da gudu sai kuma ta dawo ta nufi inda Hanne take zaune ta fada jikinta da sauri ta fashe da kuka jikinta ya fara rawa.
“I'm sorry”
Hanne ta maida ta bayanta ganin Maleek ya tunkaro inda suke.
“Ayi mata hakuri yallabai a daga mata kafa”
Maleek be ce komai ba daman kuma ba zai ce ba, ya ayyana a ransa sai ya doketa a yau ba Hanne ba ko da kuwa Ummi ce a falon. Yana isa ya fisgota jikin Hanne ya jefar da ita kan kujera ya nufi gurin da Kristen yake ya ya cire wayar da zai iya cirewa ya nufo Waira, a maimakon ta tashi ta gudu stairs ko waje sai kawai ta yi zaune a gurin sai kuka take tana jarfar da hannu. Yana auna mata daya ta daka tsalle ta kwala wani uban kara tana murza jikinta, bata san wata rana da take da wayo da aka daketa da wani abun dukaba tun tana garinsu, sai daia yi mata hukunci idan ta yi wani abu, shi ma kuma ba sosai ba, bata taba sanin zafin jikinta ba irin yau. Mahmood ne ya sauko da gudu stairs saboda ihun da take, kamar zai same ya fadi haka ya iso gurin ya fisge bulalar da Maleek yake shauda mata.
“Meye haka me ta yi?”
Ta tashi da sauri ta boya a bayan Mahmood tana kuka sosai kamar ranta zai fita. Maleek can't tell laifin da ta yi dan haka ya fice daga falon yana hakki kamar shi aka daka ba shi yayi dokan ba. Mahmood ya kalli Hanne da mamakin abun da Maleek yayi ya ce.
“Me ta yi?”
“Toh Wallahi ni ma ba zan iya fada ba, dazun dai gaban Hajiya aka yi komai, balle na ce ko ta yi laifi, wata kila ko dan ta shigo da kudi ne yayi mata wannan dukan”
“Kudi?”
Ta nuna masa inda ta zubar da kudi, Mahmood ya nufi kudin ya dauka yana dubawa.
“Waya baki dollars haka Waira?”
Kofa kawai take iya nunawa, kuka ya ci karfinta ta yadda bata iya furta komai. Kofar Mahmood ya nufa ya leka waje be ga kowa ba ya dawo cikin falon.
“Babu kowa kin san wanda ya bata kudi”
Ya mikawa hanne tambayar kamin ta amsa Ummi ta shigo falon Yesmin na bayanta rike da warmers. Da sauri ta karasa gurin Waira dake kuka ta rikata. Waira kamar makira tana ganin Ummi sai ta zube a jikinta ta kara fashewa da kuka. Sosai ran Ummi ya bace bayan Mahmood ya fada mata abun da ya faru, sai ta hau masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.
“To me zai saka ya dake ta?”
“Waya sani, Mahmood kira shi mana”
Mahmood ya dan daga gira yana kallon yadda ran Ummi ya bace, rabon da ya ga bacin ranta irin haka an jima. Upstarts ya nufa ya tura kofar dakin Maleek, sai da ya karewa dakin kallon be ga kowa ba, motsin da yaji na ruwa a bathroom ya tabbatar masa da yana ciki.
“Alhaji fito ka taba Waira Ummi na nemanka kasa”
Mahmood na rufe baki sai ga Maleek ya fito daure da tawul, gudun ya batawa Ummi lokaci ya saka shi saka short tare da jallabiya ya sauko kasa, be karasa saukowa ba yaja ya tsaya jikim stairs yana kallon Ummi wadda ta bude nasa sabon shafin ihu.
“Tun da kake a gidan nan ka taba ganin na taba yarinyar nan? Ka taba ganin na saka hannu na daketa? Akan me kai saka zaneta? Tun farkon zuwanta gidan nan ka tsinka mata mari ba tare da hakki ba”
“Wacan marin mistake ne”
Ya amsa yana jin kamar ya karasa ya kara mata dukan domin har yanzu zuciyarsa bata daina tafasa da abun da Waira ta yi ba. Da mugun fusata Ummi ta ce
“Wannan kuma intentionally ko?”
“Ummi baki ganin abun da take yi? Mu fa musulmai ne, kina kallom yadda take a jikin Ameer amman baki ce mata komai ba, ta raka shi baki hanata ba, ta dawo da kudi a hannunta duk be miki ciwo ba sai dukan da na yi mata? Haba Ummi, ko dan abun da yayi Nimra ai ya kamata ce an saita yarinyar nan a hanya domin ita na lura sam bata da hankali kuma bata san ciwon kanta ba”
“Idan ya bata kudi, wata kila ya bata ne dan ra'ayin kansa, bana tunanin Waira zata roke shi kudi, kana ganin yawan kudin ma kasan ba rokonsa ta yi ba, saboda ita ya zo gidan nan yau, saboda ita ya sha abun da na zuba masa, idan ba a gode mata ba be kamata a saka mata da duka ba, saboda ita ďana zai dawo gareni”
“Hakan na nufin ke kika bashi damar yaje ya dauke ta a school kenan? Abun da kike kokarin ginawa a tsakaninsu is very wrong Ummi”
Ummi ta mike tsaye.
“Ni mahaifiyarka ce, this should be the last time da zaka ce I'm wrong, ni ban gina wani abu a tsakaninsu ba, duk wata alaka ko shakuwa da soyayya da ka gani a tsakanin Waira da Ameer su suka gina abarsu, ba ni da masaniya akan zai je ya dauketa a makaranta karka sake zargina, kuma karka sake saka hannu ka doki Waira, an yi n karshe”
Daker ya samu saukar da numfashin da ya hau masa saman zuciya. Sannan ya juya ba tare da ya sake cewa komai ba ya shige dakinsa.
After two weeks later...
Yana tafe Fiyya na bayansa rike da basket din da Mummy ta zuba masa kulolin abincin da za a kawo asibitin. Shi ya fara tura kofar ya shiga ya rike mata kofar ta shiga sannan ya rufe. Fiyya ce ta fara karasawa gurin gadon ta aje musu abincin tana yi ma Tsohuwar ya jiki tare da isar musu da gaisuwar Mummy, domin ita bayan kwana biyu take zuwa ta duba su, kanensa kuma time time idan zai so ko direba zai kawo abinci, Ameer kan kullum idan zai je aiki ko ya dawo sai ya shigo asibitin duba tsohuwar, domin jin yake kamar nauyinta a yanzu yana kansa.
“Ya jikin?”
Ya tambaya yana kallon Tsohuwar dake rike da ayaba tana ci.
“Jiki Alhamdulillah ďan nan, Allah yayi albarka kana ta fama da dawainiya”
Humaira ta mike tsaye ta bashi kujera, sai dai ta san ba zai zauna ba, domin ba gwada zama a dakin ba duk zuwan da yake.
“Kullum zai kin kin ba ni kujera, kuma kin san ba zama nake ba”
Ta yi murmushi.
“Ina jin ba dadi ne ace ina zaune kana tsaye”
“Kuma kullum sai na tararda ke a nan ke kike jinyarta bayan ga mahaifiyarki, ba kasafai nake tararda ita, Allah yass dai kina zuwa aiki”
“Duk lokacin da zaka zo kana sa'a da ina nan ne shiyasa, aiki kuma na daina zuwa ai tun a wacan lokacin”
Ya daga mata kai.
“You got lucky na canja if da yanzu na koreki”
Dariya Fiyya ta yi kamar yadda Humaira ma ta yi dariyar.
“Baka bukatar ka koreni ai, ni na kore kaina?”
“Why?”
Ta daga kafadunta.
“Kawai dai”
Be sace cewa komai ba, ya kalli agogon hannunsa.
“Kuna bukatar wani abu?”
“Aa bama bukatar komai a yanzu”
Shigowar da Dr yayi ne ya katse hanzarinsa daga yi musu sallama ya fice. Likitan dake cikin shiga ta kayan likitoci ya iso gurin ya mikawa Ameer hannu suka gaisa.
“An fada maka sakona”
Ameer ya kalli Humaira wadda ta dago tana kallon Likitan.
“Yanzu nake kokarin yi masa bayani”
Likitan yayi murmushi.
“Kin manta kenan?”
“Aa na tuna yanzu da na ganka”
Ta fuskanci Ameer dake jiran abun da zata fada masa.
“Yace gobe za a kwance daurin da aka yi mata, a duba, idan yayi haka ake so, idan kuma be yi ba sai an sake wani”
Tana fadar idonta na cika da kwalla.
“Sarkin kuka daga magana sai hawaye, haka jiya kika min fa”
Likitan ya fada yana kallonta.
“Bana son tashin hankali, ba mu da yawa a dangi kusa, bana son na sake rasa kowa”
“Ba saki rasata ba, aiki ne kawai kuma ni ba cinye ta zan yi ba, I'm not zombie”
Ta yi murmushi tana share hawayen idonta.
“Ni ban ce ba”
“Da dai yafi”
Duk abun da ake Ameer be ce uffan ba, sai kallon tsohuwar dake cin ayarba hankali kwace yake kamar ba ita ake fadar za a sakewa aiki ba.
“Ita hankalinta a kwance ma yake naki ne a tashe”
Likitan ya fada yana kallon Humairah
“Toh abun da Allah ya kawo ba sai hakuri ba, gwagwarmaya wace kala ce ba mu gani ba?”
Ameer yayi murmushi yana kallonta, karfin halinta da imani ya burge shi.
“Allah ya kara lafiya”
Ya fada sannan yayi ma Fiyya alama da su tafi da ido, Fiyya ta yi musu sallama suka fice. Likitan ya juya ya kalli Ameer har sai da ya fice sannan ya maida dubansa gurin Humairah.
“Am ya sunanki ma?”
“Humairah..”
“Haka ashe na rike sunan”
Ta yi murmushi tare da sauke kai kasa, sai ya dauki file din da ya shigo dashi bayan ya gama duba Tsohuwar ya fice. Zaunawa Humairah ta yi tana fadin.
“Yau Mama bata zo da wuri ba, gashi ina son na shiga makaranta kar na yi latti”
“Ki zuba min abinci da aka kawo sai ki tafi, ai zata zo wata kila ta tsaya wanke tsumman da tafi da su jiya ne”
“Maybe”
Ta dauki plate din ta bude coolar jalof din shimkafa ce da aka yi mata ado da doya ta sha kayan kamshi da vegetables ga kuma mai har yayi yawa. Rabin plate ta zuba mata ta dora mata a saman gadon ta matsa mata da ruwa kusa.
“Ba zaki ci abincin ba?”
“Sai na dawo zan ci”
“Toh Allah ya kiyaye hanya, yau ba su bada kudin da suka saba fadawa ba”
“Yau da gobe ai sai Allah Hajiya, wata kila sun fara gajiya ne ko kuma sun manta”
“Ba dai gajiya ba, sai dai ko mantuwa amman dan dan abun da suke ba mu ai be taka kara ya karya ba a dukiyarsu. Ni ba dan ba a son kaddara ba ai da na ce kara da aka yi haka, dubi ki ga kullum sai an kawo abinci, ga kudin nan, kuma sun dauke duk wata hidima ta asibitin nan, gaskiya suna da kirki, ko da can ke ce da masifar ki kike ganin kamar ba shi da kirki, kullum fa sai ya zo, mamansa ma kullum tana hanya”
“Hmmm Hajiya, ke dai kin ganshi kawai amman da can ba haka yake ba, yanzu ne ya canja”
“Ke ma ai na san halinki fitina ta miki yawa”
Ta yi dariya ta nufi gefen gadon Hajiya ta dauki jakarta ta goya, sannan ta yi mata sallama ta fice, tana tafiya harabar asibitin ta ji an kira sunanta.
“Humairah”
Ta dan juyo kadan sai ta yi arba da Likitan dazun, murmushi.
“Doctor”
“Na'am fita zaki yi?”
“Eh makaranta zan je”
“Wace makaranta? Ina kike karatu”
Ya jera da ita suna tafiya.
“Sky King University”
“Ah makarantar manyan mutane kenan, wane course?”
“Microbiology”
“Wow, ke babba ce”
“Kune manya ai”
“Kika ce ba, muje na sauke ki”
“No akwai inda zan biya kamin na wuce”
“Karki damu duk zan iya sama direbanki, kin ga wata rana zan yi alfahari na ce na taba daukar Humairah yar Microbiology a motata, zan ce ta yi min alfama ta shiga motata”
Murmushi ta sake yi ta girgiza kai.
“Bana son zolaya, Likita za'ayi ma alfama?”
“Eh mana ke baki san babba ce ba?”
Bata son jan zancen da tsawo dan haka ta yi shiru bata sake cewa komai ba har suka isa gurin motae yar yayi mai matukar kyau, kana ganinta kasan sabuwar mota ce, sai da ya saka key sannan ta bude front seat ya shiga ta zauna.
AMEER POV.
A Area 2 ya sauke Fiyya gidan wata kawarta da zata yi birthday, sannan yayi driving kansa zuwa gida, tun a harabar gidan yake kallon bakuwar motar da ke fake a compound din. Domin ba ta yi kama da motocin gidansu ba, yanayin yadda akai parking din ma ya fahimtar da ba direbobin gidansu ba ne. Yana wasa da key hannunsa ya shiga falon, sai ya samu Mummy da Ummi zaune, Daddynsa yana kan dayar kujerar fuskarsa dauke da murmushi. Ummi na ganinsa ta mike tsaye kamar karamin ma'aikaci ya ga boss dinsa.
“Ameer ka dawo”
Daddy ya fada, sai ya nufi inda Daddy yake ya zauna yana yi ma Ummi kallon tsanaki, ta yi rama sosai farinta ya wuce na ainahin fatarta wani fari ne mai sheƙar da fata, fatan idonta ta yi fari kana kallonta ka san lafiya bata isheta ba.
“Baka gaishe da Mamanka ba, tun fitarku take nan tana jiranka”
Mummy ta fada tana murmushi, still be ce komai ba, sai kallonta kawai yake. Hakan ya saka Ummi jin wani iri sai ta ji kamar ta tsargu, domin ganin take komai ta yi ma Ameer a yanzu ba zata burge shi ba.
“Na zo ne kawai na ganka, Daddyka ya fada min abin da ya faru, ina addu'a Allah ya tsare gaba, kuma idan ka ba ni dama ina son ni ma naje na dubata for the sake of you”
Ta karasa maganar muryarta na rawa kamar mai tsoron abun da zai fito daga bakinsa. Ya dauke kai sannan ya mike tsaye.
“Lemme drop her home”
Fadar sai sauke ta a gida, abun mamaki ne a gurin Mummy da kuma Mahaifinsa Daddy ya san da be son ganinta ba zai sauketa gida ba, ba ma zai zauna a falon ba, sai dai Daddy be san manufarsa ta yin haka ba, hakan ya saka shi mikewa tsaye tare da kai hannu ya dafa kafadarsa.
“Karka fada mata magana marar dadi please”
Cikin wata siga mai kamar rada ya fada masa haka, Ameer ya girgiza kai.
“Ba abun da kake tunani ba ne”
Yana bashi amsa ya wuce yayi gaba, Ummi ta dauki jakarta zuciyarta na raya mata maybe Ameer zai yi amfani da wannan damar ne ya fada mata karta sake zuwa gidan duba shi. Mummy ta rakota har gurin motar ta tuko kanta, hakan ya saka Ameer barin jikin motarsa ya iso gurinta ya mika mata hannunsa.
“Key”
Ta ciro key a jakarta ta mika masa, ya nufi motar ya bude mata backseat, ta ji kamar ya karramata yayi mata alfarma a cikin daruruwan mutane.
“Hajiya na gode sai anjima”
“Toh Allah ya kiyaye hanya, ni ma zan shigo wani lokacin In Shaa Allah”
“Allah ya nufa”
Ummi ta fada sannan ta nufi motar ta shiga, Ameer ya rufe motar ya zagaya ya shiga mazaunin direba yayi ma motar key. Yana tukin Ummi na hawaye ko da ace ba a cikin dadin rai Ameer zai tukata ya kaita gida ba, ita abun farinciki ne a gurinta.
“Karki sake zuwa duba ni, idan kina son ganina ki min waya zan zo”
Ya fada yana tukin a hankali.
“Ba lallai idan na ce ina son ganinka ka zo ba”
“Saboda me?”
“Saboda ban kyautata maka ba, a lokacin da kake bukatata, na san kana kallona da wannan abun a kullum”
Yayi shiru na tsawon lokaci kamin ya sake fadar.
“Me yasa to kika yi?”
Hannu ta saka ta share hawayen idonta.
“A lokacin ina tsoron rasa rayuwar mahaifinka ne, saboda likitoci sun tabbatar min, idan ba a yi masa aikin ba, zai iya mutuwa, mun siyar da gidan gadonmu da kayan dakin Yayata Maryam mun hada duk be wadatarwa na bi yan'uwana da abokan mahaifina, kowa be taimaka min ba, ina cikin wannan halin ne Dr Hamid ya kawo min mafitar cewar akwai wacce take son siyen ciki, idona a rufe na aminta aka siyar, sai bayan da aka