Showing 210001 words to 213000 words out of 271643 words

Chapter 71 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel

you tell me why kike zubar da jini a idonki?”

Ta sake kai hannu ta taba jinin.

“Hakan na nufin faruwar wani abu, a gareni ko ga wani masoyina wani abu da zai min ciwo”

“Kamar ya?”

“Ya Maleek ni ina da banbanci da kai, ina ya ji abubuwa da yawa da zaka iya ji ba, zan iya ganin abubuwa da yawa da ba zaka iya gani ba, wata kila shiyasa nake ganin mace a duk lokacin da na shigo dakin nan alhalin kai mai dakin baka ganinta”

“Haka ne, wata kila shiyasa kike ganin wani mai kama da ni yana shiga dakinki yana taba ki, saboda ya bata ni a idonki, maybe fuska ya saka mai kalar tawa ko kuma”

“Ko kuma kai din ne...”

“Kin ce kina iya gane abubuwa me yasa baki gane waye shi ba?”

“Saboda ban taba rumgumarsa ba, sai na rumgume mutum ne nake iya ganewa”

“Toh ki gwada yau mana, kina tsafi ne Waira”

Ta girgiza kai a daidai lokacin da hawayen jinin ya daina zubo mata. Ba tare da tace masa komai ba ta juya.

“Dole ne sai kin tafi? Indai saboda ni ne ki zauna mana, ba zan sake yin wani abu da zai saka Ummi ta yi fushi da ke ba”

“Ba saboda kai zan tafi ba, zan tafi ne saboda lokacin tafiyar yayi, wata kila lokacin mutuwar ne yayi, daman na fada muku, wata rana za amin sako, ashe ba sako za a min ba ni zan tafi da kaina”

Ta bashi amsa ba tare da ta juyo ba sannan ta bude kofar dakin ta fita, ido hudu suka yi ita da Ameer, ya fito dakinta ita kuma ta fito dakin Maleek. Ya kalleta sama da kasa zuciyarsa na suya kamar yayi mata magana sai kuma ya dauke kai ya karaso inda take ya wuce ya sauka kasa. Ita kuma ta bishi da kallo sannan ta sake nufar kofar dakin Ummi ta murda kofar ta tura ta shiga. Daga bakin kofa ta tsaya tana kallon Ummi dake zaune gaban madubi tana hawaye, ta cikin madubin take kallon Ummi, Ummi ma take kallonta kamin ta kai hannu ta dauki tissue ta goge hawayen idonta ta juyo ta kalli Waira saboda jinin da ta hango a fuskarta da saman rigarta.

“Me ya same ki? Me ya faru? Ina kika samu jini?”

Waira ta kalli rigarta sannan ta kalli Ummi.

“Ummi me yasa kike kuka?”

“Fara fada min dalilin jinin da na gani a jikinki, kina tsorata ni a yanzu Waira”

“Hawayene, daga ni ne hakan na nufin faruwar wani abu a gareni ne marar dadi, tun a lokacin da aka sakamin tsafi ina jin irin wannan sako ne”

Idon Ummi ya sake cika da hawaye, ta kai hannu ta cire dankwalin dake kanta, Waira ta yi arba da gashin kanta da babu komai a kai sai kwalluwar kai.

“Lokaci yana ta tafiya Waira, shekaru na ta raguwa, ko da ciwo ko babu na sani zan iya mutuwa, amman ciwo na tunatarwa ce a gareni na mutuwa, na kusan cinye lokaci bukatu kuma sun ki biya, burika sun yi wuyar cika, kullum da kyakkyawa niyar nake aikata komai, amman daga karshe sai na karbi mummunan sakamako, kalli abun da na aikatawa Ameer daga karshe kaina na cutar, ke ma na rike ki da zuciya daya, gashi sanadinki kan yayana zai tarwatse, burin da nake da shi yana da wahala ya iya cika, kin saka min tsoronki a zuciya zaman dardar nake dake ba kamar da ba, zaman a gidan daga karshe ya haifar min matsalar da ba zan iya magancewa ba”

Waira ta zube kasan guiwoyinta.

“Mai baki tsoro ta shigo ta yi miki bankwana ne, wanda kike ganin kamar burinki ba zai cika ba idan tana kusa, zata tafi tafiyar da babu dawowa, lokaci yayi da zan koma cikin dangina na karbi hukuncin abun da ban aikata ba, da kuma wanda na aikata na guduwa na bar garinmu bayan dokokin da aka gindaya min, zan tafi Ummi hankalinki ba zai sake tashi saboda ni ba, yayanki ba za su sake fada saboda Waira ba, kuma ni ba zan taba cutar da ke ba, kin rike ni kamar yarki, kin nuna min soyayya da kauna, kin wayar da ni kin bude min ido daga duk wani jindadi na gode, sosai na kwadaitu da addininku kuma na so ace na yi rayuwa a cikinku, sai dai ban samu wannan lamanin ba, ba zan taba iya bari a cutar da ke ba, ina kaunarki Ummi, ke kika nuna min dadin uwa, a jikinka da siffarki da kalamanki, kulawarki da kaunarki ta sanar min da abun da ake nufi da uwa, ni ban taba sanin uwa ba, sai dai na zo gurinki, ban taba rabar jikin wata ta kaunace ba sai ke, kuma duk bayan wannan sai na saka miki da cutarwa? Sai na zama sanadin zubar hawayenki na zama silar damuwarki?”

Ta mike tsaye tana kuka, Ummi ma kukan take tana jin kamar tace mata kar ta tafi sai dai ta san tafiyarta zai fi zamanta a gidan alheri, idan ma ta roke ta ta zauna gidan Ameer ya aureta Maleek zai yi ta kallonta da ciwon zuciya ne Waira ta fice daga dakin ta nufo dakinta, ga mamakinta sai ta samu Ameer a tsaye yana jiran shigowarta. Tana kallonsa sai ya sauke idonsa kasa kamar mai tsoronta, murya can kasa kasa ya ce

“Na kasa natsuwa da jinin da na gani a idonki, ciwo kika ji? Ko kuma wani abun ne?”

Bata amsa masa ta taka daga bakin kofar da take tsaye ta isa inda yake tana kallonsa.

“Ameer ka cire ni a zuciyarka, ka manta da an taba halittar wata mace kamar ni a duniyarka, ka goge duk wani hoto rayuwata da idonka suka dauka, ka karya alkalamin dake zana maka shirme akaina, ka yage littafin layin kaddarar dabam tawa dabam, babu ta inda muka dace da juna, ko da ma mun dace aure ba zai taba wanzuwa a tsakaninmu ba”

“It's because of abun da Maleek ya fada miki?”

“Aa saboda ciwon da kake sakawa Ummi, da kuma gabar da kake yi da dan'uwanka saboda ni, sanadinka Ummi ta canja min, ta zubar da hawaye a kaina, kuma take tsorona, idan ka shiga rayuwar mutum lalata kake yi Ameer”

Kamar ba shi ba, haka ta risina kasa yana kallonta.

“Zan canja Waira zan zama duk yadda kike son na zama, karki duba yadda soyayya ta maida wani sakare a gabanki ki yi amfani da wannan ki cutar da ni, ban taba so ba sai kanki saboda haka ban san zafinsa da haukarsa sai a yanzu, ban san haka yake maida mutum ba sai a yanzu”

“Yanzu kana iya jin yadda Nimra ta ji?”

Ya mike tsaye.

“Sunanta kawai idan kika kira, ji nake kamar hukunta ni kike yi, karki duba abun da na yi dan Allah Waira, abun da ya wuce mu bar shi a wuce”

“Shiyasa zan bar maka gidan, ba zaka sake ganina ba, and it means forever”

“Ba sai kin tafi ba, zan iya bar miki gidan na yi nisa da inda zaki gan ni, amman please ki zauna a nan din, karki tafi saboda ni, idan baki so ne ba laifi ba ne, zaki iya auren Maleek, ki musulunta ta hannuna ko da wannan sai na karu”

Ya kauce daga gabanta ya fice daga dakin yana jin zuciyarsa kamar zata rabe biyu, be taba jinsa a irin wannan yanayi ba, sai a yau shi kam da ma zai mutu ya hutu, yaushe soyayyar Waira ta kama shi amman sai azabtuwa yake da abun da be yi zato ba, yaushe ya zurfafa a kaunar ko dan be taba yi ba sai a yanzu, ko kuma saboda yana tarayyar kaunarta da wani ne? Ya sauko kasa yana jinsa kamar ba shi ba, kasar ma takawa kawai yake yana tafiya amman ji yake kamar ba duniya yake ba. Yana isa gurin motarsa ya jingina jikin motar ya kife kansa ya rasa abun da ke masa dadi a duniyar nan. Ya bude motar ya shiga yayi mata key baya yaja motar ya tsaya saitin da zai iya hango window Waira ya faka motar ya bude ya fito ta jingina yana kallonta, kallon windows dinta ma dadi yake masa, a haka zai ji sanyi ko da kuwa be shiga ya ganta ba. He spends hours yana kallon gurin yana jin kamar ta leko ta ce masa magana. Ta inda be yi zato ba ya ganta tsaye a bakin kofar falon tana saukowa ta nufo inda yake, da sauri ya mike tsaye daidai yana kallonta zuciyarsa sai halbawa take, da ace wani ne ya fada masa cewar zai hadu da yarinya kamar Waira ya haukace a sonta ba zai yarda, ko da kuwa za a buga kasa a kafa masa haka.

“Akwai abun da kike so ne?”

Ya tambaya yana jin kamar yaje a gushe ya rumgume ta. Ta tsaya daidai shi ta daga kai ta kalleshi.

“Kai ka wayar min da kai akan addinin musulumci, ka fada min abubuwa da yawa da ban tambaya ba, ka sanar da abubuwan da ban sani ba, na fahimci addinin saboda kai kuma na ji ina kaunarsa duk a ta dalilinka, ina son na musulunta, musulunci kadai abun da zan tafi da shi, da zan zo ban zo da komai ba, dan haka ba zan dauki komai ba, zan tafi daga ni sai abun da na koya... Ya ake shiga musuluncin ina son na shiga, na yi rayuwa mai tsafta kamar ku, ka karu da abun da ka koyar, kuma ka cika burinka kamar yadda ka roko...”

Ya hade yawu da karfi, farinciki da kishiyarsa suka ziyarce a lokaci daya.
Daga kwance da Ummi take ta dago ta kalli Abiey daya shigo dakin sanye da tufafin bachi, abun ka da mace mai kula da miji sai ta yaye zanen da ta rufa da shi ta tashi zaune tana kallonsa har ya iso inda take ya zauna bakin gadon yana kallonta.

“Madam yau kuma a nan zaki kwana?”

Ta sauke kai kasa ba tare da tace masa komai ba.

“Tun da ciwon nan ya bayyana a garemu, sai duk kika canja, abubuwa da yawa wadanda ba halayyarki ba kika ara kika yafa, wadanda suke naki kuma kika zubar, lokacin da ya kamata ace kina cikin farinciki da jindadi, sai kika mayarda da su na bakinciki da damuwa, alhalin ni yanzu ban ga wani abun damuwa a tare da ke ba”

“Haka dai kake gani, amman har yanzu ban gama cika burina ba, balle na zaba zama cikin farinciki, ko kuma damuwa ta zabi rabuwa da ni”

“Toh me ya rage? Ina ce yanzu kina tare da Ameer, iyayen Deen sun san komai, bayan shi akwai wani abun da kika aikata kuma da kike jiran neman yafiyar wani?”

“Ranka ya dade yanzu ba yafiyar wani nake nema ba, hadin kan ƴaƴa nake da bukata, yadda za tafi na bar Ameer yana rashin jituwa da yan'uwansa ne damuwata, yadda kake nuna masa tsana da kiyayya ne matsala ta, ni na rike naka yayan da zuciya daya, na kaunace na nuna musu so, amman kai ka kasa nunawa Ameer nawa kwaya daya tal, har ya gama fahimtar baka sonshi, gashi duk wasu kalamai da zan yi amfani da su na sauya tunaninsa sun kare, kuzarina ya tafi, ina tausayin rayuwar Ameer idan bana raye”

Abiey ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta.

“Na taba furta cewar bana son Ameer? Kamin yanzu ban fada miki ki yi iya yadda zaki yi Ameer ya zauna a hannunki ba, ni kuma zan goya miki baya, amman kika zabi abun da kika zaba? Zaman a gidan nan na taba hana shi shiga wani bangare na gidan ko kuma na taba cewa ya fice min daga gida? Zahra ki rika sara kina duba bakin gatari, kar son Ameer ya rufe miki ki kasa ganin gaskiya a inda take marararta”

“Idan har son wani zai rufe min ido na kasa ganin komai, to sonka ne farkon abun da ya fara cutar da ni, kuma ya cutar da Ameer, a duk lokacin da zan yi maganar Ameer ko na nemi ganinsa ina ganin kiyayyar haka a idonka, ka sha canja mu'alama da ni saboda kawai na nuna ina son ganin ďana, ka kasa daina kiyayya da wanda ya manta da ya taba wanzuwa a duniya, ka kasa nuna min soyayyar da kake takamar kana yi min tun kurciya har tsufa, saboda ka kasa tirsasa zuciyarka ka fi karfinta ta cusa mata son ďana jinina”

Abiey ya sauke ajiyar zuciya.

“Laifina a yanzu saboda kawai na ce Maleek yana son Waira?”

Sai Ummi ta dube shi duba na tsanaki.

“Ka bata tambayar lafiyarsa? Ka taba cewa Ina Ameer? Me Ameer yake so miye baya so? Me dace mu yi akan Ameer?”

“Yanzu dai ki bar abun da ya wuce ya wuce, tashi muje mu kwanta, kuma likita ya min waya satin nan za ki kwanta asibiti for some months or weeks ya danganta da yadda jikinki ya karbi maganin, idan kin samu lafiya kamin lokacin da ake tsammanin zamu iya dawowa gida ma”

“Lokacin ziyartar asibiti ya wuce kenan, sai dai kwana”

“Hakan kuma ba yana nufin ba zaki warke ba, ko kuma ki dawo gida, kawai mu yi addu'a saukin ya zo a kusa babu cutar da bata da magani ai”

Ya sauko da kafafuwanta kasa ya rikata sai ta mike tsaye ya kwanta jikinta, shi kuma ya daga kansa sama saboda ya hana hawayensa zubowa, yana matukar tausayin matarsa da kaunarta fiye da tunanin duk wani mai tunanina. Da taimakonsa ta fito dakin ta sauko kasa yana rike da ita har suka isa bangarensa, ya kwantar da abar kaunarsa akan gadonsa ya lullube ta sannan ya shiga bandaki yayi alwala ya gabatar da shafa'i da wutiri yayi ma matarsa da yayansa addu'a sannan ya kwanta bayanta ya rumgume abarsa. Washe gari Abiey be bari Ummi ta fito daga bangarensa ba, shi ya shiga bangarenta ya tasa yaransa a gaba daga Maleek har Namra da Mahmood Waira ce kawai aka bari a daki, su kuma suka dunguma zuwa kitchen ko Hanne be yarda ta saka masa hannu a cikin a breakfast din da suke shiryawa ba, kawai so yake yau ya burge matarsa, rabon da ya shiga kitchen irin haka tare da yaransa ko Ummi tun yana da sauran kurciya, kamin ayukan da iyali su fara girma su sauya masa rayuwa.
Hadin girkin ya saka kowanensu nishadi, Namra ta saka wayarta tana musu hotuna da video, kamin ta saka su hawaye tunawa da ta yi da yar'uwarta, tana fadar ina ma ace Nimra tana raye, kusan kowa sai da yayi hawaye har Abiey.
Suna fara jera abinci a dinning Ummi ta iso bangaren, bata a cikin yanayi mai dadi amman hakan ba hana ta murmushi da farinciki ganin iyalanta a haka ba. Abiey da kansa ya ja mata kujera ta zauna. Yana zolayarta wai idan bata bashi rate na 100 ba za su samu matsala.

“Abiey to ai bakai kadai ka yi girkin ba”

“Then n OK da yayana na yi”

Ya amsa yana cire gilashin idonsa. Nimra ta koma gefen Ummi taja kujera ta zauna.

“Toh ni ina bangaren Ummi, saboda na saka hannu girkin yayi dadi”

Ummi ta kalleta tana murmushi.

“Aa daman ni mijina ya iya abinci, tun kamin a haife ku yake min girki”

Sai duk suka sa dariya jin Ummi ta shigarwa mijinta kai tsaye.




AMEER POV.

“Hakan ma abun farinciki ne a gurina, zan gabatar da maganar nan a gurin Daddy sai mu yi abun da ya kamata”

Ya juya ya bude motarsa ya shiga ya barta a gurin tsaye tana bin motarsa da kallo har ya fice.
Har ya isa gida da hannu daya yake driving dayan hannunsa na dafe a kirjinsa, gaba daya ya rasa abun da ke masa dadi ga zuciyarsa sai zafi take. Ya faka a daidai lokacin da motar Daddy ta faka harabar gidan, shi ya bude ya fito Daddy kuma direba ya bude masa ya fito, tsabar hankalinsa da tunaninaa ba a jikinsa suke ba sam be lura da Daddy ba sai kokarin shigewa ciki yake har sai Daddy ya kira sunansa.

“Ameer”

Sai ya juyo kamar a rude ya kalli saitin inda ake kiran sunan nasa. Ganin Daddy ya saka shi hanzarin isa gurin motar, wani abun da be saba ba sai ya bawa Daddy hannu su gaisa, kamar wanda ya tarardar wani abun kunyarsa ba Daddy ba. Kallon tsanaki Daddy yayi masa yana karantar damuwar dake tare da shi, hakan kuma be hana shi mika masa hannu su gaisa ba.

“Ameer me yake damunka? Yau kuma ni kake bawa hannu mu gaisa?”

Ameer ya kalli Daddy sai kuma ya sauke kansa kasa, be san ta inda zai fara fadawa Daddy damuwarsa ba bayan ya gujewa bukatarsa kuma ya kara masa da yin karya. Daddy ya kai hannu ya dafa shi.

“Ameer ďana ban taba ganinka a irin wannan yanayin ba, fada min mw ya faru? Wani abu ya same ka ne ko Ummi? Ko wani ya fada maka wata magana marar dadi ne? Waya jefaka a wannan yanayin? Tell ko miye zan magance maka shi”

Ameer ya hade yawu ya girgiza kai ya soma magana kamar zai yi kuka.

“Ba zaka iya ba Daddy, wani abu ne da kudi baya siya, kyau ilmin martaba ko isa basa siya, kima mutumci da daraja basa siya”

Daga saman kafardarsa Daddy ya gangaro zuwa kasa ya rika hannunsa.

“Zo mu shiga ciki”

Ameer ya jera tare da Daddy suka shiga cikin gidan, sai da suka isa a inda za su zauna sannan Daddy ya sake hannun Ameer ya zauna a kujerar da ya saba zama.

“Ina iya fahimtar halin da kake ciki Ameer, na san damuwarka na san farincikinka, sai dai wannan karon ka shiga a wata kalar damuwa da ta wuce misali, a yanayin yadda ka jera min abubuwan da na za su iya siyen damuwarka su kawo maka farinciki ba sai na fahimci so ne am I right?”

Ya daga kai ba tare da ya kalli Daddy ba.

“Ya sani yi maka karya Daddy, ya maida ni mahaukaci, ya jefa ni a halin da ban taba mafarkin shiga ba, sanin cewar kai ba mahaifina ba ne, sanin abun da Ummi ta yi, gorin da za ayi min da duk wani abun da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login