Showing 120001 words to 123000 words out of 271643 words
Chapter 41 - Wani Gari Book 1 Complete Hausa Novel
na gane gaskiya yake fada, Ummi wannan kalmar ta fi tsaya min a zuciya fiye da kokarin raba ni da shi da kuka yi”
Ummi ta kara jimke hannunta with shock.
“Yaushe ya fada miki haka?”
“Dazun, na kira shi da wayar Umar dake hannuna ya fada min haka, shi ne dalilin da ya saka na kasa numfashi....”
Ta lumshe ido daker ta bude kana ganin yadda take jan numfashin kasan tana cikin wahalar numfashi.
“Miyasa yayi miki haka toh?”
“Saboda ya dauki fansar Ya Maleek da kuma ni da yake ganin kamar hada kai aka yi da ni a cutar da shi”
Ummi ta hade yawu da tana jin bacin rai akan abun da Ameer ya aikata for the first time, miyasa zai fada mata hakan a lokacin da take cikin tashin hankalin rabuwa da shi? Kuma daman can ba sonta yake tsakani da Allah ba da akwai aure a tsakaninsu haka zai saka mata ya ki aureta ya bayan yayi breaking heart dinta?
“Ummi ina kaunarki sosai”
Ta fada tana kara jimke hannun Ummi tare da dagowa ta sai Ummi ta kai jikinta kadan ta rumgumeta, suna haka aka turo kofar dakin Abiey ya shigo fuskarsa dauke da damuwa sosai.
“Tun da muka kawo yarinyar asibiti kin ki barta ta huta, a gabanki dazun likitan ya fada mana cewar hutu take bukata, na san kuma idan kina dakin nan ke ba zaki huta ba ita ma ba zata huta ba”
Ummi ta daga jikin Nimra ta mike tsaye gaba daya tana kallonta da hawaye a idonta.
“Mutuwa kadai ta isa ta shiga tsakanin uwa da ya Abiey, idan bana kusa da ita damuwata karuwa take, kuma zamana a kusa da ita ita kuma kara mata damuwa yake”
“Dan Allah ki kwantar da hankalinki, ciwo ne fa kawai zata ji sauki ta tashi kamar ba ayi ba, yanzu da wanne zan ji tashin ha kalinki ko ciwonta?”
Ummi ta sauke kai kasa ba tare da ta sake cewa Abiey komai ba ta saki hannun Nimra ta juya ta fice daga dakin. Abiey ya zauna a kujerar data tashi yana kallon Nimra dake kallonsa oxygen a hancinta da bakinta. Ya dade yana kallonta sannan ya mike tsaye ba tare da yace da ita komai ya nufi kofa sai ta cire Oxygen din dake bakinta ta ce.
“Abiey ka yafe min dan Allah ka yi hakuri”
Ya juyo da sauri ya dawo ya zauna ya kai hannu ya shafa goshinta.
“Da ban yafe miki ba, ba zan so asibitin nan kuma har na shigo cikin nan ba, kin yi kuskure a matsayinki na ya kuma yar adam, ni kuma na yafe miki a matsayina na mahaifinki, Allah ya baki lafiya kuma yayi miki albarka”
“Ameen Abiey”
Ta fada tana jin sanyi a ranta.
“Abiey da gaske Ummi ita ta haifi Ameer”
Abiey yayi jimm kamar ba zai ce komai ba, be mamakin sanin da ta yi ba wata kila Ummi ce ta fada mata haka saboda ta warware mata tsakanin tsare da abawa, na haramcin aurenta da Ameer.
“Nimra kina a yanayin da be kamata mu yi doguwar magana da ke ba, hutu kike bukata a yanzu, idan kin samu lafiya sai mu yi magana kin ji”
“Abiey dan Allah ka fada min, ina son na sani, gaskiya ne ko?”
“Gaskiya ne Zahra ita ta haifi Ameer kuma jininta ne”
“Amman Abiey miyasa bata tare da shi? Mutanen da yake nunawa a matsayin iyayensa su waye su?”
“Idan kika samu lafiya zan fada miki komai da kaina, fata dai yanzu ki samu lafiya karki zurfafa tunani zai kara haifar miki da damuwa i love you you should know that”
Ya sumbanci goshinta hawayensa na diga a saman kanta, sai ta yi murmushi ta lumshe ido tana jin son mahaifin nata a ranta. Bata bude idon ba har ya fice daga dakin, yana tafe yana tunanin Ummi a ransa, tausayinta ya cika masa zuciya fiye da kullum, shi da yake a tsakanin rayuwar yarsa da rasata yana jin kamar ba zai iya jurewa idan ya rasa ta, saboda mugun son yayansa da yake da kuma shakuwa da yayi da su, balle kuma Ummi da ta rayu a tsaye shekara da shekaru babu danta a kusa da ita, alhalin yana raye a yanzu kam ya tabbatar ciwon nan yana tare da ita, ta wannan babin kan ya jinjina mata matuka. Ya isa gurin da su Ummi da Dr Zajnab, Yesmin da Juwairiyyya, Mahmood da Maleek suke zaune har da Namra. Ummi na ganinsa ta mike tsaye sai yayi mata alama da ta zauna.
“Matukar kika ce zaki tare a dakin can to mota zan saka ki mu tafi gida yanzu nan, domin na ga alamar ba zaki barta ta samu hutu ba”
Ummi ta koma ta zauna suna kallonta.
“Ba a barin marar lafiya shi kadai ai”
“Toh ga Dr nan sai ta tafi gurinta ta zauna, ke kuma sai ki tashi mu tafi gida saboda babu kowa a cikin gidan an kwashe duk kun zo nan kun tare, kamar ni ne ba ni da lafiya”
Duk sai da suka yi murmushi da ba su shirya masa ba har Ummi dake cikin damuwa.
“Abiey idan kai ne baka da lafiya ai har masu gadin gidan sai sun tare a nan”
Maleek ya fada yana daga zaune a dayan carpet din da aka shimfida. Abiey yayi murmushi ya ce.
“Balle ma ba zan yi ba, sai dai Umminku”
“Ummin ma muna sonta Abiey”
Namra ta fada, sai duk suka saka dariya kamar babu damuwa a ransu. Sun dan taba hira sannan ya wuce tare da Maleek Juwairiyyya, aka bar Namra daman tace ba zata tafi ba, sai Yesmin dake lake da Mamarta wato tsohuwar likita Dr Zainab inda suka tare a dakin Nimra, harabar ta zama daga Mahmood sai Ummi da Abbie ya hana ta shiga ciki da Namra wacce ganin halin da yar'uwar haihuwarta take ciki yake daga mata hankali.
Abiey na gaba zaune Maleek na tuka motar Juwairiyyya na baya tana taba wayarta, titi kawai Abiey yake kallo amman hankalinsa yana wani gurin har suka isa gida. Masu gadin suka bude musu gate, kamin Maleek yaja motar su shiga ciki Police din da tarbi Humaira ya iso gurin motar Maleek na ganin hakan ya saukewa Abiey gilashinsa domin ta side dinsa ya tsaya.
“Ranka ya dade, dazun na so na baku wayar da yarinyar nan ta bari da wasika amman ban samu dama ba saboda kun fita hankali a tashe”
“Wace yarinya?”
Abiey ya tambaya domin shi be san abun da ke faruwa ba ma.
“Yarinyar da ta so dazun akan cewar ita kawar Nimra ce tana son ta ganta wai wayar Nimra ma tana hannunta, toh na zo na kira wayarka a tambayi Nimra ko ta san da zuwanta ko kuma akwai wanda ya santa a gidan, gudun kar mu barta ta shiga wani abu ya faru bayan dokar da ka saka mana cewar kar mu sake barin Nimra ta fita, toh fitowar da aka yi da ita cikin rashin lafiya sai yarinyar ta saki wayar da takardar hannunta ta gudu, mun bita sai dai ba mu samu nasarar kamata ba saboda ta shiga wata motar kuma mai tukin yaja da gudu sun tafi, sai dai muna son fadada bincike idan ka ba mu dama”
Abiey ya mika hannu ya karbi wayar da takardar with curious face. Maleek ma da mamakin guduwar ya ja motar suka shiga compound din gidan, Juwairiyyya ce ta fara fita, Abiey ya warwar takardar ya fara karantawa bayan ya gama duba wayar da ya tabbatar ta yarsa ce.
‘I'm sorry Nimra, ban dauka abun zai kai ga haka ba, ina tunanin kiran wayata da kika ba zai gamsar da ke ba kamar ganin wannan sakon nawa a rubuce, na rubuto ne saboda na kara tabbatar miki kuma na jadda miki cewar ni ban tana jin kaunarki ko digo daya a zuciyata ba, na san zaki min kallon maci amana, amman yayanki ya fara ai ni kawai fansa na dauka, kuma ki gode Allah ban taba mu'amala dake ba, wata kila da sai abun yafi taba ki, i wish you all the best, i kila da wanda zai nuna miki so kuma wanda zaki fada sonsa a nan gaba
Ameer’
Sunansa ne daga karshe tare da sa hannunsa, Abiey na gama karantawa ya mikewa Maleek yana jin wata sabuwar tsanar Ameer a ransa. Maleek ya karba ya karanta.
“Me kake tunani idan ta karanta wannan sakon? Yaron nan so yake kawai ya kasheta”
“Ta sani ai, Ummi ta fada mana haka dazun kamin ka zo, kuma tace shi yayi silar da aka kaita asibiti, daman na fada mata ai bata yarda ba ne, amman ni na san waye Ameer, ba zai taba sonta ba ko dan tana kanwata, sai dai yayi amfani da ita ya cin ma wata manufa”
Abiey yaja dogon tsaki ya bude motar ya fita ya nufi sashensa. Maleek ya juya gafensa da zimmar bude gambun motar ya hango Waira dake tsaye nesa da motar rike da dan zomonta tana kallon motarsu, jiran take waye zai fito mazaunin direban ko Ummi ce, domin ita kadai take son gani. Samun kansa yayi da tsayawa kallonsa kasancewar bakin gilashi ne na waje baya iya ganin na ciki, sai dai na ciki ya ga na waje, idonta yayi sumtum kamar an dafa shi saboda kukan da ta ci na tafiyar Shuraim. Ganin kamar ba za a fito ya saka ta laraso gurin motar ta saka hannunta daya ta dafa zata leka ciki sai ya sauke gilashin motar, ta kalleshi ya kalleta ido cikin ido, ba tare da tace komai ba ta juya.
“Waira”
Ya kira sunanta da tattausan lafazi, ta juyo tana kallonsa sai ta fashe da kuka.
“Toh me na ce miki kuma na kuka?”
“Ka ce Waira”
Ta fada tana kuka hawaye na mata zuba kamar bata san zafinsu ba. Hannu ya mika ya ciro tissue a motar Abiey ya mika mata bata tare da ya ce komai ba, sai ta saka hannu ta karba ta share hawayen, sannan ta juya ta koma gurin da ake mata lessons dinta. Sai a sannan ya bude mota ya sauko ya shiga cikin gidan. A kujerarta ta zauna tana share hawayenta har lokacin. Dattijon dake mata darasin ya ce.
“Kin tafi ki gani ko Ummi ce?”
“Ta daga kai”
“Ummi tana can asibiti gurin Nimra”
“Me ya same ta?”
Ta tambaya cike da son sani, domin ita dai tun da Maleek yayi mata tsawa dazun saboda tafiyar su Shuraim sai ta boya a kitchen tana kuka duk abun da ya faru bata sani ba.
“Saboda rabata da aka yi da wanda take so”
“Amman miyasa Ummi ba zata bari ta aureshi ba”
“Baki san Ummi ta haife shi?”
“Na sani”
“Na gani ai”
“Ta ina?”
Sai ta yi shiru bata son ta fada masa yadda aka yi ta sani saboda kar ya mata fahimta dabam, domin ta lura nan ba kamar garinsu ba ne da suke girmama tsafi. Dariya yayi ya matso kusa da ita
“A addininsu idan mace da namiji suka sha Nono daya ba a aure, ko da kuwa uwar su daban daban”
“Amman miyasa addininsu yake da zafi? Kai ma ai addininsu kake yi”
Ta tambaya domin ita dai bata ga illar haka ba, saboda sun sha nono daya ace ba za ayi musu aure ba bayan ba uwa daya ta haife su ba. Ya daga mata kai yana murmushi.
“Addininmu daya mana, amman ina fatar ba zaki jefar da na ki addinin ba ki dauki na mu, kuma ki daina kuka har idonki ya kumbura haka”
Kallonsa take kamar mai tunani ko mai son gano wani abu. Ganin hakan ya saka shiikewa tsaye ya isa gurin blackboard din suke rubuta ya cigaba da yi mata darasi.
AMEER POV.
Sai da suka yi nisa sosai sannan ya rage gudun da yake ya kalli Humaira dake gafen motar tana kukan da babu hawaye.
“Sai ki fada min gudun me nake wai?”
“Toh ba kamani za su yi ba, yarinyar nan na ganta a fito da ita da alama ma mutuwa ta yi, ai na san ina tsayawa za su kamani kashina ya bushe, Ameer ka ci amanar yarinyar nan kuma nima ka ci amanata, yanzu sun rike fuskata ko a wani gurin suka gan ni za su gane ni”
“Amman ke kin raina wayon mutane saboda wannan kika saka na taka mota ina da gudu kamar mun yi sata? Fitar min a mota Malama”
“Wallahi ba zan fita ba sai ka kai ni gidanmu, kuma ba zan yafe maka halin da ka jefa ni ba, kai dai haduwa da kai masifa ne babu alheri sam”
“Kuma rabuwa da ni bala'i ba, ina wayar?”
“Tana can na saki mana har da takardar na bar su a can, ni ba ta raina nake ba, Kuma Wallahi yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali kila ma ta mutu, ni ba ruwana da alakarku amman yanzu ka dauke ni ka saka ni cikin masifa, gashi iyayena talakawa babu ruwansu ka ja min matsala”
“Me aka ce ya samu yarinyar?”
“Ni ina zan sani wai, kaddara ce kawai ta hada ni da kai, gashi ka zame min kaya, Allah kadai ya san iya abun da ka yi ma wannan yarinyar ita ba, bakin mugu”
Ya taka turki yayo slow down ya faka ya fita ya zafaya ya bude gambun motarta.
“Fita, ba zaki zauna min a mota kuma ki zage ni ba”
“Ba zan fita nan ba Wallahi ban san abun da zai sake samuna ba, Ameer ka sakawa kanka imani ta tausayi haba, sai ka rika treating mutane kamar su basa da zuciya da jini kamar kai”
Wannan karon hawaye ne ya zubo mata.
“Ina kallo kana rubutawa mata cewar fake love kake mata fa, haka ake yi kwanan baya a gabana ka saka iyayenta kuka kuma ka saka tana zuwa nan kana taba ta ashe ma kai ba da gaske kake sonta ba, ina ta mata hannunka mai sanda ta gane amman bata gane ba”
“Gaskiya na fada mata ai, miye laifina a haka?”
“Bayan ka gama cutar da ita, ni Wallahi da ace mahaifiyarka ce sai na maka dan banzan duka, kuma sai na kai kararka gurin police na nuna min wukar da ka yi”
“Ko yanzu ai zaki iya marar kunyar yarinya”
“Marar kunyar yara dai”
Ta rama tare da kai hannu ta jango gambun motar ta rufe ta bar shi nan tsaye. Shi har mamakin yadda ta iya rashin kunya kuma take iya tsayawa ta fada masa magana son ranta yake. Zagaya ya shiga side din direba yaja motar har suka isa inda yake kyautata zaton unguwarsu ce domin ya ganta a gurin sau biyu kuma ta jadada masa a lokacin da ta kai shi cikin gidansu. Ya faka be ce mata komai ba ita ma bata ce masa ba. Bude motar ta yi ta fita sai da ta yi nisa sannan ta juyo cikin daga murya ta ce.
“Allah ya isa, mugun kawai, bakin mugu”
Gudun kar ya biyota da mota ya saka ta cire talkamimta ta ranta a ana kare. Ta gishin gaban motar yake kallonta har ta shige kwanar sannan ya ja motar ya juya kanta yana fadin.
“Wannan ta fi tunanina, idonta a tsaye suke bata tsoron kowa”
Yaja motarsa ya fice daga unguwar, sai dai har ya isa gida tunanin halin da Nimra take ciki yake, babu abun da yayi masa dadi kamar rashin tarar da mahaifinsa a gidan da yayi saboda ya san zai masa maganar wukar da aka ce ya dauka dazun. Tunani kala kala ne a ransa na yadda zai yi ya san halin da Nimra take ciki, sai yayi kamar ya kira number data kira shi da ita sai ya ji ba zai iya ba domin ba san wayar a hannun waye take ba. Cam dabara ta fado masa ya kira abokinsa Abdull, Abdull na dauka ya gabatar masa da bukatar ta son sanin inda Nimra take.
“Ni ban ma san abun da ke faruwa ba ai”
“Na dauka ko Maleek din ne yake dubata ai”
“I don't think so kasan Maleek baya duba mata ai, ko da kuwa yan gidansu ne”
“Dan Allah bincika min lafiyarta da inda aka kwantar da ita yanzu please”
“Hope dai ba wani abun zaka yi ba”
“Wai Abdull kun mai da dan ta'addane ko minene?”
Abdull yayi dariya ya kashe wayar. Ameer ya jefar da wayar saman gadonsa ya cire rigarsa ya wandon ba tare da tunanin ko gudun kar wani ya shigo dakin nasa ba ya nufi bandakin haihuwar uwarshi ya shiga ya sakarwa kansa shower ya rufe ido ya bude hannayensa ruwan na tsasa shi. Sai da ya ji ya gamsu da hakan sannan yayi wanka ya fito ya dauki tawul a dress room ya daura. In less then 20min ya shirya cikin korean trouser da farar T-shirt ya saka snipers masu kyau da tsada sannan ya nufi wayarsa ya dauka ya duba sakon da Abdull ya turo masa na asibitin da aka kwantar da Nimra.
“Good My Guy”
Ya nufi inda keys dinsa suke ya dauki na wata motar dabam ya fito dakin. Da sassafa ya saukk Stairs Mummy ta kalleshi ta ce.
“Daddy ya dade yana jiranka, wani uzurin ne ya taso masa shiyasa ya tafi, da ka jira ya dawo kamin ka fita”
Kallonta kawai yayi ya dauke kai ya fice kamar ba da shi take magana. Yana isa gurin motar da key ta ke hannunsa ya bude ya shiga, masu tsaron gidan suka bude masa gate ya fita ya fara shimfida gudu a titi kamar shi ma na ubansa ne.
A lokacin da ya isa asbitin sai ya samu guri ya faka yana ta kalle kalle, can kuma ya fito yana tunanin ta ina zai fara, domin sunan asibitin kawai Abdull ya turo masa amman be fada masa inda take ba, sai dai tunaninshi na ba shi ba zata wuce Emergency ba, sai dai idan ya shiga ya gane dakin yayi me? Bayan ya fada mata gaskiya kuma abun kunya Maleek ya ganshi ya zo gurin ma, wata zuciyar ta katsi hanzarinsa. Sai kawai ya fasa yin abun da zai yi a asibitin ya juya da zimmar tafiya sai ya ji an kira shi da wata bakuwar murya.
“Ameer”
Ya juyo sai yayi arba da Ummi dake rike da coolar Mahmood na gefenta rike da key mota, da alama su ma kusa da inda ya aje motarsa suka aje ta su ko kuma sun