Showing 33001 words to 36000 words out of 212491 words
sai zare ido take tana kallon gwaggon,
Gwaggo ta mik'e tana k'are mata kallo tace"yaushe kika shigo gidan? Kuma lafiya kike yin bacci haka? Saukko da k'afafunta tayi k'asa tace "tun d'azun na shigo"tasa hannu tana goge idanunta,
"amman ba ke kika zo da abincin da na gani a kofan kitchen ba" tace "ni nazo da shi,hajiya ta bani" Gwaggo tace to "bazaki ci bane kika aje kika zo kina bacci,kuma ma nasan ko salla baki yi ba" ita dai fatuu sai faman zare ido take hakan yasa gwaggo tace"wai mike damunki ne kike ta faman zaro idanu,da gani baki da gaskia,halan wata rigimar kika jawo,don nasan wannan baccin dama ba na Allah bane,da gani na rashin gaskiya ne" gaban fatuu ya fadi rass cike da tsoro take kallon gwaggon, tasan in har gwaggon taji abunda ta aikata kashinta ya bushe balle kuma taji mutumin dan gidan hajia ne tabb......,tsawa taji gwaggo ta daka mata "ba dake nike bane fatuu,mi ya faru ki ka zo kika kwanta haka? A daburce tace "da..dama kare ne ya biyo ni" sam bata san ta ambaci karen ba,
Gwaggo ta harareta tace"kece ke tsoron wani kare,sau nawa kike zuwa kina tono karen,ina kwanan nan kika je kika kinkimo d'an karya ta biyo ki har kofar gida,shine zaki wani ce man kare ne ya biyo ki...." da sauri ta katse gwaggon ganin zata gano k'arya take tace "ai ba irin shi bane fa,wannan fa irin mai gashi buzu buzu ne mai kaman zaki" ta kai maganar tana ta zare idanu tana hadiyar yawu,
gwaggon tace "to ke miya had'a ki da irin wannan karen, ina ki ka ganshi da zai biyo ki? tace "ina fitowa daga gidan hajia wani mutumi yazo zai wuce dashi shine yaji kamshin abincin hannuna yayo kaina shine na rugo" gwaggo ta girgiza kai don ta yarda da abunda fatun ta fad'a,tace "Allah ya kyauta to" da sauri fatuu tace "Amin,ganin ta yarda da k'aryar da ta gandara,
Gwaggo ta juya tana fadin "ki fito kici abincin,kiyi sallah sai kiyi baccin da kyau..."daga haka ta fice,fatuu ta dafe kirjinta alamar tasha,ta mik'e tabi bayan Gwaggon.
Amadu na gab da fita hannunshi rik'e da plate din daya d'ibi abinci yaji gwaggo ta fito daga dakin fatuu tana magana,ya juya yana tambayarta fatun na ciki? Gwaggo ta ta6e baki tace "tana nan,wai kare ne ya biyo ta shine ta tsorata,harda su baccin dole" dariya Amadu yayi yace "Ashe akwae karen da zai iya firgita ta haka"ya girgixa kai daga haka ya fice.
Washegari Safiyar Lahadi,Fatuu na zaune a ajinsu na islamiyya,tana ta zuba ido taga zuwan Haulat don dama tana riganta zuwa saboda gidansu Fatun yafi kusa da Islamiyyar inta biya ma haulat d'in ta koma baya sosae,sai dai ko in haulat din ta fito da wuri su hade sai in an tashi ne suke tafia tare,
Har aka kusa tashi shiru haulat bata shigo ba,hakan yasa fatuu ta fara damuwa a ranta kuwa tunani ta shiga yi tana fadin"To lafia haulat bata zo ba??,sai kace ba fushi fatun take da ita ba,duk tabi ta damu,har aka tashi islamiyyar Haulat bata zo ba,hakan yasa fatuu ta yanke shawarar zuwa gidansu ta gani ko lafia,
Tafe ta ke ita kadai a hanya don sam bata da k'awar da take tare da ita inba haulat ba, duk wadda ta fara k'awance da ita ba'a daukan lokaci ake rabuwa ta tsiya tsiya,
da fatuu taga mota ta taho sai ta rufe fuskarta wai don kar ace mutumin nan ne na gidan hajia,dama ko da safe da zata zo islamiyyar cikin dar dar ta fito daga gida,karshe ma da gudu ta shige lungun jikin gidan hajiyan duk don kada Haisam ya fito su yi kacibus,a ranta ta ke cewa"Yanzu shikenan sai dai in daina zuwa gidan Hajiar...."ta girgixa kai a fili tace"kam aikam bazan daina zuwa ba tunda ma naga hajiyan bata sani ba ai" "to kuma in ku ka had'e wata rana yace ma hajiyar kece ki ka fasa masa gilashin mota fa?? wani 6angare na zuciyarta yace, sosae gabanta ya fad'i ta kasa cewa komae,
Daidai lokacin da ta karya kwanar da zata hau layin gidansu a lokacin kuma Gaye da Abokinshi suma suka shigo kwanar,kai da kagansu sai dai kace Allah ya shirya,tun daga kan askin kansu har zuwa shigar da suka yi,tsayawa yayi yana yin arba da Fatuu,ya rik'e baki da hannunshi guda yace "Kee! Wai har yanzu kina yawo a gari ba'a damk'e ki ba?
Wani irin kallo Fatuu tayi mashi tace "A damk'e ni akaini ina? Gaye yace" inda ya cancanta akai ki wato gidan yarii...." Idanu waje Fatuu tace "kaji man gaye da Muguwar fata,yo minayi za'a kaini gidan yari??? Wata yar iskar dariya yayi "Oh baki ma san mi kika yi ba ko,to glass din mota da kika fasa ma wannan mutumin rannan.."sakin baki fatuu tayi tana kallonshi cike da mamakin yadda akai yasan hakan,ya ci gaba
"nasan komae yarinya ki ke wani kallo na,don akan ido na kika jefi motar,Oh ke kin d'auka kin jefi banza ko" ya k'ara shek'ewa da dariya "to billahillazi baki ci bulus ba,ruwa kika 6allowa kanki,don kud'in wannan glass din ko wanda ku ka fito ciki d'aya kika fasa mawa na rantse da sarkin da yake busan numfashi bazai kyale ki ba,yo kin kuwa san nawa glass d'in nan yake?
Fatuu dake tsaye kaman gunki zufa har ta fara tsatstsafo mata ta girgiza masa kai alamar a'a,gabanta sai fad'uwa yake,Yace "to wannan gilashin yayi naira miliyan d'aya,don ita kanta motar zata yi miliyan 10..." Fatuu ta zaro idanu waje gaba d'aya,sai Maimaita million d'ayan take a cikin ranta,a razane tace "Nawa ne Miliyan d'aya? Gaye da ke kallonta,da mamaki yace "yo ke dama hakanan kike zuwa makaranta kwalwar kifi ce dake,miliyan d'ayan ce baki sani ba? Da sauri tace"nasani, kawae yawan kudin ne a zahiri ban sani ba don ban ta6a ganinsu ba" Gaye ya gyara tsayuwa yace "to kinsan dubu d'ari?" "dubu d'ari..." ta maimaita tana dan tunani,can tace"Eh nasani,Baffa na ya ta6a saida shanuwa dubu dari da talatin kuma har kud'in ma na rike a hannuwana,daya hannu na rike dubu d'arin,dayan kuma dubu talatin d'in" da sauri yace"Yauwa toh,ita dubu d'arin irinta sau goma sune miliyan daya,kudin gilashin kenan,ai mu ma barshi a kudin shanuwar sau goma kawae..." Cikin tsananin tashin hankali Fatuu ta katse shi, "kace kuma dubu d'ari sau goma yanzu kuma kace duka kudin shanuwar...." Gaye ya katse ta"Oh kina nufin baza'a biya kudin gyara ba kenan,ai dole abashi harda na wanda zai yi aikin sa glass din ko Aljana" Idanu waje fatuu ke kallon gaye tama kasa yin kwakkwaran motsi ga zuciyarta dake bugawa ba k'akkautawa lokaci guda taji fitsari na niyyar zubo mata,kana kallonta zaka fahimci tsananin tashin hankalin da take ciki ba kad'an bane, zuciyarta kuwa tana bugawa tana maimata mata "kudin shanu gomaaa!!!"
Kamar Gaye yasan abunda take fad'a a zuciyanta yace "kin dai san bazan maki karya ba,don ba inda bama fad'awa a Nigeria,har legas dai tasan da zamana,ba kalar motar da bansan kud'inta ba,ke har kudin jirgi na sani balle wata mota k'aramar Alhaki.
Abokin gaye da tunda suka tsaya bai tanka ba kunnansa d'aya mak'ale da earpiece yana sauraron waka yana dan jujjuya kai,yasa hannu ya cire earpiece din yace"Baabah wai yane? mi tayi ne naji sama sama kana ta mata bayani harda uban lissafi?" Gaye yace "ruwa ta 6allo ma kanta baabah....,nan ya bashi labarin abunda fatun ta aikata,
yace "na gidan da muka wuto yanzu ka ke tambayata gidan waye,nace ma gidan Uwar Sanata ne kuma Matar tsohon Ministan tsaro? Abokin ya gyad'a kai alamar"Ehh,gaye yace"to mutumin gidan ne ta yi ma wannan aika aikar,don ni farko ma bansan d'an gidan bane ina dai d'an ganinshi kwanan nan yana wucewa a Motoci kala kala,har wani gangamemen Bike yake hawa,ina jin wannan bike din yayi million goma shima ko ma fi, sai shekaranjiya tsoho yaja ni zuwa sallar juma'a a Masallacin gidan,na ganshi tare da Hajiyar sun zo suma,to nan nagane dan gidan ne ashe"
Ya cigaba"Kasan masu kudin nan da shegen wayo,in suka gina tangamemen gida sai suyi dan Masallaci wai Allah ga naka,don kar a masu surutun basuyi ba,duk da dai su nasu babba ne" yana maganar yana watsa hannuwa sai kace mai yin debate,
Abokin fuskarshi da mamaki yana jinjina kai yace "kai kace master ce ta rashin ji" Gaye yace"ehh mana,wannan da kake gani furofesa ce ba master ba,don inta 6allo wani aikin yasin ko ni jinjina mata nike,dubi dai abunda ta aikata yanzu ni yaushe zan fara haka,ban aje ba,ban ba wani ajiya ba,Iyaye kuwa sai dai ace lahaula saboda talauci" yana maganar yana wani janta,
Abokin ya kwashe da daria yace kama aikatan ai kasan inda za'ai da kai,billahillaxi gidan yari straight inbaka biya ba,aje aita cin gabza.."Gaye ya tuntsire da dariya yana rik'e wando,
Yace"Allah yai man tsari da cin gabza baabah,shiyasa nike taka tsantsan,nadai je cell inyi kwanaki in fito don wannan yama zama gida,don ina daraja tuwon gyatuma ta,baka sanin dadin shi sai an had'aka da gabza yasinn..." gaba d'aya suka tuntsire da wata yar iskar dariya,ita dai Fatuu sai kallon su take tamkar yau ta fara ganinsu,zufa kuwa tuni ta lullu6e fuskarta,sai had'iyar miyau mai d'aci take.
Abokin gaye ya kalleta cikin nuna tausayi yace"Wayyo baiwar Allah na tausayi maki wllh,yanzu zaki bar tuwon gyatumarki ki koma cin gabza,duk wannan hasken fatar naki da kyawun fuskar ki sai ya disashe qur'an,in kuma kina da gashi to duk kwarkwata sai ta cinye shi,sai dai ko in kuna da kud'i sai ku biya shi abunshi kawae...."
Gaye ya katse shi da sauri "yo ina suka ga wani kud'i duk kanwar ja ce yasin,itafa kakarta ke ruk'onta kuma in fada maka kakar attendar ce a asibiti irin masu share share da goge gogen nan,ina zata ga miliyan d'aya ai yasin ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba,ko kwatan miliyan bata da"
Abokin yace "Kace dai dole sai anje an had'e da gabzar dai...." da sauri Gaye yace "Comfat,don a ranar sai da ya tambayeni nayi masa kwatancen gidansu,shiyasa nayi mamaki dana ganta har yau ba'ai ramm da ita ba, amman nasan kilan sunje basu samu kowa a gidan ba,kuma kaga jiya da yau ba aiki,amman na tabbatar gobe Monday dole azo a damk'e ta",
Ya juya kan Fatuu yace "To Aljana,sai ayafi juna,sai Allah kuma ya k'addara za'a sake ganawa,don can d'in ba sauki, wasu ma wuya ke kashe su, nidai na yafe maki" daga haka ya juya kan abokin nashi yana fad'in "hayya,Baabah mu ware ko.." suka yi gaba abunsu suna wata yar iskar tafia.
Kasa motsawa Fatuu tayi daga inda take don k'afafunta ba k'aramin nauyi sukai mata ba,Kalaman gaye na k'arshe sun matuk'ar razana ta"Ashe mutumin har yasan gidansu...! Shine abunda ya kara tada mata hankali,kallonsu gaye tai tayi har suka 6ace ma ganinta, irin su Gaye sai su kashe mutum,don halin da Fatuu take ciki tsaff zuciyarta zata iya bugawa don tunda take bata ta6a janyo rigima irin wannan ba,iya ta 6arar ma yara abu gwaggo ta biya ko ta bugi mutum har ta raunata shi gwaggon ta biya kudin zuwa chemist ta tsaya,yau gashi ta janyo rigimar da tabbas tafi karfin gwaggon,duk'awa tayi a wurin don kafafunta rawa kawae suke,ga kwakwalwarta sai tariyo mata da maganganun gaye take,bugun zuciyarta na k'ara tsananta ga zufa da ta wanke mata fuska har wuyan Hijab dinta ya fara jik'ewa,da za'a auna jinin Fatuu a lokacin tabbas daba k'aramin hawa yayi ba.
Tsawon mintuna Fatuu na duk'e a wurin kafin tayi k'arfin halin mik'ewa ta fara tafiya a hankali,da kyar ta ke taka k'afafunta da sukai mata wani irin nauyi,a ranta kuwa ba abunda take Maimatawa fa ce "Kud'in Shanu Gomaaa..!!!!"
*Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp message banda phone call,Thanks🤝*
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
*BY ZAINAB LALUH📲*
~(Oummu Imam)~
*Paid Book*
*Free Page 21
Wani mutum ne ya shigo kwanar ta bayan Fatun yana zuwa saitin ta yace "Ke bake ki ka yada jaka bane? sam Fatuu bata lura da ba jakarta a hannunta ba,don bata cikin hayyacinta,d'agowa tayi ta kafe Mutumin da idanu tama kasa bashi amsa,ganin yanayinta,ga fararen idanunta sun rikid'e sunyi ja yasa Mutumin cewa"baki lafia ne? d'aga masa kai kawae Fatuu tayi alamar "eh,juyawa yayi ya d'aukko mata jakar ya dawo inda take tsaye yace "Muje" bata ce komae ba tabi bayanshi a hankali take tafiyar har suka fito suka hau hanya Mutumin yace"ina ne gidanku?" da yatsa Fatuu ta nuna mashi,
"to zaki iya k'arasawa?ya tambayeta,Kai ta k'ara dagawa,ya mik'a mata jakar yace "Allah ya sawak'e,ni ta can zan bi ne, ki bi a hankali ki k'arasa kinji" nan ma kan ta d'aga,Mutumin ya juya ya tafi, Ikon Allah wai yau Fatuu ce ta kasa magana,lalle ba karamin tashin hankali kalaman gaye suka jefa ta ba,
Lokacin da ta iso gida shagon Amadu a rufe yake,tana shiga zaure taga k'ofar dakinshi a bud'e,shigewa ciki kawai tayi, tana shiga ta wuce band'aki tayi fitsarin da tuni ya d'aure mata mara don har ya d'an zubo ma,tana fitowa ta shige ciki,a bakin k'ofar dakinta ta aje jakarta ta shige,bata bi takan gwaggo ba don tasan bata nan tunda safe ta sanar da ita cewa aikin rana take,amman zata fita da wuri don zasu je Walimar d'iyar abokiyar aikinsu da aka d'aura ma Aure jiya Asabar,daga can zasu wuce Aiki,
Can k'arshen d'an gadonta ta haye ta had'e kafafuwanta ta tura kanta ciki,tayi zuru tana ta tuna maganganun Gaye,
kwata kwata ta kasa yin tunanin Mafita,don tana ganin ba wata mafita tabbas abunda gaye yace sai ya faru,don kud'in gilashin da yawa ba zai yuwu Mutumin ya yafe ba, tunda gashi harma ya tambayi kwatancen gidansu,sai lokacin wasu kwalla masu zafi suka zubo mata don tun d'azun ta kasa ma yin kukan,wani irin d'aci take ji a bakinta,
Ta dau tsawon lokaci a haka, ta kasa ko kwanciya don komae bai yi mata dad'i,tana a haka har aka kira sallar Azahar,tana ji ana yin sallar amman ta kasa saukkowa daga gadon ga yunwa tana ji amman bata jin ma zata iya cin abinci,
Amadu ne ya shigo cikin gidan don d'ibar Abinci bayan ya dawo daga salla,ya hango jakar Fatu da takalmanta a bakin k'ofar daki a ranshi yace "Yanzun haka tana can tana baccin tsiya bata tashi tayi Sallah ba" ya nufi dakin Fatun ya d'age labulen,kafin yace wani abu Fatuu tayi zumbur ta d'ago,hawaye duk ya wanke mata fuska,ganin haka yasa Amadu shigowa cikin d'akin yana kallonta yace"Miya faru?" dakyar murya can ciki tace "ban lafia.." Amadu dake ta kallonta har ranshi ya yarda bata lapiyan don da ganin fuskarta ma,yace"mike damunki",
Tace"zazzabi da ciwon kai" yace"kinsha magani" girgixa masa kai tayi alamar "a'a"
"To ai ba kwanciya zaki yi kita wani kuka ba,ba kinsan inda Gwaggo ke aje magunguna ba sai ki d'auka kisha ko" har ya nufi k'ofa zai fita ya juyo yace "Kinci Abinci" tace "a'a" juyawa yayi ya fice,ba'a jima ba ya dawo,hannunshi rik'e da plate d'in abinci yace"saukko ki ci" aje mata yayi a k'asa ya sake fita,sai gashi ya sake dawowa da Cup d'in ruwa da magani Panadol,tsayawa yayi yana mata wani irin kallo ganin bata saukko ba yace "ba saukkowa nace kiyi bane,in ki ka ban haushi sai in kyale ki kiyi ta zama da ciwon..."
A hankali ta saukko cikin zuciyarta tana fad'in"in kayi hakuri ma daga yau ba sake ganina za kai ba" aje mata ruwa da maganin yayi ya nufi k'ofa yana fad'in "kafin in sake dawowa ki tabbatar kin cinye shi kinsha maganin"daga haka ya fice,
Tunda ya fita ta kafe abincin da idanu,ta zabga uban tagumi tana ta faman tunanin a ina za'a samu kudin shanu gomaaa a biya mutumin nan,ita dai bata so akaita gidan yarin nan,gashi Gaye yace wasu wahala ke kashesu acan....,Zuciyarta ce ta raya mata "ARD'O" dammm gaban Fatuu ya fad'i,lokaci guda kuma ta fashe da matsanancin kuka,a fili take fad'in "Shi kadai ne zai iya biyan wadannan kudin,amman nasan ko kashe ni za'ai a gabansa da kwarankwatsa ba zai biya ba...." a zuciyarta tace "to ko in fad'ama Kawu Amadu ne..."da sauri ta girgiza kai a fili ta sake cewa"kafin gwaggo ta dawo nasan ya karairaya ni, don dama shi ake sawa yana zaneni"haka dae Fatuu tayi ta tufka da warwara,k'arshe ta maida hankalinta kan Abincin wanda jallof din shinkafa da taliya ne,a hankali tasa hannu ta d'iba ta kai baki ta fara taunawa da kyar take hadiye abincin,tana yin loma ukku ta tsame hannunta,sam bata jin dad'in abincin,shima d'aci yake mata a baki,tayi zuru tana kallon shi don tana jin yunwa sosae,a ranta tace "dama tuwo Gwaggo tayi kilan in fi jin dad'in shi...."Wata zuciyar tace"A ina zaki k'ara ganin tuwon ma,dama kinci Abincin don daga yau shima ba sake ganinshi zaki ba sai dai ki rink'a ganin gabza" da sauri ta jawo Abincin ta shiga turawa a baki ba don dad'i ba.
Bayan ta cinye Abincin tana cikin shan Maganin Amadu ya d'aga labulen ganin ta cinye yace" Yauwa,yanxu sai kitashi ki yi sallah inkin gama sai ki kwanta,insha Allahu zaki ji kin wartsake",a hankali tace "toh" ta mik'e don yin sallar,
Bayan ta gama sallar ta d'aga hannuwa sai Addu'a take tana fadin,"Allah don Allah na rok'e ka kada kasa a kaini gidan yari,don Allah,don masoyinka Annabi Muhammadu kasa Mutumin ya manta da abunda ya faru kwata kwata,nayi maka Alkawari na daina rashin ji,zan zama kamar Haulatu....." haka tai ta rok'on Allah tana kuka har tagama ta tofe a hannuwanta ta shafa,A saman abun sallan ta kwanta ta takure jikinta tana ta ajiyar zuciya a haka bacci ya kwashe ta.
Bayan an kira Sallar