Showing 180001 words to 183000 words out of 212491 words
raina sosae d'an zaman da nayi da ita nima na fara jin kewarta" fuskarshi d'auke da dariya yace "ai haka take shiyasa suke shiri da H,zakeen sosae though dae dama shi sai kayi mu'amala dashi zaka fahimci sauk'in kanshi" jinjina kai tayi alamar gasgata zancenshi sai kuma tace "dama ya aureta don sun matuk'ar dacewa wllh kuma a yadda take yanzu kaga sai yay playing role biyu, gashi matsayin Yayanta kuma mijinta, kai abun zai bada citta fa" ta k'arasa tana dariya shima Abbas dariyar yake yi yana ayyana yadda zamansu zai kaya matsayin miji da mata kafin yace "kema kinsan hakan bamai yuwuwa bane ai",
da sauri tace"yo dear mi zai hanashi yuwuwa sai dae in bai sa kanshi auren nata ba but it's possible" d'an ta6e baki kawae yay yana murmushi bai dae ce komai ba.
Suna hawa hanya Najeeb ya fad'i mashi sunan wata shopping mall yace ya kaisu zaima Zarah shopping, kai ya d'aga mashi kawae, bayan sun k'arasa awurin da ake yin parking ya parker Motar Najeeb ya bud'e ya fita kafin ya bud'e ma Fatuu yace ta fito, k'in fitowa tayi ta bishi da ido yace "ko nima sai Ya Handsome din ya baki izini ne?" shiru bata ce komae ba hakan yasa ya duk'a yace ma Haisam "ka bata permission" kallonta Haisam yay ta cikin madubi suka had'a ido da ita ya lumshe mata ido alamar taje sannan ta fita daga cikin Motar Najeeb yai wani Murmushi had'i da jinjina kai yay mata alamar suje,maimakon ta tafin sai ta lek'a ta kopar data fito tace ma Haisam "Ya Handsome banda kai zamu?" d'aga mata kai yay kafin yace "kuje ina nan" janye kan tayi ta rufe kopar tabi bayan Najeeb d'in suka nufi cikin Mall d'in, da kanshi ya d'aukko shopping cart yace ta d'auki duk abunda take so,tsaye tayi mashi tana kallonshi yace "Zarah baki ji mi nace ba?" yay Maganar ya kafeta da lumsassun idanunshi, d'an yamutsa fuska tayi kaman zata yi kuka tace"to ai fa ni ba abunda nike so ina da komae" d'an murmushin gefen baki yay yace"i know,amman ai k'ari baya k'in dad'i ko,ko dae ni baki d'auke ni kaman yayanki bane?"
tace "to ai shi an sanshi a gidanmu kai kuma ba'a sanka ba in ka siya man abu fad'a za'ai man",
"Owk in muka siyan sai in biki muje gidan in fad'a masu nine na siya maki don kar ayi maki fad'an hakan yayi maki?" shiru tayi sai kuma ta d'aga kai alamar ta yarda, zagayawa suka fara yi yana tura cart d'in saidae sam ta kasa d'aukar komae hakan yasa ya fara daukar mata da kanshi, sosae ya jidar mata kaya har saida tace mashi amman dae duk ba nata bane ko yace to na waye, tana jin hakan tace ita gaskiya sunyi yawa ganin zata yi mashi rigima ne yasashi dakatawa ya nufi wurin biya tana ta faman tura baki sai kace ba abun arziki akai mata ba, bayan ya biya aka juye kayan acikin manyan shopping bags ma'aikatan wurin suka biyo su dasu, boot yace ma Haisam ya bud'e aka zuba kayan kafin ya shiga Motar suka tafi, tambayarshi Haisam yay gida zai dropping nashi ne yace a'a ya fad'i mashi yadda sukae da Fatuu na zaije gidansu ya fad'i shi ya siya mata kaya kar a doketa yayi Maganar yana dariya ya dan juya ya kalleta ta tura mashi baki, shima haisam Murmushi yayi kafin yace ya rabu da ita kawae, gida ya maidashi suna isa mai gadi ya wangale masu k'aton gate d'in ya nufi parking space, tunda suka shiga Fatuu ke bin gidan da kallo har suka tsaya, juyawa Najeeb yay ya kalleta da Murmushi yace "to Zarah gaki a gidana zaki shiga ku gaisa da matana ko?" d'an murmushi tayi batare data ce komae ba hakan yasashi cewa "Oh I forgot, ashe kefa sai Yayanki ya baki permission d'in yin abu kike yi" kallon Haisam yayi yana niyyar magana ya rigashi cewa "permission not granted" dariya Najeeb yasa yace"gaisawa kawae zasuyi nothing else" Haisam yace "Inason na kaita gida before Magrib and it's almost time" ya kai Maganar yana duba wrist watch d'in hannunshi, jinjina kai Najeeb d'in yayi alamar gamsuwa kafin yayi mashi sallama yace sai sun had'u gobe ya juya kan Fatuu yace "to yar bafullatana sai watarana ko don ni gobe zan bar kasar nan" zaro ido tayi alamar mamaki sai kuma tace "ina zaka?",
da Murmushi yace "k'asan da nike zaune" da mamaki ta k'ara cewa "amman ba kace nan ne gidanka ba?"
"Yeah but bamu cika zama nan ba saboda acan nike aiki sai in munzo" cike da jin dadin yadda ta bud'e baki tana yi mashi Magana yake bata amsa, gyad'a kai kawae tayi yace "ko kina da waya ne mu rik'a gaisawa tunda nima na zama yayanki" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a yace "to ya za'ai,ko shikenan bazamu k'ara gaisawa ba?" shiru ta d'an yi sai kuma tace "in ka kira Ya Handsome in ina nan sai mu gaisa" jinjina kai yay ya sakar mata kayataccen murmushi kafin ya juya ya bude Motar ya fita yace ta dawo gaba, bayan ta koma Haisam yaja Motar Najeeb na d'aga mata hannu har suka fice daga gidan. Tunda suka hau hanya ba wanda yace komae shi idonshi na akan hanya ita kuma tana ta kalle kallenta har suka karaso gida, bud'e Motar tayi ta fita yace ta d'auki abunta data aje a bayan tace to, bayan ta d'aukko ledar kayan da Feenah ta bata juyawa tayi zata nufi gida don duk a gajiye take ganin haka yasashi sauke glass ya kirata, komawa tayi ta tsaya tana kallonshi ta gaban yace "kayan boot wa kika bar mawa ne?" ita sai lokacin ma ta tuna dasu don ta manta tace "to duka zan d'auka?" wani kallo ya bita dashi kafin yace "ke dawa aka siya mawa?" shiru tayi tana kallonshi bata ce komae ba, bud'e Motar yay ya fito ya nufi baya,bud'e boot d'in yayi ya fito da jakunkunan ya aje gefe bayan ya rufe yace ta kai wasu sai ta dawo ta d'auki sauran, maimakon ta daukan sai ta fara yamutsa fuska kaman zatayi kuka tace "to ai gwaggo na iya buguna in taji wani ne ya siya man wannan uban kayan" shiru ya d'anyi sai kuma yace taje ta kira mashi uncle d'inta in yana nan don shagon a rufe yake tana shirin nufar gidan Amadun ya fito yana gyara hannun rigarsa da alama alwala yayi yana ganinsu ya nufi Haisam yana washe baki ya shiga gaisar dashi, bayanin kayan yayi mashi yace ya fad'i ma gwaggon ya amsa mashi da to da sauri ya d'auki shopping bags guda biyu ya nufi gidan Haisam yace ta d'auki dayar ta bishi ya juya zai shige Mota sai yaji tace "kai bazaka dauki komae ba?" d'an kallonta yay bai ce komae ba hakan yasa tace "akwae turare da yawa" sai lokacin ya d'an girgiza mata kai da d'an Murmushi alamar a'a yay shigewarshi Mota,ganin bata tafi ba yasashi sake fitowa yace ta shiga gida sai lokacin ta kai hannu ta dauki d'ayar jakar ta nufi gida tana yi tana waiwayenshi har ta shige sannan ya tafi, Lokacin data shiga a gefe ta samu kayan da Amadu ya shigo dasu gwaggon kuma tana band'aki, aje d'ayar jakar da wadda Feenah ta bata tayi a wurin sauran kafin ta shige cikin d'akinta ta canja kaya zuwa doguwar riga ta fito lokacin gwaggo tayo Alwala tana shirin tada salla tana ganin Fatun tace an dawo d'aga mata kai tayi alamar eh tace taje tayi salla to, saida suka gama sallan ne gwaggon ta jawo jakunkunan ta fara duba kayan ciki fatuu dai na gefe sai zare ido take, uban kayan shafa ne kala kala da turarurruka, takalma jakuna yan kunne fashion harda jallabiyu guda ukku da kuma kananan kaya, tana cikin dubawa Amadu ya shigo don shima yana son ganin kayan da abokin haisam d'in ya siya mata, da tsananin al'ajabi gwaggo ta d'ago ta kalleta kafin tace "yanzu duk wannan uban kayan abokin nashi ne ya siya maki?" da sauri ta d'aga mata kai ta kuma cewa "to hakanan zai kashe uban kud'i ya sai maki kaya har haka sai kace lefe?" da sauri Fatun ta fara mata bayanin yadda ya siya matan har zuwa gidanshi da suka maidashi ta kuma ce mata shine ya bata kud'i masu yawa barka da salla ranar salla, shiru gwaggon tayi tama kasa Magana don mamakine kunshe cikin ranta har fuskarta ta bayyana, Amadu ne yace "su fa masu kudin nan basu d'auki wannan a wani abu ba wllh don haka kar ma ki wani damu" ya juya kan Fatuu yace "inyee kefa yanzu kin zama mai sa'a abun arziki kota ina samu kike bari nima in d'auki rabona to duk da ma bai wuce turare tunda duk abubuwan kune na mata" ya kai hannu bayan ya gama Maganar ya d'auki manyan turare guda biyu yace "na d'auki wad'annan don turaren ma duk na mata ne, daga yanzu in za'ai maki siyayya ki rink'a d'aukko abubuwan maza ba naki kadae ba" ya kai Maganar yana jaddada mata da hannu kafin ya nufi hanyar fita gwaggo ta dan ta6e baki ta bishi da ido har ya fuce, juyawa tayi ta kalli Fatuu data yi mata k'uri da ido ta sauke ajiyar zuciya kafin tace ta kwashe kayan ta kai cikin d'aki an gode Allah ya saka da Alkhairi, a sanyaye fatun ta amsa da Amin, bin ta da ido tayi tana kwashe kayan har ta gama,
bayan sallar isha gwaggon ta bata warmer guda biyu babba da k'arama mai dauke da abinci tace ta kai ma Amadu tace ya kai ma Haisam Fatun tace ita takai mashi mana tace a'a dare yayi ta kai ma Amadun, ba don taso ba taje ta kai mashi, lokacin daya kai mashi abincin yana zaune a falonshi yana operating laptop, bayan ya gaida shi yace dama abinci ne gwaggo tace ya kawo mashi shiru ya d'anyi don shi ba kowane abinci yake ci ba da daddare yafi son mara nauyi duk da baisan miye aciki ba, godiya yayi mashi bayan Amadun ya tafi ne ya bud'e babbar warmer din mai dauke da farar shinkafa da taliya sai k'arama kuma miya ce aciki harda nama rufewa yayi ya d'auki wayarshi ya kira tk, tambayarshi yayi yana gida yace mashi eh yace ya kawo mashi plate da spoon ya amsa da to, bada jimawa ba sai gashi ya kawo masan bayan ya gaidashi yana kokarin d'aura plate d'in kan c-table haisam din yace ya wanko mashi su a basin ya amsa da to, bayan ya dawo ya d'aura kan c-table d'in yace "shikenan Ya Haisam?" alamar ya tsaya yayi mashi da hannu saida ya k'arasa abunda yake a laptop d'in sannan ya kalleshi yace "a ina kake cin abinci ne?" dariya tk yayi yace ina dafawa ne" jinjina kai yayi ya bashi umarnin ya zuba mashi abincin dake a cikin warmer d'in ya amsa da to, yana zuba d'an kad'an yace ya barshi haka ya bude miyan ya zuba mashi naman ma yana sa tsoka biyu yace ya isa,umarnin ya d'auki warmers din abincin yaje yaci ya bashi yace in ya gama ya kai warmers din gidansu Zarah ya amsa da to, har zai tafi sai kuma ya dakata cike da kulawa yace "amman ya Haisam wannan abincin kaman yayi kad'an ba zai kosar da kai ba" maida bayanshi jikin kujera yayi fuskarshi asake yace ba wani abu zai ishe shi yaje kawae,
"to ko in had'o maka tea?" Tk d'in ya tambaya, shiru ya d'anyi sai kuma ya d'aga mashi kai alamar eh, cike da jin dadi ya nufi hanyar fita shi kuma ya fara cin abincin ba'a dau wani dogon lokaci ba Tk ya kawo mashi tea d'in ya zauna yana mashi yar fira har ya gama ya dauke abubuwan abincin kafin yayi mashi saida safe, cigaba da abunda yake yayi wayarshi ta fara ringing ya kai hannu ya d'auka, Murmushi ya saki ganin mai kiran nashi wato Hajiya, handsfree yasa ya aje wayar agefe hajiyar tayi mashi sallama,
"Sweetheart hope u'r work" ya fada idonshi akan screen,
"Lafiya lou nike kaifa?"
"Same" ya bata amsa a takaice,
"Yau mi kaci ne?" ta tambaya, har saida ya d'anyi Murmushi kafin yace mata abinci, tace "da safe kaci abinci?" yace mata eh yaci a wurin aiki, ta tambayi da rana fa yace mata yaci a gidan Abbas,
"To yanzu da daddare fa?" ta sake tambaya, d'an girgiza kai yay kafin yace "in kin damu da wannan ki dawo mana" a d'an fad'ace tace "nima ai nan d'in kaman akan k'aya nike kawae banda yadda zanyi tunda an fi karfi na" dariya yayi har hakoransa suka bayyana kafin yace gidansu ne k'ayar tace eh mana,
"Pls tell me kaci abinci yanzu kuwa, kodae insa Saude ta dawo ne dama don nasan tukur ya iya dafa abinci shiyasa nike kyaleta sai na dawo itama ta dawo amman yanzu ko don kai inaga zan sa ta dawo kawae tunda a gaban idona ma ba son ci kake ba balle yanzu da bani ba kuma mai dafa makan" d'an ta6e baki yay kafin yace ta kyaleta kawae sai ta dawo tace to ya fad'i mata abunda yaci yanzu,
"Zarah ta kawo man" daga jin muryarta taji dadin hakan tace "yauwa naji dadin hakan wllh sun kyauta Allah ya saka, in kana son wani abun zaka iya sa tukur ma yayi maka don ya iya dafa abinci sosae" amsa mata yay da owk daga nan suka ci gaba da yin hira yana daddana Computer din. Washe gari Friday misalin Karfe bakwae Fatuu ta zo part d'inshi ganin bai cikin parlon yasa ta kware baki tana yin sallama sai gashi ya fito cikin suit Maroon Colour, sakin baki tayi tana kallonshi hakan yasa yay mata wani kallo mai kaman harara ta saki Murmushi, k'arasowa yay cikin falon ya zauna ganin tayi tsaye yace mata ta zauna mana sannan ta zauna ta gaidashi tana ta Murmushi dae, bayan ya amsa ta nuna mashi d'an basket da ta d'aura kan c-table tace "gashi nan abun kalaci ne na kawo maka" d'an waro ido yay ya kalli basket d'in kafin ya maido idon kanta calmly yace "breakfast dis early?" tura baki tayi tace "to ba aiki zaka tafi ba shiyasa ai na kawo maka da wurin" still idonshi akanta yace "ban iya breakfast a wannan time en" wani kallo tay mashi sai kuma ta juya mashi bayan kanta tana fad'in "Allah sai kaci shi" bin ta da kallo yay da d'an murmushi akan fuskarshi sanin in ya biye mata haka zasuyi ta jan magana kuma so yake ya tafi yasashi cewa ta had'a mashi amman d'an kadan in yaci da yawa zai iya yin amai ne da sauri ta kalleshi ta washe baki tace to, had'a mashi ta shiga yi dama an sako cup da spoon don ruwan tea ne acikin flask da ledar biredi mai kyau sai kayan hadawa madara da milo da sugar a gefe sai kuma soyayyen kwae rufe cikin bowl, komi sai ta tambayeshi in yayi bayan ta gama ta koma ta zauna kan carpet tana wasa da yatsunta shi kuma yana cin breakfast din a nutse can ya tambayeta ita ta yi breakfast dinne tace a'a sai ta koma gida, jinjina kai kawai yay don sauri yake, yana gamawa yace ta tafi da kayan tace ai ance in ya d'iba ta kaima Tk sauran ya amsa da owk yana nufar Bedroom dinshi, brush ya sake yi kafin ya fito ya shiga d'ayan d'akin bada jimawa ba ya fito hannunshi ruk'e da bak'ar jaka ya nufo falon, saida ya kira Tk a waya lokacin baima tashi daga bacci ba yace mashi in ya tashi yazo part d'inshi ya d'auki breakfast cike da girmamawa ya amsa mashi kafin yayi mashi adawo lafiya, ce mata yay tazo ya ajeta gida ta mik'e da sauri tabi bayanshi,
Ana gama sallar Juma'a gwaggo tace ma Fatuu taje taga in Haisam ya dawo daga aiki lokacin ta ci gayun juma'a da d'aya daga cikin jallabiyun da Najeeb ya siya mata ash colour tasha adon duwatsu sai salki take, koda taje bai dawo ba sai kawae ta dawo ta d'auki rigar da gwaggo tace ta ba Haulat cikin kayan da aka siya matan da su kayan shafa ta tafi kaima Haulat, sosae tayi farinciki tana ta faman godiya harda innarsu sai washe baki haulat take don sam bata da jallabiya dama, sosae kuma ta yaba ta jikin Fatun gab da la'asar ta dawo gida ta k'ara zuwa ta duba ko haisam d'in ya dawo ta iske bai dawo ba,sai bayan sallar la'asar Amadu ya shiga yace ma gwaggo gashi nan ya wuce dayake tace in yaganshi ya sanar mata,zumbur Fatuu ta mik'e dama suna zaune a tsakar gidane don inuwa ta sauka, Kitchen ta nufa ta d'auki kayan abincin ta tafi kai mashi, da sallama ta shiga cikin falon saidae bai ciki sanin bai dade da dawowa ba yasa tayi tunanin kilan wanka yake, wuri ta samu ta zauna bayan ta d'aura basket d'in a saman c-table shiru bai fito ba hakan yasa ta d'auki remote ta kunna tv taci gaba da kallo abunta tun tana zaune har ta d'an kishingida sai can bayan wani lokaci ya fito cikin Sportswear suna had'a ido ya bud'a mata ido ita kuma tayi mashi dariya, wuri ya samu ya zauna ta gyara zamanta dama a d'ayan bangaren inda take zama ta zauna gaidashi tayi kafin tace "nayi kyau ko?" kai ya d'aga mata tace "cikin kayan da abokin nan naka ya siya manne wai ya sunanshi?" shiru ya d'anyi sai kuma a hankali ya furta "Najeeb" jinjina kai tayi ta kuma cewa "amman dai yana da kirki kaman kai hakanan bai sanni ba ya kashe uban kud'i ya siya man kaya,Allah ya saka maku da Alkairi ya saka ku a Aljanna