Showing 15001 words to 18000 words out of 212491 words

Chapter 6 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

956

sam basu yarda ba yadda aka tura yaransu sukaje suka yi karatun Allo,to dole shima t.k din yaje,ba yadda bai ba ya fahimtar dasu hakan k'aruwarsu ce gaba daya,amman firr suka ki amincewa don bakin ciki,ba k'aramin tashin hankali ya fuskanta ba,ba yadda ya iya haka ya turasa,mahaifiyarsa
Hasiya nata kuka,don ta so yayi karatun,dayake Allah hakimun ne sai gashi tafiyar tasa ta zame masu Alkhairi,rabo kuma ya rantse,Malam halliru ba k'aramin girgiza yayi ba lokacin daya kaima t.k ziyara,ganin cikin daular da d'an nashi yake,bada niyyar kwana yaje ba,amman hajia ta matsa ya kwana,da zai tafi ta hada masa sha tara ta Arziki harda Atamfofi ya kaima matansa.
Zaune malam halliru yayi a tsakan gida yana basu labarin irin Arzikin da t.k yake ciki,ya sanar masu mahaifiyar sanata ce yake wurinta kuma matar tsohon ministan tsaro Gen.Adamu zakee,kaman yadda t.k ya fad'a masa,murna wurin Hasiya kam ba'a magana,sai ma da t.k din yazo da Sallah,har gida aka rinka zuwa ganin tukur dan gidan sanata,haka mutanen gari ke fada.
Private school hajiya tasa shi yayi secondary,bayan ya gama kuma ya tafi Polytechnic dake nan katsina inda yanzu ya shiga ND2 yana karantar SLT,ba faman da Hajia bata yi dashi ba akan aikin da yake ba kaman wankinta da ya hana kaiwar da ake dry cleaning shike wanke mata su fess ya goge a cewarsa baiga abun wahala ba abunda da injin ake yin wankin,Manyan abubuwa irinsu barguna,labulaye da carpet kawae ake kaiwa wurin wanki.
Lokacin da Haisam ya dawo hajiya tace ma tk ya samo wanda zai rink'a gyara masa part dinsa acikin abokansa yan makarantar allon su dake kawo masa ziyara akai akai,nan ma cewa yayi shi duk zaiyi ai ba wani aiki ne mai wahala ba,kuma dama yana bala'en son Haisam,ba k'aramin burgesa yake ba,shiyasa in yana gyara masa part din nasa cike da himma yake aikin,ba algus don dama shi tun yana k'arami aikinsa ba ha'inci,shiyasa in ya dage shi zaiyi abu sai hajia ta kyalesa don tasan zai iya din,kuma ba'a ganin ba daidai ba wani lokacin takan tsokane shi tace "na manta jikan nawa fa kakkarfa ne don tun yana karami kunya goma yake nomewa" sukan yi dariya atare,
Shikam t.k duk yana yin hakanne don hud'ubar da mahaifiyarsa ke masa duk in yaje ganin gida,takan ce ba abunda zamu iya saka masu dashi,haka zakaga ana zuwa gaida t.k in yaje tamkar shine Senator din,iyaye har tura yaransu yanmata suke wae ko zai taya,basu san t.k ya wuce ajinsu ba sai yar birni,in ya tashi dawowa haka mahaifiyarsa zata bashi,su kuka,kubewa,daudawa,barkono da sauran su ya kawo ma hajiyar,mahaifinsa da har hatsi yake bashi ya kawo,Hajiar ta hana tace iya su kayan miyan ya isa ta gode.
Wannan kenan game da Tukur Halliru Birnin magaji,wanda tuni yazama dan gida a gidan Hajiyar sanata don har Senator Ali Adamu zakee yasan da zamansa.

A next page zamu fara nitsawa cikin labarin In shaa Allah,aci gaba da share pls. Thanks as u do so🤝🥰

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*


*BY OUMMU IMAM📱*

*Paid Book*

*Free Page9️⃣&🔟*

Washe gari juma'a,daga cikin d'aki gwaggo ke magana"Wai fatuu bazaki fito ki tafi ba sai kin makara,kuma a buge ki kizo kina cewa malami kaza ya tsaneki ko" fitowa fatuu tayi sanye da uniform din makaranta hannun ta d'aya dauke da jaka School Bag dayan kuma takalma ne Sandals na roba,a k'arkashin hammatarta ta sak'a jakar ta duk'a tana kokarin sa sandals din saidai igiyan tak'i sawuwa sai faman kici kici take yi dashi a fili tace"Wannan shegen takalmin ni wallahi na gaji dashi" haushi taji ta buga shi da k'arfi a k'asa tace banzan takalmi yaki sanyuwa.

Duk maganganun da take a kunnan gwaggo,fitowa tayi ta tsaya a bakin k'ofa hannunta d'aya dafe jikin bango tana kallon Fatun sai kiciniya take.
"To taya zai sanyu kin kasa natsuwa kisa shi sosae,ji bi yadda kika wani takure kin cusa jaka a hammata,d'agowa tayi tace"to yaya zanyi" fuska a tur6une da alama takalmin ya k'ule ta,
"Ki aje jakar mana a gefe,ki zauna sosai kisa" Aje jakar tayi ta dan zauna a bakin k'ofa kamar yadda gwaggon tace,aikuwa sai gashi takalmin ya sanyu ba wani 6ata lokaci,da sauri fatuu ta d'ago ta kalli gwaggo tana daria tace "Kinga d'an banza ya sanyu kuwa" gwaggo ta dan ta6e baki"Uhm ba wani d'an banza,dama ba ki yadda ya kamata ya sanyun bane,ace komi mutum zai yi bazai sa natsuwa ba,
Mik'ewa fatuu tayi tana kokarin goya yar jakar goyon a bayanta tace"zan tafi" gwaggo tace"To adawo lpy,Allah ya tsare" wani irin kallo fatuu tayi mata tace adawo lafia kuma?
Gwaggo tace"Eh mana ko baki son Addu'ar ne?, "A'a ina so mana amman ai banji bayani ba" tayi maganar tana yi ma gwaggo alamar kud'i da hannuwanta,gwaggo tace"wai don Allah ba ranar da zaki ce yau dai gwaggo kibar kudin ki ne?
Da sauri fatuu tace "iyeee,to kuma dami zan hau mota kuma inyi break,in baki bani ba? Gwaggo tace "to acici baki da magana dama sai ta abinci,a duk satin duniya sai kin cinye mani naira d'ari biyar wani satin ma sai sun fi haka tunda sai ki dawo kice man baki samu bus ba kin ranci kudi kinyi ciko kin hau Napep ko mashin", Fatuu da ke tsaye ta k'agara gwaggo ta sallameta ko ta tafi tace"Don Allah gwaggo kiban,taya karatun zai yiwu da yunwa to ko mota dai ai sai an zuba mata mai take aiki ko" yar daria gwaggo tayi, fatun tace "yau baki zuwa aikin ne? "Zanje,amman sai da rana",
Fatuu tace"kenan zan dawo in iske ki? Gwaggo tace "Anya kuwa kinsan yau juma'a,da wuri zan tafi,wurin k'arfe d'aya haka",
"to ammn dai zaki yi mana abinci ko ba sai na dawo ba inyi"tayi maganar da sigar shagwa6a" gwaggo ta rike baki tace"Ah kajita ko da yaushe-da yaushe nike tafiya in bar mata wani yin abinci,ai sai dai in ina aikin safe ne kuma shima kusan tare muke dawowa,kamar wadda ta iya wani abincin arziki",
Fatuu tace "ai dai ina yi kuma ki ci har kice yayi dad'i" daria gwaggo take tace"Mai karya.....fatu tace"d'an Aljanna,tana daria,"gwaggo kiban don Allah" mik'o mata naira d'ari tayi wadda ke cikin hannun da ta dafa bango dashi,da sauri fatuu ta amsa tace"daman kudin na a hannun ki,amman sai kinja man rai,juyawa tayi ta fara tafia,sannan tace "Kar ki damu kakus,zan biya ki duka kud'aden da kika kashe man in nazama Doctor" har lokacin gwaggo daria take ta girgiza kai tace"nadai fad'a maki ai natsattsu ne ke zama likitoci,in baki natsu ba,ba wata Doctorn da zaki zama" da d'an karfi tace"Insha Allahu zan zama harna rik'a yima ki Allura ma,na tafi" ta karasa fada yayin da ta kusa isa zaure.
Gwaggo tace" To Allah ya tsare adawo lafia ban.......,Fatuu dake cikin zaure ta k'arasa abunda gwaggon zata fadi da karfi"BANDA RIGIMA DON ALLAH FATUU" daga haka ta fice daga gidan,girgiza kai gwaggo tayi tana ta daria tace" Shiryayya,a haka ko nace d'in wani lokacin kafin ta shigo gidan an kawo man k'ararta,Allah dai ya shirya"daga haka ta koma cikin d'aki.

Tafiya fatuu take ta raba hanya biyu,sam ba natsuwa a tafiyar,hanyar shiru dayake safiya ce sai yara jefi jefi yan tafiya makaranta kamar dai ita,sai wani cilla k'afa take kamar zata tashi wai ita nan sauri take,Horn d'in da akai da k'arfi ne a bayanta yasa tayi saurin komawa gefe,sannan ta juyo tana kallon motar da ta taho,Peugeot ce 406,Maroon color,cikin ranta tace"dama mai motar nan ya rage man han....bata k'arasa ba sakamakon mutumin data ga ya wuce fuuu a cikin motar bai ko kalleta ba,da sauri fatuu ta zaro ido had'i da rike ha6arta tace"Kai! Wancan ai mutumin nan ne na jiya mai kama da Aljani,ba dai a layin nan yake ba? ta karasa maganar da sigar tunani harda d'an waigawa baya,tace"Uhm inma nan din yake,shi dai ya sani"

taci gaba da tafiya har tazo wata kwana d'an nesa da gidansu,tana karya kwanar ta tsaya da alamun mamaki a fili tace"lallai ma wannan haulatun,har yanzu bata fito ba,tana nufin in bita har cikin gida kenan" kwafa tayi sannan taci gaba da tafia,ad'an gaba kadan daidai wani gida inda yaro ya fito dauke da d'an bokitin plastic ta tsaya tace ma yaron "Kai haulatu na nan ciki" yaron yace "Eh naganta tazo ta karbi koko a rumfar da Innarsu ke saidawa" ya wuce,ita kuma fatuu ta kad'a kai ta shige cikin gidan wanda gaba daya k'asan gidan kasa ce,sai daga can gaban dakuna ne akai ma k'asan shafen siminti shima duk ya farfashe,a gefe guda wata mata ce cikin wata yar baranda da yara tsaitsaye tana zuba masu koko,matsawa fatuu tayi bakin barandar tace "Innarsu Haulatu ina kwana" da washe baki ta amsa"lafia lau fatee yan makaranta,haulatun na ciki" kad'a kai fatu tayi ciki,tana hawa saman simintin wata yarinya ta lek'o tana daria,wankan tarwad'a ce tana da kyau ba laifi,hannunta d'aya rike da hijabin Uniform dinta dayan kuma kofi ne tana shan koko,tsayawa fatuu tayi tana harararta,fuska daure tace"Ashe ma baki shirya ba don wulakanci kika sa inata sauri" haulatun wadda keta faman daria tace"wallahi markad'e innarmu ta aikan kuma sai na iske layi,amman ai na shirya hijab kawai zansa da Sandals",da yar tsawa fatuu tace "Da Allah to kisa mu tafi,salon sai mun makara wannan banzan displine d'in ya bugi mutane, daman ya tsane ni" ta k'arasa tana murgud'a baki,

Haulatu tace"bafa kyau zagin malami fat...." ta katseta"naji,wayace ya tsane ni"fatuu ta haulatu tace"bafa tsanarki yayi ba,kece kike ja ai yana dukan ki,ni kinga yana duka na?" ta kai maganar tana kurbar koko,"dalla ki fito mutafi ko inyi tafiya ta wallahi,daman ke ai baki ganin laifin kowa sai nawa"da alamar ranta ya 6aci, Haulat tace"Haba kawata daga fad'ar gaskia...."
"to ki rik'e gaskiyar banso" inji fatuu,mik'o ma fatuu kofin kokon haulat tayi tace ida shanye wa",harararta Fatuu tayi da sauri tace "Wa!Ni zan sha wani koko,kokon ma sauran ki,Allah ya kiyaye,ta tofar da miyau gefe" girgiza kai haulat tayi da d'an murmushi ta idasa fitowa,aje kofin tayi a k'asa ta sanya hijab din da Sandals din dake aje bakin kofar d'akin,ta d'auki jakar ta,ta leda irin ta biki tace"Mu tafi" atare suka nufi hanyar fita,haulat ta shiga rumfar da innarta take,ta ajiye kofin data sha koko tace ma Innar "zan tafi" kud'i innar ta miko mata naira sittin tace"A dawo lpy" Allah yasa" haulat tace ta nufi hanyar k'ofar gida,don ita fatuu tuni ta fuce.

A kan hanyarsu ta zuwa bakin titi inda zasu hau Bus fatuu sai faman masifa take ma haulat tana cewa ai in suka rasa Bus itace a matsala don tasan bata da isassun kud'in da zata hau Napep ko mashin,baiwar Allah haulatun ita dai tayi shiru tana sauraranta da alama tana da hakuri,gashi da gani ta girmi fatun ko a yanayin jiki tafi fatuu tsawo a sanyaye tace"Insha Allahu ma zamu samu,in kuma ba'a samun ba sai in dawo ba wani abu,in Allah ya kaimu Monday naje"daga haka ba wanda ya kara cewa wani abu.

Suna isowa bakin hanyar kuwa sai ga Bus din da yar fara'a haulat tace "Alhamdulillah",juyowa fatuu tayi tai mata wani kallo fuska a d'aure.

Haulatu kawar fatuu ce,tun lokacin da tazo garin,lokacin da gwaggo tasa ta a makaranta har gida taje ta had'a su suyi kawance,don tasan halin haulat yarinya ce mai hakuri da natsuwa,ita kadai ce zata iya jure halin fatun a yaran unguwar,gwaggo ta roki haulat da ta d'auki fatuu a matsayin kanwarta ta rik'a nuna mata abubuwa masu kyau,ta kuma rika hanata maras kyau,gwaggo bata 6oye ma haulat komai ba game da halin fatuu, a gabanta kuma tayi ma fatu fad'a sosai akan ta zauna lpy da haulat ta rik'a jin maganarta,intaji sun yi fad'a tasan itace ta ja,kuma sai ta sa6a mata,Innarsu haulat ta tabbatar ma gwaggo cewa haulat bata da matsala karta damu,dama kuma ana ganin mutuncin Gwaggo a unguwar,Ita kuwa haulat tunda taga fatu taji tayi mata,jininta ya had'u da ita,tace ma gwaggo zata kula da ita insha Allahu,A haka kawancen su ya k'ullu,duk da ance wai sai hali yazo d'aya ake abota,to nan dai halin sam bai zo daya ba,dama kuma sai ansamu bambanci abota ke lasting,misali,daya mai wayo daya mara wayo ko daya mara hakuri daya kuma mai hakuri kaman su kenan,Amman duk da hakurin Haulat wani lokacin sai fatu ta k'ule ta har tayi fushi,sai kuma ta dawo taita bata hakuri har sai taga ta hakura,dama ko gwaggonta haka take mata.

K'arfe sha biyu da rabi na rana daidai aka tashe su kasantuwar ranar juma'a ce,Haulatu ce tsaye tana ta faman kwala ma Fatuu kira "fatuu ki taho mu tafi kar acika bus d'in kinsan yau Juma'a fa gaba daya ake tashi harda seniors" ita kuwa fatun tana can sai faman bin students take da gudu tana bugun su,wai na bankwana daga yau sai Monday,girgiza kai Haulat take tayi don ta gaji da tsayuwar,sai da ta gama buge bugen ta taho da d'an gudu sai faman nishi take tana daria, jakarta a hannu d'aya,
Dafa kafad'ar Haulat tayi da dayan hannun tace muje k'awalliya,juyawa kawai haulat tayi bata ce mata komae ba suka tafi.
Abunda haulat ke gudu shi ya faru don kuwa School Bus d'in ta cika dam sai dai su tsaya a tsaye ko su zauna a k'asa,Haulat ta kalli Fatu tace"Kinga abun da kika ja mana ko,da ana tashi muka taho ai da mun samu seat kika tsaya shiririta,yanzu ai sai mu zauna a k'asan" ta k'arasa maganar da dan 6acin rai,fatuu tace"tabb nikam bazan zauna a k'asa ba duk a tattake ni,ga k'asan ma duk k'asar sandals din mutane,"To ya zamuyi,nidai ban iya tsayuwa gaskia da anzo tudu ko wurin yin kwana mutum yayi ta bugewa" inji Haulat,
"ki tsaya kika ga ni,sai na samu seat d'in zama" fatuu tayi maganar yayin da take kutsawa cikin Bus d'in,hango wata yar senior section tayi wadda unguwar su d'aya don tare suke hawa Bus a bakin titi,su biyu ne a zaune,a daidai wurin su ta tsaya tace "D'an matsa man in zauna, "Kamarya? Yarinyar ta tambaya,fatuu tace "Ai ku biyu ne kuma har mutum ukku ana zama ko" tayi maganar tana turo baki,"To in mu biyu ne mu tsaranki ne? Fatuu tace "Yo ina ruwan mota da wani tsara ai dai duk makaranta d'aya muke ko" da sauri yarinyar ta nunata da yatsa tace"Ke karki yi man rashin kunya yanzun nan in mari wannan kumatun naki,dama naji ance baki da kunya to ni in kika yiman zane ki zanyi wallahi" da alama itama yarinyar masifaffa ce, cikin harzuka fatuu tace "Ki zane wa,ai ni wallahi nafi k'arfin ki zane ni sai dai mu zane juna,don ba fina k'arfi kikai ba ehee" ta murgud'a mata baki,da sauri yarinyar ta yunk'uro zata mari Fatuu,ita kuma fatun tayi saurin kaucewa....Sauran Students din cikin motar ne suka had'a baki wurin cewa"Kwandasta ana fad'a" da sauri Haulat ta nufi inda fatuu take bata san mike faruwa ba,amman tana jin ance ana fad'a tasan da Fatuu ne,shima kwandastan ya nufo ciki yana fadin"suwa ke mana fad'an? "gasu nan" students suka ce,
daidai inda suke ya tsaya yarinyar ta rik'e wuyan hijabin Fatuu itama fatun haka sunyi cirko cirko,cikin daka tsawa Kwandastan yace"ku saki juna!! Kowa ya saki kowa,yaci gaba"miya had'a ku" da sauri yarinyar tace"Wannan yar rainin wayon ce,wai sai mun matsa mata ta zauna,kuma na gaya mata ba wuri amman zata yima mutane rashin kunya sai kace wani ya hanata tazo da wuri..." ta k'arasa maganar tana ta huci ita kuwa Fatuu ta cika famm kaman zata fashe sai hararar yarinyar take,kwandastan ya juya wurin ta yace "Ah kece baki da gaskia,tunda an riga ki sai ki hakura ki zauna a k'asa ko ki tsaya ki rike karfe,In kuma baki iyawa sai ki hakura ki fita kawai,Amman kar wanda ya kara yimana fad'a,in ba haka ba zan kori mutun ne" ya juya ya nufi gaban motar yana jaddada masu abunda yace.

Haulat ce ta kama hannun fatuu wadda ta cika fam,tana yima yarinyar wani irin kallo,"Zo mu zauna a k'asan kawai fatuu don Allah ki kyale ta kar a kore mu kin...."da karfi Fatuu ta fuzge hannunta,ita kuwa yarinyar sai faman cika take tana batsewa tana wani yamutsa fuska.
Wata student ce yar junior section acan dayan 6angaren motar tace"Fatuu zo ki zauna ga wuri na matsa maki" k'wafa fatun tayi ta duk'a ta dauki jakarta wadda ta yarda lokacin da zata rike hijabin yarinyar da suke fada,ta nufi inda aka matsa mata ta zauna,ita kuwa haulat baiwar Allah wuri ta samu a k'asa ta zauna sam bata iya tsayuwar.

Adaidai kan kwanar da aka saba aje yan unguwar Bus din ta tsaya students d'in unguwar suka fara fitowa harda su Fatuu,sannan yarinyar da sukai fad'an itama ta fito tana ta suratai da kawayenta yan senior guda biyu"Yan section d'insu ke tsoronta shiyasa take masu iskanci,ni in yarinya tace zata yi man wallahi maganinta zanyi yadda gobe ko ance taja wani fad'a bazata yi ba,hakanan azo garin mu ana cin arzikin mu kuma ace za'a rik'a yimana iya shegeee" wata cikin kawayen tace"Wai daman ba yar nan garin bace? "Eh yar jahar Adamawa ce,da gani ma acan d'in yar k'auye ce irin yan rugar nan,kinsan dan k'auye daya samu wuri sai iya shege iri iri" k'awayen suka tuntsire da daria,d'aya tace"kai Murja" wadda aka kira da murja tace "Allah kuwa,duk tabi ta Addabi mutane,duk da ba a layin gidansu nike ba,a layin bayansu muke inajin labarin iskancinta,shiyasa a cikin Bus din nan naso in saita mata hankali da kwandastan nan bai zo ba,tasan ni ban tsoronta" duk maganganun da suke a kunnan Fatuu don a bayansu suke kuma da karfi yarinyar ke maganar don Fatun taji,

A farkon kwanar gidansu kawayen nata yake,Murja tace "bari in biyo ku inyi fitsari" suka shige tare,tsayawa fatuu tayi wadda kiris ya rage ta fashe don fushi tana kallon gidan da suka shiga,Haulat tayi saurin cewa"Don Allah,mu tafi Fatuu,karki biye mata" tana kokarin janta" k'in tafiya fatun tayi ta cije a wurin haulat taci gaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login