Showing 183001 words to 186000 words out of 212491 words

Chapter 62 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

987

ku duka" acikin ranshi ya amsa fuskarshi da d'an Murmushi don yadda tayi Maganar kaman ba ita tayi ta ba,
"Yace yana gaidaki ya tafi d'azun" taji ya fad'a, da sauri ta kalleshi tace "kenan ya tafi kasar da yace man can yake?" kai ya d'aga mata tace "wayyo Allah ya kaishi lafiya" amsa mata yayi da amin ta nuna mashi basket tace ga abincinshi nan ta zuba mashi, shiru yayi yana kallonta har saida ta maimaita mashi sannan yace yaci abinci a wurin aiki tace to sai yaci da daddare, d'aga mata kai kawae yayi alamar to, sai kuma yace in taje gida ta fad'i adaina wahalar yin abinci dashi tunda yana ci awurin aiki da safe kuma baiyin breakfast da wuri tace "to da daddare fa?" yace "nafi son light food so Tk zai man wannan" jinjina mashi kai tayi can ya mik'e yace mata zai tafi gym,mik'ewa tayi itama tace "inzo in raka ka" girgiza mata kai yay yace "yawon zai yi yawa" daga haka ya nufi dakin lab ya d'aukko jakarshi ya fito suka fita tare, saida ta raka shi har parking space ya fiddo bike dinsa tace don Allah ya d'anata amman sai ya girgiza mata kai alamar a'a, tadashi yay ya fara tafiya a hankali yace suje suka tafi tana gefenshi sai tura baki take saboda yak'i goyata shidae sai murmushi yake kawae ahaka har suka je daidai gidansu sannan yasaka helmet ya fuzgeshi da gudu tana ta kallonshi har ya 6ace ma ganinta,tana shiga gidan ta nufi gwaggo dake zaune ta shiga fad'i mata abunda haisam d'in yace game da abincin da ake kai mashi, yar dariya kawae tayi tace ma Fatun ta kira mata shi a waya, farko data kira bai d'auka ba sai lokacin ta tuna tace mata ai fa ya fita yanzu da k'atoton mashin d'inshi kilan bai sauka ba, bayan wani lokaci sai gashi ya biyo kiran ta mik'a mata wayar, d'auka tayi ta kanga ta a kunnanta yana jin muryar gwaggon ya gaisar da ita ta amsa tace mashi taji sako wurin Fatuu ai ta d'auka anzama d'aya yana murmushi yace mata hakane tace kuma a ina yaga in uwa tayi ma danta abu yake zama wahala, nan ma dae Murmushi yayi kawae cike da zolaya tace mashi kodae bai jin dadin abincinne yaji shi ba irin wanda ya saba ci ba, wannan karon har saida yayi yar dariyar da itama taji sautinta yace mata ba haka bane tace to dole za'aci gaba da kawo mashi ai na d'an lokaci ne ko in yaje aikin ya rink'a cin kad'an in ya dawo sai ya k'ara, cike da girmamawa ya amsa mata da to kafin yayi mata godiya sukae sallama,

Washe gari Asabar ana tashi islamiyya gidan hajiya ta wuce, lokacin data je part d'inshi yana zaune a falo yana aiki, bayan sun gaisa yace taje gida kar a nemeta har ta mik'e sai kuma ta tsaya tace "Ya Handsome wai baka ce zaka koya man irin turancin nan ba ko ka fasa ne?" d'agowa yay ya kalleta ya d'anyi shiru sai kuma yace "yaushe zamu fara?" da sauri tace "yanzu tunda na dawo daga makaranta ba abunda zanyi kuma" jinjina kai yayi yace taje ta cire uniform sai ta d'aukko book da pen ta amsa da sauri ta fuce, tana komawa gidan shaf shaf ta canja kaya taje kicin ta gaya ma gwaggo tace taje, lokacin data koma tana shirin zaunawa yace suje yai mata alamar waje, mik'ewa tayi suka fita, tana biye dashi suka nufi parking space can farko inda ba Mota dama ya kira Tk yace ya kawo masa kujeru guda biyu wurin harda d'an table dinsu, nuna mata d'aya yayi alamar ta zauna kafin shima ya zauna ba 6ata lokaci ya fara mata lesson din turancin, kiran sallar Azahar yasashi mik'ewa yace zaije yin salla itama taje tayi tace dakinshi ko gida yace mata taje gida sai taci abinci tace to shima zata kawo mashi kai kawae ya d'aga mata ya nufi part d'inshi don yin alwala, tana zuwa gida tayi sallar bayan ta gama taje d'aki wurin gwaggo tace ina abincin Ya Handsome zata kai mashi, tare suka fito suka nufi kicin ta bata kayan abincin nashi har zata tafi gwaggon tace ta dawo itama taci abincin tace mata zata ci acikin nashin,

"Baku gama lesson d'in bane?" ta tambaya idonta akanta amsa mata tayi da eh, ganin ta kafeta da Ido yasa da sauri tace "wllh kuwa da gaske nike kuma in baki yarda ba ki aiki kawu Amadu ya dubo maki muna nan inda ake ajiye motoci anan yake koya man" jin hakan yasa gwaggon taji hankalinta ya k'ara kwanciya ba kuma don tana zargin wani abu ba sai don yakamata dama tasa kula duk da yardar da tayi da haisam d'in, ce mata tayi ta tafi, bayan ta koma bata iskeshi a parking space d'in ba tana niyyar zuwa part dinshi ya fito daga cikin Masallaci, komawa tayi ta zauna shima ya k'araso ya zauna ba tare data tambayeshi ba ta fiddo kayan abincin ta zuba mashi ta tura mashi kafin itama ta zuba tace mashi suyi yar rigen cinyewa, d'an murmushi yayi ya girgiza mata kai kawae, ba laifi yaci sosae bayan ya gama ya kira Tk a waya yazo ya d'auki sauran Abincin daga haka suka ci gaba da yin lesson din har saida aka kusa kiran la'asar sannan yace mata taje gida sai gobe, washe gari lahadi haka ya k'ara yi mata lesson d'in acikin parking space d'in kuma ba laifi tana kamawa sosae, ana shiga ranakun aiki ganin Haisam din yayi mata wuta daga ya ajeta a Makaranta bata k'ara ganinshi don lokacin da yake dawowa ta tafi islamiyya in kuma aka taso su shi kuma bai dawo daga gym ba gashi in tace zata kai mashi abinci da daddare sai gwaggo ta hana tace dare yayi sai ranakun da ba'a islamiyya ne kadae take samun ta dan ganshi in ya dawo kafin ya tafi gym wani lokacin kuma in gwaggon bata dawo daga aiki ba da daddare sai ta lalla6a ta saci hanya ba tare da Amadu ya ganta ba taje wurinshi kuma data je sun gaisa yake rakota gida karshe dae ta rokonshi tay wai don Allah duk in ya dawo da daddare kafin yaje gida ya tsaya ya kirata da layin gwaggo su gaisa yace mata a'a bazai kira ba tace to ya rink'a yi mata horn sai ta fito su gaisa sannan ya yarda ya rink'a yi mata hakan amman ba kullum ba.

Salla da sati ukku Hajiya ta dawo, sosae Fatuu tayi farinciki kaman ta zuba ruwa a k'asa tasha don tasan yanzu zata rink'a zuwa gidan duk lokacin da take so ba tare da an hanata ba, rayuwa taci gaba da gudana kaman da bayan dawowar hajiyar a haka har babbar salla tazo wannan karon gallelliyar shadda Haisam ya dinka ma Fatun tasha uban aiki wanda in ka kalla sai ka k'ara kallo don a Abuja aka yo mata d'inkin sai dae kawae taje part d'inshi ya bata ana saura kwana biyu salla harda takalma da gyalen da suka shiga da shaddar, sosae Fatuu taji dad'in dinkin ba kamar da yake kuma wannan sallar a nan zasu yi ta hakan yasa sai faman d'okin zuwan sallan take, ranar sallar tare suka je salla kaman k'aramar salla ana dawowa aka fara yanka ragunan layya harda na gwaggo wanda Haisam ya siya mata katon gaske, shima Haisam din yayi layyar kusan rago biyar aka yanka gidan hajiyar don tana raba ma mutane d'anyen naman sosae shima Haisam nashi guda biyun duk rabar dashi akai, washe garin sallar Tk ya tafi gida dama duk babbar salla gida yake tafiya, yan Abuja basu samu zuwa ba, dama ba kowace babbar salla suke zuwa ba wani lokacin sai bayan sallan suke zuwa to wannan sallan Senatorn da matanshi duka da wasu daga cikin manyan ya'yanshi sun tafi Hajji yayin da sauran kuma suka tafi Lagos wurin Hajiya Maryam sai bayan sallan ne zasu zo Katsina.......

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUH📲*_
~(Oumm Imam)~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


*6️⃣7️⃣*


........Sosae Fatuu taji dadin sallar don sun fita yawo da haisam duk da bai biye mata ba na iya rana d'aya kawae suka fita tare kuma yawanci gidan Abokanshi yaje da ita ciki harda gidan Abbas sosae Abdul da Feenah suka ji dad'in zuwan nata taci gayu da shaddar da yayi mata, shima Abbas d'in bayan sallan da kwana ukku ya kawo Feenah yini gidan Hajiya suka wuni tare da Fatun harda ma Haulat tazo suka gaisa ta kuma je gidansu Fatun suka gaisa da Gwaggo bayan Magrib Abbas yazo ya daukesu. Bayan sallah da sati biyu su Fatuu suka fara jarabawar gama junior secondary wato JSCE, Haisam yayi mata abubuwan graduation sosae su littattafai masu d'auke da hotonta da key holder, biro, handkerchief jotter gaba d'aya tafi kowacce d'aliba yin abubuwa don har Malamai ta raba mawa,ranar da suka gama yakama ranar laraba ne cike da farinciki ta dawo gida da yamma sam bata ji wahalar jarabawar ba ba kamar da yake tana da kokari kuma Haisam ya taimaka mata wurin koya mata abubuwan da suka shafi jarabawar hakan yasa tayi ta cikin sauki ba tare data ji wahalarta ba, tana shiga Gwaggo ta taso ta rungumeta cike da farinciki, bayan ta gama tayata Murna ta kuma yi mata Addu'oi ta nufi gidan Hajiya ba tare data cire uniform d'inba gwaggo na ta tsaya taci abinci tace sai ta dawo, can ma Hajiyar Murna ta tayata da Addu'a ita da Saude, bata dad'e da zuwa ba Haisam ya dawo tana jin k'arar bud'e mashi gate ta tashi da sauri ta nufi hanyar fita,yana fitowa bayan ya gama parking Motar ya hangota ta nufo shi hakan yasashi dakatawa har ta k'araso sai faman washe mashi baki take, shima Murmushi yake yace mata Congrats tace mashi tagode, bud'e baya yayi ya fiddo flower da card na fatan sa'a a jarabawar da tayi mai shegen kyau sai d'aukar ido yake ya mik'a mata harda Flower d'in, waro ido tayi alamar mamaki kafin ta amsa tana kallonsu d'agowa tayi ta kalleshi baki washe tace nata ne ya daga mata kai alamar eh ta hau yi mashi godiya, hannu ya kai ya d'aukko jakarshi kafin ya rufe Motar da sauri ta amshi jakar suka nufi part d'inshi, bayan sun shiga ya amshi jakar ya nufi hanyar Bedroom ita kuma ta zauna tana k'ara kallon abubuwan daya batan sai faman dariya take, mamakinta abunda take gani yan kasan waje nayi a Tv suba mutum kyautar flower yau shine itama akai mata dama ba k'aramin burgeta hakan keyi ba, tana ta farincikinta har bata san lokacin daya d'auka ba saidae ganinshi tayi ya fito cikin workout outfit yace mata suje part d'in Hajiya ta mik'e tabi bayanshi, suna shiga cikin Parlon ta nufi Hajiya tana nuna mata kyautar da Haisam din ya bata ta yaba sosae sai bayan daya gama cin abinci zai fita ne tabi bayanshi yana tafiya itama ta nufi gida. Washegari Alhamis da rana Fatun na kwance kan tabarma gwaggo na gyara mata kai ta sanar da ita cewa ta shirya kayanta ranar Asabar zasu tafi Yola gaba d'ayansu amman su zasu kwana biyu ita dawowa zatayi, sam Fatuu bata ji dadin Maganar ba ba kamar da gwaggon tace can zata baro su ita da Amadu har ce mata tayi to su dawo tare mana tace a'a ai tunda ta baro garin bata je ba don haka yakamata taje ta kwana biyu,
"To amman shi kawu Amadun ba yana zuwa Makaranta ba?" ta tambaya tana yamutsa fuska gwaggon tace "eh amman yace zai tambayi izini don shima yana son zuwan saboda ya kwana biyu baije ba, inaga ma da hankalinshi ai sau d'aya ya ta6a zuwa" turo baki tayi kawae ita dai har cikin ranta bata son taje ta wani dad'e, tana gama gyara mata aka fara kiran salla tace ta tashi tayi salla itama ta mik'e, can bayan sun gama sallan ne ta bata kudi tace tayi sauri taje ta siyo mata kuka da daddawa zata yi miya nata sun k'are sai taje kasuwa zata siyo, d'aukar hijab dinta data aje bayan ta gama salla tayi tasa ta mike ta nufi hanyar fita, tana fitan maimakon ta tafi aiken da akai matan sai kawae ta nufi gidan Hajiyar Sanata don taga in Haisam ya dawo, tana zuwa ta iske ya dawo amman bai cikin falon sanin kaman yanzu shirin zuwa gym yake yasa ta zauna kan carpet tana jiranshi sai faman kunci take, tana zaunen ya fito kallo d'aya yayi mata yasan akwae abunda ke damunta, gaidashi tayi bayan ya zauna ya amsa mata kafin ya tambayi abunda ke damunta kaman zatayi kuka tace "ba gwaggo bace....wai Adamawa zamu tafi ran Asabar kuma acan zata baro ni nida kawu Amadu wai sai munyi sati biyu zamu dawo" jingina bayanshi yay da kujera da d'an Murmushi akan fuskarshi yake kallonta yace "to ai ba wani abu bane u supposed to be happy instead, zakije kiga relatives naki especially ur beloved dad baki son ki ganshi?" tura baki tayi tace "inaso amman dae sati biyu yayi yawa ni banson ta baro ni can nafi son mu dawo tare" sigh yay gently yace "ai ba wani dad'ewa zaku yi ba 2 weeks is just like tomorrow da kunje zai yi ku dawo" d'aga kai tayi ta kalleshi kaman zatayi kuka tace "shikenan bazan rink'a ganinka ba har sai mun dawo?" fad'ad'a Murmushinshi yay dama yasan duk wannan damuwar saboda shi ne don ya lura bata son abunda zaisa ta daina ganinshi, hannu ya kai ya shafi gaban kanshi kafin yace "in kin dawo ai zaki ci gaba da ganina besides akwae vedio call ko" jujjuya kai tayi kaman zata yi kuka tace "to ai shi kawu Amadun ne fa ba lalle ya rink'a kira man kai ba yana iya hana ni wayan" shiru yay kaman yana tunanin wani abu can taji yace "ko in sai maki phone d'in?" a d'an rud'e ta kalleshi sai kuma ta fara girgiza mashi kai tace "Gwaggo bata son in rik'e waya yanzu ko ka siya man hanani amfani dashi zatayi, kasan miyasa?" ta bud'a ido girgiza mata kai yay alamar a'a, taci gaba "wai wata abokiyar aikinta ce wani saurayi yay ma d'iyarta wayo saboda ya siya mata waya yayi mata ciki kuma har ta haifi d'an shegen" bilhakki take bashi labarin shidae shiru yay yana binta da ido saidae sam bai ji komae ba don yanzu yama saba da halinta na ya6o Maganar da duk tazo mata, ganin yayi shiru yana kallonta yasa da sauri tace "bafa ina nufin kaima wayon zaka man ba kawae na fad'i maka dalilin dayasa bata son in ruke waya ne amman tace in zanje jami'a zata siya man da kanta ma" jinjina mata kai yayi yace ya fahimta zai rink'a kiran Amadun yace ya bata, amsa mashi tayi da to amman still ba don ranta na son tafiyar ba can tace "ko muje tare da kai?" d'age gira yay kafin yace "aiki fa?" tura baki tayi tace "to ai tunda ran Asabar zamu tafi kaga ba aiki sai ka rakamu ka dawo ran Monday kaga rana d'aya ne bazaka aikin ba" d'an Murmushi yay yace mata shima zai je Lagos gobe ne da mamaki tace "shine kuma baka gaya man zaka tafi ba ko wayo kaso yi man?" daga mata kai yay alamar eh yanata murmushi ta turo baki, shiru sukae na d'an wani lokaci tana ta jujjuya kud'in hannunta taji yace "ba an aike ki bane?" tana yamutsa fuska tace "eh wai kuka da daddawa zan siyo mata ita bata gajiya da yi mana tuwo wllh" Murmushi ya dan yi "ai shima abinci ne mai kyau" tace "to amman ai kai baka ci"
"Ina cin wani" ya bata amsa tace "na shinkafa?" yace "yeah and semovita" tace "itama miya baka shan mai daddawa ko?" wani kallo yay mata ba tare da ya bata amsa ba tasa dariya dama da biyu ta ambaci daddawar sarae tasan bai shan, tura baki tay tace "nima wllh na tsani miyan yauki mai daddawa hakanan nike sha" yace "kije ki siya mata in na dawo sai kizo kici dinner nan" da sauri tace "amman tare zamu ci na bankwana?" tayi Maganar tana jaddada mashi, Murmushin gefe yayi kafin yace ai zata dawo ko tace eh amman dae ai sai ta dad'e yace owk tazo sai suci tare daga haka ya mik'e itama ta mik'e suka fita,

Washe gari Friday bayan sallan Juma'a Haisam da Hajiya na cikin cin abinci Fatuu ta shigo tayi gayun juma'a, bayan ta gaishe su Hajiya tace tazo taci abinci tace ta koshi yanzun ta gama cin abinci tace bata yarda ba sai taci ko yaya ne tunda daga yau ai sai bayan wani lokaci ko, kujera taja ta zauna ta zuba d'an kad'an, Haisam ne ya fara tashi ya nufi cikin falon kafin fatuu ma ta mik'e tace ma Hajiyar ta koshi, kishingid'e ta iskeshi tana niyyar zama ya mik'e yace tazo suje ba tare da ta tambayi ina ba tabi bayanshi ya d'an daga murya yace ma Hajiya zasu je su dawo tayi masu adawo lafiya, parking space suka nufa ya fiddo Mota cikin harabar sannan Fatuu ta hau suka fice, saida ya tsaya adaidai gidansu yace taje ta fad'i ma gwaggo zasu je su dawo sannan suka wuce, Bayan tafiyarsu gwaggo ma ta fito ta nufi gidajen makwabta yi masu bankwana harda gidan Hajiya, saida suka hau hanya sosae sannan ta tambayeshi ya akai bai tafi Lagos d'in ba ko sai anjima yace mata ya fasa tafiya yau sai gobe tace sai yaga tafiyarsu kenan ya d'aga mata kai alamar eh, ganin suna ta tafiya ne yasa ta sake tambayarshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login