Showing 186001 words to 189000 words out of 212491 words
inda zasu yace mata bazata kai ma yan'uwanta tsaraba bane, jin haka yasa tace "tsarabar zamu je siyowa?" kai ya d'aga mata ta kuma cewa "to mi za'ai sai masu?" shiru yayi idonshi a kan hanya sai kuma yace "Biscuits, chocolate and so on" jinjina mashi kai tayi can kuma sai ta fashe da dariya tace "wayaga su Yaya na cin chocolate saniya kenan" d'an juyowa yay suka had'a ido nan take ta tuna da fad'an da ya ta6a yi mata na ba'a had'a mutum da dabba hakan yasa da sauri tace yayi hakuri, shiru yayi sai kuma ya tambayeta wacece yayar tace matar Ardo yace "Grandma d'inki kike ce hakan?" da sauri tace "ai ba itace kakata ba ni kakata ta rasu kuma sunanta ne ma aka sa man Fatee...." shiru tay bata k'arasa ba tunawa da sunan maman shi ne, jinjina kai yay yace "ai itama grandma d'inki ce ko" da sauri tace" Allah ya kyauta wannan muguwar ta zama kakata, kai baka santa bane bata da mutunci kuma ta tsaneni da ina can tai ta k'ala man sharri tana sawa ana buguna kuma har babana ma bata son shi saboda taga ardo yafi ji dashi haka lokacin da Mamata bata lafiya harda ita ta hana a kaita Asibiti da wuri" ta k'arasa Maganar kaman zata yi kuka, shiru yayi kawae matsalar kaima yaro abu kenan don kwakwalwarshi bata mantawa balle abu irin wannan ko babba ma bazai ta6a mantawa ba, juyawa yay ya kalleta ta kwantar da kanta da gani ranta a 6ace yake slowly ya kirata ta d'aga ido ta kalleshi yace "Do forgive her and forget everything" turo baki tayi yaci gaba "Allah ubangiji yana son bayinsa masu yafiya, don shima mai yawan gafara ne in dae ka sa6a masa ka roki ya yafe maka zai yafe maka so kema ki yafe mata ki manta don in kin rike abun zai dame ki ne" tura baki tayi batace komae ba har saida yace bata ji abunda yace bane sannan cike da shagwa6a tace "yanzu duk abunda tayi man sai kace in yafe mata......" katseta yayi "yeah in kin yafe mata Allah zai daga darajan kine kuma kema ai kina son ki laifi a yafe maki ko" da sauri tace "to ni wama na ta6a ma laif...." kasa karasawa tayi ta zuba mashi ido tana mashi kallon rashin gaskiya, ta cikin mirror ya kalleta suka had'a ido ya dan ta6e baki ganin hakan yasa tana tura baki tace "shikenan na yafe matan amman wllh indae nayi kudi zan kai kowa makka banda ita" d'an jinjina kai yay yace "baki yafe matan ba kenan" da sauri ta kalleshi "nace na yafe mata fa, ko kana nufin itama sai na kaita makkan?" kai ya d'aga mata alamar eh, wani kallo tayi mashi kaman zatayi kuka "yanzu duk abunda tayi man kuma sai kace itama sai na kaita Makkan" yadda tayi Maganar sai kace tayi kud'in kaisu makkan ne, cigaba da yi mata nasiha yay kan yafiya idonshi akan hanya har dae ta saukko tace to zata kaita makkan, wata supermarket suka je sosae ya jidar mata kayan zaki harda abubuwan wasan yara itama ya siya mata ice cream, bayan sun bar wurin zagayawa yayi da ita cikin gari tana shan ice cream d'in tana yi mashi fira k'arshe ya wuce da ita Gym duk da ba exercise d'in zaiyi ba don baizo da shirin yi ba, lokacin data je wurin Anah sosae tayi farinciki da ganinta harda ma sauran yan wurin wad'anda suka santa koda tace zata hau machine hanata Anah tayi mutane nata masu dariya sai gab da Magrib ya maidata gida, sosae gwaggo taji dadin tsarabar da yayo mata tasa Albarka da Addu'oin da ta saba yi mashi, Bayan sallar isha sai ga Hajiya tare da Saude wai ta k'ara zuwa bankwana, d'akin gwaggo suka shiga dayake akwae wutar Nepa, bayan sun gaisa suka shiga yin hira harda Fatuu data shigo ta gaishesu hajiyar na ce mata zatayi missing dinta Allah yasa kar in taje su ruketa su aura mata d'an Fulani Fatun tace da kuwa ta gudo wllh gaba d'aya suka sa dariya, suna cikin hiran tasa Saude ta bud'e ledar da ta ruko mai d'auke da kaya, atampopi ta nuna ma gwaggon tace gashi nan akai ma Yadikko da Fatuu ke yawan bata labarinta da kuma k'annenta su d'inka sai shaddoji suma tace na Baban Fatun ne da ardo sai kuma yayanta kamalu, saboda tsabar farinciki har gwaggo ta rasa wace irin godiya zatai mata sai faman washe baki take tana sa Albarka daga baya sukai masu rakiya da zasu tafi bayan sun k'ara yin bankwana da juna, Washe gari wuraren Karfe shidda na Asuba Haisam ya parker a kopar gidansu don kaisu tasha dama tun jiya ya kira Amadu ya tambayeshi lokacin da zasu tafin ya fad'i mashi yace zaizo ya kaisu, kiranshi yay a waya ya sanar dashi yana kopar gida aikuwa ba tare da 6ata lokaci ba Amadun ya fara fitowa da jakunkunansu Haisam ya bud'e mashi boot ya fara sakawa yana gamawa Gwaggo da Fatuu suka fito gwaggo na sanye da lace da Hijab kalar kwalliyar fulawoyin leshin itama Fatun lace d'in da Haisam yayi mata ne da k'aramar salla tasa ta yafa golden gyalenta da takalmanta masu madauri hannunta ruke da jaka sai dae sam Fuskarta ba walwala saida gwaggon tayi Addu'a tasa Fatun tayi don neman tsari sannan suka fito, Amadu ne ya bud'e ma gwaggon kopar baya ta shiga yace ma Fatuu ta zagaya ta shiga shi kuma ya koma ya kulle gidan kafin ya dawo ya bud'e gaba ya shiga, gaisawa sukae da gwaggon ita kuma Fatun saida suka had'a ido ta mirror sannan tace mashi ina kwana d'an Murmushi yay kafin ya amsa yana kokarin kunna Motar daga haka kuma yajata suka tafi, ktsta ya kaisu cikin sa'a kuma suka samu Motar da zata tafi direct Yola don da ta Kano zasu hau in suka je can sai su hau ta Yolan, yaron Motar da Amadu ne suka fiffito da jakunkunan daga cikin boot suka saka cikin Motar, bayan an gama kintsa kayan aciki aka nuna ma su gwaggo seats na biyun karshe akace nan zasu zauna shi kuma Amadu daga gaba inda maza suke, Godiya tayi ma Haisam ta k'ara mashi sallama yayi mata Allah ya tsare, shiga gwaggo tayi ita kuwa Fatuu k'in shiga tayi tay tsaye tana kallon Haisam daya jingina da Mota yana sanye da farar jallabiya shima idonshi na akanta yayi folding hannayenshi a kirji da dan Murmushi akan fuskar bai dai ce mata komae ba bai kuma kirata ba don ya lura abu kad'an take jira tayi kuka, daga cikin Motar gwaggo tace mata tsayuwar mi take yi ne wai bata shigo ba hakan yasa ta juya ta shiga, kiran Amadu Haisam yay ya fito yaje wurinshi, Mota ya bud'e ya shiga batare daya rufe ba ya kirgo kudi masu yawa ya mik'a mashi amsa yay tare dayi mashi godiya shi kuma yay mashi Allah ya tsare daga haka yaja kopar Motar ya rufe shi kuma Amadun ya koma Motar lokacin idon Fatuu na akan Haisam din ta dan lek'a kanta ta tagar Motar da yake glass din a bude yake, tada Motar yay lokacin kuma glass d'in kopar ya fara sauka kasa slowly d'an lek'a kanshi yay suka had'a ido da ita a hankali ya d'aga mata hannu itama a sanyaye ta d'aga mashi daga haka kuma yaja Motar ya tunkari gate d'in fita glass din yana komawa sama a hankali ya fice, tana ganin ya tafi ta kifa kanta a cinya bata d'ago ba har Motar ta tashi, sai Fatan Allah yasa a sauka lafiya,
Haisam na komawa gida shima ya fara shirin tafiya Lagos don da wuri yake son ya sauka saboda baisamu tafiya jiyan ba, Tafiya akace yankin azaba Fatuu saidae tay ta kalle kalle tay bacci ta farka wani lokacin har dan tsoki take ja in ta farka ta tambayi gwaggo sun kusa tace mata da saura gashi bunu bunu tace yunwa take ji duk garin da aka tsaya sai tasa an siya mata abun ci, lokaci bayan lokaci Mahaifin Fatun ke kiran Amadu yaji ya hanya da yake in suka sauka jimeta wani abokinshi ne zai daukesu ya kaisu rugar saboda shi bai nan yaje kasuwar wani gari, lokacin da suka sauka jimetan yamma tayi lis Fatuu ko Magana dakyar take yi ba 6ata lokaci wanda zai daukesu yazo don suna gabda sauka Amadu ya kira Baban Fatun ya sanar mashi, gab Magrib suka isa rugar wadda da ka kalleta zaka fahimci ruga ce ta ainihin fulani tun daga kan jama'ar dake kai kawo wad'anda ke sanye da shiga ta fulani mafi akasarinsu daga kiwo suka dawo, garin nada albarkar shuke shuke ba kamar da yake damuna ta fara kankama ko ina yayi luff da korayen ganyayyaki sannan yawanci duk bukkoki ne masu ginin k'asa basu da yawa an zagaye su da dannin kara, tunda suka shigo garin Fatuu tayi kuri tana kallon masu wucewa a amalenken shanu dayake anfi amfani dashi saboda akwae yawan yashi a hanyar, daidai gaban wani babban gida na ginin kasa Motarsu ta tsaya nan da nan kuma yaran dake a kopar gidan suka yo ma Motar caa da ido wad'anda ke a tsugunne suka mik'e amman ba wanda ya tunkari Motar haka mutanen dake a gefe kasan bishiya suna yin Alwala suma duk suka maido hankalinsu kan Motar dama anan kopar gidan daga can gefe inda ardo ke zama ake taruwa ayi salla, adan can gefe guda kuma akwae teburi mai d'auke da rake a samanshi wanda yayan Fatuu Kamalu ne ke saidawa, tunda yaran gidan wadanda suka san Fatun suka ji batun zuwansu suke ta zaryar zuwa kopar gidan dalili ne kawae ke maidasu cikin gidan ba kamar k'annenta, Amadu ne ya fara fitowa duk suka kura mashi ido don basu sanshi ba wanda kuma suka ta6a ganinshi sun manta shi yana fitowa Fatuu ta fito gyalenta a hannu itama dae idon suka bita dashi da alama itama basu ganetan ba wasu kuma wasiwasi suka fara acikin ransu ba kamar kanwarta Ameena da ake ce ma Mino wadda suke bala'en kama da ita don itama Babansu ta biyo kuma tafi kowa d'okin ganin Fatun don suna kaunar juna kuma lokacin da tana garin bata bari wani ya ta6ata in kuwa akayi mata wani abu sai ta rama mata amman fa ita tana dukanta in tayi mata ba daidai ba, tsaye sukae suna kallon kallon da ita, ita Fatuu ta ganeta ita kuma sai kokonton anya itace take a ranta, gwaggo ce tazo inda suke bayan ta gama yi ma mutumin daya kawo su godiya Amadu kuma yana firfito masu da kayansu,
"Ya aka tsaya ana kallon kallonne, Mino baki gane yar uwar taki bane" gwaggo ta fad'a cikin harshen fullanci, kallon gwaggo da tayi maganar tayi sai kuma ta maido idon kan Fatuu harararta tayi nan take ta gane itace ta saki wata uwar k'ara da fullanci take fad'in ga inna wuron sun iso hakan duk yaja hankalin mutanen wurin sauran yaran kuma suka watsa gida aguje don su sanar saiga Kamalu ya fito shima yana yanayi da Fatuun saidae ba sosae ba don yafi daukko kamannin mahaifiyarsu amman shima fari ne yana hangosu ya watsa a guje yaje ya rungume Amadu wanda yake matsayin babanshi kuma Abokinshi, ita kam mino ta kasa ma rungume Fatun saboda mamaki da kuma Al'ajabin yadda Fatun ta koma sai faman washe mata baki take kawae tana kare mata kallo daga sama har kasa fatun na mata Murmushi, wasu daga cikin mazan gidanne suka zo suna yi masu sannu da zuwa baka jin komae sai fullanci ke tashi yayin da kowa ke mamakin girman da Fatun tayi, ciki harda Yayanta Kamalu baki bud'e yake binta da kallo yana tambayar gwaggo wai wankan inji ta kaita akayi mata ne kuma mi take bata tayi girma haka ba kamar da yake takalma masu tsini ne a kafarta sun k'ara mata tsawo, ita dae gwaggo murmushi kawae take Fatun kuma na tura baki, Kamalu da wasu ne suka d'auki jakunkunan don shigar masu dasu su gwaggo suka rufa masu baya, Babban gida ne mai d'auke da gine ginen wasu gidajen aciki ma'ana yana da 6angarori sosae aciki don gaba d'aya a halin ardo na acikin gidan kowa da bangarenshi, suna shiga Yadikko da ta kosa su shigo tunda ta samu labarin isowarsu ta nufosu cike da farinciki tana masu maraba Mino dake ruk'e da hannun Fatuu ta nuna ma yadikko ita tana Fad'in taga yadda inna wuronsu ta koma, waro ido tay tasa hannu ta ruk'e ha6a alamar mamaki yayin da Fatun ke mata Murmushi buda mata hannu tayi bayan ta gama al'ajabin Fatun ta nufeta ta rungumeta cike da kauna da nuna kewa, saida gwaggo ta gama amsa sannu da zuwan da wadanda suka leko keyi mata sannan suka wuce ciki ita dae Fatuu ba kowa take tanka mawa ba saidae ta bi mutum da ido kaman yadda suma suke binta da idon fuskokinsu dauke da tsantsar Mamaki, koda suka shiga dakin wanda babbane ba laifi yana da shafen plasta amman ba fenti haka saman ma anyi ceiling irin na leda mai kyalkyali akwae gado babba mai rumfa sai kuma karami na katako yana da dan mirror mai dauke da tarkacen kayan shafa sai wardrobe mai gida biyu sai kuma cabinet mai dauke da jeren k'orai da kwalla da kwanoni jikin bangon d'akin ma anyi adon korai masu zane mai kyau da fayafai haka kasan dakin rufe yake da ledar tsakar daki akwae kujera mai mazaunin mutum ukku a gefe a samanta gwaggo ta zauna Fatuu kuma ta nufi gefen k'aramin gado ta zauna mino dai na gefenta sai faman kallonta take tana zabga Murmushi da gani ba karamin burgeta Fatun tayi ba, bayan sun k'ara gaisawa gwaggo ta mik'e don yin salla ita kam Fatuu kwanciyarta tayi koda gwaggo tace bazata tashi tayi salla bane cewa tayi sai ta huta bata iya tsayuwar sallan, bayan gwaggon ta gama saida tayi mata da gaske sannan ta tashi tayi sallan tana gamawa anan kan abun sallan bacci ya kwasheta, kan kace mi an cika d'akin da kwanoni da k'oran abinci dasu Fura da aka aiko ma baki ba yadda ba ai ba Fatuu ta tashi taci abinci amman ta kiya gwaggo tace su rabu da ita in taji yunwar sosae zata tashi ne, sai can bayan isha Mahaifin Fatun ya dawo cike da girmamawa ya duk'a suka shiga gaisawa da gwaggo dama shi Amadu sun gaisa dashi acan waje wurin Kamalu, sai lokacin gwaggo ta tada Fatun tace ta tashi to ga Baffanta ya dawo ai tana jin hakan ta mik'e zaune idonta akanshi shi dae sai faman Murmushi yake mata yadikko nace mashi ashe haka inna wuron ta koma da yake kwanaki da yaje bayan ya dawo yana ta basu labarin girman da tayi, bayan sun gama gaisawa ne gwaggo tace mashi yayi mata jagora zata gaishe da ardo, koda gwaggo tace mata tazo suje ta gaishe shi cewa tayi taje gobe taje ita yanzu yunwa take ji abinci zata ci hakan yasa ta rabu da ita, tana gama cin abincin lokacin gwaggo ta dawo tace ta watsa ruwa tafi jin dadin jikinta, bayan tayo wanka canja kaya tayi zuwa na bacci ta nufi d'akin Baffanta wai acan zata kwana da kyar ya lalla6ata yace ta dawo cikin yan'uwanta ta kwanta don sunyi kewarta sosae, saida ya rakota har kopar daki sannan ya koma maimakon ta shiga sai kawae tayi hanyar waje ta nufi dakinsu Kamalu dake acan soro lokacin tuni Amadu yayi bacci amman saida tasa aka tashe shi tace wai Ya kira mata Ya Handsome zata gaya mashi sun iso tunda da suna Mota ya kira ya tambaya, uban tsoki ya ja ya hau yi mata fadan tashinshi da tasa akai karshe rai 6ace yace bai kira tunda bai dade da yayi waya da Haisam d'in ba kuma ya sanar dashi sun iso lafiya don haka ta tafi ta bashi wuri, ba don taso ba tana kumbura baki Kamalu na mata dariya ta baro soron ta nufi cikin gidan dama don tasan gwaggo bazata bari ta kirashi a wannan lokacin bane yasa taje wurin Amadun.
Washe gari tunda safe ko karyawa bata yi ba ta kira Haisam d'in yayi mata ya gajiyar hanya sai faman washe baki take suka d'an ta6a hira har ta tambayeshi ya tafi Lagos din yace mata eh yana can daga baya yace taje tayi breakfast tace to anjima ya kirata Video call da wayar Amadu ya amsa mata da owk, lafiyayyan abun karin kumallo aka shirya masu irin nasu na yan birni duk da dama a gidan sunfi kowa yin lafiyayyen abinci irin na yan birni don shi dama sam bai abubuwan k'auyawa saboda mu'amala da yake da yan birni da kuma yawan zuwa birnin, daga wasu gidajen cikin gidan ma an aiko masu da abun karin kumallon, tare da mino Fatuu tayi kalacin sauran yan kannansu guda ukku kuma suna gefensu da yake yadikkon yaranta hudu Mino ce ta farko zatayi shekara tara zuwa goma, suna gamawa gwaggo tace ma Fatuu ta shirya taje ta gaida Ard'o dasu Yaya tace to sai tayi wanka mino zata rakata, fiddo kayan tsaraba da suka kawo gwaggo tayi taba yadikko tace a rarraba kafin ta fito da sakon Hajiya ta bata, kasa rufe baki yadikkon tayi saboda tsabar farinciki tana fadin su basu Gajiya da alheri ne su dama ba'a sansu ba amman aka biyosu da abun arziki haka, dama tasan labarin hajiyan da haisam lokacin da Baffan Fatun yaje sosae take ta godiya kuma da hausa suke magana da gwaggon don tana jin hausa sosae sai jefi jefi suke canza harshe, fiddo kayan da ta tattaro na Fatun ta kawo ma mino tayi ta bata sosae tayi murna don kaya ne da yawa k'arshe mik'ewa tayi tana tsalle farincikinta itama ta samu kayan da zata rink'a yin gayu kaman Fatun,