Showing 93001 words to 96000 words out of 212491 words
sai aka ce yayi kondem sai dae in sake wani,to yalla6ai kadae san yanayin rayuwar yanzu kudi basu taruwa in ba samunsu ake da yawa ba,lokacin banda wasu kudi da zan siya wani,a dole na hakuri naci gaba da noma wata yar gona da nike da ita acan kauyenmu to da amfaninta naci gaba da gudanar da rayuwata da ta iyalina,to matsalar da ance kaka ta wuce sai kaga anata fama,Amman dae Alhamdulillahi",
Jinjina kai Sp yayi"To yanzu ina ganin sai ka siya sabon injin din facin ko",
"Eh in sha Allahu abunda nike niyyar yi kenan,sannan akwae d'ana Habu yaron kirki ne,shi Allah yasa nutsattse ne ga hakuri,to yana da son yin sana'a tun ba yanzu ba,da ya samu yan kud'i sai kaga ya kafa trader a kopar gida bayan d'an lokaci kuma sai ta rushe saboda cinye mashi jarin da ake cikin gidan,to yanzu zan bud'e mashi dan kes sai azuba kaya sosae muga abunda Allah zai yi"fuskarshi d'auke da Murmushi ya k'arasa maganar,
"Ma sha Allah hakan yayi sosae,Allah yasa Albarka a duka kasuwancin,shi kuma dan'uwan nashi kaci gaba da yi mashi Addu'a kar ka gaji in sha Allah zai shiryu shima",
"Kullum acikin yi mashi Addu'a nike bama shi kadai ba,ina kuma da yakinin Allah zai amsa man wataran", jinjina kai Sp yayi"Allah ya amsa,yanzu zan baka kati na akwae lambar wayata ajiki tunda kaga ba waya gareka ba bamu san kudin ko sun shiga ba amman ina sa ran sun shiga ma,gashi baka tare da Atm card dinka da sai mu bincika awurin masu Pos,amman yanzu in ka koma gida sai ka daukko katin kaje a bincika aga in sun shiga,komi ake ciki sai ka sanar dani",
"To,to in sha Allahu,ai Habu ma nada yar waya in na koma sai in amshe ta in sa layina inga ko sun turo man sakon sun shigan kafin inje in siya wata nima",
daga haka suka yi sallama bayan ya amshi card d'in Sp yasa a Aljihun rigarsa,atare suka fito daga cikin Motar Sp ya tsaida masa Keke Napep ya biya masa kud'in,Mlm Garba nata faman cewa ya barshi ai akwae kud'in wayarsa daya saida sai ya biya cikinsu,Godiya sosae ya shiga yi masu shi da Haisam had'i da Addu'oi yana d'aga mashi hannu,har saida Napep d'in tayi nisa kana ya daina dagawa Sp hannu,daga haka Sp ya koma cikin Motar shi ya jata.
**** **** **** ****
Tun bayan da suka baro Police Station din ba wanda ya tanka ma wani a cikin su,idonshi na akan hanya yana ta driving yayin da Fatuu ta kwantar da kanta tana kallon gefen hanya,da ka kalleta zaka fahimci ba k'aramin Sanyi jikinta yayi ba,ta firgita sosae da jin abunda su Gaye sukai niyyar aikata mata,
A hankali Haisam ya juya ya kalleta,d'an Murmushin gefen baki yayi ganin yadda duk tayi laushi sai kace ba ita ta tak'alo Maganar ba,A daidai gaban wani Babban Shopping Mall Haisam ya parker motar,kallon inda suka tsayan tayi kafin ta juya ta kalleshi,
"Come out"Calmly yayi maganar kafin ya bud'e Motar ya fita,bud'ewa tayi itama ta fito ta yafa gyalenta asaman kai kallabin kuma na acikin Motar ta barshi,nufar cikin Mall d'in yayi ita kuma tayi tsaye bakin motar,
tsayawa yayi ya juyo"What are waiting for?" jin hakan yasata bin bayanshi suka shiga ciki,wurin shopping carts ya nufa ya turo guda daya ya dawo inda take tsaye tanata faman kalle kalle,
"muje"yace mata,wurin da Cosmetics suke ya nufa yana tsayawa wayarsa ta fara ringing,fiddota yayi daga cikin Aljihun rigarshi ya duba mai kiran nashi,kallon Fatuu yayi"ki fara selecting perfumes ina zuwa"daga haka ya juya ya nufi hanyar fita waje,
After few minutes ya dawo,tsaye ya isketa a inda ya barta bata saka komae cikin cart d'in ba,wani kallo yabi ta dashi fuska a d'an daure yace"baki ji mi nace kiyi ba kafin in fita ne?",
ta6e baki ta fara tana d'an jujjuya kai"to ni ai bansan wanda zan d'auka ba,bana ce maka irin na kwalbar fiya fiya muke amfani dashi ba,sai irin wanccan d'an dogon(body spray) shima gwaggo na siyo shi,kuma ma ni banta6a zuwa irin wurin nan ba a TV kawae nike gani",tana kai Maganar kwallah suka zubo mata sharrr,dama tunda ta fara Maganar idonta ke cike tab da kwalla,ahankali ta sadda kanta tana shessheka,still haisam yayi yana kallon ikon Allah, yanzu har yayi maganar da zata sa ta kuka ne?,
Sigh yayi cikin sanyin murya ya kira sunanta"Zaraah",amsa mashi tayi ba tare da ta d'ago ba,
"Zarah look at me",a hankali ta d'ago ta kalleshi,
"na buge ki ne??"ya tambaya had'i da d'age mata gira,girgiza masa kai tayi alamar a'a,
"to mi nayi da yasa kike kuka?"
Cikin Muryar kuka tace"ba kai man komae ba Yaya Handsome,kukan ne ke zuwa da kanshi",har lokacin idanunshi na a kanta,ya lura tunda suka baro PS ranta a dagule yake,da ka kalleta zaka fahimci akwae damuwa atattare da ita,
d'an matsawa yayi kusa da ita yace"is okey,mantawa nayi kin fad'a man,ki daina kukan",d'aga mashi kai tayi alamar toh daga haka tasa k'asan gyelenta tana share hawayen,
da kanshi yasa hannu yana za6o turarurrukan,sealed guda ukku masu kyau da tsada ya d'auka sai body spray shima guda ukku,roll-on biyu duk ya zuba a cikin cart din,d'an matsawa yayi saitin mayuka nan ma set biyu ya d'auka harda na Olive,kowanne Complete set d'inshi ya d'auka su Body Cream,lotion,hair oil and lotion,conditioner,shampoo,soap,shower gel da dai sauransu harda Mouth freshner spray ya saka,abunda zai baka mamaki shine ya iya za6en abubuwan mata masu kyau wanda ko wata macen yar gayu ba lalle ta iya za6arsu ba,alamu yayi mata na ta biyo shi,lafiya lou ta tura cart d'in don taga yadda wasu ke tura nasu kuma ko a tv ma tana ganin yadda ake amfani dashi,6angaren Underwear ya tsaya,d'an shiru yayi yana kallon kayan wurin kafin ya kai hannu ya ciro wasu yan rigunan bacci masu kyau da taushi,dogaye guda biyu sai mai had'e da wando guda d'aya ya juya ya zuba su cikin cart d'in,kallon kayan ya sake yi sai kuma ya juyo ya kalli Fatuu wadda gaba d'aya hankalinta na a wani wuri ta d'aga kai tana ta kallon wurin har gyalenta ya sauka daga kanta,kai ido yayi inda yaga tana kallo,6angaren da jallabiyu suke ne ta k'ura ma ido tana ta kallon rigunan,tana bala'en son dogayen riguna,in taga mace tasata ta nad'a gyalen ko a tv ne burgeta take ita kuma guda d'aya gareta wata Brown,saboda yawan sawar da take mata yasa tuni ta tsufa,gyalen rigar ma gurin guga ta k'one shi,
"Zarah"ya kirata,bata ji shi ba har saida ya maimaita kiranta da d'an karfi,firgit ta juyo ta kalleshi,hannunshi ya d'aga yana nuna saitin da undies d'in suke"in kina buk'atar wani abu anan ki d'auka"maida idonta tayi inda yake nuna matan,ai tana yin arba dasu bras da pants da sauri ta duk'ar da kanta kasa sai kace wadda taga wani mugun abu,zuba mata ido yayi yana kallon ikon Allah,ganin bata da niyyar d'agowa yasashi cewa"Don't u need anything?"d'aga mashi kai tayi da sauri,dan ta6e baki yayi hadi da d'an murmushin gefen baki,ashe tasan kunya ya ayyana a ranshi,gaba yayi abunsa bai dauki komae ba tunda tace bata buk'ata,har zai karya kwana ya juyo don yaji kaman bata biyoshi ba,aikuwa dai tana a inda ya barta har lokacin kanta na duk'e,
"zaki kwana anan ne?"d'agowa tayi ta kalleshi ya d'age mata ido hakan yasa ta tura cart d'in tabi bayanshi,6angaren da Jallabiyun suke ya tsaya,itama ta tsaya,
kallonta yayi yace"Choose d colours you want"zaro ido tayi,sai ta kalleshi sai kuma ta kalli rigunan,
"baki ji bane?"da sauri ta d'aga hannu ta nuna wata Yellow,kallon rigan yayi sai kuma ya kalleta ya d'an yamutsa baki da alama bata yi mashi ba kuma da gani tayi mata yawa ma,sake kallonta yayi sama da k'asa kafin ya kai hannu ya curo wata Maroon mai ratsin brown,ya sake ciro wata Black sai kuma Red colour su kenan colours masu kyau da zasu yi mata,daga d'an gaban jallabiyun ya daukko wasu riga da skirt pink color sun matukar had'uwa kayan shima kyau suka yi mashi,alama yayi mata su tafi tabi bayanshi sai da ya tsaya 6angaren su Sweets ya d'ebo wasu chocolate masu kyau ya watsa acikin kayan,daga nan suka nufi wurin biya,card ya bada aka cire kud'in wanda ba k'ananun kudi ya kashe ba don ko iya dogayen rigunan da riga mai skirt wata 50k ce ta tafi banda sauran kayan,kwashe masu kayan aka yi acikin wata katuwan Shopping bag mai d'auke da tambarin Mall din,d'aya daga cikin ma'aikatan ya bisu da ledan har mota,Back door Haisam ya bud'e mashi ya saka masu daga haka yayi masu Godiya ya koma,
ganin tana ta tsaye bata da niyyar shiga motan yace"Get into d car",
yamutsa fuska tayi tace"k'ishin ruwa nake ji" juyawa yayi ya kalli gefen Mall d'in,akwae wasu shaguna ciki harda na kayan sanyi,kallonta yayi"am coming"daga haka ya nufi shagon ta bishi da ido,bai jima ba ya dawo hannunshi ruke da leda ya mik'a mata kafin ya zagaya ya bud'e motan itama ta shiga suka bar wurin.
Har suka hau hanya sosae bata bud'e ledan ba Haisam da idonsa na kan titi yace"dama ba kishin kike ji ba kenan don ki wahalar dani ne ko?",
kallonshi tayi"a'a da gaske ina ji",
"So what are u waiting for da baki sha ba" a hankali ta bud'e ledan,bottle water ne had'i da babbar robar ice cream,fiddo ruwan tayi ta bud'e ta kafa baki tana sha,sai da tasha kusan rabi sannan ta cire robar daga bakinta ta rufe ta mayar da ita cikin ledan,shiru tayi sai ta kalli ice cream d'in sai kuma ta saci kallon haisam,can dai tasa hannu kaman mara gaskiya ta ciroshi,a hankali ta bud'e tasa d'an cokalin ta fara d'ebowa tana kaiwa bakinta,d'an juyowa haisam yayi ya kalleta aikuwa da sauri ta d'ago robar tana mik'a mashi,maida idonsa yayi kan hanya ba tare da ya amsa ba,
"mi zanyi dashi",ya tambaya,
"ka sha kaima",
d'an guntun murmushi yayi,
"baki ga ina driving bane....',
katseshi tayi"to in rage maka?",
waro ido yayi irin mamakin nan ya d'an k'ara kallonta kafin ya juya"ni bana shan saura ai"shiru tayi ta aje robar kan laps d'inta,ganin ta daina sha ya kalleta"ki sha abun ki,na k'oshi ne da zan sha"ya kai maganar had'i da d'an dage mata gira,jinjina mashi kai tayi taci gaba da sha a hankali.
A daidai kopar gidansu ya tsaya,tana ganin haka ta fara k'okarin bud'e motar,kallon ledan sauran ice cream da ruwan data aje yayi"kije dasu"ba tare da tace komai ba tasa hannu ta d'auka ta had'a da kallabinta da yar jakarta ta fita,har zata rufo mashi kopar yace"ki d'auki kayan baya",barin kofar Motar tayi a bud'e ta bud'e ta bayan ta kinkimo ledan ta dawo gaban tana k'okarin shigar da ita,ganin abunda take yi ya dakatar da ita"Zaraah,i mean ki shiga dasu gida naki ne",
waro ido tayi baki bud'e take kallonshi don ita tsakani da Allah bata yi tunanin kayanta bane ko da yace ta za6i kalar riga ta zata yana nufin ta za6ar mashi kaloli ne,
"ki d'auke ina son in tafi"yayi maganar ganin ta kafe shi da idanu,
Murya kaman zata yi kuka tace"to in Gwaggo tace ina na samo su fa?"wani kallo ya bita dashi jin wata tambaya mara kan gado da tayi mashi,
k'ank'ance ido yayi yasa hannu yana shafa beard dinsa"kice mata wani Mutum ne kika had'u dashi shine yaje dake inda ake saida su ya siya maki",
zaro ido tayi sosai cikin rawar murya tace"wani mutum kuma,ba kaine ka siya man ba",
harararta yayi"Oh ashe kinsan hakan kike tambayana,C'mon d'auke su ki shiga gida",jiki a sanyaye ta fiddo ledan kayan waje ta aje ta a gefe,dawowa tayi don ta rufe masa kopar,suna had'a ido tace"Nagode",kai kawae ya d'aga mata sai kuma yace"kisa sauran kayan aciki don kiji dad'in d'auka,
"to"tace ta rufo masa kopar da karfi,yin yadda yace tayi har ta nufi hanyar shiga gidan,ya kirata bayan ya sauke glass k'asa,aje ledan tayi ta komo bakin kopan tana kallonshi,
"U look worried,ki saki ranki in ba haka ba grandma d'inki zatai ta tambayan ki abunda ke damunki,ko kina son tasan abunda ya faru ne?",da sauri tace"a'a" jinjina kai yayi yai mata alamar ta tafi da hannu,tana kaiwa bakin kopan shiga zauren gidan ta aje ledan ta juya ta kalli haisam da har lokacin bai ja motan ba kuma bai rufe glass d'in ba yanata kallonta,suna had'a ido tayi mashi Murmushi shima Murmushin ya maido mata,tunda suka je PS har suka dawo sai yanzu tayi Murmushi,hannu ta d'aga tana mashi bye bye hakan yasa shima ya d'an d'aga mata hannun daga haka ta d'auki ledan ta shige,yana ganin ta shige ciki yaja motan dama a kunne take,bai wuce gida ba reverse yayi ya mik'i hanya don zuwa gidan Abbas.
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_
_*BY ZAINAB LALUH📲*_
_Barkanmu da Sallah,fatan kowa yayi sallah lpy,Allah ubangiji ya maimaita mana ya kar6i ibadunmu,Amin._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*4️⃣4️⃣*
Tana shiga cikin gidan gwaggo ta fito daga cikin d'akinta hannunta ruke da parker da alama shara tayi dama gwaggo ba dai tsafta ba in dai tana gida bunu bunu ta share wuri ko ya taga d'an dirty,fuskarta d'auke da Murmushi ta nufo Fatuu tana fad'in"Yan unguwa har kun dawo",kai fatuu ta d'aga mata alamar eh ta nufi cikin gidan ita kuma gwaggo ta nufi inda dustbin yake ta zuba sharan kafin ta dawo tsakar gidan,a tsaye ta samu Fatun agaban d'akinta,
tana zuwa inda take tace"to ki shiga cikin d'aki ki huta ko",ledar kayan ta nuna ma gwaggo tace"gashi",
bin ledan kayan da ido gwaggon tayi tace"minene?",
Shiru bata ba ta amsa ba,
duk'awa tayi ta bud'e ledan tana duba kayan ciki,idasa durk'ushewa tayi tana k'ara bincike kayan,kallon fatuu tayi"kayan wanene haka?",
K'yakkyafta idanu ta fara"wai nawa ne Yaya handsome ne ya siya man",
da mamaki gwaggo ta k'ara kallon kayan kafin ta kuma kallon fatuu"daman dashi ku ka fita ne?,
"Eh shi ya kaimu,to da muka dawo ne ya biya da mu kantin da ake saida kayan"ta k'arasa tana cigaba da kyakkyafta idanu,
jinjina kai gwaggo tayi"duk wannan uban kaya haka,kai Haisam ba dai kirki ba wllh,shima kaman hajiya yake duk kirki ne dasu ga yin Alkhairi,Allah ya saka masu suma da alkhairi,amman fa fatuu bansan rok'o,kar kiga yana maki abu kice zaki rok'e shi"tayi Maganar idonta akan fatuu,
da sauri fatun tace"Wllh gwaggo ban rokonshi,ko turaren da ya bani bana fad'a maki yadda akai ba,yanzun ma ban rok'e shi ba wllh,kinji na rantse",
jinjina kai gwaggo tayi"ai dama bance rokonshi kikai ba nasan halinshi sarai haka yake, to amman dae ko ba yanzu ba banson ki rokeshi abu kin ji,kuma idan ya maki abu ki rink'a mashi godiya",
amsa mata tayi da toh,
gwaggo tace"to yanzun wad'annan uban mayukan kinma san yadda ake amfani dasu kuwa"fuskarta da fara'a tana kallon fatun ta fad'a,
Yar dariya tayi tace"ai ajikinsu duk akwae sunayen kona miye da yadda ake amfani dasu in na karanta zan gane"gyad'a mata kai gwaggo tayi kafin ta kuma cewa"to ki kwashe ki kai d'aki,an dae gode wllh da gani ba kudi yan kad'an ya kashe ba,ji rigunan nan masu kyau dasu,to koma kibar su sai Sallah",
turo baki tayi"ni dae so nike in sa,in sallan tazo ba sai kiyi man ba",d'an girgiza kai gwaggo tayi"don kawae baki son na huta,kud'in dinkin ba sai a siya wasu abubuwan ba",cike da tsokana gwaggon ke mata Maganar,
"To zan aje guda d'aya,ai dae na rage maki ko,kuma in ban sawa ai kinga zai gani ko",
Dariya gwaggo tayi"To shikenan mai wayau,nima wasa nike maki",
dariya fatuu tayi,gwaggo tace ta kai kayan daki,
"to gwaggo baki dau komai ba",
mik'ewa tayi tana fad'in"to ni mi zan d'auka anan wannan duk sai ke,sai dae ko turare kuma tunda suna a gidan in ina buk'ata zanyi amfani da su",
amsa mata tayi da to,daga haka ta d'auki ledan kayan ta nufi d'akinta dasu,har ta kusa shiga gwaggo ta tsaida ta,
"Fatuu ki d'ebi ko kayan shafanne da turare ki kaima Haulatu",
"To daman zan d'ibar mata" ta bata amsa daga haka ta shige cikin dakin,
Lokacin da ta shiga cike da Murna ta fad'a saman gadonta,da duk damuwa ta hana tayi murnar,sai faman Murmushi take saki,zazzage kayan tayi saman gadon tana sake dubawa,sai faman sambatu take tana yaba kirkin haisam,saukkowa tayi ta fara kokarin gwada rigunan,ba k'aramin kyau suka yi mata ba,sun hau da fatarta sosae gashi duk sunyi mata daidai sai kace ya gwada mata ne kafin ya za6ar mata,guda d'aya ce bak'ar ta d'an so yi mata yawa itama ba sosae ba,data sa takalmi mai tudu zatayi mata daidai kuma ita ta yanke shawarar bari sai sallah don ta had'u sosae har wani d'aukan ido take,duk wadda tasa sai taje ta nuna ma gwaggo,cike da farinciki gwaggon ke yabawa don ba karamin dad'in kayan taji ba,kowa na jin dadi in yaga anyi ma nasa,ba kamar fatuu yar lelenta,
**** **** ****
Ranar Lahadi Misalin k'arfe ukku na rana haisam ya shigo cikin parlon Hajiya bakinshi dauke da sallama,hajiya dake zaune saman 3-seater ta d'an kishingid'a idanunta sanye cikin gilashi ta amsa mashi, juyawa tayi tana kallonshi har ya k'araso,agefenta ya zauna yana mata murmushi,itama murmushin take mayar masa,
"Yau ba aikin latse latsenne naga ka fito"d'an kwantar da kanshi yayi"yea,ai gobe zanje Office",
"Haka fa tunda kasamu sauki,Allah ya tsare gaba",can k'asan makwoshinshi ya amsa "Amin",
shuru sukayi na d'an lokaci,to break the silence hajiya tace"ko akawo ma wani abu ka dan ta6a?",
d'age mata gira yayi"not too long naci fa abinci",
"Eh ai dama ba abincin nike nufi ba d'an abu mara nauyi haka da zaka d'an tauna",lumshe mata ido yayi nan take ta gane abunda yake nufi,Saude ta kwala ma kira ta bata umarnin kawo abun da zasu dan tauna,bada jimawa ba ta kawo masu meatballs cikin plate da fork hajiya ta amsa,tana k'okarin kinkimo sofa table hajiya ta dakatar da ita tace taje kawae,a tsakiyansu ta aje