Showing 114001 words to 117000 words out of 212491 words

Chapter 39 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

979

kace man baka da Budurwa ko" ta k'arasa tana tura baki tana yi mashi wani kallo irin ya raina mata wayon nan,

Murmushi yayi yace"Who told u dat?" tana tura baki tace"ba gashi nan kace mata Sweethrt ba kuma tayi maka..." kasa k'arasa Maganar tayi tana guntse dariya,shiru yayi yana kallonta still da Murmushi afuskarshi,ita kuma sai faman guntse dariya take,

Sigh yayi"ai wannan duk wanda ka damu dashi who is important to u zaka iya ce mashi hakan ba sai wanda ake Soyayya dashi ba" daina yin dariyar tayi tace"da gaske?" gira ya d'aga mata"yeah,kaman Grandma d'inki da Uncle d'inki duk zaki iya ce masu hakan is normal",cike da mamaki tace"ashe ba dole sai wanda ake Soyayya ba?"kai ya d'aga mata kafin ya kuma cewa"Mutum mai kirki ma zaki iya ce mashi hakan,kaman wanda yayi maki wani abu kika ji dadi" zaro ido tayi "to kuma in Namiji ne kada yayi tunanin sonshi nike fa",hannu yasa ya shafi forehead dinshi"ai zaki ce ne yadda zai fahimta kaman kice,u're such a Sweethrt"dariya tayi tace"Ya Handsome u are such a Sweethrt" shima dariyar yayi har hakoransa suka bayyana ya furta"thanks,har kin gama fushin dani kenan" turo baki tayi"ai na kyaleka kaci gaba da cin abunda ka saba",

"Kin daina damuwa da Ulcer zai kamani na mutu kenan" d'an yamutsa fuska tayi"to ai tunda su ka saba dasu kilan kana koshi ko,kuma koma na matsa ma ba bari zakai ba" ta k'arasa da sigar shagwa6a,d'an ta6e baki yayi kafin ya kai hannu ya d'aukko sauran cake din da ya aje agefen Laptop,har yakai baki zai gutsira suka had'a ido hakan yasa ya dakata don baida sauranshi da zai bata,mik'a mata yayi ta kalli cake d'in ba tare data amsa ba hakan yasashi cewa"take"maimakon ta amsa d'in sai ta turo mashi baki tace"Nima bancin sauran wani",
waro ido yayi lokaci guda ya gane Magana ta gaya mashi,wato abunda ya fad'i mata rannan data bashi ice cream acikin motane itama ta gaya mashi yanzu,ganin yadda yake kallonta yasata fashewa da dariya tana rufe bakinta da hannunta,aikuwa baisan lokacin da ya dauki throw pillow dake a gefenshi ba ya jefa mata a fuskar,dukar da fuskar tayi tanata dariya kitsonta ya zuba yaraf akan kujeran,still yayi yanata Murmushi shima,can ta d'ago ta mik'a mashi hannu alamar ya bata,shiru yayi yana kallonta kaman bazai bata ba sai kuma ya mik'a mata ta amsa tace"thank u Sweethrt ya Handsome"dariya yayi ya d'an girgiza kai kawae ita kuma ta fara cin cake din,

"Mi yasa kike fitowa haka,where is ur headtie?" yayi mata tambayar had'i da dan kwantar da kanshi jikin kujeran,sai lokacin ta tuna da abunda ya kawo tan,baki cunkushe da cake tace"ba kawu Amadu bane ya biyo ni zai bugeni shiyasa ban koma na daukko kallabin ba",
"Mi kika yi mashi?" idasa cinye cake d'in tayi sannan ta fad'i mashi abunda ya had'a su,idonshi akanta yace"har yanzu kina rashin kunya ko Zarah!"ta6e baki tayi kaman zatayi kuka"to ya kasa yi mun kuma maimakon ya barni inji da abunda ya isheni sai yake ta man maganganu ni kuma naji haushi bansan lokacin dana fad'i mashi hakan ba wllh kaji na rantse,amman bazan k'ara ba" ta k'arasa maganar tana d'age baki had'i da jujjuya kai alamar nadama,still yai yana kallonta ya d'an 6ata fuska,ita kuma sai sussune kai take,

Sauke ajiyar zuciya yayi yace"Let me see d Assignment " aikuwa da sauri ta juya gefenta ta d'aukko littafin,mik'a masa tayi bayan ta bud'o daidai inda tambayar take,hannu yakai ya amshi book din,
"Wai wannan tambayar za'a fidda kuma ga amsar da yake so asamo nan a k'asa wai in batayi irinta ba to ba'ayi daidai ba",shiru yayi yana kallon Assignment d'in can k'asan mak'oshinshi ya furta" CALCULUS" janye littafin yayi ya kalleta da mamaki"Ajin ki nawa kika ce ma?" da sauri ta bashi amsa"Js 3 nike kuma ban dade dana shiga bama" d'an jinjina kai yayi ya k'ara d'aga littafin yana sake kallon question d'in,yasan lissafin sosae tun yana 100lvl yake yinshi,yana da wahala amman awurin wasu don shi lokacin yana degree d'insa na farko yana koya ma mutane shi sosae wadanda basu ganewa in akayi masu,yayi mamakin ganin tana js 3 an bata shi, dama a Senior Secondary take anayinshi a Further math ga wad'anda suke yin Subject d'in shima kuma wanda ake yi masun introduction ne ba'a nitsa masu can ciki don lissafi ne mai rikitarwa sosae gashi yana da yawa,

"Mi kika yi aka baki wannan Assignment d'in?" ya tambayeta fuska a d'aure,nan ta fara inda inda tana zaro ido ba abun tayi mashi karya ba don ta fahimci ya gane laifi tayi,
"Am asking u Zarah!" ya d'an yi mata tsawa aikuwa a rud'e ta fara kora mashi bayani bata 6oye mashi komai ba,tana gama fad'i mashin kwalla suka zubo mata sharrr,shiru yayi baice mata komae ba,a zahiri ta wani 6angaren tana da gaskiya yadda ya rikesu tsawon lokaci dole su gaji kuma dama lissafi in rana tayi ba kowa ke fahimta ba shiyasa mafi akasari aka fi sa period dinshi da safe,ko kuma ana dawowa break kaman yadda tashi take sai kuma ya had'e masu da double periods d'in malama dole ma su gaji ai,matsalan yadda Fatun tayi Maganar dole zaiga tayi mashi rashin kunya,

"Ke kad'ai ne ajin?" haisam ya tambayeta,girgiza mashi kai tayi idanunta sunyi rau rau,
"Ke kika fi kowa rashin kunya kenan", da sauri ta k'ara girgiza kan tace"a'a wllh nifa bada niyyar rashin kunya nayi Maganar ba,kawae gaskiya na fad'i mashi don ya sani"shiru yayi yana ta kallonta fuskarshi still a d'aure hakan yasa ta sunnar da kanta k'asa tana ajiyar zuciya,
Sigh yayi"as from today,i don't want u to dat again,ba ko ina mutum keda right na ya fad'i abu ba koda yana ganin yana da gaskiya hakan na iya zama ma mutum matsala like it happens to u now,ki koyi yin shiru understand?",
da sauri ta d'aga mashi kai"to ya Handsome wllh bazan k'ara ba",jinjina kai yayi yai shiru yana d'an tunanin yadda zai solving mata don lokacin Sallar la'asar ya riga yayi gashi sai dae ya hakuri da zuwa gym don ko zata fahimta sosae har ta yi bayani a aji sai an d'auki d'an lokaci,ana haka aka fara kiran sallar la'asar mik'ewa yayi tsaye yana gyara rigarshi Fatuu ta d'aga kai tana kallonshi,

"Zanje sallah sai na dawo zan nuna maki yadda yake",jin haka yasa lokaci guda ta saki Murmushi,hanyar Bedroom dinshi ya nufa yana shigewa ta hau yin murna tana bubbuga kujeran kaman sabon kamu, bayan wani lokaci ya fito lokacin ta natsu har ta kwanta ma asaman kujeran,tana ganinshi tayi saurin mik'ewa zaune yana zuwa zai wuce yace"ke bazaki sallan bane?"tana kallonshi tace" to ai banda Hijabi"
"Kije wurin Hajiya sai kisamu kiyi sallan inna gama zanzo nan" amsawa tayi tare da mik'ewa tabi bayanshi,

_________________

Lokacin data shiga parlon hajiyan ba kowa aciki hakan yasa ta nufi dakin Saude don tasan Hajiyan Salla take,da sallama ta shiga cikin dakin lokacin Sauden na niyyar tada salla,juyowa tayi ta kalli bakin kopan shigowan tana ganin fatuu ta saki Murmushi,
"Fateema ce"
"Eh Aunty Saude ina yini"
"Lafiya lou ya Makaranta an dawo ko",
" Eh,Don Allah hijabi zaki ban zanyi salla",amsa mata tayi da to ta nufi wardrobe din bango ta d'aukko mata wata wadda take tunanin bazata yi mata yawa ba sosae ta aje mata agefen Katifarta don fatun ta riga ta shige toilet.

A tare Haisam da Hajiya suka shigo parlon sai kace tare suka je masallacin,yana ganinta ya sakar mata Murmushi ya nufeta,hannunta ya kamo suka nufi kujera 3 seater ya zaunar da ita kafin shima ya zaunan,
"Sai yanzu kaga damar shigowa bacin tun d'azu kana gidan nan" yana niyyar bata amsa Fatuu ta shigo cikin parlon ta nufi kujera one seater ta zauna tana yima hajiyar Murmushi,
"Ke kuma yaushe kika shigo?" gaidata ta fara yi kafin tace"da aka fara salla",
Kai hajiya ta d'aga sai kuma tace"yau baki zuwa islamiyya ne kuma ina kallabinki?"amsa ta biyun ta bata tana tura baki"ban zo dashi ba,kawu Amadu ne zai bugeni shine na taho haka"
"Laifi kikai mashi ko" shiru bata ba ta amsa ba hakan yasa Haisam fad'i mata laifin data yi mashi,girgiza kai hajiya tayi"Fateema hoo,baki dai daina rashin ji wllh,Allah ya shiryeki"maida kallonta tayi kan haisam tana yar dariya"kace yau ba zuwa d'aga karfe kenan,yar gidanka ta jawo aiki,Allah ma yasa kai ka iya ai da tasha punishments ja'ira"ta k'arasa idonta akan Fatuu tana dariya itama dariyar tayi tana sunna kai k'asa,
"Ko har kayi mata ka fitan?" hajiya ta tambaya jin baice komae ba,
"No,we need enough time,zanje Gra after magrib sai inyi acan", kai hajiya ta d'aga"wannan abu dae shima kaman shaye shaye yake ace dole sai mutum yayi zai jishi daidai ya zauna lafiya"wani kallo yayi mata ba tare da yace komae ba,
"a zubo maka Abinci ne ko yau ma yar gidan taka tasa kaci Abinci awurin aiki?"da sauri Fatuu ta d'ago ta kalleshi lokacin shima ya d'an kalleta suka had'a ido ta tura mashi baki,d'an murmushin gefen baki yayi ya janye idonshi Hajiya dai nata murmushi,

"Yanzu nagama cin abu,amman zanci bada yawa ba", Saude hajiya ta kwala ma kira,bayan ta fito ta bata umarnin kawo mashi Abinci,kallon Fatuu tayi tace" ko kema zaki ci?"kai ta d'aga mata alamar eh dama kuma bata wani ci abincin kirki ba,
"bi Sauden kice wai ta zubo harda ke acikin nashin sai kuci tare" amsawa tayi da to ta mik'e ta nufi kitchen d'in,shi dae Haisam shiru yayi bai tanka ba dama Hajiyar da biyu tayi hakan wai ko yaci sosae,bayan ta kawo abincin tashi Hajiya tayi ta koma saman 2 seater tace ma Fatun ta zauna sai su saka abincin a tsakiya,yin yadda tace tayi,ganin Haisam d'in idonshi na akan waya ahankali tace"Ya Handsome ga abincin"ba tare daya kalleta ba yace"ki ci" k'in ci tayi ta bishi da ido fuska a daure alamar fushi can ya d'an d'ago ya kalleta ganin yadda tayi yasashi d'an yamutsa baki ya kai hannu ya d'auki spoon d'in ya fara ci,sai lokacin itama ta d'auki nata cokalin ta fara ci,abun mamaki,in yaci sai taci,in ya tsaya sai ta tsaya itama,duk wannan abun hajiya dake kallo na satar kallonsu sosae abun ya bata dariya amman sai tayi kaman ma bata san abunda suke ba,ganin zata 6ata mashi lokaci yasashi aje wayar ya maida hankali kan abincin,ba 6ata lokaci suka kusa cinyewa ya aje spoon d'in tana niyyar ajewa ya wurga mata wata uwar harara hakan yasa ta idasa cinyewa,

Mik'ewa yayi "ki same ni can" yace mata daga haka ya fara k'okarin nufar hanyar fita daga parlon,
"Ba za'ayi anan ba nima in koya" Hajiya ce tayi Maganar cike da zolaya,
"Yana da d'an yawa we need to do it on board" ya bata amsa yana tafiya,mik'ewa Fatuu tayi tana niyyar d'aukar tray d'in da aka d'auro kayan abincin ta kai kitchen,
"Ki barshi za'a d'auke kije ya koya maki yamma na yi" amsawa tayi da to tana niyyar juyawa Hajiya ta kira sunanta,amsawa tayi tare da kallonta,

"Badai zaki daina rashin ji ki natsu ba ko Fateema!" fuska a Matuk'ar d'aure tayi Maganar, nan da nan Fatuu ta rud'e ta nufi gabanta ta duk'a"Don Allah Hajiya kiyi hakuri wllh na daina ko rannan saida Gwaggo ta fad'i hakan yanzu ba ruwana da kowa",
"Amman ai har yanzu kina rashin kunya ko tunda gashi kinyi ma kawun ki da Malaminku",idonta cike tabb da kwalla tace" shi Malam wllh bansan rashin kunya bane nayi tunanin gaskiya ce na fad'i mashi amman Ya Handsome ya man fada yace in rinka yin shiru,shi kuma kawu Amadu raina ne ya 6aci da baiyi man ba kuma yana ta yiman fad'a,amman wllh tllh kinji na rantse bazan k'ara ba",sauke ajiyar zuciya tayi"in kika k'aran fa mi zanyi maki?"da sauri tace"komi"jinjina kai tayi tace"tashi kije" mik'ewa tayi tana goge kwallan da suka gangaro mata ahaka ta fita daga parlon.......

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔


*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

5️⃣0️⃣

Lokacin da ta shiga parlon yana zaune saman kujera yana daddana Laptop d'inshi,yana ganin ta shigo ya mik'e,
"ki daukko Book d'in" yace mata yayin da ya nufi corridor d'in Bedroom,d'akin da Fatun ta ta6a zuwa yin fitsari ya tura ya shiga itama tabi bayanshi bayan ta dauko littafin da biro,d'akin kaman d'an Computer Lab yake duk IT tools ne aciki gaba d'aya d'akin zagaye yake da Desk,abud'e yabar d'akin ya tokare k'opar da kujera,Desk chair ya jawo ya nuna mata alamar ta zauna ta yadda zata iya kallon d'an madaidaicin whiteboard d'in dake manne a bango,wata drawer dake jikin desk ya jawo,marker ya fiddo ya dawo gaban allon ya fara yin rubutu,abun mamaki tambayar ya rubuta ba tare da ya duba littafin ba kenan har ya haddace tambayar,ak'asan tambayar ya rubuta Solution yaja layi kafin ya fara fidda mata tambayar a nutse yake mata bayani kai kace shi d'in Malami ne gashi ko Calculator bai dubawa da ka yake fidda komae ita dae tayi kasak'e tanata kallon ikon Allah,Abunfa ashe aiki ne ja,ashe sai anyi amfani da wasu formulas da wasu rules an gano wace tsiyace,kai ni dai bama ganewa nike ba balle in ma masu karatu bayani🤣,tambaya guda d'aya amman sai da ya kusa cika allon wai ahakan ma don yayi mata shi atak'aice ne yadda zata gane,lokacin daya fitar da amsar k'arshen kallonta yayi yace ta duba taga tayi iri d'aya da wadda Malamin ya bata, cike da mamaki tace"Kai Ya Handsome, kodae kaima Malami ne?kaga yadda kake yin bayanin wllh har kafi duka malamanmu iyawa ma" goya hannuwansa yayi a k'irji yana kallonta fuskarshi ba wasa yace"is dat what i asked u to do?" da sauri ta girgiza mashi kai ta bud'e littafin daidai inda Assignment d'in yake tana kallon amsar da malamin yace ta samo,d'agowa tayi ta kalli wadda haisam ya gano ta sake kallon ta littafin nata,cike da Al'ajabi ta d'ago tafin hannunta guda rufe da bakinta ta mik'e tsaye,wani tsalle tayi cike da farinciki tace"wllh tllh iri d'aya ne ba bambanci Ya Handsome, kai innalillahi....? "Sosae take washe baki tana dan d'add'aga hannuwa,

"Can u do it?"ya tambayeta, hakan yasa ta tsaya cakk jin yace zata iya yi,zaro ido tayi tana kallonshi ya d'age mata gira alamar amsarta yake jira,a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a,
"Baki da baki ne!"
"A'a,bazan iya yi ba don ban gane ba sosae" wata uwar harara ya wurga mata"taya zaki gane dama tunda attention d'inki bai anan"ganin kaman ransa ya 6aci yanata kallonta yasa ta duk'ar da kai,

"I will explain it one more time,idan baki maida hankali kika iya ba,ba k'ara maki bayani zanyi ba" ya yi maganar yana jaddada mata abunda yace d'in da marker din hannunshi,hakan yasa ta tattara dukkan natsuwarta guri guda ta goya hannayenta a kirji ta k'ura ma allon ido,su fatuu an natsu kaman duka kenan,goge wanda yayi akan allon yayi ya faro mata daga farko,a nutse yake mata bayanin dalla dalla kuma sau biyu yake fad'i mata abu kafin ya wuce gaba ahaka har ya sake fidda irin amsar da malaminsu ya batan,kallonta yayi yace akwae abunda bata gane ba tace ta gane,hakan yasa yace mata ta taso tayi mashi bayani kaman yadda yayi ba tare daya goge ba,tsayawa yayi ajikin bango ya goya hannayensa akirji yana kallonta ta fara yin bayanin kaman yadda yayi har tazo k'arshe,jinjina kai yayi ya nufi board d'in yasa duster ya goge ya bar iya tambayar daga haka ya nufi kujerar data zauna da farko ya zauna,mik'a mata marker d'in yayi yace ta fidda da kanta har saida gabanta ya d'an fad'i jiki asanyaye ta amshi marker d'in ta koma gaban allon,a d'arare ta fara fiddawa hannunta har Dan kerma yakeyi ganin hakan yasashi kiran sunanta ta waigo yace ta kwantar da hankalinta ta natsu zata iya,jinjina kai tayi ta juya taci gaba da solving a nutse har saida ta wuce rabi sannan ta kakare,tayi tayi ta tuna abunda zatayi agaba ta kasa,jiki a sanyaye kaman zatai kuka ta juyo ta kalleshi ga mamakinta sai taga yayi mata d'an murmushi don ba k'aramin kokari tayi mashi ba data kawo har nan d'in ma,daga inda yake ya tadata taci gaba ahaka yana d'an tada ita in ta kakare har tazo k'arshe,mik'ewa yayi ya amshi marker d'in ya sake yi mata bayani a wawware yadda zata gane sosae har kusan sau ukku yana maimaita mata sake gogewa yayi ya bata tayi shi kuma ya zauna,wannan karon a nutse ta fara fiddawa har ta samo amsar k'arshen,juyowa tayi asanyaye ta kalleshi ya d'aura kafa daya kan daya still hannuwanshi na goye a kirjin sam ta kasa karantar ko tayi daidai daga yanayin fuskarshi,ganin yak'i cewa komae yasa tasha jinin jikinta,

"Banyi daidai ba ko Ya Handsome?" murya na rawa ta tambayeshi,daga yadda yake yace"check your book"da sauri ta nufi saman Desk inda ta aje littafinta ta d'aukko shi ta dawo gaban allon tana duba amsar data samo da wadda Malamin Maths d'in ya bata,sai ta kalli cikin littafin sai ta d'ago ta kalli allon,wata uwar k'ara ta fasa ta daka uban tsalle kai kace zata ta6o ceiling d'in dakin ne,cike da farinciki ta fara fad'in"Wllh iri d'aya ne,nayi daidai...."sai faman tsalle take wutsiyoyin kitsonta na tashi sama suma,sai lokacin ya saki wani k'ayataccen Murmushi ya sauke hannayenshi daga kan kirjin ya d'an had'a tafin hannunshi ya tafa mata sau ukku kafin ya saka yatsun cikin na juna yana ci gaba da kallonta da d'an murmushi,(Jama'a wai Fatuu bata san ta fara girma bane wannan uban tsalle haka,yakamata team Fatuu kuyi mata karatun ta natsu fa😂),cike da murna tanata dariya duk dimples dinta sun lotsa sosae ta nufi haisam dake zaune yana kallonta,tana zuwa ta d'aga mashi hannu alamar su tafa,d'an bud'a mata ido yayi had'i da dage gira hakan yasa da sauri tasa bayan hannunta ta rufe bakinta,ganin yana mata wani kallo yasa ta sunnar da kai k'asa alamar taji kunya,

"Zarah!" taji ya kira sunanta,koda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login