Showing 141001 words to 144000 words out of 212491 words
ba alamun wasa tana niyyar k'ara magana ya dakatar da ita da hannunshi yace "Zarah kije karki late" tana jin hakan ta mik'e tana k'ara sautin kukan da take, shiru yay yana bin ta da ido lokaci guda yaji wani abu ya fara ratsa zuciyarshi mai kaman tausayi dama Haisam baison yaga mutum yana kuka don shi Mutum ne mai tausayi sosae ba kaman ita da ta kasance mace kuma ma yarinya saidae bazai iya yi mata yadda take so ba don alamu sun nuna inba hakan aka yi mata ba to bazata ta6a sabawa da azumin ba,
"Zaraah" taji ya kirata lokacin har ta kama handle d'in kopar zata bud'e, da muryar kuka ta amsa tace "Na'aaam",
" wait let me drop u" daga haka ya mik'e ya nufi bedroom dinshi, bai jima ba ya fito hannunshi ruk'e da Car key batare da ya cire sleeping dress d'inba, tana ganin ya fito ta juya ta fita, bayan sun fita daga gidan amota ya tambayeta inda Islamiyyar take ta fara kwatanta mashi, ba tare da sun d'au wani dogon lokaci ba suka k'arasa, tanata faman cin magani tace mashi ta gode kaman anyi mata dole, d'an Murmushin da bai bayyana kan fuskarshi ba yay a fili kuma sai ya tambayeta k'arfe nawa suke tashi baki kumbure tace 11:00 daga haka ta bud'e kopar Motar ta fice, lokacin da taje aji ta makara amman saboda azumi ake yasa ba'ayi mata komae ba, koda taje ta zauna bin ta da ido Haulatu tayi ganin yanayinta, bayan malamin dake ajin ya fitane ta tambayeta mike damunta kaman bazata fad'i mata ba, can da haulatun ta matsa matane ta fadi mata yadda Ya Handsome yasata yin azumin dole duk da bai zamar mata dole ba da kuma irin wuyar da tasha jiya ta k'arasa kwalla na zubo mata tana sa bayan hannunta tana gogewa, ita dae haulatu jinjina kai kawae tayi tace tayi hakuri amman acan k'asan zuciyarta ta masifar jin dad'in hakan don ita kanta ba k'aramin fama take da Fatun ba akan ta daure ta rink'a kai azumi amman sai tace ana wannan uwar ranar zatayi azumi bacin bai zamar mata dole ba wllh batayi don dama sam bata da jumurin yunwa in har kaga bataci abinci ba kuma tana jin yunwa saboda wani dalili to kuwa babban daliline, har aka tashi tana ta bak'in rai don har ta fara complain din yunwa ita dae Haulat d'an Murmushi kawae take, suna fitowa daga cikin islamiyyar ta hangi Motar Haisam, da farko tsaye tayi tana kallon bayan motar kaman bazata je ba saidai tsoronshi da take bazai bari tayi hakan ba kuma ko ba wannan bama tana buk'atar shiga motar don rana ta bud'e sosae, kallon Haulat tayi tace mata suje ga Ya Handsome can yazo daukarta, nufar Motar sukayi Haulat nata jinjina kirki irin na Haisam acikin ranta lokacin da suka k'arasa bakin motar baya haulat ta bud'e ta shiga haka itama fatun sa6anin d'azun da zai kawota agaba ta zauna don tasan baison ba kowa a agaba a zauna baya, yana sanye da Jallabiya fara sol ga d'an kamshi mai sanyi ba mai hawa kai ba na tashi had'i da ni'imtaccen sanyin Ac, suna zaunawa Haulat ta gaidashi tace mashi ya ibada ya amsa da Alhamdulillah ba tare daya kallesu ba daga haka ya tashi Motar Fatuu batace mashi komae ba, lokacin da suka zo center d'in gidansu tana ganin zai nufi gidansu tana tura baki tace gidan Hajiya zasu hakan yasa ya nufi can, bayan yayi parking d'in Motar a Parking Space Haulat tayi mashi godiya ya jinjina mata kai ganin fatun bata yi ba yasa ta d'an zungureta amman sai ta kalleta ta tura mata baki hakan yasa ta bud'e motar ta fita, tana shirin fita itama kamar ance ta d'aga kanta suka had'a ido ta cikin madubin gaban motar, ganin kallon da yay mata ne yasa da sauri tace "An gode" banza yai mata saima ya bud'e motar ya fita bayan ya rufe kopar ya nufi part d'insa, Haulat dake atsaye tana jiran Fatuu tabi shi da ido Allah kadae yasan mi take ayyanawa aranta,
Jin Fatun ta fito ne yasa ta maida kallonta kanta fuska ad'an daure tace "Wllh Fatuu baki san baki san mutunci ba, yanzun mutumin nan yaje har islamiyya ya d'aukko mu amman shine bazaki iya ce mashi angode ba sai ma wani tura baki kike ke ala dole yayi maki laifi daga abun arziki wanda inma kinyi ke zai amfana bashi ba",
" to ba nace mashi ba yay banza dani" ta fad'a tana d'an hararar Haulatun,
" To shi tsaranki ne ko ko ajeshi kikai da sai kingadama zaki ce mashin, kuma dayake tsoronki yakeji sai ya amsa ko" a tsiwace tace "dalla ni ki k'yale ni, Mutum na azumi ki wani cika shi da Surutu" daga haka ta nufi part d'in Hajiya, d'an girgiza kai Haulat tayi cikin ranta ta ayyana samun wuri, a fili kuma da d'an d'aga murya yadda Fatun zataji ta furta "Don kin samu yana kulaki ne ai, amman bari kija ma kanki bake kika sani ba" daga haka tabi bayanta,
Lokacin da suka shiga ba kowa acikin falon hakan yasa ta nufi d'akin Saude Haulat d'in tabi bayanta, lokacin da suka shiga Sauden na kwance tana hutawa don bata jima da gama gyaran gidan ba tana jiran ayi azahar ta fara aikin bud'a baki don ita ke yin na cikin gidan kuma ba laifi shima aikin yana da d'an yawa don ana yin abubuwa sosae don Hajiya na gayyato yan shan ruwa wani lokacin, da sallama suka shiga ta d'ago fuskarta da fara'a ta amsa, mik'ewa tayi zaune tace suzo su zauna ta nuna masu bakin katifa,
"Sai yau muke ganinki" Saude ta fad'a tana kallon haulatu da Murmushi, gaishe da ita ta fara yi kafin tace "ai ina zuwa amsar sadaqa ban dai shigowa nan d'in" jinjina kai saude tayi ta maida idonta kan Fatuu dake zaune fuska a d'an d'aure tace "Fateema ya azumin kinayi yau d'in ko?" kai ta d'aga mata kawae, taci gaba da cewa "in kika daure a hankali zaki ga kin saba" sai lokacin ta bud'a baki tace "amman ai wuya nakesha fa, ko jiya da akasha ruwa har amai nayi" ta k'arasa idanunta sunyi rau rau alamar kwalla, d'an Murmushi saude tayi tace "eh haka naji d'azun abakin Hajiya data kira gwaggonki, amman tace mata ai ruwa kikasha da yawa kuma dama ko babba ne yakai azumi yasha ruwa da yawa wani lokacin amai yake sawa, ki rinka shan d'an daidai daidai in aka kira sallar daga baya sai ki k'ara kinji" ta k'arasa Maganar ta sigar lallashi ita dae kai kawai ta d'aga mata, hira suka ci gaba da d'an ta6awa sai dae yawanci ita da haulat ne suka fi Magana ita kuma ta kwanta gefe guda,suna ahaka aka fara kiran sallar azahar lokacin Fatuu har tayi bacci, alwala suka yo suka kabbara sallah, bayan sun gama ne saude ta tada Fatuu itama tayi sallar, anyi arziki yau batayi rarrafen ba saidae d'an yamutsa fuska da take tana dafe ciki ahaka har ta shige toilet d'in, haulat dake kallonta ta girgiza kai afili tace " naga randa Fatuu zata saba da azumi",
" zata saba ne ahankali tunda gashi yau da kafafunta ta shiga toilet jiya ai rarrafe tayi" bud'a ido haulat tayi ta maimaita abunda saude tace sai kuma ta fashe da dariya tana fad'in Allah ya shiryi fatuu, saude da itama ke dariyar don abun ba k'aramin dariya yabata ba a jiyan ta amsa da Amin, suna zaunen saude tace zataje kitchen ta fara aiki haulatu tace bari tazo ta tayata suka fita atare bayan duk sun cire hijjaban suka bar Fatuu na yin sallah, Bayan wasu mintuna saiga haulat ta dawo d'akin lokacin Fatuu ta dad'e da gama sallar tana kwance kan abun sallar,
" ki taso mu tayata aikin tare zaki ji kin rage jin yunwa, dama in kana yin aiki baka fiye jin azumin ba" haulat dake tsaye akan Fatuu ta fad'a,banza tayi mata sai kace ba da ita take magana ba, har k'ara maimaita mata Maganar tayi amman ko ci kanki bata ce mata ba hakan yasa ta juya ta koma kitchen d'in, suna cikin feraye dankali da doya sai gata ta shigo fuskarta sam ba annuri ta kasa bacci saboda yunwa gashi kuma ta d'an damu da fushin da taga kamar Haisam yayi hakanne yasa ta fito ta d'anyi wani abu wai ko ta daina jin yunwar kamar yadda haulat tace, saude na ganinta tayi d'an Murmushi tace "masu azumi anzo taya mu ne?" kai ta d'aga mata alamar eh,
"To zo ki zauna kuci gaba nikuma sai in gyara cefane" ta fad'a yayin da ta mik'e don fatuu ta zauna saman kujerar, cigaba da feraye dankalin sukai tana yi tana d'an watsa ruwan dankalin a fuska Haulat dai nata kunshe dariya ita kuma tana harararta, bada dadewa ba suka gama Haulat tayi ma Saude sallama zata tafi gida sauden nacewa gashi ba'a gama komai ba haulat d'in tace ba komai, amman duk da haka saida ta bata lemun roba da fruit tai mata godiya tace ma Fatuu kawata asha ruwa lafiya daga haka ta tafi tana dariya ganin hararar da fatun ke mata ta d'aga murya tace ba ita ta kar zomon ba rataya aka bata.
Bayan tafiyar Haulat bada jimawa ba fatuu ta tambayi Saude karfe nawa tace mata ukku saura yan mintuna kad'an nan take tayi yar dariyar da duk ranar bata yi ba jin lokacin yayi sauri, ci gaba da taya sauden aiki tayi har tana ce mata taje ta huta tace ai lokacin baya gudu in ta kwanta, dama kuma Fatuu ba raguwa bace tana da zafin nama kawae azumine yasata tayi laushi, duk bayan d'an lokaci sai ta tambayi Saude karfe nawa yanzu kuma, da ta d'anyi aikin sai ta zauna ta huta in na tsayuwa ne, tana cikin yankan fruit da za'ai fruit salad aka kwad'a kiran salla cike da mamaki tace "kai, wai har la'asar tayi?" gyad'a mata kai Saude tayi tana yar dariya aikuwa nan take ta fara murna tana washe baki, ashe da sauran dariyar azumi bai k'arar da ita ba, bayan sunyi sallar la'asar ne saude tace taje gida ta taya Gwaggo aiki amman da ansha ruwa ta dawo susha ruwa tare tace to, dama ko ba wannan azumin ba agidan hajiya take wuni tana taya saude aiki don ita da wuri take farawa, gwaggo kuma sai yamma wani lokacin ma in aikin rana take tunda safe take yin rabin aikinta koma fi ta bar ma Fatun d'an wanda zata karasa, koda ta koma gidan bata kwanta ba aiki ta shiga taya gwaggo wanda hakan ba k'aramin mamaki ya bata ba don tayi zaton tana can baje bata iya ko mik'ewa ganin yadda ta tashi hankalinta da Asuba shiyasa ma bata yi niyyar kiranta ba sai ankusa shan ruwa tunda can zata fi shan iska, gab da kiran sallar Magrib sun gama komae fatun ma ce ke jera abubuwan shan ruwan asaman katuwar darduma hakan kuma ba k'aramin dad'i yay ma gwaggo ba, ba kamar da ta tambayeta kodae ta karya azuminne ta rantse mata da Allah bata karya ba tace to taje ta watsa ruwa kafin akira sallar, lokacin da tayo wankan ta fito wani nishadi ta rinka yi tanata washe baki sai kace ba Fatuu mai kukan azumi ba gwaggo dae sai girgiza kai take tana Murmushi tace taje ta samu kaya maras nauyi tasa ta amsa da to, yar shimi da wani dogon wando ta sanyo tazo ta zauna gaban kayan shan ruwan da ta jere kiran Salla kawai take jira, aikuwa bata dad'e da zama ba liman ya kwad'a kiran salla kaman don taji, da sauri takai hannu zata dauki jug d'in ruwan sanyi sai kuma ta tuna da abunda Ya Handsome yace na tasha abu mai dumi in zata iya hakan yasa ta aje Jug d'in ta janyo bokitin kunu ta kafa baki ta kurba kaman sau ukku sannan ta aje ta d'auki ruwan sanyin shima ta kafa baki saidae sam bata sha da yawa sosae ba sakamakon abu mai d'umi da ta fara sha kuma tajita tayi wasai cikinta daidai kuma bata jin wata kasala, bud'a baki ta fara hankalinta kwance sai ta janyo wannan ta d'an ci ta maida ta janyo wani ta tsakura tana ci har wani rawa take da kai ita kam gwaggo saida tayi sallah sannan tazo ta zauna alokacin shima Amadu ya shigo suka ci gaba da yin bud'a bakin atare yana tayi ma Fatuu tsiyar abunda tayi jiya sai faman kyalkyatar dariya take sai kace ba ita ba, bata cika cikinta sosae ba don tasan Saude zata aje mata kayan shan ruwa dama ko ba yanzu ba tana aje mata intaje sallar asham sai taci ko kuma bayan angama sallar shekaranjiya dae saboda ansata azumin dole da jiya duk bataje sallar ba,
Mik'ewa tayi ta d'aukko Hijab acikin d'aki bayan ta fito tace ma gwaggo ta tafi salla Amadu na fad'in shifa bai yarda da ita ba anya cikakken azumi tayi yau, lokacin da ta kai bakin kopar zaure ta juyo da karfi tace "Da kenan" daga haka ta fuce sunata mata dariya, Lokacin da ta shiga Falon Hajiya suna saman table ita da Haisam jin sallamarta yasa ta juyo ta kalleta banda haisam d'in, alamar tazo tayi mata da hannu hakan yasa ta nufe su ta tsaya agefen hajiya tace "Hajiyar Sanata ansha ruwa lafiya" saida ta cinye abunda ke bakinta sannan tace "Lafiya lou kema kinsha ruwan lafiya ko?" kai ta d'aga mata tana satar kallon haisam da bai ko kalleta ba yanata bud'a bakinshi a nutse,
" Ya Handsome barka da shan ruwa" ta fad'a a sanyaye don taga kamar yayi fushi da ita, hannu kawae ya d'an d'aga mata ba tare da ya ce mata komae ba hakan kuma ya tada mata hankali sosae,
" Zo ki zauna kici abinci dama saude ta ban labarin yau harda ke tayi aikin, naji dad'i sosae ki rink'a daurewa kinji a hankali zaki saba" a hankali ta amsa mata da to taja kujerar gaba ta zauna dama hajiyar facing d'in juna suke da Haisam d'in, cemata tayi ta zuba duk abunda take so daga haka ta mik'e tace bari taje ciki kafin a kira salla dama kuma ta riga Haisam zama shi bai dad'e da ya shigo ba, soyayyar doya da dankali ta zuba bada yawa ba sai farfesun yan ciki dake ta zuba uban kamshi, koda ta zuban sam sai ta kasa ci sai bin Haisam take da ido shikam tamkar ma baisan da ita awurin ba yana ta cin hadaddan chips din dake gabanshi ga farfesun kifi tilapia agefe,
"Ya Handsome" ta kirashi a d'arare, shiru bai amsata ba balle kuma ya kalleta yana ta cin abunda ke gabanshi a nutse,
K'ara kiran sunan nashi tayi aikuwa ya d'an juya ya jefa mata wani kallo da bata ta6a ganin yayi mata shi ba, nan da nan ta razana har saida tasa tafin hannu ta rufe bakinta, ganin hakan yasashi maida idonshi kan abunda ke gabanshi ya d'an kara ci kad'an kafin ya janyo wani luxury flask ya bud'e, hadaddan kunun gyad'a ne da yaji peak milk musamman shi aka had'a mawa don bai shan kunun tsamiya ko na kanwa, a glass cup ya tsiyaya kaman rabi kafin ya aje flask d'in ya maida marfinshi ya rufe, cikin aji yake d'an kurbarshi gwanin burgewa duk wannan abun idon fatuu na akanshi ta d'an kwa6e fuska kaman zata yi kuka yayin da take tuno da Maganar Haulat ta d'azun da tace bari taja ma kanta ya daina kulata da alama hakan ce ta faru kirjinta sai bugawa yake, tsam ya mik'e bayan ya gama sha ya rage d'an kad'an acikin Cup d'in, saida ya gyara rigarshi kafin ya nufi cikin Falon idon Fatuu a kanshi ta zaro su, tana ganin alamun fita zaiyi ta wani zabura ta mik'e kamar walkiya sai ganinta yay tasha gabanshi lokacin har ya fita daga cikin falon yana niyyar shiga harabar gidan, shiru yay yana bin ta da ido da yake akwae haske ya gauraye ko'ina kaman da rana, ganin hakan yasa ta kama kunnuwanta da hannayenta murya na rawa tace "am sorry Ya Handsome, don Allah kar kayi fushi dani" yadda tayi yaso bashi dariya dama gata ba wani tsawo ne da ita ba amman sai ya basar ya k'ara tamke fuska, cigaba da yi mashi magiya tayi har kwalla sun fara zubo mata duk tabi ta tashi hankalinta saidae baiyi mamakin hakan ba don yasan dama bata so taga anyi fushi da ita,
Kokarin bi ta gefenta yay don ya wuce tai saurin matsawa ta tare shi harda bud'a hannuwa alamun kar ya wuce, goya hannuwansa yay a k'irji yana kallonta daga sama har k'asa wata yar guntuwa da ita, acan k'asan zuciyarshi kuma mamaki ne ya cikashi don tanayi mashi abubawan da ba wani mahalukin da ya taba yi mashi, wannan daba yarjejeniya atsakaninsu bai tunanin ma zata ji shakkarshi balle harta aikata abu in ya bata umarni ya ayyana hakan aransa don ya gama fahimtar sam bata da tsoro,
"Don Allah kai man Magana" tayi Maganar kaman mai niyyar rushewa da kuka tana wani ta6e baki,
Sauke hannuwan yay ya zurasu cikin Aljihunan wandonshi kaman an masa dole yace "kin yi man wani abu ne?" shiru tayi tana kyakkyafta ido ta rasa mi zatace,
" baki man komai ba, nine nayi maki dana takura kiyi abunda bakya so but yanzu zaki iya yin yadda kike so i won't care anymore........."
ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCIππππππππππ08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu