Showing 174001 words to 177000 words out of 212491 words
gwaggo ta leka ta sanar mata zai tafi, fitowa tayi suka yi sallama yayi mata godiya tana fad'in haba ai ba wani abu bane duk yima kaine tunda ai anzama d'aya daga haka ya nufi hanyar fita tana mashi sai Allah ya kaimu Fatuu ta bi bayanshi suka fita tare, suna fitowa waje ya juya yace mata ta koma saida safe, har ya juya ta kirashi ya sake juyowa,
"In shirya gobe tunda ba islamiyya muje yawo?" ta tambaya tana d'an kare fuskarta da tafin hannunta guda, still yay kaman bazai ce komae ba sai kuma calmly yace "baki gajiya da yawo ne?" a ashagwa6e tace "ai to tun fa salla ban k'ara zuwa ko ina ba, kuma koda sallan ma ban gama yawon ba Tk din ya kwanta rashin lafiya kuma ma ciwon kaman na k'arya wllh don washe garin ranar da yace bai lafiyan na ganshi kan sabon mashin dinshi yaci gayu ya fita da nace ma gwaggo zanje mu idasa yawon tunda naga ya samu sauki sai ta hana ni" still idonshi na akanta slowly yace "ina zan kaiki?" watsa hannuwa tay "duk inda ka kaini" shiru yay yana d'an tunanin inda zaije da ita can ya tuna d'azun bayan ya iso sunyi waya da Abbas yake ce mashi ya kamata su kaima Najeeb ziyara don ya kusa barin kasar,
"Zaki je gidan Abbas?" da sauri tace "eh dama ban ta6a zuwa ba"
"Owk ask ur Grandma in ta barki zan kaiki..." tun kafin ya rufe baki ta katseshi "ai zama ta barni wllh",
"ki dai tambayeta, kuma bani nace ba" dariya tasa tana fad'in ai bazata yi mashi karya ba, ganin yana shirin juyawa yasa tace "to da yaushe zamu?" dakatawa yay "ba kince lokacin islamiyya tunda ba'ayi",
"Eh amman dai ba ina nufin da yamma d'in ba, mutafi tunda safe tunda bani zuwa makarantar boko saboda wannan satin aka koma kuma duk mutane basu zuwa" juyawa yay yana fad'in zai sanar ma Auncle d'inta time din da zasu fita, cike da murna ta d'aga murya tace "Thank u Sweetheart Ya Handsome d'ina" hannu guda ya d'an d'aga mata ba tare daya juyowa ba ta juyo da gudu ta koma cikin gidan, lokacin data shiga gwaggo ta kauda komae har ta shige d'aki hakan yasa ta bita cikin dakin ta sanar da ita zancen zuwa gidan Abbas don itama yanzu ta sanshi sosae, cewa tayi Allah ya kaimu kafin kuma tayi mata fad'a kan ta rage takura mashi tace to daga haka ta nufi d'akinta cike da farinciki.
Yana komawa part d'inshi ya zauna kan kujera ya kira Abbas, yana d'aga kiran ya hau yi mashi iskanci yana fad'in wai baisan lokacin daya dace ya kira mai aure bane, shidae d'an Murmushi kawae yay bayan sun gaisa ya kara yi mashi ya gajiya Haisam d'in ya sanar dashi game da zuwansu gobe shi da Zarah, sosae yaji dadi dama yana ba Feenah labarinta yace ma Haisam amman dae yini zai kawo ta ko yace mashi bai kaiga fidda time ba nan Abbas d'in yace ya kawo ta da wuri sai ya ci Abincin rana anan gidan tunda Hajiya bata nan kuma daga nan ma sai suje gidan Najeeb din ya amsa masa da owk, daga haka yai mashi saida safe Abbas d'in na fad'in bai bari suyi hira yace No baiso yayi mashi kora da hali daga haka yay rejecting call d'in Abbas nata kyalkyatar Dariya, sanin Amadu na shago lokacin yasashi kiranshi ya bashi sakon ya fad'i ma Zarah zasu fita around karfe 1:00 na rana cike da girmamawa ya amsa mashi da to, bayan ya katse kiran ya kira Fanan Vedio call ya hada a laptop dinshi dake kan c-table suka ci gaba da yin hira.
____________
Washe gari da safe lokacin da Amadu ya shigo d'aukar abun karin kumallo ya fad'i mata sak'on Haisam, cike da zumudi ta gama yin kalaci da sauri tayi aikin da zata yi tana gamawa ta fad'a wanka, ba 6ata lokaci ta fito ta nufi daki ta hau yin kwalliya, cikin kankanin lokaci ta gama ta zumbula wata yar doguwar riga mara nauyi saboda lokacin fitan baiyi ba, sam ta kasa zama sai tayi nan tayi nan ji take kamar ta matso da lokacin don gani take bai sauri, karshe dai data gaji sai tasa hijab ta fita waje wurin Kawu Amadu tace don Allah ya ara mata waya zata fad'i ma Ya Handsome wani abu jin hakan yasa ya bata wayar bayan ya kira mata layin nashi, tana jin ta fara ringing ta nufi zaure da sauri wayar kange a kunnanta, yana d'agawa cike da shagwa6a tace mashi ta shirya tun d'azun zaune take kawai ba abunda take yi don Allah yazo su tafi, shiru yay yana saurararta har ta gama sannan yace mata ba gaisuwa, da sauri tace au ta manta ya yi hakuri don Allah ta hau gaidashi yace baiso tunda saida ya roka, Magiya ta shiga yi mashi akan ya amsa sannan ya amsa gaisuwar yace ta jira shi zaizo yanzu, maida ma Amadu wayar tayi kafin ta shige gida da gudu don tasa kaya, cikin kankanin lokaci ta ci gayu da jeans da riga ta gyara gashinta ya zuba a gadon bayanta don har yanzu ba ai mata kitso ba, nan da nan ta koma kamar yar balarabiya, golden d'in gyalenta da takalma tasa don rigar nada adon flowers golden mai walwali agabanta, wow kuzo kuga Fatuu ita kanta data kalli kanta a d'an Mirror dinta saida tasa hannu ta rufe bakinta ganin fitinannan kyaun da tayi, da sauri ta juya ta nufi hanyar fita don ta gwado ma gwaggo gayun da tayi, tana fita ta fara kwala mata kira hakan yasa gwaggon lek'owa daga cikin kitchen dama bata dad'e da ta shiga ba don d'aura girki, sototo tayi tana kallonta da alamun al'ajabi akan fuskarta ita kuwa Fatun sai faman washe baki take tace "gwaggo kinga na zama kaman yar kasar waje ko",
"Ina zaki je haka?" ta tambayeta fuskarta a d'an daure hakan yasa Fatun dakatawa da dariyar da take yi tace "gidan Abbas da na fad'a maki Ya Handsome zai kaini jiya ko" canza harshe gwaggon tay ta fara mata fada sosae tana fad'in "saboda baki da hankali shine zaki fita haka kaman ba musulma ba, to ki koma ki canja sutura ba dai wannan ba!!" kwa6e fuska tay kaman zata yi kuka ta fara mata magiya tana fad'in a Mota fa zasu je kuma su dawo, shiru gwaggon tayi tana kallonta kafin tace to taje ta saka hijabi dogo Fatun tace ai bata da dogon hijab tace to kuwa dole ta cire kayan, tana shirin k'ara mata magiya ta daka mata tsawa hakan yasa ta nufi dakinta da gudu tana kuka, saman gadonta ta fad'a ta shiga rusa kuka kai kace wani abu akai mata, jin irin ihun da take mata ne yasa ta bita d'akin daga waje ta d'age labulan a kausashe tace wllh in bata yi wasa ba har fitan ma zata hanata ne tunda bata da hankali bata san daidai ba, jin Maganar gwaggo yasa ta tsagaita da kukan don tasan in ta k'uleta tsab zata hanata fitan, saukkowa tay daga kan gadon ta nufi wardrobe d'inta ta fiddo d'ayar atamfar da babanta yayi mata wadda bata sata ba da salla anyi mata d'inkin doguwar riga, bayan ta gama shiryawa tasa bak'in gyale da takalmi ta d'auki yar jakarta daga haka ta fita daga d'akin ta nufi hanyar fita, kaman zata wuce sai kuma ta tsaya a bakin Kitchen d'in baki kumbure tace ma gwaggon ta tafi kallonta tayi kafin tace mata adawo lafiya ta juya ta fuce daga gidan, tana fita Motar Haisam na tsayawa hakan yasa ta nufeta,bud'e d'ayan side d'in driver tayi ta shiga idonta cike da kwalla ta d'an kalli Haisam da shima yay adon k'ananan kaya sai fitinannan kamshi yake saki, gaidashi tay ya amsa yana kallon cikin idanunta,
"What's d problem?" ya tambaya yana kallonta, shiru ta d'anyi kafin cikin shashsheka tace "ba gwaggo bace saida naci gayu na da kayan da nike son sawa wannan riga da wandon da ka siya man awurin Aunty Zee d'innan tace wai bazan fita dasu ba sai nasa babbar hijab kuma ni banda ita duk hijabai na basu kai har k'asa ba" ta k'arasa Maganar kwalla na gangaro mata da gani ranta a 6ace yake sosae, still yay yanata kallonta ya d'an jingina kanshi jikin headrest ya kuma fahimci dalilin dayasa gwaggon ta hanata fita da kayan,
"Ko muyi cancelling fitanne?" taji ya fad'a, da sauri ta kalleshi ta girgiza mashi kai alamar a'a,
"But look at ur face taya zamu fita haka?" shiru tayi tana binshi da ido sai kuma tace ta bari tasa hannu tana goge kwallan dake zubo mata bayan ta gama ta kalleshi ba tare da tace komai ba, har zai tashi Motar ya dakata yace mata "ba kina da Abaya ba?" cikin rashin fahimta tace "ai tace sai wadda takai man k'asa kuma na fad'i maka banda ita" shaking head dinsa yay yace "i mean dogon riga"
"Jallabiya?" kai ya d'aga mata alamar eh tace tana da wad'anda ya siya mata,
"Akwae mai bud'ewa?" ya tambaya yana nuna mata da hannunshi tace "eh guda biyu na budewa in an zuge zip d'insu"
"Ok kije ki saka kayan sai ki d'aura dogon rigan sama" sai da yayi Maganar sannan ta tuna da yadda take ganin larabawa nayi a tv, da sauri ta amsa mashi da to ta bud'e kopan ta fita, lokacin data shiga gidan gwaggon bata cikin kicin bata bi ta kan nemanta ba ta wuce d'akinta, shaf shaf ta canza kayan jikinta zuwa riga da wandon ta bude wardrobe ta d'aukko Maroon jallabiyarta ta daura sai faman washe baki take, takalman data cire golden ta maida ta bud'e zip d'in rigan yadda za'a rinka ganin kayan ciki, har ta nufi kopa zata fita ta tuna da gwaggo hakan yasa ta rufe zip d'in tana fita suka yi kacibus da gwaggo ta fito daga dakinta, kallonta tayi tana ta washe baki ta k'ara ce mata sai sun dawo ta nufi hanyar fita da sauri gwaggon ta bita da ido har ta fice kafin ta d'an ta6e baki ta nufi kicin duk a tunaninta kaya ta dawo ta canza, tana shiga zaure ta zuge zip d'in sannan ta fita wajen tayi d'as da ita, tana shiga cikin Motar suka had'a ido ta washe mashi baki tana dariya, yar harararta yayi ta rufe fuskarta da sauri alamar kunya,
"rigimamma kawai" taji ya furta, cire hannun tayi ta kalleshi tana tura baki yaja Motar suka tafi........
ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,
ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
*Mallakin*
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
6️⃣5️⃣
.......A nutse yake driving d'in yayin da Fatuu keta kallon gefen hanya ta 6angaren da take can ta juya ta kalli Haisam ta kira sunanshi, d'age mata gira yay idonshi akan hanya tace "ka kunna mana waka" shiru ya d'an yi kafin yace mata babu wakar,
"To a wayanka fa baka da wak'oki?"
"Ba wanda kike so" ya bata amsa a takaice,
"To ka kunna mana radio k'ilan suna yin wakokin" ba tare daya kalleta ba yace "baki iya kunnawa bane?" jin hakan yasa ta kai hannu ta kunna radio d'in don ta iya, jin ba'ayin wak'okin yasa ta canja wani gidan radion nan ma wani shiri sukeyi d'an tsoki ta ja a fili tace "duk ma basu yin wakokin" har ta koma ta zauna ta tuno da sabon gidan radion da aka bud'e wanda kullum cikin sa wak'oki suke, da sauri ta kai hannu ta kamo shi aikuwa sai gashi suna cikin yin wak'okin Umar m sharif ana gama wadda ake yi aka sako wakar zan rayu dake, Murmushi Fatun tayi ta fara bin wakar kai kace ita ta rairata, tana cikin bi ta juya ta kalli haisam dake driving tace "Ya Handsome muma atare zamu cigaba da rayuwa har mu Mutu ko?" d'an Murmushi yay ba tare daya kalleta ba bai kuma ce komai ba hakan yasa ta cigaba da cewa "kaga tunda kana da bangarenka agidan Hajiya in kayi aure sai akawo maka Matarka nan in ka tafi aiki sai in rink'a zuwa ina tayata fira in kuma ta haihu sai in rink'a goya babyn ina yi mashi wasa" sai lokacin ya juyo ya kalleta da Murmushi suka had'a ido yace "ke bazaki yi auren ba kenan?" tace "zanyi mana, amman fa sai nazama likita" jinjina kai yay "zamu rabu kenan tunda zaki aure kema" yay Maganar yayin da yake maida idonshi kan hanya, tace "ai lokacin na fara aiki sai in sayi gida anan unguwar ko kuma tunda gidan Hajiya akwae k'aton fili sai nima abani in gina kaman naka ba shikenan ba sai muci gaba da yin rayuwa atare" d'an ta6e baki yay hadi da jinjina kai sai kuma yace "kyauta za'a baki ki gina kenan",
"Sai na biya? Ta tambaya ta d'an waro ido, d'aga mata kai yay alamar eh tace "to sai in biya tunda lokacin na fara aiki shikenan kaga sai mu cigaba da rayuwa atare tunda muna gida d'aya ko?" kai ya d'aga mata ta koma ta jingina bayanta a jikin seat tana ci gaba da bin wakar da ake, basu dad'e ba suka k'arasa estate d'in da Abbas yake, a gaban gate d'in gidan ya dakata ya latsa horn sau biyo sai ga Abbas d'in ya lek'o yana ganinsu ya shiga idasa bud'e gate din, yana gama wage masu shi ya kutsa kan Motar ciki, can gefe inda Motar Abbas take fake ya nufa, yana parker Motar Fatuu ta bud'e ta fito tana ma Abbas Dariya, shima dariyarce akan Fuskarshi ya nufeta yana fad'in "u'r highly welcome Mom Zarah" still dariyar ce a fuskarta bata ce mashi komae ba adaidai lokacin Haisam ya bud'e Motar ya fito,nufarshi Abbas yayi ya mik'a mashi hannu suka gaisa yana k'ara yi mashi an dawo lafiya, hanyar shiga cikin gidan suka nufa yayi ma Fatuu alamar ta taho, suna zuwa bakin entrance d'in yaron Abbas wato Abdul ya fito da gudu yana sanye da jeans da t'shirt ya nufi haisam yana fad'in "Oyoyo Baba zakee" haisam na ganinshi ya ca6eshi had'i da d'aga shi sama suna ma juna dariya ya saka hannunshi cikin sumar haisam d'in yana cakud'ata, sauke shi yay yana fad'in in ya lalata mashi gashi sai ya gyarashi Abdul d'in yace Mommyn shi nada Comb da yawa sai ya gyara mashi gaba d'aya sukai dariya harda Fatuu dake ta binsu da ido tana mamakin yadda haisam kema yaron don batai tunanin yana ma yara wasa har haka ba, juyawa yay ya kalli Fatun irin kallon rashin sani kafin yace "Baba zakee wacece wannan?" d'an kallon Fatun yayi yace mashi "wata rigimamma ce" waro ido yay ya kalli haisam yace "rigimamma irina?" gaba d'aya suka sa dariya haisam d'in ya kai hannu yaja hancinshi yace "ashe kasan kai rigimamme ne" kafin ya bashi amsa sai ga Feenah ta fito tana sanye da doguwar riga A shape ta atamfa tayi daurin dankwali mai kyau, fara ce saidae ba irin tas d'innan ba tana da kyau ba laifi kuma doguwa ce sam bata da jiki kana kallonta zaka fahimci wayyayar yar boko ce kuma haskenta Abdul din ya d'aukko harma ya fita fari amman sak da babanshi yake kama,
"Ni dae na gaji da jiran bak'uwar tawa ta shigo na biyo sahu" ta fad'a idonta akan fatuu tana mata Murmushi itama Murmushin take mata kafin ta gaidata, bayan ta amsa tace su shigo mana duk suka nufi ciki wanda madaidaicin falo ne daka shiga yana d'auke da duk wani abu da akan samu a falon yan gayu masu matsakaicin k'arfi, kujera ta nuna ma fatun tace ta zauna shi kam haisam tuni ya zauna saman 3 seater sofa Abdul na akan cinyarshi Abbas ma ya zauna agefenshi, gaida Haisam din ta shiga yi tayi mashi anyi salla lafiya duk da da sallan tayi mashi ta waya, bayan sun gama gaisawa Abbas ya nuna mata fatuu yace "yau dae ga Mom Zarah" Murmushi Feenah tayi tace "aikam H,zakee ya kyauta man ai da ya kawo man ita inata jin labarin Mom d'inmu ba tare dana ganta ba" ita dae fatuu Murmushi kawae take, kallonta Abdul yayi kafin ya juya yace ma haisam "wai wacece wannan Baba zakee" kafin ya bashi amsa Abbas yace "Mom din shi ce" zaro ido yay yana bin fatuu da