Showing 210001 words to 212491 words out of 212491 words
kai yay idonshi akan hanya yace ta had'a ta sha, kawae sai gani yay ta aje duka harda nata a gaban motan ta koma jikin seat tana tura baki, d'an kallonta yay ganin abunda tayi ya d'an girgiza kai da Murmushi yaci gaba da driving can bayan wani lokaci kawae sai gani tay ya kai hannu ya d'auka ya kai baki bayan ya fasa ya fara sha a hankali dama abunda yasa yace bazai sha ba saboda bai cika son shan abu a leda bane, wani kallo tay mashi kafin ta juya ta kalli Haulat ta kashe mata ido d'aya ta juyar da kai tana Murmushi, tabbas yanzu ta fara gasgata Maganar Haulat ta Haisam na sonta.......
A takaice.......
Tun daga wannan ranar kallon da Fatuu ke ma Haisam na yayanta ya canja ya dawo na masoyinta wanda kuma zata aura da zarar ta gama Makaranta don sosae take jinshi a ranta, ranar Juma'a bayan an sakko daga Masallaci suna zaune a falon Hajiya ita dashi hajiyar bata nan Saude kuma tana dakinta, bata je makaranta ba don anyi masu hutu wanda daga shi kuma sai gama Makarantar tana yin wanka ta taho gidan anan ma taci abincin rana don yanzu ta koma mai gida biyu har tama fi zama gidan Hajiya sai dae kuma yanzu sam Haisam bai bari tana zama a part d'inshi da taje suka gaisa in ba fita zaiyi ba sai yace suje part d'in Hajiya tun tana jin abun wani iri harma ta saba in yana aiki da laptop dinsa sai ta d'aukar mashi su tafi can yanzu ma da suke zaune aiki yake da laptop d'in ita kuma tana zaune tana kallon tv jikinta sanye da riga da skirt na atampa sun kamata ba laifi don son matsattsun kayanta na yarinta har yanzu bata daina ba kallabinta na akan kafad'arta tayi parking gashinta dake a kwance gyalenta kuma na ajiye a gefenta, tana cikin kallon aka sako irin sakon gaisuwar nan da tashar Arewa 24 ke ma garuruwa na Katsina anan suka nuno Masarautar daura tare da rijiyar kusugu mai dumbin tarihi dake garin idonta akan Tv din tace "Wllh ina son zuwa inga rijiyar nan anyi mana tarihinta a Hausa ance ma har ruwan ake d'ebo ma Mutum ya sha" shiru ya d'anyi yanata Operating laptop d'in gabanshi daya d'aura akan c-table can taji yace "ba'a kaiku excursion ba daga skul?" da sauri tace "eh an kai wasu amman mu banda mu da yake muna da yawa to sai aka raba mu gida biyu wasu suka je nijar da suka dawo ne aka tsaya dasu daura da kuma Ajiwa Dam mu kuma Kano aka kaimu, mukaje gidan zoo da gidan tarihi da kuma wani gidan fata da wurare dae da yawa, ba kasan lokacin da muka je ba farkon shigarmu s.s 3?" kai ya d'aga mata alamar eh taci gaba "sun zo sunata bamu labarin rijiyar da kuma Dam d'in sunce babban Dam ne ance masu shi ke ba Katsina ruwa" jinjina mata kai yay ta juya taci gaba da kallon,
"Ki shirya within dis weekend sai in kai ki but ki fara tambayar Grandma d'inki" kaman daga sama taji Maganar da sauri ta juyo ta kalleshi daidai ya d'ago suka had'a ido tace "daurar zaka kaini?"
"yea ko bakya so ne" da tsananin mamaki tace "ina so wllh,to harda Ajiwa Dam d'in zamu?" kai ya d'aga mata cike da farinciki ta fara mashi godiya sai washe baki take tana rufe fuska, da Murmushi yake kallonta kafin ya mik'e tace tafiya zai yi yace eh yana son zaije yayi shirin gym don la'asar ta kusa, jin haka yasa ta mik'e itama ta d'auki gyalenta ta d'aura saman kan ta ruke kallabin a hannu yana kokarin daukar laptop din ta nufeshi tana ya barshi ta d'auka, atare suka fito harabar gidan suka jera suna nufar part dinshi har yanzu bata ida kai kafadarshi ba suna zuwa bakin Corridor ya mik'a mata hannu alamar ta bashi laptop d'in tace bari ta kai mashi har bakin kopar shiga parlon bai ce komai ba ya wuce tabi bayanshi, yana hawa balcony ya juyo ta mika mashi tana sakar mashi Murmushi har zai juya tace "thank u Sweetheart for making me Happy always" d'an bude ido yay jin yadda tay turancin cike d kwarewa sai kuma ya jinjina mata kai ta juya ta nufi hanyar fita tana yi tana waiwayenshi don bai shiga falon ba tana kaiwa bakin kopar fita ta d'aga hannu tana yi mashi bye bye, d'an Murmushi yay ya d'aga mata hannu guda daga haka ta fuce shi kuma ya shige ciki, tana fitowa daga gidan bata nufi ko ina ba sai gidansu Haulat sauri sauri gudu gudu ta rink'a yi ta d'an d'age skirt dinta da hannu don a k'agare take ta ganta a gidan, lokacin data isa k'annenta kawae ta gani a tsakar gidan ta tambayesu ina Haulat suka ce mata tana cikin d'aki ko sallama bata yi ba ta fad'a ciki lokacin haulat d'in na kwance kan katifa tayi wankan juma'a tana karatun Novel a wayarta wani ihu Fatuu tayi ta fad'a samanta cike da farinciki da k'yar haulat ta tureta daga jikinta tana Fad'in "so kike ki kashe ni tun ban shiga d'akin mijina ba......" katseta Fatuu tayi da fad'in "Albishirinki kawata" da sauri Haulat tace "goro fari kal",
"Ki tayani murna wllh ta tabbata Ya Handsome sona yake" da sauri ta yunkura ta tashi zaune cike da zak'uwa tace "ya fad'i maki ne?" girgiza mata kai tayi "a'a bai fadi man ba amman abunda zai man ya tabbatar da hakan" haulat tace "to bani in sha mana ya akai?" nan take Fatun ta kwashe komae game da inda zai kaita ta gaya mata, wata shewa haulat tayi tace "kice yawan shakatawa zaku kawae, ai k'ilan ma acan zai bayyana maki soyayyarsa fa" waro ido Fatuu tayi ta dafe bakinta da hannunta guda haulat tace "Wllh, Allah yasa ma hakane, ke ko bai furta makin ba iya hakan ma ya tabbatar da soyayyarsa gareki" ita dae Fatuu Murmushi kawae take saki duk farinciki ya lullu6eta har tafi jin dadin Maganar yana sonta fiye da inda zai kaita, hira suka ci gaba da yi yawanci duk kan soyayya ne har saurayin haulat wanda zata aura da zarar sun gama Makaranta kuma d'an uwan Mahaifiyarta ne d'an Nijar don Mahaifiyarta yar can ce ya kira har suka gaisa da Fatun, sai can gab da Magrib ta baro gidan Haulat tayo mata rakiya akan hanya take ce mata gaskiya ya kamata a tafi da ita ko don su samu photographer da zata yi masu hotuna don irin wannan fitar saida hotuna, harararta Fatuu tayi tace ba'a zuwa da ita salon ta takura masu haulat d'in tasa dariya tace wayaga sabon shiga a daidai nan suka iso inda zasu rabo suka yi sallama kowa ya tafi.
Ranar Lahadi Misalin karfe goma da wasu mintuna Haisam ya parker a kopar gidansu don tun jiya ta gaya mashi gwaggon ta amince ya fad'i mata time d'in da zaizo, zuwa Amadu yay suka gaisa yace don Allah ya kira mashi Zarah yace to, bada jimawa ba ya dawo Fatun na bayanshi tayi shigan kananan kaya kaman Haisam d'in shima kananun kaya ne jikinshi amman ta d'aura bak'ar after dress asama mayafin kuma ta nada shi daga baya yayi tudu sosae kafafunta sanye da takalma masu tudu tayi kyau sosae, bud'e Motar tayi ta shiga tana Murmushi ta gaidashi fuskarshi a sake ya amsa mata kafin yaja Motar suka tafi, sama sama suke yin hira tana kuma yin kalle kallen hanya cikin awa guda da wasu yan mintuna suka isa Daura, Kofar sarki Abdurrahman suka nufa inda gidan sarki yake, sosae ya zagaya da ita gidan sarkin bayan sun je sai kalle kalle take daga baya kuma suka je inda rijiyar take tasa yay mata hotuna aka kuma dibo mata ruwan tasha shi dae bai sha ba, gidan yan uwansu dake nan ya wuce da ita har da gidan kawu Mani daya ta6a zuwa gidan Hajiya, duk inda suka je sai an tambayi wacece ita ya fad'a masu a makwabtansu take bayan anyi sallar Azahar suka bar daurar dama tun suna hanyar zuwa ta gaya mashi gwaggo tace in ba damuwa su biya su gaishe da kawunta shi6ado dake a karkarku garin Fulani ne don da wuya ka samu wanda ba bafullatani ba a kusa da garin daurar yake, ba k'aramin karramashi sukai ba lokacin da suka je don kawun yasan da labarin haisam a wurin gwaggo da duk abun alkhairin da yake masu sai faman zuwa ake gaishe shi a mutunce yake amsa ma kowa, basu wani dad'e ba suka yi sallama aka had'asu da uban dawon fura da fresh nono, wuri biyu akai masu wato na Haisam daban sai wanda Fatuu zata kaima Gwaggo,
AJIWA DAM
Babban Dam ne mai matukar girman gaske yana d'aya daga cikin wuraren da ake zuwa yawon bude ido a Jahar Katsina da Rijiyar kusugun da suka je, Farkon Dam din akwae masu saida kifi iri iri d'anye da soyayye akwae hanya da zaka bi kaje wurin ruwan wadda tun kana tafiya zaka fara ganin ruwan a gefen hanyar akwae Ofisoshin masu aiki a dam d'in a gefe guda, lokacin da suka isa Fatuu rudewa tayi don ba kamar irin ruwan data saba gani a garinsu bane cike da farinciki ta bud'e mota ta fito tana dariya shima Haisam din fitowa yay ya jingina da gaban Motar yana kallon ruwan, ganin tana matsawa yasashi cewa "Zarah u ave to be very careful" kai ta d'aga mashi sam fuskarta ta kasa 6oye tsantsar farincikin da take ciki wurin akwae kayatarwa sosae ga Mutane nan da suma suka zo ganin ruwan, akwae gadar karfe data bi ta cikin ruwan wadda zata kai ka har tsakiyar ruwan yadda zaka hangi ko ina mutane nata hawa suna zuwa tsakiyar ruwan, kallonshi tayi tace "nima in hau Ya Handsome?" girgiza mata kai yay alamar a'a ta marairaice tace "plssss" shiru yay yana kallonta tana ta langa6ar da kai yace taje amman ta kula cike da murna ta nufi wurin sai kuma ta tsaya ta juyo tace "kai bazaka hau ba?" shiru ya d'anyi da alama tunani yayi ya nufota yace suje, atare suka hau sai faman washe baki take ganin yadda take hango ruwan sosae saida suka je can k'arshe inda keda girma kaman dan gini mai rumfa suka tsaya sunata kallo fuskarshi a sake, tanan akwae inda zaka bi kaje kasan ruwan, ganin anata yin hotuna tace suyi suma don Allah ba tare daya ce komai ba ya fiddo wayar ya fara yi mata tace shima bari tayi mashi yace ta barshi karshe ma sai cewa yay su sauka hakanan don ya lura da yadda aketa faman kallonsu shi kuma baison kallo, koda suka saukan a kasan ma sawa tayi yayi mata hotunan a bakin ruwan cikin ciyayin dake wurin,
Suna baro wurin ta fara gyangyad'i ganin hakan yasa yace ta sauke seat din ta kwanta sosae tace to, wuraren karfe biyar da wani abu suka shigo Katsina har saida suka iso bakin layin gidansu ta farka ganin inda suke yasa ta juya da alamun mamaki tace "wai ashe har mun dawo" kai ya daga mata idonshi akan hanyar layin ita kuma tana a kwance bata tada seat d'in ba,tunkan su k'arasa ya hango wata babbar bak'ar jeep fake a gefen gidan Hajiya tana facing d'insu da alama wanda ke ciki tafiya zaiyi daga jikin kopar motar ta wurin driver watace tsaye ta duk'ar da kanta da alama tana Magana ne da wanda ke acikin Motar, k'ura ido yay yana k'are mata kallo kafin da tsananin mamaki kan fuskarshi ya furta "What a Suprise!!!" jin abunda yace yasa Fatuu kallonshi ganin inda ya k'ura ma ido yasa ta juya ta kalli glass d'in gaban Motar itama ta kalli abunda yake gani, daidai gaban jeep d'in wadda Lexus GX460 ce ya parker tashi Motar lokacin kuma ta jikin kopar ta juyo, Tubarakallahu ahsanul khaliqin shine abunda na furta, kallo d'aya zakai mata ka yanke ba bahaushiya bace, doguwa ce ba kamar da yake takalman kafarta masu tsinine sosae tana sanye da straight gown ta babbar atampa glitter rigar ta bayyanar da dirinta sai dae sam bata da jiki ga d'amamman cikinta kai kace bata cin abinci, a bangaren kyawun fuska kuwa abun ba'a Magana don fara ce sosae tana da dogon hanci da d'an madaidaicin baki wanda lips dinsu ke jajur duk da da gani ta k'ara da janbaki, tayi d'aurin kallabi zara buhari yayin da yalwatacciyar sumarta brown ke d'aure da ribbom ta saketa saman gadon bayanta wuyanta na sanye da yar ziririyar sarka wadda da gani zinari ce haka ma d'an kunnan dake kunnanta barima ce ta zinari hannunta na hagu na sanye da golden agogo sam bata da mayafi ajikinta, tana juyowa ya bud'e Motar da sauri ya fita, nufarta yay tana ta faman sakar mashi kayataccen Murmushi koda ya isa gabanta kawae sai ta bud'e hannu ta rungumeshi can yasa hannu ya d'ago da ita suka had'a goshinsu suna ma juna dariya................End Of Book One,
Shin wacece wannan? Mi kuma ke tsakaninta da Haisam? Da gaske Haisam na son Fatuu kuma zai aureta? Amsoshin wadannan tambayoyin na acikin A Sanadin Makwabtaka kashi na biyu.
ALHAMDULILLAH, Anan na kawo karshen A Sanadin Makwabtaka kashi na farko wanda kamar gabatarwa ne ga ainihin Labarin dake a cikin kashi na biyu, ina rokon Allah yadda ya bani ikon kammala kashi na farko ya bani ikon kammala kashi na biyu cikin koshin lafiya, ya kuma bani ikon rubuta abunda zai amfaneni ya amfani Al'ummar Musulmi gaba d'aya Amin.
Ga mai bukatar cigaba da karanta kashi na biyu wato Book 2 zai biya kudin karatu Naira 300 kacal ta wannan Account din👇
1509618776
Zainab Bature
Access Bank
Za'a turo da shedar biya ta daya daga cikin wadannan Lambobin wayan ko kuma tuntu6a don neman karin bayani, 09013804524 ko 08169856268.
Thanks and i luv u as u patronize🤝🥰