Showing 111001 words to 114000 words out of 212491 words

Chapter 38 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

980

matsalar ma bata san sunan topic d'in Assignment d'in ba balle ta duba table of contents na text book d'in ta gano page din da akayi irin topic d'in ko zata samu koda shigen tambayar ne,duk ta had'a uban gumi,k'arshe data gaji ta buga littafin da kasa tana ta faman huci ga uwar yunwa dake faman cinta don dole ta mik'e ta nufi Kitchen ta zubo abinci,bata wani ci na kirki ba taji duk ya fita aranta don hankalinta ba'a kwance yake ba bata da burin daya wuce taga tayi Assignment d'innan ba kuma don tana tsoron hukuncin da za'a mata bane sam ta saba da Wannan kawae so take ta k'ure Malamin da sauran yan ajin,can ta tuna da bata yi sallah ba zuciyarta ta raya mata k'ilan ma shiyasa ta kasa yin Assignment d'in,zumbur ta mik'e taje tayo Alwala tazo tayi Sallah data gama harda yin Addu'ar Allah yasa tayi shi daidai,bayan ta gama ta k'ara d'aukko littafin Maths d'in don ta k'ara gwadawa ko tayi daidai amman ina ko steps d'in dama zata bi har tasamo irin amsar daya batan bata sani ba,duk da hakan bata sare ba taci gaba da jagwalgwalawa a paper in tagama taga baiyi ba sai ta yaga paper din ta ciro wata ahaka sai da ta yaga fefofi masu yawa da abun ya isheta sai kawae ta zabga uban tagumi fuskarta a yamutse ta rasa yadda zatayi tai solving dinshi,tana cikin wannan yanayin Kawu Amadu ya fad'o mata arai aikau zumbur tayi ta mik'e ta nufi waje duk da batasan ko ya dawo bama don bata ji motsin shigowarshi ba kuma bata ji ya shigo d'aukar Abinci ba a kicin,tana zuwa zauren taga kopar d'akinshi a rufe alamar bai dawon ba,komowa tayi cikin gida amma ta d'an ji sanyi cikin ranta don zuciyarta na tabbatar mata da k'yar inba shi zai iya fidda mata shi ba tunda shi d'an Senior ne kilanma su anyi masu irinshi dama kuma yana yi mata Assignment in bata iya ba,cike da kwarin gwuiwa ta koma daki don ta jira dawowarshi,can ta mik'e tace bari taje tayi wanka kilan kafin ta gama ya dawo.

Bayan tayo wanka ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ko mai bata shafa ba burinta kawae taji Kawu Amadu ya dawo,zaune tayi ak'asa ta tasa littafin Assignment d'in agaba tayi zugudum ahaka ta fara gyangyad'i amman taki bari baccin ya d'auketa duk da tana jinshi sosae,tana hakan ta jiyo k'arar bud'e d'akinshi aikuwa a sukwane ta rarumi littafin Assignment d'in da biro tayi waje,tana zuwa d'akin nashi ta banka ko sallama babu,lokacin yana cikin cire Uniform d'inshi don har ya cire rigar daga shi sai singileti amman bai kaiga cire wandon ba,kallonta yayi fuska amurtuke,

"Kina da hankali zaki shigo man d'aki haka ko sallama babu!" shiru tayi tana kallonshi fuska a yamutse, ganin hakan yasashi cewa"lafiya?",
cikin yar en ena tace"Daman tun d'azu nike jiranka Assignment ne don Allah zaka yi man ni nayi nayi amman na kasa",yar harararta yayi"shine don baki da hankali daga dawowana zaki banko man d'aki ko,to banyi ki futa ki ban wuri",ta6e baki ta fara yi kaman zatayi kuka ta hau yi mashi Magiya,fuska a d'aure yace ta fita to ya gama cire kaya,da sauri tace to,ta juya ta fita,abakin kofar d'akin nashi ta tsaya bayan wani d'an lokaci ta kware baki tace"in shigo ka gama?"banza yayi mata ta k'ara maimaitawa,jin shiru yasa ta d'an lek'a kanta cikin d'akin lokacin yana tsaye daga shi sai d'an boxer shorts amman sai cewa tayi"Kawu ka gama ne in shigo"a fusace ya kai hannu ya rarumo jakar Makarantarshi zai jefo mata tana ganin hakan ta janye kan da sauri,
ci gaba tayi da tambayar kawu ka gama in shigo,daga wajen ta maida abunma kamar wak'a,d'an guntun tsoki yaja lokacin daya gama shiryawa yace"in kin gadama ki kawo man Abinci",da sauri ta amsa da toh,

Kawo mashi Abincin tayi harda ruwa masu sanyi,tana ajewa a gabanshi ya d'an rankwashi kanta"shegiya dayake buk'ata kike awurina harda su ruwa baccin kullum sai nayi fama dake kafin ki kawo man" ya k'arasa Maganar yayin da yake zaunawa a gefen yar katifarsa, itama zaunawa tayi ak'asa hannunta guda tana d'an sosa inda ya rankwashetan,fara cin abincin yayi ita kuma tayi mashi k'uri da ido,yana cikin ci ya kware ya hau yin tari ta hau yi mashi sannu,a fusace ya kalleta bayan tarin ya lafa"Sannun ubanwa,kin k'ura man wad'annan idanuwan naki uwa na mujiya ba dole in kware ba ko ki daina kallona ko ince banyi wllh"turo baki tayi ta juyar da kanta gefe har ya gama cin abincin,

"Kawo muga Assignment d'in in zan iya ko kya tashi kiban wuri kin wani tsareni sai kace wanda yaci maki bashi"da sauri ta mik'a mashi Littafin bayan ta bud'o daidai inda Assignment d'in yake,kar6ar littafin yayi ya k'ura idanu yana kallon tambayar da za'a fiddan,
"Wannan wane topic ne,Quadratic Equation ne ko mi?"yayi tambayar had'i da kallonta,watsa hannuwa tayi tace "wllh nima ban sani ba ya dae ce wai ga amsar da za'a samo nan ak'asa in ba'a samo irinta ba to ba'ayi daidai ba,amman na duba ma Quadratic equation d'in da akayi mana naga kwata kwata basu kama da wannan har a textbook d'ina na Maths na duba banga wanda yayi ko shige dashi bama" k'ara kallon Question d'in yayi kafin ya d'ago yace"to shi wannan din a wane topic yayi maku shi?",

"Bansani ba,kawae tambayar ya bada" jinjina kai yayi"aikau dae wllh dakyar in zan iya yinshi nima don gaskiya ba'ayi mana irinshi ba,amman bari dai in duba textbook d'ina nima muga ko za'a samu irinshin"da sauri tace to,don da har gabanta ya fad'i,

Ba irin k'okarin da Amadu baiyi ba don ya fidda mata shi amman abun yaci tura duk ya had'a uban gumi, shima sai faman yago papers yake yana jagwalgwalawa kaman dai yadda Fatun tayi, a k'arshe dakyar ya samo wani problem anyi solving mai shige dashi acikin textbook d'inshi, a hankali ya rink'a bin steps d'in da akayi waccan wai ko zai iya fidda mata,sai faman sharce zufa yake Fatuu nayi mashi sannu,can ya d'ago a fusace ya wurga mata bangon littafi yace tayi mashi firfita baiwar Allah da sauri tace to ta d'auki bangon ta fara yi mashi don bata da burin da ya wuce taga yayi mata Assignment din,abu fa ya ture,lissafi an koya maka ma ya gagareka yi balle wanda ba'a koya maka ba,baka ma san hanyar da zaka bi kayi shi ba,kwalwar Amadu fa ta cazu iya cazuwa gashi ba abun yace zaiyi goggling ba tunda wani abunma ba yadda za'ai ya rubuta shi da wayarshi,ak'arshe dae da ya fusata sai ya cillar da biron ya d'auki paper d'in da yake solving d'in ya kekketata a fili yace"ina dalili,haka kawae in haukata kaina,ke nifa dama wllh ban kaunar Maths don ba yarda zanyi nike yinshi tunda ya zama dole",

Fatuu na jin haka idanunta suka cicciko da kwalla ta fara ta6e baki zatai kuka,cikin muryar kuka ta fara mashi Magiya,a harzuke kaman zai kai mata bugu yace"to wai ya kike son inyi ne?ba kiga duk irin kokarin dana yi bane,inda na iya ai zan maki ko,shima malamin daya baku Assignment dinnan ina tunanin yaci kai,taya zai baku abu alhalin bai maku irinshi ba,kuma ya rubuta question kawae ba wani d'an bayanin da mutum zai gane ko wane topic ne",ita dae Fatuu sai faman matsar kwalla take,wani kallo ya wurga mata mai kama da harara ya dan ja guntun tsoki can ya kai hannu ya daukko wayarsa,

"Bari in kira wani abokina d'an Class dinmu yana da kokari sosae shi ke yin na daya a ajinmu kilan shi ya iya yinshi", har Fatuu taji dan sanyi a ranta,bayan ya kirashi yayi mashi bayani kan Assignment din,yace kanwarshi ce aka ba shi kuma yayi iya bakin k'okarinshi ya kasa,Abokin nashi yace ya tura mashi Question d'in ta Whatsapp ya gani,bayan sun gama wayan ya d'auki hoton tambayar ya tura mashin daga haka suka yi jugum jugum suna jiranshi,bayan wani lokaci sai gashi ya kirashi a waya,Amadu na d'auka tambayar daya fara yi mashi itace wai under wane topic ne aka ba sister d'in nashi wannan question d'in,Amadu yace itama bata sani ba kawae tambayar ya rubuta masu yace ga irin amsar dayake so su gano nan,nan take Abokin yace to gaskia wannan zasuyi ta wahala ne kawai,tunda ko su ba'ayi masu irinshi ba balle su san hanyar da zasu bi su gano irin amsar da yake son ba,abunda za'ai ya bari gobe in sunje Makaranta sai su ba Malamin Maths d'insu yayi masu bayanin yadda za'a fidda shi kawae,nan take Amadu yace hakan za'ai,ai shi sam yama manta yayi wannan tunanin kuma yasan Confirm Malamin nasu zai fidda masu don ya had'u a lissafi,daga haka suka yi sallama yayi mashi godiya,

Koda yayi ma Fatuu bayanin shawarar da suka yanke da Abokin nashi sai tasa mashi kuka tana fad'in"ai gobe zai amsa fa,kuma da safe muke dashi",a fusace Amadu ya d'auki littafin ya wurga mata ajikinta,
"Gashi nan to sai kije kisan yadda zaki fidda kayanki,ni ina zargin ma wllh wani laifin kika aikata aka baki wannan aikin mai dan banzan wahala shine zaki zo ki wahalar da Mutane a banza a wofi,da ganin yadda kika tashi hankalinki baki da gaskiya,in ma laifin kikai aka baki Allah ya k'ara yasama karki iya fidda shi har goben tayi a zane ki tunda haka kika fi so,kinga in halinki ne gobe ma sai ki k'ara yin laifin da za'a baki irinshin,dalla tashi ni ki fita ki ban wuri kinzo kin hanani hutawa balle ko shago inje in bud'e",

Cikin tsananin fushi ta mik'e har wani huci take tana d'an harararshi,d'aukar littafin tayi da bironta da ya wurgar can gefe ta nufi hanyar fita,adaidai bakin koparshi ta tsaya,juyowa tayi lokacin yana niyyar kwanciya,
A tsiwace tace"Eh laifin nayi,kuma inna k'ara yin laifin an sake bani wani ai ko na kawo makan ba iya yimun zakai ba tunda yanzu ma gashi ka kasan balle kaman surut....."bata k'arasa ba sakamakon wani kukan kura da yayi ya nufo ta a fusace,aikuwa da gudu kaman walk'iya ta fice kopar gida da gudu,tsaye tayi tsakiyar center tana kallonshi yayi tsaye cikin zaure sai huci yake,yasan in ya biye mata wahalar dashi kawae zatayi ta maidashi kaman Mahaukaci,kwafa yayi a fili ya furta"zaki dawo gidan",daga haka ya shige cikin d'akinshi,

Tsaye tayi awurin abun Duniya duk ya isheta,wani kunci take ji acikin ranta na rashin yin Assignment d'in gashi tasan in dai ta sake ta koma cikin gidan to kuwa kashinta ya bushe,yadda Gwaggo bata nan ai sai kawu Amadu ya kusa kasheta gashi dama bak'ar zuciya ce dashi sam bai iya bugu ba,sai lokacin ta fara danasanin abunda ta gaya mashin,tana cikin tsayuwar nan Ya Handsome ya fad'o mata arai,nan take ta fara tunanin ta kai mashi Assignment d'in kilan shi ya iya shi tunda ya gama karatu har yana aiki,lokaci guda ta saki Murmushi duk da bata da tabbacin ya iya d'in,har ta juya zata tafi ta tuna ai ko kallabi bata dashi kuma gashi tana tsoron shiga gidan ta d'aukko,nan take dubara ta fad'o mata,bud'e tsakiyar littafin tayi ta kifa asaman kanta daga haka ta nufi gidan Hajiyar Sanata.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔


*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

4️⃣9️⃣

Haisam zaune saman kujera L-shape ya dan kishingida jikinshi sanye cikin bak'ak'en kaya jeans da t-shirt gaban rigar anyi rubutu golden colour hannunshi sanye da Agogo golden,tun bayan daya dawo daga aiki wanka kawae yayi ko part d'in Hajiya baije ba yaci abinci ya zauna yana yin video call,yana yin firan yana d'an gutsiran cake dake ajiye gefen laptop dinshi dake kan c-table hannunshi guda na ruke da glass cup mai d'auke da ruwan lemu yana d'an sipping ahankali,

Turo kopar tayi bakinta d'auke da sallama ta shigo,a gefen kujeran ta tsaya idonta akanshi,a hankali ya wurga eyeballs d'inshi kanta suna had'a ido ya d'an yi Murmushi hakan yasa itama tayi mashi,

"Who is dat?" wata zazzak'ar murya daga cikin laptop d'in ta tambaya da alama wadda yake yin video call d'in da itace,maido idanunsa yayi kan screen d'in slowly ya furta"Zarah"yayi Maganar had'i da lumshe ido,
"Oh really?" mai muryar ta tambaya,d'aga mata kai yayi alamar eh,
"I wanna see her,where is she" ta sake fad'a alamar tana son ganin Fatuu,daga yadda take turancin zaka yanke ba bahaushiya bace,kallon fatun yayi yai mata alamar tazo da kanshi,sai lokacin tasa hannu ta cire littafin dake asaman kanta ta d'an matso gaba kadan,da yatsanshi ya nuna mata Laptop dinshi yace"zaku gaisa da ita ne"cikin rashin fahimta tace"wa?",
wani kallo yayi mata"ki duba inda nike pointing mana" da sauri ta juya ta kalli inda yake nuna matan,Matashiyar budurwa ce da zata iya kai shekara 21 zuwa 22 haka,tana zaune asaman gado ta jingina bayanta da kan gadon,lokacin da Fatun ta kalli Computer d'in budurwar ta juya gefe ta dauki ruwan roba dake aje saman bedside drawer ta daga tana sha hakan yasa bata ga ainihin fuskarta ba sai dai dogon gashinta dake gefe da gefen fuskar ya zuba har kan cikinta wanda launinsa brown ne sosae haka fatar jikinta ma fara ce sosae wanda kallo d'aya zakai mata ka kirata da farar fata,sai dae sam kalar hasken fatarta dana haisam ba iri daya bane kowa da launin haskensa,

Ai Koda Fatuu tayi arba da ita a firgice ta juya ta kalli haisam tace"Ya Handsome da wannan zamu gaisa din?"fuskarshi a sake kaman zaiyi dariya ya d'aga mata kai don yadda ta firgitan taso bashi dariya,
a rud'e ta kuma cewa"to amman ai ni fa ban iya irin turancinsu ba mai saurin nan,ba rannan na fad'a maka ba har kace zaka koya man amman sai ka samu isashshen lokaci to yanzu ya zanyi magana da ita....."kafin ta k'arasa budurwar ta katseta da fad'in,
"karki damu nima bahaushiya ne ai" yadda tayi hausar gwanin dad'i,da sauri Fatuu ta maida kallonta gareta lokacin ta gama shan ruwa ta juyo da fuskarta sosae,Tubarkallah Ma sha Allah,kallo daya zakai mata ka shaida kyawun fuskarta,kyakkyawa ce matuk'a ga kwayar idonta brown ce har wani kyalli take,waro ido Fatuu tayi tana kallonta arazane,ba kyawunta ne kad'ai ya razana ta ba, harda furucin da tayi na wai itama bahaushiya ce to ta yaya?shine abunda ya tsaya ma fatun arai.

Hannu ta d'aga ma Fatuu"hi,Zarah how're u?",
Cike da mamaki fatuu tace"da gaske ke bahaushiya ce?"

"Yeah,kuma ina jin hausa kaman jakin kano ba" tayi Maganar tana dariya haka kuma ba k'aramin kyau ya k'ara mata ba,kan fatuu fa ya Matuk'ar daurewa hannu guda tasa ta rufe bakinta alamar mamaki kafin tace"wai har sunan jaki ma kin sani kenan!",ba budurwar ba har Haisam dake saurararsu saida ya d'an murmusa,

"Na fad'a maki nima bahaushiya ne ko baki yarda ba,nasan komae ai saboda nima yar Nigeria ne, anan aka haifeni, anan nayi wayo har na girma",
kai abunfa nayi ne,neman wurin zama Fatuu ta fara don da a duk'e take tayi ruku'u,ganin haka yasa Haisam janye kafarsa daya mik'e kan kujeran ya matsa can gefe,zama tayi sosae tace"to ke wacece,kuma wane gari kike ko ke yar gidansu Ya Handsome ce amman kuma naga ba kalarku daya ba"duk ta jero mata tambayoyin nan,

Murmushi tayi tasa hannunta tana gyara gefe da gefen gashinta kafin ta fara magana"sunana FANAN,ni yar Lagos ne and ni kanwarsa ce but am his Cousin sis kinsan me cousin ke nufi ko?"da sauri Fatuu ta d'aga mata kai"Eh nasani anyi mana shi a English,diya ko dan kanin ko yayan iyayen Mutum",

"Yeah,You're right Zarah ni d'iyar kanwar babanshi ce", cike da mamaki Fatuu tace"wllh nama gane ki,Mamanku diyar Hajiya ce wadda ke lagos kuma Babanku Bature ne ko?" Fanan na dariya ta d'aga mata kai alamar eh,
"To ke yaushe zaki zo nan Katsina?" fatuu ta tambaye,
"Currently now am not in Nigeria,ina India ina karatu,sai dae watarana in nazo" zaro ido Fatuu tayi"India!yanzun nan da nike yin magana da ke kina India?"kai Fanan ta d'aga mata alamar eh,

"To mi kike karantawa anan d'in?",
"Medicine"ta bata amsa,
"had'a Magunguna kenan?",
"No,karatun likita kenan",cike da mamaki Fatuu ta ruk'e baki tace"kai ashe wai shine Medicine,shifa nike son in karanta amman bansan sunan karatun ba kenan,ni karatun Doctor kawai nike cewa",sosae Fanan d'in ke dariya jin shirmen Fatuu nan suka shiga yin hira sosae atsakaninsu da alama itama Fanan d'in bakinta asake yake har Fatuu na tambayarta wai tana zuwa wurin yan Film d'in suburbud'a dasu Sharukhan,tace mata a'a ai Karatu ne ya kawota amman dae wani lokacin suna ganin yan Film d'in in sunzo makarantarsu shooting ko akan hanya ko a Mall in sunje Shopping da dae sauran wurare kaman wurin shak'atawa haka,anan Fatuu ke ce mata wai in zata zo tayo mata tsarabar sari amman ba wanda ake nad'awa ba wannan kada ita zai rink'a yi irin masu wando take so irin wanda Roshni d'in Aman na cikin film d'in Shu'umin iko take so,nan Fanan d'in tace mata bata gane irinsu ba don ba kallon film d'in take ba,Fatuu tace mata in anayi a tauraruwa zatasa Ya Handsome ya d'auki hoton irinsu ya turo mata tace to,daga haka Fanan d'in tace mata zata tafi tutorial yanzu sai wani lokacin zasu sake gaisawa Fatuu ta amsa da toh,

"Beb where are u?" Fanan ta fad'a tana d'an kallon gefen Fatuu,Haisam na jin hakan yayi ma Fatuu alamar ta juyo mashi da Laptop d'in,kallonta yayi fuskarshi da Murmushi itama Murmushin take mashi tace"I will be offline now so u can have more time wit ur Funny Mom"lumshe ido yayi still da Murmushi akan fuskarshi slowly ya furta"Ok,Bye Sweethrt",
"Bye Beb"ta d'an ja Maganar daga karshe had'i da yin kiss daga haka ta sauka,waro ido Fatuu tayi tasa tafukan hannayenta duka biyun ta rufe baki alamar mamaki tana kallonshi,kallonta yayi,ganin abunda tayin yasashi cewa" What?"
cire tafukan tayi tana d'an murmushi tace"Nagane Budurwarka ce,amman shine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login