Showing 72001 words to 75000 words out of 212491 words

Chapter 25 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

961

kan wayar yana ci gaba da cin Apple d'in,
"U have a message" Haisam ne yayi maganar,juyowa hajiya tayi tace"sak'on mi?" batare da ya bata amsa ba ya d'an d'aga mata wayarshi lokaci guda wata zazzakar murya ta fara magana,_"Hi Granny!how are u,kin manta dani ko?"_ daga yadda mai muryan tayi magana da hausa zaka fahimci hausar tata bata nuna ba sosae,
lokaci guda hajiya dake kallon haisam ta washe baki tana fad'in"Allah sarki Fanan,ai in dae na manta dake na manta da kaina kenan,kira man ita don Allah in wanke kaina" sauke wayan yayi ya fara kokarin kiran fanan d'in,tana fara ringing haisam ya kalli fatuu yayi mata alamar tazo ta amshi wayan ta mik'a ma hajiyan,tasowa tayi ta kar6i wayan kaman yadda ya mata umarni,hajiya na amsa aka d'aga kiran suka fara waya da Fanan din,

A hankali fatuu ta mik'e ta nufo wurin da haisam ke zaune,tsayawa tayi daga gefe tana kallonshi had'i da yin d'an murmushi,hannu yasa ya daukko ayaba yakai bakinsa yad'an gatseta kafin ya d'ago idanunsa ya kalli fatuu dake atsaye,sauke kafansa guda k'asa yayi d'ayar kuma mai ciwon ya mik'ar da ita kan kujeran,kallonta ya sake yi yace"Seat" a hankali ta zauna d'ayan 6arin kujeran ta d'aura hannunta d'aya kan hannun kujeran tayi tagumi dashi har lokacin da Murmushi akan fuskarta,ci gaba da shan fruit din yayi idonsa akan tv can suka had'a ido da ita,ganin tana ta kallonshi ne yasa shi tunanin ko fruit d'in take so ne,ita kuma yadda yake sha ne abun yayi mata dad'i tayi zaton ba zai sha ba kaman yadda hajiya tace,

d'aukko plate d'in fruit din yayi ya aje agabansa ta yadda ya kasance atsakiyansu kenan,kallonta yayi a hankali yace"eat"da sauri ta girgiza mashi kai"ni da na kawo maka kuma sai in shanye ma" yar harara ya wurga mata"what did i told u yesterday?ba nace in nace kiyi abu ba kawae kiyi"ganin yadda yayi mata maganan yasata saurin cewa"yi hakuri to"hannu takae ta d'aukko 6allin kankana ta fara sha tana satar kallonshi,shikam hankalinshi na kan tv,duk wannan abun hajiya na akan waya sai faman hira suke da Fanan din da aka kira mata,

Hannu fatuu ta kai zata d'auki fruit carab Haisam yaji ta kama yatsan hannunshi,da sauri ya kae idonshi kan hannunta dake ruke da yatsan nasa,da mamaki ya d'ago ya kalleta sam hankalinta na akan tv da ake Indian film,batama san ta kama yatsan nasa ba,jan yatsan ta fara duk a tunaninta fruit d'inne,jin yaki daukuwa yasa ta juyo takai idonta kan fruit din,zaro ido tayi ganin ta kama yatsan Haisam,da sauri ta saki ta dago suka had'a ido dashi a rude tasa tafin hannun damanta ta rufe baki tana girgiza masa kae alamar batasan tayi ba,cire hannun tayi tana kokarin yin magana ya dakatar da ita da hannunshi,cigaba yayi da shan fruit din yana kallo,ganin haka yasa itama taci gaba da sha tana kallon sai dae duk in zata dauka sai ta juyo ta kalli fruit d'in gudun karta k'ara ruke masa yatsa,

Juyowa hajiya tayi bayan ta gama wayan ta kallesu, mamaki ta shiga yi cikin ranta na yadda akae suka san juna haka,shidae haisam tasan ba mai shiga harkar mutane bane balle kuma yarinya kaman fatuu,tunowa da halin fatun na sam bata jin magana kuma bata da shariya sannan tana da saurin shiga ran mutum yasa ta kawar da mamakin,

"Abun yar wariyar launin fata ce kenan" hajiya ce tayi masu maganar,juyowa fatuu tayi ta kalleta tana dariya hajiyar taci gaba"wato don kun ganku farare shiyasa ni bak'a aka ware ni ko"sosae fatun ke dariya,shima haisam d'in da idonsa ke akan tv d'an murmushin gefe yayi jin abunda hajiyan ke cewa,fatuu tace"ai akwae saura a kitchen in kawo maki ne?" kafin hajiyan ta bata amsa haisam ya maida dubansa kan fatuu da ta juyo ta kalleshi tana dariyar maganar hajiya"d'auka kikae mata" da sauri tace"da gaske fa akwae saura bari in..." katseta yayi"ki kai mata wannan na koshi" sukuku tayi da fuska ganin haka yace"zan sha sauran anjima" yayi maganar idanunsa ad'an lumshe,mik'ewa tayi ta dauki plate din ta nufi wurin hajiyan,

"Sauranku zaku ban in sha don kun raina ni ko" d'an murmushi fatuu tayi"to ai shi yace in kawo maki ya koshi"ta aje plate din a gefen hajiyan itama ta raku6a gefe ta zauna,hannu hajiya takai ta fara shan fruit din,itama fatun tasa hannu zata ci gaba da sha,da sauri hajiya tace "a'a sauran ma bazaki barman ba,ke baki koshin bane?"dariya fatuu tasa ta jingina kanta da kujeran,atare suke shan fruit d'in suna kallon Indian film d'in da ake a Bollywood da alama yana masu kyau ne,

Haisam ne ya fara k'okarin gyara kafarsa mai ciwo jin ta sage masa,hakanne ya jawo hankalinsu kanshi,
"Sannu kabi a hankali" hajiyace tayi maganar,d'aga mata kai kawae yayi taci gaba da magana"ni wllh har yanzu mamakin yadda ka taka wai kwalba nike,muda ko lemun kwalba bama amfani dashi,in kaga kwalba a gidan nan sai ta turare ko tasu salad cream su kuma wannan dama iyakarsu cikin kicin ne,da sun k'are kuma sai cikin dustbin amman sai gashi wae ka taka kwalba a part d'inka,abun ya d'aure mun kai,wae ko dai ka fita waje ne?" ta k'arasa maganar idonta akan haisam tana jiran ya bata amsa,fatuu kau gaba d'aya ta zaro idanu ganin kaman hajiyan nason gano gaskia,

da sauri fatuu tace"a...ai hajiya k'ilan a k'asan take fa"a rude tayi maganar,
"taya hakan zai yiwu bacin harabar part d'in nasa interlock ne,bafa k'asa bace balle ace kwalbar ta shige ciki ne" sosae gaban fatuu yake bugawa"ai ko shi d'in kwalbar zata iya shiga..." hajiyar ta katseta"bulo ne fa fateema" duk maganganun da suke Haisam d'in na jinsu don yana niyyar yaba hajiyan amsa lokacin da ta tambayeshi fatun ta rigashi yin maganar shiru yayi yana sauraransu idanunsa akan tv,so yake yaji yadda zata fidda kanta,

Fatuu taci gaba"ai a bulonma kwalba na mak'alewa" hajiya tace"kai fateema anya kuwa,su masu yin bulon har basu gani ba lokacin da suke yi su cire" fatuu dake ta zare ido tace"to ai ba inji bane yake kwa6a masu simintin da yashin ba,ai ba lalle fa su gani ba,ni nasha ganin kwalba ajikin bulo a gidajen da ake ginawa a hanyar islamiyyarmu" cike da al'ajabi hajiya ta ruke ha6arta"kuma fa hakane wllh,dama kinga part d'in nasa sabone kafin ya dawo akulle yake,ko ada in yazo kafin ya dawo nan,acikin nan yake zama,yanzu saboda zai dade ne aka idasa gina can d'in.."fatuu dae sai gyad'a kai take,hajiya taci gaba"aikuwa bari zansa Tk ya samo almajirai abi k'asan part d'in nasa adudduba inma akwae saura su cire saboda gaba kar ya k'ara takawa..." fatuu ta kar6e"haka yakamata nima zan tayasu aduban",

"Yauwa haka kawae za'ayi ma..." hajiya bata k'arasa maganarta ba sakamakon sautin yar dariyar da haisam ya saki,abunda ya bashi dariya shine yadda yarinya k'arama ta zauna tana mata wayo,

"kaji wulakanci muna tattauna yadda zamu kare lafiyarsa yana mana dariya" Hajiya ce tayi maganar idonta akan haisam,d'an juyowa yayi ya kalleta suka hada ido tace"mu kake ma dariya don mun damu da lafiyarka" d'an girgiza mata kai yayi"baki ga ina kallo bane",ya kai idanunsa kan fatuu bayan yayi maganar,tayi wuki wuki gaba daya tayi kalan rashin gaskiya,wani kallo yayi mata da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa kafin ya ci gaba da kallonshi,

"Fateema yakamata kizo ki tafi gida dare yayi sai kuma Allah ya kaimu" hajiyace tayi maganar idonta akan agogon dake parlon,
"Ni yau nan zan kwana" ta ba hajiyar amsa,kallonta tayi"amman dae kinsan gobe akwae makaranta ko,ki bari ran juma'a in Allah ya kaimu sai kizo nan kiyi weekend ma tunda ita islamiyyar bada sassafe ake zuwa ba" turo baki tayi tana niyyar yin magana haisam ya jefo mata wani kallo nan da nan taja baki tayi shiru,dama abunda yasa tace anan zata kwanan saboda ta kasa ta tsare don kada ta gano gaskiya,jiki a sanyaye ta mik'e zata tafi,hajiya tace"gashi ko abinci ma baki ci ba,mun zauna munata zance....",

"na koshi"ta fada fuskarta a yamutse,
"A'a bari dae a zuba maki ki tafi dashi in ke bazaki ci ba ai Dije da Amadu sa ci" tana kai maganar ta juya tana kwala ma Saude kira,fitowa sauden tayi ta nufo cikin parlon hajiya ta dakatar da ita"ki zubo ma fateema abinci cikin kula"amsawa sauden tayi da to ta juya ta nufi kicin,sai lokacin fatuu ta tuna da jakarta dake a d'akin sauden taje ta daukko,lokacin da ta fito sauden ma ta fito daga cikin kicin wurin fatun taje ta mik'a mata,amsar kular abincin tayi ta rungume a hannunta d'aya,gudan kuma yana rataye da jakarta,daga haka ta dawo cikin parlon kallon hajiya tayi"sai Allah ya kaimu hajiya",
"To fateema Allah ya tashemu lafiya,ki gaida dije",kai kawai ta d'aga mata,hajiya ta maida kanta kan tv,juyawa tayi ta kalli haisam da idanunsa ke kan tv shima"Yaya handsome sai da safe" jinjina mata kai yayi batare da ya kalleta ba,ba haka fatuu taso ba,so tayi ya kalleta don ta k'ara rokonshi akan karya fad'a ma hajiyan,

Hanyar fita daga parlon ta nufa tana yi tana waiwayen haisam wai ko zai juyo amman har takae bakin kopan bai juyo ba,tsaye tayi tana ta kallonshi ta kasa fita,kaman yaji ajikinsa ne yasa shi waiwayawa ya d'an kalli kopan fitan,da sauri fatuu ta aje kulan abincin ak'asa ta had'a hannayenta ta fara rokonshi tana magana kasa kasa had'i da jujjuya kanta,still yayi yana kallonta fuskarshi a sake kaman zaiyi murmushi,suna cikin haka hajiya ta juyo da niyyar yi mashi magana,ganin inda yake kallo yasata juyawa ta kalli bakin kopan karaf idanunta suka sauka akan fatuu,cike da mamaki ta furta"Fateema......."aikuwa da sauri fatun ta d'auki kulan ta fice.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F

_*BY ZAINAB LALUH📲*_


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

_Gashi nan 2 pages ne,ku da update sai Next week in Allah ya kaimu kar inji wani yace yau ba'a posting ne,within the Weekend🤨_


*3️⃣7️⃣&3️⃣8️⃣*


Da sauri Fatun ta d'auki kulan ta fice,maido idanunta tayi kan haisam da shima ya d'an kalleta kafin ya mayar da idanunsa kan tv,kanta ne yai matuk'ar d'aurewa,tunanin anya ba wani abu suke 6oye mata ba ta shiga yi,tasan halin kowannensu sarai shiyasa tun farko tayi mamakin ganin suna shiri sosae,
"Haisam" hajiya ta kira sunanshi,juyowa yayi ya kalleta ba tare da ya amsa ba,taci gaba"mike tsakaninka da fateema ne?"
d'an guntun murmushin da iyakarsa kan lips dinsa yayi"kinji ki da wani magana sweetheart mike tsakanina da ita fa..." katseshi tayi"ina nufin ya akai kasanta,ko tayi ma wani abunne don nasan halinta bata jin magana,kuma naga kaman kuna 6oye man wani abun" shiru haisam yayi yana tunanin ko ya fad'i mata kawae don ta san halin da ake ciki agame da yaran da yasa aka kama,yasan dole zata fi shi sanin abunda ya akamata ayi dangane da case din don ita aikinta ne,

Ganin yayi shiru yasa hajiya fad'in"talk to me haisam ka kafe ni da idanu,da akwai wani abu ne???" kai ya d'aga mata alamar eh,kafin a nutse ya soma magana"I first saw her On Thursday when i was Coming back frm Work........"nan take ya kwashe duk abunda ya faru tun ranar daya fara ganin fatun har zuwa jiyan"tunkafin ya rufe bakinshi hajiya ta shiga zabga salati,hannuwanta duka biyu dafe da kirjinta"innalillahi wainna ilaihir rajiun,hasbunallahu wa'niimal wakeel!!yanzu fateeman ce jiya mutum ukku suka kusan hakke mata?"cike da tashin hankali tayi mashi tambayar,lumshe ido yayi alamar eh,

"Kai jama'a wannan masifa dami tayi kama ni Hauwa'u,rape cases everywhere,everyday,fyade dae fyade dai,duk gargad'in da ake ana fadakarwa a banza kaman ma ana tunzura mutane" cike da takaici take maganar ci gaba tayi"Amman fateema bata yi wayo ba,wannan sakarci har ina,ina ganinta kaman mai wayau bazata bari a cucetaba ashe doluwa ce" sigh haisam yayi"tace Guy din wae bai ta6a ko ruke mata ko hannu ba shiyasa bata yi tunanin zai cucetaba",

Tsoki hajiya taja"sakarci dae kawae,wannan har hujjace da zata sa tabi shi kango karfe goman dare bacin tasan bashi kadae ke yin shaye shaye a wurinba kuma don bai ta6a ruke taba ai baikamata shima ta yarda dashi ba tunda tasan halinshi sarae daya samu dama zai iya cutar da itanne..."kwafa tayi kafin taci gaba"zata zo ta same ni ne,wato shiyasa ta zauna tana ta tsaran zance ta maida ni shashasha....harda cewa wani nan zata kwana,haba nifa wllh nayi mamakin ganinku tare don nidae nasan ba saninta kayi ba",
Sauke 6oyayyar Ajiyar zuciya haisam yayi"ina ganin ki kyaleta kawae...."da sauri hajiya ta tari numfashinshi"ta tafka wannan rashin wayon amman kace wai a kyaleta...",
"No kingane,duk wani abu da yakamata afad'i mata don ta kiyaye gaba i hv done dat,kuma nasan bazata k'ara yin makamancin hakan ba tunda nace mata nasa shi a yarjejiniyar glass da ta fasa man and kinga tana tsoron ki sani hakan zaisa ta k'ara kiyayewa sosae",

Cike da takaici hajiya tace" Fateema bata jin magana wllh,kar kaso kaga yadda kakarta Dije ke k'okari akanta,ni kaina nan kullum cikin yi mata fadan ta daina rashin ji nike,yanzu ina amfanin hakan,sannu kaima kayi Babban taimako,Amman ka tabbatar dae basu cutar da ita ba?ko dae akaita asibiti ne??"Hajiya ta tambayeshi fuskarta a yamutse,Al'amarin ya Matuk'ar tashi hankalinta,
D'an girgiza kai yayi"gaskia basu yi mata komae ba,kawae dai sunyi tying Bakinta da Hannu so tana ta basu wahala don naji wani cikinsu yana magana kan hakan lokacin da naje,Da sunyi matan ma i think da ba'a ganta haka ba",

jinjina kai Hajiyan tayi"yanzu wani mataki kake ganin ya dace a daukar masu?" gyara zama Haisam yayi"shiyasa ai na fad'i maki don ke aikinki ne,d'azun da Sp khamis ya kirani ya sanar dani sunyi arresting nasu gaba daya so suna bukatan akai ita Zarah station d'in,na sanar dashi sai zuwa Friday lokacin kafana ya k'ara warkewa yace ba matsala"Jinjina kae tayi"shikenan before then zamu yi magana"

"Ok,amman shi guy din kin sanshi?",
"Uhm sani kam,ai Ashirun babanshi d'aya daga cikin limaman masallacin gidan nan ne malam tanimu,ko last da aka kamashi akan case d'in sata ni nayo mashi belinshi,amman yanzu ai ba batun insa kaina tunda wannan babban Case ne,shi kuma tanan Allah ya jarabeshi,Allah ya shirya mana zuria",
"Ameen" haisam ya amsa,Saude ce ta k'araso cikin parlon,A gefen kujerar da hajiya take ta tsaya"Hajiya na gama shirya table tun d'azun,kai kawae ta d'aga mata alamar toh,juyawa tayi ta kalli haisam"ka tashi kaje ga abinci can kaci dare nayi"har lokacin fuskarta akwae alamun damuwa,

"Ke bazaki ci abincin ba" haisam dake kallonta ya tambaya,"kaje zan taso"mik'ewa yayi ya nufo wurinta,agabanta ya tsaya"C'mon,Stop Worrying ur Self,taso muje kici abinci"ganin tana niyyar yi masa gardama yasa shi sa hannu ya sunkuceta sai kace ya dauki k'aramar yarinya,hajiya na bugun hannunsa tana ya sauketa amman saida ya kaita har Dining area din.

_______________

Ranar laraba da yamma gwaggo zaune atsakan gida saman tabarma tana jiran lokacin magrib ya k'arasa yi fatuu ta shigo da gudu,a gefen kopar zauren ta aje jakar islamiyyarta ta nufi toilet,girgiza kai gwaggon tayi a fili tace"Allah ya shirya"fitowa tayi tana gyara wandon uniform din islamiyyar jikinta ta d'auki jakarta kafin ta nufo cikin gidan,fuskarta d'auke da dariya tace"sannu da gida kakus"ta6e baki gwaggo tayi"yauwa"daga haka ta juya zata shiga daki,"in kin cire kayan islamiyyar ki fito in gyara maki kanki,zuwa gobe in sha Allah tunda ba islamiyyar sai in kitse maki shi"amsawa tayi da toh kafin ta shige dakin,bata dade ba ta fito jikinta sanye da doguwar rigar material kanta ba kallabi,
"Ki shiga cikin dakina ki dauko masharci da mai" gwaggo tace mata,

A saman tabarmar ta kwanta ta d'ora kanta saman cinyar Gwaggon,warware fakin d'in da akai ma gashin gwaggo tayi ta shafe gashin da mai kafin tasa comb ta fara taje mata,duk yadda take bi a hankali amman fatuu sai cije baki take tana k'orafin zafi can tace "gwaggo tun da dadewa kika ce zaki ban labarinki amman har yanzu kinki ki bani"yar dariya gwaggo tayi"to ke miyasa kike son jin labarina,ba kinsan garinmu da yan'uwana ba...",
"Amman ai bansan su waye iyayenki ba ko,kawu shi6ado na Daura kawae nasani da matansa da ya'yansa sai wasu dae yan'uwanki yan kad'an"gwaggo da har lokacin fuskarta ke d'auke da Murmushi tace"to ai na fadi maki sun rasu tuntuni ko...",
"a ina" fatuu ta katse ta,

"Tunda labarin dai kike so bari in baki a takaice,mu Asali Fulanin tashi ne wato masu caccanja wurare,na taso a kudancin kasarnan acan nayi wayo,fad'a tsakanin manoma da makiyaya ne ya rutsa da mahaifina har ya rasa ransa,to a lokacinne kawuna k'anin mahaifina ya dawo damu arewacin kasarnan ta dalilin wani Abokinsa wanda ke kai shanaye can kudun amman ba'a can yake zaune ba d'an nan Daura ne,bayan wasu shekaru da dawowarmu nan itama mahaifiyata ta rasu sakamakon jinya da tayi daganan ya rage bani da kowa sai kawu shi6adon da kika sani na daura....",
"amman to ke kad'aice baki da yayye ko kanne?" fatuu ta tari numfashinta,

"Ni kad'ae iyayena suka haifa,ina shekara goma sha biyu aka man aure,lokacin wani abokin su kawu ne Bello ya kwallafa rae akaina saida aka bashi ni ba don ina son shi ba amman bani da yarda zanyi,can yankin Safana aka kaini cikin matansa biyu nice ta ukku,matansa suka hade man kai,ba k'aramar wahala nasha ba agidan wannan bawan Allahn k'arshe dae matansa saida sukayi yarda sukae suka sa ya sake ni lokacin shekararmu biyar da aure,to bayan na dawo Daura ne Allah ya had'a ni da kakan ki Abdullahi a kasuwar mashi ina kai tallan nono,farko k'in saurararshi nayi don lokacin tsoron maza nike saboda wahalan dana sha a gidan Bello,daga karshe dae na Amince mashi muka fara soyayya har Allah yasa mukayi aure....",

d'ago kai fatuu tayi"Enye su Gwaggo ashe ansha soyayya" harara gwaggon ta wurga mata kafin taci gaba"shi asalinshi bahaushe ne d'an nan katsina wannan dalilinne ya kawo ni katsina shima lokacin yana da mata guda d'aya Habiba,Mutuniyar kirki ce sam bata d'auke ni kishiya ba face d'iya duk abunda zata yima yayanta shi take man,wani lokacinma in taga kakannaku nayi man fad'a in nayi masa ba daidai ba ita ke kwa6ar shi ta rinka cewa baka ganin yarinyace,shekararmu biyu da aure sannan nasamu cikin Innarki bayan na haifeta kuma saida nayi shekara sha biyu har ma na fidda ran sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login