Showing 87001 words to 90000 words out of 212491 words
"Fatima zahrah,ya School kina zuwa ko?" kai ta d'aga mashi alamar eh,
Kallon haisam yayi"is she d girl?"kai haisam ya d'aga masa alamar eh,jinjina kai Sp yayi kafin yace"let's get in"jerawa suka yi da haisam,yayi ma fatuu alamar ta biyo su,bin bayansun tayi suka nufi cikin station din,Office d'in DPO ya nufa dasu,
A zaune suka iske dpo d'in bayan sun shiga yana cikin duba wasu files,nuna masu kujerun dake agaban table sp yayi alamar su zauna,hannu dpo ya mik'o ma haisam bayan ya d'ago suka gaisa,gaishe da shi Fatuu tayi,fuska a sake ya amsa mata kafin yace"Fine girl,what's ur name?"fuskarta da Murmushi tace"Zarah"jinjina kai yayi,ya maida idonsa kan Sp,bayaninsu yayi mashi nan take ya gane case d'in,hannu ya kai ya jawo wani file gabanshi,bude ciki yayi yana sake duba statement d'in haisam kafin ya dago ya bada Umarnin a kawo mashi su gaye,lekawa cikin corridor din Sp yayi yace "Sergeant" da hanzari Sergeant d'in yazo gabanshi hadi da sara mashi,umarnin kawo su gaye ya bashi daga haka ya dawo cikin Office din,
After few minutes sai ga su gaye an shigo dasu da ganinsu sunji jiki sosae,don farko da aka kamosu aka fadi masu laifin da ake tuhumarsu dashi sai suka karyata don basu san waye ya kawo kararsun ba,shi kuma Sp yasan haisam bai ta6a yi masu karya,ko ba haka ba gama shaidar raunin da haisam d'in yaji,sai da suka ci na jaki sannan sukai confessing,tun lokacin suke cikin mawuyacin hali don ba wanda yayi yunkurin zuwa belinsu jin babban laifin da sukae yunkurin aikatawa,a k'asa suka zube kan gwuiwoyinsu,
Kallon Fatuu Dpo yayi"kinsan wad'annan"kai ta daga mashi alamar eh,
"Mi sukai maki?"gyara zama tayi ta fara kora mashi bayanin yadda sukai yunkurin yi mata fyade a kango" jinjina kai dpo yayi"tun farko ya akai kika san su"shiru tayi ta d'an saci kallon haisam dake opposite da ita,alamar ta fad'i masa yayi mata da kai,nan take ta juya ta fara kora mashi bayani tun daga kan glass da ta fasa ma haisam har zuwanta kangon,ta k'arasa sai faman nishi take,
Kallon su gaye dpo yayi fuska a murtuke yace"gaskiya ne abunda ta fad'a" inda inda suka fara Sp ya kwatsa masu tsawa nan take goga ya fara magana don Gaye gaba d'aya ya firgice,tsoronshi kar ace za'a kaisu kotu don yasan daga can sai gidan yari,tsananin tashin hankali ne akan fuskarshi,
"Yalla6ai hakane,duk abunda
ta fad'a gaskiya ne,amman wllh sharrin shaidan ne bada niyya ba...."da sauri Fatuu ta katseshi"Wllh karyane,kar ka yadda yalla6ai so yake ya maida kai sakarai baka san aikin ka ba,Allah da niyya sukae kokarin yi man fyaden,shi wanccan gayen shine baiso ayi mun ba,yace a kyaleni don Allah don babban laifi ne hukuncinshi daurin rai ne,amman wannan katoton banzan gogo ne ko miye sunanshi ma yace sai yayi",ta k'arasa tana ta nishi ta kumburo baki,gyalenta gaba d'aya ma ya dawo hannunta don da tana bayanin har d'an yunkurawa take kaman zata mik'e daga kan kujeran,Sp khamis sai faman Murmushi yake don confidence din yarinyar ya burge shi,irinsu zai yi matukar wuya a cucesu suyi shiru,
A kausashe Dpo ya fara magana idonshi akan su goga"akwae wani shaidan da ya wuce ku masu lalata yaran mutane,duk irin yadda aketa fadakarwa da gargad'i amma abanza bakwa ji ko,kun lalata rayuwarku da shaye shaye hakan bai ishe ku ba sai kunbi yaran mutane kuna lalatawa,to tunda bazaku daina ba mukuma bazamu yi kasa a gwiwa ba wurin ganin an yanke ma duk wanda yake aikata irin wannan laifin hukunci,Don ubanku duk sai kunje gidan yari",a fusace ya kai maganar,gaba dayansu suka rud'e,gaye har ya fara kuka,kwalla nata zubowa daga idanunshi,magiya suka shiga yi ma dpo suna sun tuba bazasu kara ba,
"Yalla6ai ka wa Allah da manzonsa ka yafe mana,wllh ba halinmu bane sharrin zuciya ne,amman munyi alkawari bazamu sake yunkurin aikata hakan ga kowacce yar......" tun kafin goga ya rufe baki fatuu ta katseshi a fusace"sa6a lamba(sarar su ce a makaranta da mutum yayi k'arya ko ya fad'i abu ba daidai ba,sai suce sa6a lamba),karyane yalla6ai,wllh k'arya yake lokacin da suke k'okarin yi man fyaden wannan gayen na hanashi cewa yayi wllh sai yayi wai rabonshi da ya samu irin damar tun akan wata hajara,to yalla6ai sunan Akuya ne hajaran ba mutum ba?kar ka yarda wayo zai maka"ta k'arasa tana ta huci tana hararar goga,kaman zata kai mashi bugu,hannu Dpo ya d'aga mata alamar ta zauna"it's Okey,bazan bari suyi man wayo ba,nagode da bayani"
shi kam Sp khamis d'an juyar da kanshi yayi yana dariya,haisam dai na zaune yayi shiru kanshi na kallon k'asa yanata sauraransu don yasan abunda yafi hakan Fatuu zata fada ne.
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_
_*BY ZAINAB LALUH📲*_
~(Oummu Imam)~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*4️⃣2️⃣*
Kallonsu Dpo yayi tun kafin ma yayi magana goga yasha jinin jikinshi sai faman zare ido yake,
"Wacece ita hajarar??"zare ido goga yayi ya fara inda inda,hannu Sp ya d'aga zai kwasa mashi mari da sauri goga ya idasa durkushewa yace"zanyi bayani..." sauke hannu Sp yayi fusakarshi a d'aure yace "uhun" alamar yayi magana,
Juyawa yayi ya kalli Dpo"Yalla6ai ita wannan Hajarar wllh ba fyade nayi mata ba,dama ita ta saba,yar talla ce in dae za ka siye abunta to zata baka had'in kai da ka buk'aci hakan,sau d'aya wani abu ya shiga tsakanina da ita,kuma ko lokacin ta riga ta saba kuma tun daga nan ban k'ara yin wani abu da ita ba,an ma dad'e da hakan ta faru,ni yanzu ma wllh bansan a ina take ba ga 6aure nan ka tambayeshi wllh zai fad'a maka gaskiya don shima yasan hajarar kuma shima wani abu ya ta6a shiga tsakaninsu",
gaba d'aya idanunsu suka koma kan 6aure dake ta zaro ido yayi wuri wuri,tun kafin ma a tambayeshi ya fara magana"Wllh yalla6ai duk abunda ya fad'a gaskiya ne,yanzu mu bama musan a ina take ba",
Jinjina kae Dpo yayi,a kausashe ya fara magana"I don't care da ta saba ko bata saba ba,all i know is that kun bada gudummawa wurin lalata rayuwar ita yarinyar,Ku yanzu idan k'anwarku ce ko diyarku zaku so ai mata haka?wato don ita ba wata bace a wurinku shiyasa baku damu da yadda rayuwarta zata kasance ba saboda tsabagen mugunta,kun manta da cewar duk abunda kayi ma yar wani kaima za'ayi ma yarka ko kanwarka ko ma matarka,yanzu idan ku ka auri mata irin ita hajaran na tabbatar bazaku zauna da ita ba,in kuma kun zauna da itan tofa zata rayu ne cikin Wulakanci da kaskanci saboda ta riga ta saida mutuncinta tun awaje bakuyi wannan tunanin ba akan ita hajaran da kuka aikata ma hakan ba saboda son zuciya,kuma da kuke cewa an dade da kuka aikata hakan gareta ai ba bari kukai ba tunda gashi yanzu kunzo kuna yunkurin aikata ma Wata"dakatawa yayi yana maida numfashi,su haisam dae sun natsu suna saurararshi yaci gaba"Addininmu addini ne na yanci,ya bamu damar auren mata daga daya har zuwa hudu,idan son abun kuke why not bazaku yi aure ba...." Fatuu ta katse shi tace"atoh"tayi maganar had'i da gyad'a kae,kallon k'asan ido haisam yayi mata da sauri ta sadda kai,
Dpo ya d'aura"gaba daya kun bi kun lalata rayuwarku,look at u don Allah,sam baku da wani buri kuna matasa masu jini a jika amman kuna neman kashe rayuwarku,ku kalle ni,ku kalli kowa dake wurin nan muma mutane ne kaman ku, inda munso sai muma mu lalata tamu rayuwar amman bamu za6i yin hakan ba don munsan ba hanya bace mai 6ullewa,mun tsaya munyi karatu gashi yanzu muna cin ribarshi,gaba daya munyi aure muna da iyali kowa girmama mu yake,kufa ba wani uba na gari da zai baku auren diyarshi a irin halin da kuke ciki,mutane gudunku suke saboda kun zama tamkar liability a garesu da kun gansu sun san da wuya in baku rok'e su kudi ba,yan siyasa su yi amfani daku don su ci za6e a d'irka maku kwayoyi don kuyi hatsaniyar da zata sa dole su ci,da zarar sun samu mulkin shikenan amfaninku ya k'are a wurinsu,wani kuda ku ganshi sai dae ko a TV,yana can yana jin dadi shi da iyalinshi,Wani fa ko da mahaifiyarka da ta tsugunna ta haifeka har yaci moriyarka kaje magashiyyan rai hannun Allah da sunan kana son ganinshi ya taimaka maka baza'a ta6a bari ka ganshi ba,kana ji kana gani karshe sai dae ta fadi ta mutu a gabanka akan wasu yan Kud'in da dakun tsaya kun gyara rayuwarku wallahi tallahi kunfi karfinsu,ko dama ba duka ba baku rasa wata hanyar da zaku samu,ina maku wannan Nasihar ne ba wai don bani da aikin yi ba ko ba za'a yanke maku hukunci ba,na kuma tabbatar ba lalle ku d'auka ba,sai dae duk wani wanda aka kawo mana nan ina kokarin ganin nayi mashi Nasiha,idan Allah yasa yana da sauran dama agaba in ya gadama yayi amfani da ita in bai gadama ba yayi watsi da ita,Amman mu munfi son ayi amfani da itan don ba dad'i muke ji ba ayi ta kawo mana masu laifi,burinmu kowa ya zamo nagari"d'an dakatawa yayi,a hankali fatuu ta kalli haisam ganin ba ita yake kallo ba yasa ta kalli Dpo tace"Yalla6ai,d'azun naji kace duk kuna da mata da ya'ya,shifa Yaya Handsome bai yi aure ba har yanzu" tun da yayi maganar ashe abun ya tsaya mata,tana son tayi masa magana tsoron kallon da haisam yayi mata d'azun ne yasa tayi shiru,amman sam ta kasa jurewaa saida ta tanka,
d'an Murmushi Dpon ya yi, don daga d'an zaman da suka yi tsaf ya karanci halin Fatuu,
"To ai k'ilan ra'ayin auren ne shi Yaya h......", kasa fad'in sunan yayi don bai fahimci yadda tace ba,kallon haisam yayi"wai ya sunan yake ne?"kafin ya bashi amsa Sp ya rigashi"Haisam ne sunanshi,ita naji kaman Handsome take cewa"ya k'arasa yana dariya, jinjina kai Dpo yayi da d'an murmushi yaci gaba"Yauwa to kilan bai tashi yin auren bane,amman nasan yana da kudin yin auren tunda yana aiki ko"kai ta d'aga"eh yana aiki "gyad'a kai Dpo yayi"to kinga shima yayi karatunshi yana aikinshi,su wad'annan sun ki tsayawa su yi karatun balle suci moriyarshi,kan Naira hamsin sai su fitar ma junansu jini" dan kya6e baki tayi tana kallon su goga,
"Yanzu Sp ina ganin kawae zamuyi filing case d'inne mu mik'a su kotu...." tun kafin ya rufe baki Gaye ya d'aura hannu aka"Don girman Allah yalla6ai ka rufa man asiri,wallahi tallahi ni ba ruwana ba yadda banyi dasu ba akan kar ayi mata ko itama ta fad'i hakan"yana yin shiru Goga ya kar6e"Yalla6ai mun tuba,a yafe mana don Allah zamu yi amfani da nasihar da kayi mana,dama wllh ba wanda ya ta6a zaunar damu ya nuna mana illar abunda muke yi shiyasa...."tun kafin ya rufe baki Dpo ya daka mashi tsawa"karya kake,har ni zaka fad'i ma hakan,duk irin fadakarwar da ake yi ba dare ba rana a kafafen sadarwa, besides,baku da iyayene?ko kana son kace man suna jin dad'in halin da kuka jefa rayuwarku??" shuru goga yayi ya duk'ar da kanshi,sai lokacin haisam ya d'ago ya kallesu tun bayan da aka shigo dasu,Calmly ya fara magana yana nuna gaye"shi wannan babanshi ma is an Imam a Juma'at mosque dake nan Unguwarmu"girgiza kai suka shiga yi gaba dayan su,
"Look at it pls,kana d'an liman kake wannan rayuwar ina amfani don Allah,na tabbatar banda fad'a da yake ma har zubar da kwallarshi bai rasa yi akan ka....."hannu fatuu ta d'an daga alamar zatayi magana,har saida gaban su goga ya fad'i rass duk da basu san abunda zata fad'a ba,kallonta sukai gaba daya Dpo yace"Zarah akwae abunda kike son cewa ne?"
kai ta d'aga mashi"na tuno wani abu ne,ai na fad'i maka shi wannan gayen baiso ba ko,shi wanccan gagon ne ya matsa masa,to lokacin da yace mashi a kyaleni babban laifine sai kuma yace na san gidansu in suka aikata man Asirinsu zai tonu ne,to shi gagon sai cewa yayi wai shi wawa ne da zai bari asirinsu ya tonu,wai akwae abunda zasu yi,shine yace ma gayen ya kawo kunnansa ya rad'a masa wata magana ni dae bansan miya ce mashi ba amman naga gayen ya firgita ya zaro ido yana girgiza mashi kai alamar a'a,to Yalla6ai ka tambayesu kaji miye yace zasu yi man don kusan abunda suke aikatawa in suka yi fyaden don kar a gane su",tun kafin takai k'arshen maganarta cikin gaye yayi wani kuka ji kake kuuuu,gaba daya suka shiga tsantsar tashin hankali,da ka kalli fuskokinsu zaka gane basu da gaskia,
Gaba daya idanun kowa ya dawo kansu alamar su ake jira suyi magana,su kam sai faman zare ido suke,gaye tuni jikinshi ya fara kerma,a hankali goga ke dan ta6a cinyarshi alamar ya natsu amman ina tuni zufa ta fara wanke mashi fuska,
"Bazakuyi magana bane,miye zaku yi mata bayan kun yi mata fyaden wanda bazai sa agane ku ba???"Dpo ne yayi maganar ya tsaresu da ido ba alamun wasa atattare dashi,inda inda suka fara an rasa wanda zai yi magana sai faman zungurin gaye goga ke yi alamar kada ya fad'a,suna cikin hakan ta bayansu ba zato ba tsammani Sp ya shiga faffaska masu mari hannu bibbiyu,gaba dayansu sai da suka baje suna ta faman zabga salati,
Furiously Sp yace"zaku yi magana ko sai ansa ku" gaye ne ya d'ago yana motsa baki kamar zai yi magana,sai dai tsoro ya hanashi,
"Kai naga kafi su gaskia,tell me miye yace zaku yi mata" Dpo ya fad'a yana kallon Gaye,baki na kerma ya soma cewa"Yalla6ai zan fad'i maka gaskiya,amman don Allah na rokeka ka yafe man,wllh ni ba ruwana"kai ya d'aga masa alamar to,kafin yace"ina jinka"
Duk yadda goga yaso hana gaye ya k'asa,don gaba daya idanunsu na akan gayen,cikin en ina gaye ya fara magana "C...ce...cew...cewa ya..yi in munyi mata mu k....kashheta" Wata zabura fatuu tayi lokaci guda kallabinta ya fad'o kasa,ya rage daga ita sai riga da skirt din jikinta dama gyalenta tuni yabar jikinta,lokaci guda ta furgice ta gigice,kwayar idonta kaman zasu fad'o kasa,ta matukar razana,nan da nan jikinta ya fara rawa kamar mai jin sanyi da kyar ta iya bud'e baki ta fara magana"Yalla6ai DOP kaji da kashe ni zasu yi in sunyi man fyaden,Yaya handsome da baka zo ba kashe ni zasu yi...."maido idonta tayi kan Sp"d'ayan Yalla6ai kaji wai kashe ni suka so yi acikin kangon in sun gama...."baiwar Allah duk ta furgice,sai kiran Dpo take da dop,dama tunda zasu shigo taga sunanshi asaman kopan shiga office d'in,gaba daya hankalinsu ya matukar tashi haik'am da jin abunda su gaye sukai niyyar aikata ma fatuu,gaye kam kuka yake wi wi yana fad'in shi ba ruwanshi wllh,Wata gigitacciyar tsawa Sp ya kwatsa masa had'i da buga table"ka rufe mana baki,idan ba ruwanka uban miyasa ka bashi had'in kai,shi ubanka ne da zai tursasa maka dole ka aikata ba daidai ba,ko ubanka yace ka aikata ba daidai ba ba'ace kai masa biyayya ba bare wani,duk zaku yabawa aya zakinta wllh",
shi dae dpo zuru yayi yana kallonsu hakan yasa goga fara yi mashi magana"Wallahi tallahi Yalla6ai,na rantse da sarkin da yake busan numfashi ba ina nufin zamu aikata mata hakan bane,shi gaye ne naga kaman bazai bamu hadin kai ba saboda ta sanshi,shiyasa na fad'i masa hakan,amman wllh bani da niyyar kashe ta kaji na rantse"Dpo da yayi still yana sauraranshi ya daki table yace"Ubanku zaku ci"d'ago kai yayi ya kwalama sergeant dake bakin kopa kira,shigowa yayi ya sara mashi,dpo yace"take dem back,where is corpral Gajere?",
"Ya fita siyo abu ne",
"Ok,in ya dawo tell him to have meeting with dem",
"Okey Sir"daga haka ya tasa su gaba,gaye nata kuka shida 6aure,goga kam idanunsa sun kad'a sunyi jawur tsananin tashin hankali,Allah sarki Gaye,dama ance son zuciya bacin zuciya,Saboda kar a hanashi kayan maye ya jefa kansa a tsaka mai wuya,Allah ya rabamu da aikata aikin danasani,Ameen.
Ana fita dasu gaye fatuu dake tsaye tayi tsuru har lokacin jikinta kerma yake,ta kalli Dpo tace"Yalla6ai Dop fitsari nike ji"jinjina kai yayi kafin yace wani abu Sp ya leka waje yana kwalama Corpral Jummai kira,ba tare da 6ata lokaci ba jumman tazo sanye cikin uniform,tana da d'an tsawo da jiki,hakan yasa kayan suka yi mata cuf cuf,sara masu tayi had'i da fadin"Sir",nuna mata Fatuu Sp yayi"ki kaita Toilet ",ta amsa da Ok,daga haka ta nufi fatuu idanunta akan haisam da ya sadda kai yana ta6a wayarsa,ruko hannun fatuu tayi tace ma haisam" Barka da rana",Slowly ya d'ago suka had'a ido,cikin cool voice dinsa yace"Yauwa,ya aiki",da sauri tace"Alhamdulillah,gamu a cikinsa",kai kawae ya jinjina kafin ya maida idonsa kan wayarsa,still dpo yayi yana kallonta,shikam Sp khamis juyar da kanshi yayi yana dariya,cikin ransa yake fad'in"su jummai anga kyakkyawa",
Tsaye Jummai tayi tana jiran fatuu ta fito daga cikin toilet",fitowa tayi tana gyara skirt dinta,jummai ta kalleta da murmushi"har kin gama?" kai fatuu ta d'aga mata,
"Ya sunanki ne" tace"Fateema"dama abunda yasa tace ma su Dpo sunanta Zarah saboda haisam ne kada ta fad'i sunan mamanshi a gabanshi,jinjina kai corpral jummai tayi,kafin tace"Wannan da kuka zo dashi yayanki ne?" kai ta kara d'aga mata,
Inda inda jummai ta shiga yi kafin ta kuma cewa"kinsan Number d'in wayarshi ki bani?"wani kallo fatuu tabi ta dashi har sai da tasha jinin jikinta,a hankali ta girgiza mata kai"ni bansan number din shi ba,nida ba waya gare ni ba",
Hannu jummai ta kai ta dafa kafadarta"Ok muje,amman karki fad'a ma kowa na tambayi no dinshi kinji",a hankali tace toh,uhmm jummai bata san wacece fatuu ba,ba don halin da fatun take ciki ba nasan tana komawa cikin Office din sai ta fallasa ta,
Suna zuwa bakin office din,jummai tace mata ta shiga ita kuma ta wuce,bayan fatuu ta shiga iske su tayi su ukkun suna cikin tattaunawa,nuna mata kujerar da ta tashi Sp yayi alamar ta zauna,idonta akan haisam ta zauna,d'an kallonta yayi kafin ya janye idonshi,gyaran murya Dpo yayi"Kema Zarah kina da laifi"a firgice ta kalleshi,yaci gaba"miyasa zaki je wurinsu karfe goman dare bacin kinsan me suke aikatawa awurin,ko bama