Showing 66001 words to 69000 words out of 212491 words

Chapter 23 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

968

kaman an tura biredi" yar dariya haisam yayi jin abunda tace,

Mikewa tayi tace"to ka nuna man yadda zan canja kallon,d'agowa yayi ya shiga nuna mata sannan ya mik'a mata ta koma inda ta taso ta fara caccanja channels d'in,in ta fara kallon wannan sai ta canja ta koma wannan shi dai yana ta bin tv d'in da kallo,can ta kamo wata tasha ta turawa saurayi da budurwa suna romance,budurwar nata kakkaucewa shi kuma saurayin na kara jawota kaman wani maye k'okarin saka bakinshi yake a cikin nata da sauri Fatuu tace "A'uzubillahi minash shaitanir rajim,wannan d'an iska ne irin su Gaye.." k'okarin juyowa tayi haisam na ganin hakan yai saurin d'age kansa akan bayan kujeran yana facing sama pretending he's not watching the tv,

"Yaya handsome", fatuu ta kira shi,shiru yayi kaman bai ji ba,ta k'ara kiranshi sai lokacin ya dago ya kalleta had'i da d'an dage gira" ya akai?" turo baki tayi tace"wannan tashar ta yan iska ce wllh ka cire shi,ko kuma in baka iya ba kasa azo acire ta,irin su gaye ne fyade ake yi,kalli ka gani..." ta juya zata nuna mashi lokacin budurwar ta amince mashi har sun had'e bakunansu sun wani rurruke juna,da sauri fatuu tasa tafin hannun hagunta ta kare gefen fuskarta, "ka gani ko,itama ashe yar iska ce,wllh ka daina kallon irin wannan kar kaima su maida kai d'an iska kai da ba ruwanka atoh" still haisam yayi ya d'an daure fuska,duk da tun farko taso bashi dariya,

jin abunda tace yasashi cewa"don kin ganshi sai aka ce maki ina kalla",
"to amman kai kasa ko?" girgiza mata kai yayi Calmly yace"haka suke",
"a cikin dish din?" kai kawai ya daga mata,ta6e baki tayi tace"so suke su iskanta mutane,Allah ya shirye su,don Allah yaya handsome duba man kaga sun daina"ta fad'a har lokacin hannunta na kange da gefen fuskanta,
D'aga idanunsa yayi ya d'an kalli tv kafin ya maida idon kanta"to mi ya kai ki nan,ba inda ake yin hausa kika ce kina son kalla ba?" ya yi maganar fuskarsa ad'an daure,da sauri tace"gani nayi su duk basu wani sabon abu fa shine nike neman tashar yan indiyawa kawae sai gani nayi na fad'o awannan,k'ilan ma wllh su suka ja ni na kamo nan don inga iskancin da suke",

yar harara ya wurga mata yace"jiyan ma inda kika je ai jan ki akai ko" da sauri ta sunnar da kai k'asa,can ta d'an dago idanunta taga ita yake kallo hakan yasa ta d'ago kan gaba daya tana kallonshi itama,sigh yayi kafin ya fad'i mata lambar da zata kamo Mbc Bollywood d'in,da sauri ta juya ta canja sai gashi ta kamo ana yin wakar india,gaba daya ta maida hankalinta kan tv d'in ta fara d'an jujjuya kanta tana yin rawar itama,

Kallonta haisam yai tayi ganin yadda take rawa daga zaune hankalinta a kwance,hakan yasashi cikin ranshi yin tunanin da suna da kayan kallon k'ilan da bata rinka fitowa tana yin rigima ba don zasu rinka dauke mata hankali,bayan wasu mintuna ya duba time a wayansa ukku saura kwata,hakan yasa ya mik'e ba tare da ya d'auki wayarshi ba ya nufi Bedroom dinsa,juyowa fatuu tayi ta bi shi da ido tana kallon yadda yake yin tafiyan a hankali har ya shige cikin corridor d'in sannan ta juya kan tv taci gaba da kallo.

Almost 40 minutes ya d'auka kafin ya fito,k'amshin turaren jikinshi ne ya bugamma fatuu hanci hakan yasa ta d'ago da sauri ta kalli bakin corridor din,baki bude take kallon haisam da ya fito cikin jeans bak'i da t-shirt fara ta mashi cif a jiki,k'irarsa ta kakkarfa ta bayyana,a gaban rigar anyi babban rubutu bak'i ansa XL,gashinshi a nad'e yasha gyara sai salki yake,ganin ta k'ura masa idanu yasa ya kauda nasa idon dama shi baison kallo,nufo inda fatuu take zaune yayi daga gefenta ya aje mata abubuwan da ya ruk'o a hannunsa kafin ya juya ya nufi inda desk yake,laptop d'in dake asamanshi ya d'aukko ya dawo cikin falon,inda ya tashi ya koma ya zauna ya jawo c-table ya d'aura computer d'in,budeta yayi ya fara kokarin kunnata,

K'ura ma abubuwan da ya aje mata ido tayi wanda Milk pop corn ne anyi sealing dinsa a leda da k'aton biscuit sai wasu manyan chocolate guda biyar wanda ko ledar da aka nade su abun kallo ce,cike da mamaki ta juya ta kalli haisam wanda keta operating laptop d'in gabanshi,
"Yaya Handsome" fatuu ta kira sunanshi,ba tare da ya kalleta ba ya d'age gira"yess"ya amsa, ta ci gaba"wannan abubuwan da aka ajiye a gabana fa,mi za'ai dasu?" still bai kalleta ba yace"kallonsu zaki yi" tace toh,

bayan wasu yan mintuna ya yi mata kallon k'asan ido yaga ko ta fara ci,don yaga jiya da yayi mata gatse ta gane har tace irin abun gwaggo,aikuwa cike da mamaki ya idasa d'ago kanshi yana kallon ikon Allah,ashe bata ma d'auki komae ba, yadda yace matan tayi,wato k'ura masu ido sai kallonsu take tana hadiye miyau,Murmushi Haisam yayi ya d'an girgiza kai"Zarah" ya kirata, juyowa tayi ta kalleshi ta gwalo ido,gently yace"u can eat" fuskarta d'auke da mamaki ta juya ta kalli abubuwan kafin ta sake juyowa ta kalli haisam "yanzu duka wannan ni ka ba in ci?" kai kawae ya d'aga mata,
d,aukar Pop corn din tayi ta fara kokarin budewa dama duk shi yafi tafiya da ita saboda madarar da ke cikinsa,

"Wllh Yaya handsome kai mutumin kirki ne,yanzu duk abunda nayi maka kuma ka bani wannan kayan dadin,harfa ciwo naja maka"

"Gashi ma kinzo ko abun ciwo baki kawo man ba" haisam dake ta latsa computer ya fad'a,
"To ai mu fa bamu da irin wad'annan kayan dadin wllh,ko Kawu Amadu bai saida su,to ko inje in zubo maka abinci"?
Girgiza mata kai yayi alamar a'a,tace"shinkafa ce fa"sosae ta bashi dariya amman sai ya basar,ya lura tana son shinkafa don ko jiya ta ambace ta,
"Ko baka cin shinkafa ne?"ta tambaya,
"Ina ci,amman yanzu na koshi ne" gyad'a kai tayi daga haka ta fara tura Pop corn din a baki,wani kalan dadi ne ya ratsa cikin bakinta,lokaci guda ta fara k'okarin gyara zamanta gaba daya ta d'aura kafafunta asaman kujeran ta lankwashe su tayi zaman cin tuwo,mutsu mutsun da take yi ne yasa ya d'an yi mata kallon k'asan ido dai dai ta juyo da alama magana zatayi suna had'a idanu tace"don kar na 6ata maka k'asan parlon yasa nayi haka" jinjina kai yayi kawae.

"Wllh yan gayu sun ji dadinsu,Allah muma kasa mu a Aljanna muci kayan dad'i tunda nan mu ba masu kudi bane balle muci,komai na masu kudi na daban ne" tana maganar tana taunar Pop corn d'in har wani lumshe ido take da alama santi takeyi,haisam na jin duk abunda take fad'a bai dae tanka mata ba,
can ta juyo ta kalleshi"Amman dae Yaya handsome wannan guggurun na kasar yan turanci ne ko?" ya fahimci tana nufin yan kasan waje,girgiza mata kae yayi"na yan kasan hausa ne" ya bata amsa,
"To a ina ake yin shi Abuja ko lagos",

" ki duba jikin takardar ciki" da sauri ta ciro yar takardar tana dubawa,cike da mamaki tace"kai wai anan garinma ake yinshi,tabb lalle amman mu an raina mana wayo,kasan wanda ake kawo mana makaranta wllh duk tsakuyoyi gashi ba madara kuma duhu gare shi duk ya k'one,kasan mi?" girgiza mata kai yayi alamar a'a,
"Shi fa ko sugar babu sosae kuma da gishiri suke had'awa da sugan kana ci kana cin gishiri,kawae dai mu don anga talakawa ne ake mana irinshi mugaye kawae" daga haka ta ci gaba da taunar Pop corn d'in tana jujjuya kai,

"Ba kina zuwa Islamic school ba?"haisam da ya d'ago yana kallonta ya tambaya,
"Eh amman lokaci bai yi ba sai an kira sallah,sai inje in shirya" nodding kai yayi,sai kuma yace"dama kenan baki wanka",
Cakk ta tsaya da taunar pop corn d'in ta juyo baki cunkushe"wllh ina yin wanka,duk yanmatan unguwan nan nafi so yin gayu" jinjina kae kawae yayi da d'an murmushi ya maida kan aranshi yana fad'in wai duk yanmatan unguwannan ko ina abun yake,

K'okarin mikewa tayi ta kwashe su biskit d'in ta rungume ta nufi hanyar fita tana fad'in"bari inje inyi wankan to kafin a kira sallan" d'aga mata kae yayi ba tare da ya kalleta ba,ita kam tana nufar kopar fita amman idonta na akanshi ba k'aramin kyau yayi mata ba,yadda ya duk'ar da kanshi sumar kanshi mai matukar kyau da tsawo ga daukar ido a nad'e,ga ta gefen fuskan a kwance luf haka hannunshi da yake latsa computer dashi duk suma liya liya a kwance,
tana kaiwa bakin kopan ta tsaya"Yaya handsome"ta kira sunanshi,sai lokacin ya d'ago ya kalleta had'i da dage gira alamar amsa kiran nata,fuskarta d'auke da murmushi tace"thank u so much da abubuwan da ka bani"d'an murmushi yayi ya jinjina kanshi,daga haka ta juya ta kama handle d'in kopan ta bude,sake juyowa tayi ta k'ara kiran sunanshi,kallonta yayi "What" runtse idanunta tayi tace"A wodi masha Allah" tana fad'in hakan ta juya da gudu ta fita,shiru yayi yana tunanin ko mi take nufi da abunda ta fad'a don ya fahimci fullanci ne tayi,koma dae miye yasan ba rashin kunya tayi ba don ta had'a da masha Allah,dan ta6e baki yayi yana k'okarin juyawa aka turo kopan,itace ta lek'o da kanta tanata dariya duk dimples dinta sun lotsa sosae"yaya handsome kasan mi nace?" d'an girgiza mata kai yayi alamar a'a,
"Cewa nayi kana da kyau masha Allah" rasa abunda zaice mata yayi kawae yaci gaba da kallonta,hakan yasa ta kyalkyace da dariya ta janye kanta ta turo mashi kopan,haisam dake kallon side d'in kopar d'an murmushi hadi da girgiza kai yayi daga haka ya juya ya ci gaba da abunda yake.


Sai da ta koma gidan sannan ta tuna da gwaggo tace ta share kitchen da tsakar gidan,da sauri shaf shaf ta share su kafin ta zuba ruwa ta shige band'aki don yin wanka,bayan ta fito tasa Uniform tayi sallah sai lokacin ta dan zubo abinci ta ci kafin ta d'auki jakarta ta fito don tafiya islamiyya lokacin kusan karfe hudu da rabi.

Da sauri take tafiya bayan ta fito ta hau hanya tana gab da shan kwanar gidan hajiya taji an kwala mata kira"Fatuu" da sauri ta juyo ganin haulat ce yasa ta tsaya har ta k'araso wurinta"ya akai kika makara yau keda baki makara?"haulat ta tambayeta,
"Gwaggo tasa in yi mata wani aiki" fatuu ta bata amsa bayan sunci gaba da tafiya,jinjina kai haulat tayi kafin tace"in muka dawo sai muje in raka kin abashi hakurin" kallonta fatuu tayi ta d'age gira"wa kenan"ta tambaya cike da rainin wayo,

"D'an gidan Hajiya mana da kika fasa ma glass ko" wata yar iskar dariya tayi tace"sai dae ko ni in rakaki ki bashi hakurin"da sauri Haulat ta kalleta" yo ni hakurin mi zan bashi kamar dae ni na fasa masa glass din...." fatuu ta katseta"to wadda ta fasan taje ta bashi hakuri kuma ya hakura" zaro ido haulat tayi cike da zumudi tace"don Allah da gaske kinje fatuu,kuma ya hakuran?"
"Bari kiga dil" fatuu ta fad'a tana kokarin bud'e cikin jakarta,biscuit da chocolate din da haisam ya bata ta fiddo harda ledan d'an sauran Pop corn da bata k'arasa cinyewa ba,ta mik'a ma haulat,

Cike da mamaki baki bude haulat ta kar6a"wai don Allah da gaske kike shi ya baki wadannan abubuwan?" fatuu tace"eh mana shi ya bani,kuma yace ya hakuri amman fa sai da yasa nayi masa alkawarin na daina rashin ji ko fad'a yace kar ya sake ganina ina yi"ta k'arasa tana yar dariya,
cike da farinciki haulat tace"kai amman wllh naji dadi da ya hakura,daman nayi tunanin zai hakuran don ni banma yarda da maganganun gaye ba,amma fa nayi mamakin saukin kanshi keda kika yi masa laifi wai kuma har ya baki wadannan kayan dadin",

"kinsan ni d'in jinin sa'a ce" fatuu ta fad'a tana murmura idanu ",
"Ah lallai ni ce sheda,jinin sa'a mai kukan za'a kaita gidan yari ta rink'a cin gabza kwarkwata ta gwaigwaye mata kai ba,yar rainin wayo zaki wani gaya man jinin sa'a bayan kin gama 6are ma mutane baki"haulat ta fad'a tana dariya itama fatun dariyar take,ta bude chocolate guda ta tura baki,kallon haulat tayi "ke ba zaki sha ba",

"Gani nayi akan hanya muke..." fatuu ta katseta"yo miye ina ruwanki da wani kuma ma hanyar ai ba wasu mutane" haulat tace to ta 6are guda itama ta tura cikin baki ta fara taunawa"wai fatuu micece gabza?"fatuu da dad'in chocolate ya ratsata har cikin kwanyarta ta d'age idanu tace"oho ni wllh bansan miye gabzar ba,kaman dae abincin gidan yari ne,kuma ni abunda ya tada man hankali dana ji gaye yana neman tsari da ita,har fa cewa yayi wai yana taka tsantsan kar akaisa gidan yari saboda tuwon babarsa..." tunda ta fara magana haulat ke kyalkyatar daria hada dafe ciki"yanzu ashe dama baki san ma micece gabzar ba amman kika tashi hankalinki,nifa wllh tun farko ma ban yarda da duk abunda ya fad'a ba tunda d'an shaye shaye ne fa yawancin kalamansu duk k'arya ne,amman gwara ma da akayi hakan koma karyan ne ni wllh naji dadin hakan..." fatuu ta katseta"wayace maki karya yake,da gaske ne don saida yace wai lauya d'insa ne bai a gari shiyasa ba'azo aka kamani ba",

Jinjina kai kawai haulat tayi don daga jin maganar ta san mutumin wasa yake amman bata nuna ma fatun ba tace"yanzun dae ai dole ki daina rashin ji tunda kinyi masa alkawari in ba haka ba atafi a had'e da gabza tunda dae ba kudin shanu gomaa da za'a biya shi" ta k'arasa tana ta tik'ar dariya,hakan yasa fatuu d'aga jakarta zata buga mata da sauri haulat ta ruke jakar"ke fatuu baki da hankali ne akwae fa Al'qurani aciki" cigaba da tafiya sukae haulat nata tsokanar fatuu har suka kae islamiyyar,sun dae makara sosae hakan yasa aka yi masu bulalar makara kafin suka shige aji.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_*A heart touching love story.*_


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F


_*BY ZAINAB LALUH📲*_


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


*3️⃣5️⃣*

Bayan antashi islamiyyar atare suka taho kaman yadda suka saba sai lokacin suka bud'e biskit d'in suna ci,hannu fatuu tasa ta dafa kafad'ar Haulat"wllh Yaya handsome na da kirki sosae" wani kallo haulat tayi mata tace"waye haka?"
"Yo Dan gidan hajiya mana mai gilashi",
"Haka sunanshi yake handsome? Biscuit fatuu ta tura abaki"a jikin rigarsa naga an rubuta call me handsome daya ji ina kiransa da sunan shine yace man wai ba sunanshi haka ba sunan shi ko Haisam to ni kuma sai naga ai duk d'aya ne ko" kyalkyalewa da dariya Haulat tayi"wllh fatuu kin cika iskanci ta ina handsome da haisam suka zama d'aya,handsome fa turanci ne haisam kuma ai kaman larabcine" fatuu dake taunar biscuit tayi wata yar iskar dariya"to ni dae nafi jin dadin cewa handsome kuma ai ya dace da sunan tunda yana nufin mai kyau kuma shi d'in mai kyaun ne"girgiza kae kawai haulat tayi suna ci gaba da tafiya,

"k'awata nagode sosae da shawarar da kika bani kinga tayi man amfani kaman dae yadda duk in kika ban shawara take yi,Allah ya barmu tare har abada"fatuu ta k'arasa maganar had'i da k'ara dafa kafad'ar haulat din,

Murmushi Haulat tayi"ai shiru nayi na zuba maki ido inga in zaki man godiyar kaman yadda kika ce jiya in bari sai shawaran tayi aiki sannan ki goden" fatuu ta langa6ar da kai"ai kinsan dai inada hankali nasan daidai ko,dama ai zan maki godiyar...."katseta haulat tayi"ah kina da hankali kam,ni ce dil nafi kowa sanin k'awata yar fillo d'an kai ne da ita" a fusace fatuu ta juyo ta kalleta"ni ce mai d'an kai?mara hankali fa kenan" ganin haulat d'in tasa hannu ta guntse dariya yasata d'aga hannu zata kai mata bugu, aikuwa da gudu haulat ta juya fatun ta rufa mata baya suka yanki hanya suna ta gudu,cikin haki haulat ke fad'in"Don Allah fatuu yi hakuri kinsan ni ban iya yan guje gujen nan ba,wllh har na fara ganin juwa",

Suna isowa bakin lungun gidan hajiya haulat ta tsaya tafin hannunta guda asaman kirji sai faman haki take,ita kam fatuu koda ta zo wurin amaimakon itama ta tsaya sai kawae ta mik'i hanya straight taci gaba da gudun,cikin d'aga murya haulat tace"fatuu ina za ki?" hannu ta d'ago mata"kije sai mun had'e gobe da safe,zanje wani wuri ne"daga haka tayi gaba,gyada kai haulat tayi ta juya ta shige cikin lungun.

Juyowa fatuu tayi ganin haulat d'in ta tafi yasa ta tsaya da gudun ta ci gaba da tafiya,bakin titi take son zuwa don ta siyo ma Haisam wani abu,bata son haulat d'in ta sani ne shiyasa tayi mata hakan don in suka tafi tare tasan sai ta tambayeta dalilin siya mashi abun kuma gashi ya gargad'eta kada ta fada ma kowa abunda ya faru game dasu gaye.

A dai dai bakin titin ta tsaya ta shiga tunanin mi ya kamata ta siya mashi,ko taje wanccan shagon taga in akwae abunda ya kamata ta siya...."yanmata zo ga kayan marmari masu kyau..."fatuu taji an fad'a daga d'an can gefenta,juyawa tayi ta kalli mutumin da yayi maganar,ya ci gaba"zo ki siya zan maki sauki"shiru tayi tana kallonshi sai kuma ta fara tafiya ta nufi wurinshi,
"Yauwa yar fillo to mi za'a baki" wani kalan kallo ta yi mashi"ni ba sunana haka ba sunana fatuu"ta k'arasa tana turo baki,yar dariya yayi"to ai daga jin sunan naki na fillon ne,ba fatima yake nufi ba?" tace"to ni dae ka kira ni da sunana kawai in ba haka ba in tafiyata" da sauri yace"ah to yi hakuri hajiya fateema dami dami za'a baki ne?"

shiru tayi kaman tana tunanin wani abu"kasan mi,wani ne fa zan siya mawa bai lapiya to kuma su yan gayu ne,ni sai ina ganin kaman ma bazai ji dad'insu ba tunda suna shan su kullum,har lemunan roba dana gwangwani suna dasu cike a fridge",
"Kice saurayinki ne bai lafiya zaki siya masa karin ciwo,hakan nada kyau...." cike da tsiwa ta katseshi"ni nace maka saurayi na ne,yayana fa ne shine zaka ce wai saurayina to bamma siya"ta juya zata tafi,da sauri yace"yaki zo mana,ai ni bansan yayanki bane,to yi hakuri yar fil...au fatima"tsayawa tayi tana mashi wani kallo ta kumburo baki,
"Yauwa kika ce su masu kudine ko,to ai hajiya fatima dama masu kudi ana masu kyauta ne ba wai don abun yafi karfinsu ba sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login