Showing 207001 words to 210000 words out of 212491 words

Chapter 70 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

1001

_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUH📲*_
~(Oumm Imam)~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


7️⃣2️⃣


Bayan shekara biyu

Lokaci ya shude shak'uwa sosae ta shiga tsakanin Haisam da Fatuu a wannan lokacin ya zama tamkar dan uwanta na jini da yawan Mutane ma kallon da suke masu kenan wad'anda basu san ainihin tsakaninsu ba, a babbar sallar data wuce ne ta had'u da Mahaifiyar Haisam suka gaisa a gidan Hajiya lokacin sunzo salla su Jidderh suka nuna mata ita dama tana ta jin Labarinta a wurinsu, yanzu shekararta sha bakwae zuwa sha takwas har sun shiga ss 3 an bata muk'amin Senior prefect wato SP, a islamiyya kuma sunyi sauka an had'a masu gagarumar walima har Haisam sai da yaje wurin taron walimar da akayi a harabar Makarantarsu ya kuma bada gudunmawar kudi masu yawa yanzu a ajin hadda suke, gaba d'aya dawainiyarta Haisam ne ke yi mata ta canja sosae ta koma kalar yaran hutu gashi ta k'ara girma saidae bata da tsawo sosae tsaka tsakiyace baza'a kirata gajera ba ba kuma za'a kirata da mai tsawo ba, a bangaren jiki kuwa abun saidae ace Tubarkallah don tana da k'ira gashi hasashen da gwaggo tayi akanta ya tabbata sak jikin Mahaifiyarta ta d'aukko harma ta zarta ta haka gwaggon ke fad'a don kuwa in ka kalli kafadun Fatuu bazaka ta6a cewa k'ugun dake ajikinta nata bane don ya bud'e sosae har ta cikin Uniform d'inta ana gani haka mazaunanta ma fam suke hakan yasa Sauran Students ke kiranta da Fatuu Bum Bum, har Malamai ma sun san da irin k'irar dake gareta don akwae wata rana zasu yi Cultural dance a club d'insu na English tayi shigar fulani lokacin da suka shigo cikin Assembly hall ita da wad'anda sukayi shigan fulanin gabadaya hankalin malamai da d'aliban dake cikin Hall d'in ya dawo kanta nan da nan malamai mata suka fara Maganar rashin dacewar kasancewarta haka don kayan sun fito mata da shape sosae, jin hakan yasa Formistress d'insu Malama Lubabatu ta kirata bayan sun fita waje tace mata tasa kallabinta ta d'aura a kugu sai ta nemi hula tasa Fatun tace ai k'arami ne sai lokacin ta lura da bai rufe mata kai gaba daya ba tace ta jirata anan tana zuwa ta koma cikin Hall d'in ta samo mata aron farin gyalen wata Malama ta kawo mata ta rufe k'ugun.

Zaune suke cikin Class kowa da abunda yake wasu na hira wasu na rubutu da yake free period ce malamin da ke garesu ya sanar bazai samu shigowa ba, Fatuu na zaune saman seat d'insu dake a farkon layin karshe na ajin ta juya ma allo baya suna hira da wata kawarsu mai suna Fiddausy dake zaune ita kad'ai a kujerarsu sauran wad'anda suke zaman sun tafi yawo wani seat d'in, can tace ma Fatun wai mi Haulat keyi ne ta duk'ar da kanta tun d'azun bata d'ago ba, juyawa Fatun tayi ta kalli Haulat dake gefenta can k'arshen bango ta duk'e kafin ta juya ta kalli Fiddausyn ta d'an ta6e baki tace "kema ai kinsan mi zaisa ta duk'e haka" yar dariya tayi tace "halan karatun Novel take" Fatuu tace "shine fa ta maida abu kamar ibada in batayi ba bata jin dadi Allah yasa ma in tayi auren ta rink'a kula da gidanta"

"Wllh baki sani bane karatunne shiga rai gareshi in kika saba da wuya ki iya bari" d'an ta6e baki Fatun ta k'ara yi tace "tunda fa ana rubuta iskanci ba dole a rink'a jin dadinshi ba" waro ido Fiddausy tayi tace "ke waya gaya maki iskanci ake rubutawa?"

"Haka naji ana fad'i nasan kuma shiyasa gwaggo ma ta hana ni karanta irinsu duk da dama ko bata hana ba nima bayi zanyi ba don banda lokacinshi ta karatuna nike bata shirme ba" girgiza kai Fiddausy tayi "Wllh ba yadda kike zato bane duk da ba k'arya bane Maganar gaskia akwae wanda ba komae ciki sai tsantsar batsa amman kuma akwae masu tsafta wad'anda in kana karantawa zaka k'aru sosae don ana fadakarwa da ilimantarwa ta fannin addini uwa uba kuma zaka koyi abubuwa masu mahimmanci da suka shafi rayuwa ba kamar gamu mata misali zamantakewar aure da dai sauransu wasu har abinci in suka sa anyi acikin littafi zaki ga sunyi bayanin yadda ake yi in kamar sun san ba irin wanda aka saba yi bane, ni kinga ina yin karatun Novel kuma ko Mamarmu ta sani itama tana yi kuma wani lokacin in ta karanta littafi taga yayi ma'ana da kanta take turo man tace in karanta sam bana karanta mara ma'ana don asarar lokaci ne wllh" still ta6e baki Fatuu tayi ta gyad'a mata kai, mik'ewa Fiddausy tayi tace "bari inje inyi Fitsari tun d'azun nike jinshi ina matsewa kar ya zubo man a wando in shiga ukku anma ce fa ba'a son rike fitsari don lalura yake sawa" har zata fita daga cikin seat d'in ta juyo tace ma Fatun bazata rakata ba,

"Ke dai jeki, yadda kurata tayi kuka yanzu da an ganni waje sai ace nayi laifi, bari in baki ma ki siyo man aya" tayi Maganar tana kokarin curo kud'in acikin Aljihun wandon Uniform d'inta, naira dari ta fiddo ta bata tace ta siyo mata ta Hamsin ta d'auki sauran Hamsin d'in don yanzu Fatuu zama da Haisam ta koyi yin kyauta sosae sam abunta bai sha mata kai ba daka nuna kana son wani abu nata sai ta baka ko kuma kazo aro sai tace ta baka kyauta hakan kuma ba k'aramin farinjini ya k'ara mata ba kowa sonta yake tana matuk'ar burge mutane, Godiya Fiddausyn tayi mata bayan ta amshi kud'in ta tafi,

juyawa tayi ta koma tana Facing allo ta duk'a a hankali ba tare da Haulat ta ankare ba taji ta fige yar wayarta da take karatun da ita, a wani firgice ta d'ago koda taga Fatuu ce sai ta wurga mata harara tace "Don Allah ki bani kar ki fitar man inda nike" itama hararar tata tayi tace bazata bata ba, magiya ta hau yi mata Fatun tace "to zan baki amman sai naga abunda kike karantawa in kuma baki bari ba Wllh bazan bari kici gaba da yin karatun ba" sanin halinta yasa tace to ta tsaya ta duba, kallon screen d'in wayar tayi ta fara karanta inda Haulat d'in take, suffar jarumin littafin ake bayyanawa bayan ta gama karantawa ta d'ago ta kalli Haulat tace "Waye wannan kaman Aljani?" dariya haulat d'in tayi tace "Mijin Novel kenan"
"Mijin Novel haka sunanshi yake?"
"A'a haka dae ake cewa wai ba'a iya samunsu a zahiri saboda kyaun da ake sawa suna dashi" da mamaki Fatuu ta k'ara duba wurin kafin tace "wannan ne ba'a iya samu a zahiri?" kai haulat ta d'aga mata "haka ake cewa" yar harara ta wurga mata kafin tace "to wllh ko ni nasan mai irin wannan suffar za'a wani ce ba'a samun irinshi a zahiri" haulat na dariya tace "nima nasan wani mai irin suffar amman ke wanene wanda kika sani mai wannan kamannin?" tace "yo Ya Handsome mana ke baki ga sak suffarshi ce aka bayyana ba"
"Wllh nima ina karantawa shi ya fad'o man a rai" d'an ta6e baki fatuu tayi tace "to ke miye na zama kita karanta kamanin wani Namiji bayan an bayar dake"
"To in banda abunki waya k'i abu mai kyau kuma dae nasan ba samun irinshi zanyi ba, ke dai ai kinji dad'i kinsamu mijin Novel" ta k'arasa tana dariya, da mamaki fatuu tace "ni kuma mukai dake ina da saurayi irinshi balle har ki kirashi da mijina" tayi Maganar tana harararta,

"Ina nufin wanda yanzu kika ce yana da irin sufar da aka fad'i" waro ido Fatuu tayi harda d'an juyawa gefe wai taga ba wanda yaji abunda haulat d'in tace don kowa kallon yayanta yake mashi ido waje tace "ke, nina gaya maki Ya Handsome saurayi na ne yaushe mukai hakan dake?" wata dariya haulat tayi tace "habawa yan mata an gaya maki a banza nike karatun Novel, ai ko yaro yaji labarin tsakaninki dashi zai fahimci son ki yake shiyasa yake maki duk abubuwan da yake maki kawae dai nasan k'ilan lokacin da zai bayyana maki hakan baiyi bane shiyasa bai fito ya nuna maki ba amman ina nan dake zaki ce na gaya maki" wani irin kallo Fatuu ke binta dashi da alama ta kashe mata bakinta don ita tunda take da Haisam bata ta6a sawa aranta wai sonta yake ba can tace "amman dai ai kin fi kowa sanin halinshi in don abubuwan da yake man ne ai ba ni kadai yake ma abun alkhairi ba ko",

"tabbas nasan hakan amman fa ba wanda yake ma kalan naki don ke alkhairin da yake maki special ne, haba Fatuu kiyi tunani mana tun farkon haduwarku abunda ya had'a ku har kawo yanzu gaba daya ya canja rayuwarki dubi uwar dawainiyar da yake dake, ya dauki nauyin ki gaba daya komae shi yake maki, yasa an gyara maku gida an jawo maku ruwa daga gidansu ya siya maku kayan kallo harda Solar aka sa maku ke kanki yanzu d'akinki carpet ne, gaba daya kayan gadonki an gyarasu sun zama na yan gayu don ma nasan saboda na mahaifiyarki ne yasa bai canja maki wasu ba, ji d'ayan d'akin nan da aka idasa gininshi yadda ya gyara maku shi ya zama hadaddan falo, da dai sauran abubuwa da yake maki har ni fa dana shafe ki yana mana alkhairi sosae, yanzu duk sai kice hakanan yake maki wannan d'awainiyar, Come to think of it mana" kasak'e Fatuu tayi tana kallonta don jin zancen take wani iri sam ta kasa yarda da Maganar Haulat d'in ta wani bangaren kuma zuciyarta nason gasgata hakan,

"Ni ina tunanin bari yayi sai kin gama Makaranta sannan ya bayyana yana sonki shiyasa yake ta kulawa da abunshi" tayi Maganar tana dariya, ganin Fatun tak'i cewa komae sai kallonta take taci gaba da cewa "ko baki sonshi ne" ta d'age mata gira sai lokacin tace "amman ai yasan ni karatu nike son yi ni gaskiya ban tunanin hakan" ta k'arasa Maganar tana tura baki,

Haulat tace "Uhm su karatu manya, ke yanzu in yace yana son zai aureki sai ki k'i yarda saboda wani karatu can kin kuwa san irin tsadar da maza irin Yaya Haisam ke yi in ma an samesu kenan, ke baki ganin yadda kowace mace ke sonshi tun da can ma, ai wllh kar ki sake ki bari damar nan ta wuce ki in ba haka ba zaki mugun dana sani ne, yana cewa yana son aureki ki wuff kice kin amince ya aureki kuyi tafiyarku k'asan da zai koma kinga acan cikin sauk'i zaki karatunki ga kuma mijinki a gefe inyee" bakin Fatuu fa ya mutu murus sai zare ido take ga zuciyarta sai wani irin bugu take mata tana fasalto mata face d'in Haisam yana sakin kayataccen Murmushinshi,

"Sai wani faman bina kike da ido kema fa nasan kina son shi...." da sauri Fatuu tace "yaushe mukai haka dake?" tace "Uhm dama ai ke bazaki gane hakan ba tunda yana tare dake kullum, da zaki rasa shi misali kiga wata tayi wuff dashi a lokacinne zaki fahimci kina son shi" ajiyar zuciya Fatun tayi kafin tace a sanyaye don duk jinta take wani iri "amman kina ganin da gaske Ya Handsome na sona kuma zai aure ni?"

"Shakka babu kema don baki karatun Novel ne da da kanki zaki gane haka Mrs Haisam Zakee, wai zanso inga ranar nan Allah yasa kafin inyi aure ne, ke wllh koda nayi aure ne sai nazo don dai nan da Niger ai ba wani abu bane mu da ke k'irjin biki, amman fa zanyi missing dinki sosae in kuka tafi kasan wajen nan ta wani bangaren kuma zanso hakan tunda cigaban kine yar'uwata, wayaga su Fatuu Amarya kuma a gun Handsome wai nasan dai zaisha hauka don ma dai kin d'an natsu yanzu, wata tara ki san6alo mana twins tunda naga suna da gadonsu, kai Ya Allah, har na hango kyawun da yaran zasu yi wllh Madarar kyau" da sauri Fatuu ta kai hannu ta bugi Haulat d'in tace "Wayyo Haulat stop it pls kinsa na fara imagining abubuwa wllh" tai Maganar kaman zatayi kuka Haulat na dariya tace "imagining din mi keda baki san kuna son juna bama, ni kinga bani wayata inci gaba da abunda nafi auki" tay Maganar tana mik'a mata hannu fatun ta bata wayar ta duk'a tana mata dariya taci gaba da karatunta.

Tunda suka yi Maganar take jin wani bak'on yanayi a tare da ita ga suffar haisam da zuciyarta keta tariyo mata, mik'ewa tayi ta nufi hanyar fita daga Class d'in Haulat ta d'ago ta kalleta kafin ta girgiza kai ta koma taci gaba da abunda take, a saman barandar class d'in ta zauna ta jinginar da kanta jikin katangar data rufe gaban Office d'in dake tsakiyan ajin nasu da d'ayan ajin wato Sci B, shiru tayi tana ta tariyo rayuwarsu ta baya ita da Haisam tun daga farkon haduwarsu har kawo yanzu, sai faman sakin Murmushi take, jin shiru Fatun bata dawo ba yasa Haulat biyo sahunta nan ta ganta zaune yadda take da mamaki ta k'arasa wurinta tace "ni duk nayi tunanin fitsari kika je ashe da kina nan kin fad'a kogin tunanin sahibinki" ta k'arasa tana kokarin zama, da Murmushi Fatuu ta juyo ta kalleta tace "wani abu nike ji Haulat wanda ban ta6a ji ba game da Ya Haisam sai yanzu da muka yi Maganar nan dake" Haulat na dariya tace "So kenan yan mata, ai na fad'a maki wllh kina sonshi kawae dae baki san da hakan bane saboda baki san miye son ba to shima nasan hakan take a wurinshi tunda shima ba soyayyar yake ba balle yasan micece ita" gyad'a kai kawae Fatun tayi daga haka suka ci gaba da hiran Haisam d'in har Malamin da zai shiga yazo sannan suka tashi suka shiga Ajin.

Misalin karfe 2 saura kwata aka tashi saidae basu samu fitowa da wuri ba saboda malamin dake da period d'in karshe ya rike su saida suka gama kwafar rubutu sannan, atare suka fito bayan sun gama zasu nufi gate kamar ance Haulat ta kalli gefenta ta hango Motar haisam yazo daukarsu dama wani lokacin in yasamu time ya kan zo ya daukesu amman wurin zuwa kullum shi ke kaisu, da sauri Haulat ta ta6o kafad'ar Fatuu tace "ke ga mijinki yazo d'aukarmu da alama yaji firar da mukayi a jikinshi" da sauri Fatuu ta juyo ta kalli inda Haulat d'in ke nuna mata kafin ta kalleta suka had'a ido suka sakar ma juna murmushi, lokacin da suka k'arasa bakin Motar hannu Fatuu tasa ta bud'e gaba haulat kuma ta bud'e baya ta shiga ganin yana waya yasa fatun yin tsaye ta dafa kopar tana ta kallonshi ba kaman yadda yake yin Maganar a nutse hakan yasata jin yanayin data rink'a ji dazun har bata san ya gama wayar ba ya kalleta ganin tanata kallonshi yasashi d'age mata gira yace "ya dae?" sam bata jishi ba har saida Haulat ta d'an d'aga murya tace Fatuu ana magana sannan ta dawo hayyacinta ta shige cikin Motar tana mashi Murmushi shima Murmushin ya mayar mata ta rufe kopar suka tafi, tunda suka hau hanya take ta faman zabga Murmushi tana juyar da kai saidae duk abunda take Haisam na lura da ita ba tare data sani ba can ya kira sunan Haulat idanunshi akan hanya ta amsa da sauri tace "Na'am Ya Haisam" yace "yau ko kun samu kudi ne a skul" d'an bud'a ido tayi cikin rashin fahimta tace bata gane ba, shiru ya d'anyi don dama sama sama yake Magana da ita can yace "naga friend dinki is in happy mood i thought ko kudi kuka samu" tana jin abunda yace tasa dariya itama Fatun kallonshi tayi tana dariya tace "ai Ya Handsome abunda na samu yau yafi karfin kudi don bai iya siyar manshi" d'age gira yay yace "really, dama akwae abunda yafi karfin kud'i yanzu" da sauri tace "eh mana baka sani ba" d'an ta6e baki yay bai ce komai ba can kuma sai taji yace "inason sanin wane abune haka" d'an juyawa tayi ta kalli Haulat suka yi dariya k'asa k'asa kafin ta kalleshi tace "sirri ne" d'an ta6e baki yay baidae ce komai ba, suna shan round about Fatuu tace "Lah Haulat kalli Baba mai ice cream gaban gidan man can shine yau yak'i kawowa makarantarmu ashe yana nan, juyawa haulat tayi tana kallon inda fatun ke nuna matan kawae sai ji sukai Haisam d'in ya tsaya kafin ya fara reverse da Motar ya tsaya saitin mai ice cream d'in yace ta bud'e ta siya ta amsa mashi da to ta juya zata bud'e kopar ta saci kallon haulat suka d'an bud'a ma juna ido suna guntse dariya, mai ice cream d'in na ganinta ya washe baki yana mata dariya tace Sannu Baba mai ice cream shine yau ka k'i kai mana ka tsaya anan" yace "wllh naje wanccan makarantar kudin ta kusa daku ne to lokaci ya k'ure ban samu na k'araso taku ba har aka koma tara" jinjina kai tayi tace abasu ya tambayi wanne tace Fan ice yace na roba tace a'a ya basu na leda zai fi dad'in sha tunda a mota suke, guda ukku ta amsa manya ta mik'a ma Haulat d'aya ta aje sauran gaban motar tana kokarin curo kud'i Haisam yace ta bud'e glove box ta d'auki 5k ta bashi tana Murmushi tace to, sosae ya shiga yi masu godiya da fatan Alkhairi bayan ta bashi suka tafi, mik'a ma Haisam d'ayan tayi ya dan kalleshi kafin ya girgiza mata kai alamar bazai sha ba cike da shagwa6a tace "pls ka amsa kaifa na amso mawa"? K'ara girgiza mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login