Showing 81001 words to 84000 words out of 212491 words

Chapter 28 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

998

ya matso ya mik'a masa hannu suka gaisan,fatuu na ganin zai juya bayan sun gaisan tace"Yaya haisam bari abaka biscuit da sweet" yadda tayi maganar sai kace wani k'aramin yaro,wani kallo yayi mata da sauri tace"pls"ta marairaice fuska,jin baijin dad'in bakinsa yasa shi cewa"just a Sweet"da sauri tace to,ta juya ta nufi cikin shagon,can sai gata da ledan sweet ta mik'a masa,d'an bude ido yayi batare daya amsa ba,

"Gashi nan duka yace a baka" girgiza mata kai yayi"yayi yawa inada shi a d'aki,just one ya isa"Wani kallo tayi masa"kai Yaya Handsome ya zaka ce d'aya ya isa,don Allah ka amsa duka" k'in amsa yayi ya bita da ido tace"to in d'ibar maka rabi?"girgiza mata kai yayi alamar a'a,ya d'aga mata dogon yatsansa guda alamar guda daya zata bashi,

"To bari kagan yanda za'ayi,zan baka na yawan sunanka ka yarda?" kai ya d'aga alamar eh,
"YAYA HANDSOME"ta d'aga hannunta tana k'irga yawan sunan da yatsunta kafin ta kalleshi"guda sha biyu kenan zan baka"jinjina kai yayi cike da mamakin wai shi zata ma wayo,
Fatuu tace"Kawo hannunka to"ba musu ya bud'e kyakkyawan hannunsa mai d'an fadi da tsawo,tafin hannun sumul dashi tamkar ka ta6a jini ya fito,bud'e ledan sweet d'in tayi ta fara saka mashi da dai daya tana saka gudu shidda ya rufe tafin hannun,da sauri ta d'ago ta kalleshi tun kafin tayi magana ya rigata da fad'in"HAISAM is six letter word,so guda shida ne daidai sunana" cike da shagwa6a ta d'age kai"Wayyo Yaya handsome ni zaka ma wayo..."katseta yayi cikin Sanyayyar Muryarshi yace"Nima ai wayon kika so yiman ko"jin haka yasa fatuu kyalkyacewa da dariya tana fad'in"ashe ka gano ni"shima dariyar yayi har jerarrun hakoransa masu tsari suka bayyana,dimple dinshi guda d'aya ya lotsa sosae"kije dare yayi,Gud nyt" kai fatuu ta d'aga"Gud nyt yaya handsome kabi a hankali kar ka sake taka kwalba"Wani kallo yayi mata mai kaman harara kafin ya juya,

Tana ganin ya tafi ta juyo,tsayawa tayi ta bud'e kulan hannunta ta fara zazzaga sweet d'in ciki,kamar ance Amadu ya lek'o,ya ganta da karfi yace"Fatuu dama bashi zaki ba...."bai k'arasa maganar ba ta wurga ledan sauran sweet din cikin shagon ta nufi gida da gudu.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F

_*BY ZAINAB LALUH📲*_


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


*4️⃣0️⃣*


Washegari Misalin karfe biyu da rabi na rana,Haisam zaune a parlor ya tasa laptop d'insa gaba yana lallatsa ta,Tun bayan da ya samu rauni daga gida yake aiki don bai iya zuwa wurin aikin,gaba daya ya gaji Don aiki biyu yake yi, gana nan ga kuma na U.S,Kullum wuni yake aikin latsa Computer,Wani irin bacci ne ke fizgarshi don ya gaji Sosae,A hankali yasa hannu ya d'an ture laptop din gefe ya idasa hayewa kan kujeran ya kwanta,hannu ya kai ya d'aukko throw pillow ya tura ak'asan kanshi ya mik'ar da kafafunshi,A hankali idanunsa suka fara lumshewa alamar bacci ya fara zuwa.

Turo kopar falon akayi tare da sallama,Cikin zuciyarsa ya amsa ba tare daya kalli mai shigowan ba don yaji Muryarta,k'arasa shigowa tayi jikinta sanye cikin Uniform amman yau da Hijab,kitsonta sun fito gefe da gefe yayin da k'asan kitson ki acikin hijabin,ba k'aramin kyau hakan yayi mata ba,

gaban kujeran da yake kwance ta tsaya tana kallon fuskarshi,Slowly ya bud'e idanunsa akanta,murmushi ta sakar masa hakan yasa shima ya d'an yi mata wanda iyakarsa saman lips d'inshi,ganin tayi tsaye k'erere yasa shi mik'ar da yatsansa yana nuna mata 6arin da armchairs suke alamar taje ta zauna,girgiza masa kai tayi tace"bari in Zauna anan"tana fad'in hakan ta zauna a saman Carpet ta lankwashe kafafunta tayi zaman cin tuwo still idanunta na akanshi,

kallonta yayi a kasalance yace"kindawo",kai ta d'aga masa "eh yanzun nan na dawo na iske ba kowa a gidan,Gwaggo tana wurin aiki,kawu Amadu kuma har yanzu bai kaiga dawowa ba,shine nace bari nazo na tayaka fira",nodding kai yayi kawae,hannunta ta fiddo daga cikin hijab ta mik'a masa ledar dake ruke a hannun,bin abunda take mik'o masan yayi da ido kaman bazai kar6a ba,can kuma ya mik'o hannu ya amsa,jujjuya faran ledan yayi kafin ya d'ago ya kalleta da gani bai gane miye aciki ba,

"Tsaraba ce nayo maka,su tuwon madara ne,da gwullisuwa da baban dudu da mandako sai kantun gana" d'an bud'e idanu yayi jin wasu sunaye da take fad'a,yasan tuwon madara da gwullisuwan don akwae wata Abokiyar aikinsu dake kawo su,sai dae sam ba irin wannan bane,nata masu aji ne,wurinta ne ma ya siya Popcorn d'in da ya ba fatuu rannan,sauran abubuwanne bai sani ba bai ma ta6a jin sunansu ba,

ganin yana ta jujjuya su tace"ko bazaka sha ba" d'ago idanunsa yayi"zan sha,but ba nace ki daina kashe kudi kina siyo man abu ba"da sauri tace"ai kudi nane nasiyo maka dasu ba na wasu na ta6a ba,kuma duka Naira d'ari ce ma,komai na ishirin ishirin",kallonta kawai yake da lumsassun idanuwansa kafin Calmly yace"thanks zaraah"daga haka ya aje ledan a gabanshi,

"Nafa san miyasa kake ce man Zarah" kallonta yayi ba tare daya ce komae ba,taci gaba"Gwaggo tace man sunan mamanka gareni hakane wai??"ta d'an bud'e idanu alamar amsa take jira,kai ya daga mata alamar eh,
"Kenan nazama mamanka",

Yace"ko",

"Eh mana,tunda ina da sunanta ai kaga nazama mamanka ko",still yayi yanata kallonta,
"Mom zaraah yakamata ka rinka ce man,kuma ka rink'a yiman Dariya kana man Magana sosae"ta kai maganar tana d'an tura baki alamar shagwa6a,d'an muskutawa yayi ya juyo sosae"ai ina maki wannan ko" tace"to ai ba sosae kake yi ba,in zaka yi dariyan haka kake ko kayi haka"tayi maganar tana nuna mashi yadda yake dariyan,sosae ta bashi dariya yadda ta wani d'age baki amman sai yayi murmushi kawae,
"To ai hakan ma normal ne" d'an girgiza kai tayi"a'a,haka yakamata ka rink'a yi..."ta washe baki tana nuna mashi wai hakan zai rinka yin dariyar,Fuskarshi a sake yace"Wannan ai irin naku ne na Manya Mom zaraah"sosae ta washe baki jin ya kirata da sunan da tace ya rink'a ce mata,

Hannu ya kai ya dafe gaban kanshi don rashin baccin da baiyi ba har ya fara developing headache,sosae ya runtse idonshi yana d'an yamutsa bakinsa,ganin hakan yasa Fatuu cewa"Yaya handsome mike damunka ko baka lafiya ne?"sai da ya d'an dauki lokaci kafin ya janye hannun,a hankali ya fara bud'e idanun,yana son yace mata bacci yake ji amman baison taga kaman yana korarta ne don wani lokacin kaman bata fahimtar abu daidai,
K'ura mashi ido tayi"idanunka sunyi wani iri yaya handsome,baka lpy ko?"girgiza mata kai yayi yace"lafiya na lou,kawae ina jin bacci ne"d'an murmushi tayi"to bari in tafi"tayi maganar tana k'okarin mikewa,bin ta da kallo yayi kaman mai son gano wani abu har ta karasa mikewa zata tafi,

"Zaraah..." ya dakatar da ita,tsayawa tayi tana kallonshi,shima kallon nata yake yana nazarin fuskarta sai dae sam ya kasa fahimtar yanayinta,"Yaya handsome ka tsaida ni",

"Yeah,dama ba ina nufin ki tafi ba,ba kince gidan ba kowa ba?" kai ta d'aga mashi alamar eh,
"Owk,ko ki je ki gaida hajiya sai ku d'an yi firan kafin in tashi" yayi maganar idanunshi akan fuskarta yana nazartarta,d'an murmushi yaga tayi"to Yaya Handsome bari inje"murmushi yayi don yaji dad'i da bata fahimce shi ba daidai ba,har ta fara tafiya ya sake kiran sunanta,juyowa tayi ta kalleshi ya d'ago ledan abubuwan da ta kawo mashi ba tare daya kalleta ba yace"ki kai ma hajiya"shiru tayi tana bin shi da ido,
jin bata amsa ba yasa shi d'ago da kai ya kalleta,lokaci guda ya gane bata ji dadin hakan daya ce ba,
"Ki kai mata kice ta dauki rabi sai ta aje man sauran,kinga itama duk in ta samu abu sai ta bani" sai lokacin ta mik'o hannu ta kar6i ledan tana fad'in"to ai leda biyu ce,bari in raba maku",raba masu ta fara kokarin yi shi dae yana ta bin ta da ido,
bayan ta gama ta mik'o mashi"to ga nakan ita kuma sai in kai mata wannan"hannu yasa ya amsa Fuskarshi ad'an sake ya furta"Thanks"daga haka ya aje ledan gefenshi,ita kuma ta nufi kofa ta fuce,

____________________

Sam baijin dadin Baccin da yake kan kujeran,hakan yasa ya fara motsi alamar zai farka,A hankali ya fara bude idanunsa kafin ya idasa ware su sosae,k'uri yayi cike da mamaki yake kallon abunda ke gabansa har saida ya d'an sa bayan hannunsa ya goge idanunsa don ya tabbatar,Fatuu ce zaune saman C-table d'in parlon tayi dare dare a sama tana facing dinshi hannunta guda tayi tagumi dashi gaba daya ta k'ura masa idanu,
A kasalance ya furta"Zarah!what are u doing up there,ba nace kije kuyi hira da hajiya ba?",

Cire tagumin tayi ta zuro kafafunta k'asa a shagwa6e tace"to ai naje na iske itama hajiyan bacci ya kwashe ta a Parlor,baka gan yadda ta saki baki ba sai munshari take wllh kaman rago"bud'e idanu yayi sosae yace"Hajiyan ne rago!" da sauri ta shiga girgiza kai"a'a,wllh na manta rago Namiji ne,kaman shanuwa nike son cewa",Still yayi yana mata wani kallo hakan yasa tasha jinin jikinta duk da ita gani take wai ta gyara,yunkurawa yayi ya tashi daga zaune ya jingina bayansa da jikin kujeran,ita kam tayi tsuru tana bin sa da ido,ya fahimci gani take abunda ta fad'a daidai ne hakan yasa shi cewa"ba'a kwatanta Mutum da dabba kar ki k'ara"da sauri ta d'aga masa kai"to Yaya Handsome bazan k'ara ba",jinjina kai yayi,yana jin dadin yadda da yayi mata gyara take cewa bazata kara ba,kuma ya tabbatar bazata k'aran ba.

Shuru suka yi na wani d'an lokaci tana ta kallonshi tana faman sakin Murmushi,shi kuma fuskarshi ad'an sake yake kallonta,
"Duk kujerun dake parlon nan baki iya zama sai nan,in kika fasa man abu fa",
Hannu tasa tana shafa saman C-table din"Ai yana da kwari bazai fashe ba kuma ni bani da nauyi ma,kasan mi?" kai ya girgiza mata alamar a'a,taci gaba"nafa dad'e da dawowa ina shigowa nagan kanata bacci...." katse ta yayi"shine kika zauna kina bina da ido"fuska ad'an d'aure yayi maganar,

Da sauri tace"a'a Yaya handsome lokacin da na shigo naga kana baccin wllh har zan tafi gida kawae sai naga wani abun mamaki,kasan mi?"kai ya girgiza"wllh dana kalle ka kana baccin sai naga ka koma man kaman Karan na cikin Kaddarar rayuwa da ake a Arewa 24,ka gane shi"shiru yayi mata,tace"au ashe fa kace baka kallon tashar,amman wllh kunyi kama shiyasa na haye nan ina k'ara kallonka sosae har gashin kanku iri daya ne,kuma shima yana da dimple amman kai kafi shi tsawo gaskia shi kuma yafi ka yin dariya sosai"ta k'arasa tana ta watsa hannuwa,shi dae zuru yayi mata don bai ma san wanda take magana akai ba,ganin yayi mata shiru tace"Ka bari lokacin da ake yin shirin zan nuna maka shi",kai ya daga mata alamar toh,daga haka ya d'age kansa sama yana kallon ceiling gaba daya baijin dadin jikinshi,baccin sam bai ishe shi ba,

"Yaya handsome ka gama baccin ne?"a yadda yake ba tare da ya d'ago ba ya girgiza mata kai,
"to ka kwanta ka cigaba da baccinka",still bai d'ago ba yace"I can't sleep if there's someone around", jin tayi shiru yasa shi d'agowa ya kalleta,don kar tayi tunanin korarta yake yasa da sauri yace"Hajiya ma in tana kusa dani ban iya yin bacci" jinjina kai tayi alamar ta gamsu kafin tace"to ka tafi d'aki mana ka kwanta",
"In barki ke kad'ai?" tace"Eh mana ba sai in yi maka gadi ba kar wani ya shigo ta katanga su Officer basu sani ba",d'an murmushin gefe yayi jin abunda tace kafin yace"Yau ba aikin da zaki yi ne"hannu tasa ta ruke ha6a ta d'age ido sama alamar tunani"ba aikin da zan yi,amman yau gwaggo tace zata k'arasa man kitso bansan ko ta dawo ba yanzu",

"Ok,kije ki gani in ta dawon ko",
"To,amman sai na fara gyara ma d'ana parlon shi", tayi maganar tana kare ma falon kallo,shima d'aga ido yayi yana kallon falon kafin ya maida idon kanta"ai ba abunda yayi" jinjina kai tayi"eh amman dae akwae abubuwan da ya kamata a gyara",d'an ta6e baki yayi ya dage shoulders d'inshi daga haka ya mik'e ya nufi Bedroom dinshi,yana kaiwa daidai Corridor fatuu ta juya kai daga kan C-table d'in da take tace"My son kayi bacci mai dadi kuma kayi mafarkin mamanka",d'ago mata hannu yayi murya a kasalance ya furta"Owk,Mom Zaraah",daga haka ya tura kofa ya shige Bedroom d'in.

*** **** ****

Ba k'aramin bacci yayi ba don sai can bayan la'asar ya farka,hannu ya kai ya d'auki wayansa yana duba time,da sauri ya mike zaune ganin karfe hudu da rabi hakan na nufin yayi missing Sallan la'asar,da k'yar ya saukko da kafafunsa ya nufi Toilet don ya watsa ruwa saboda duk kasala ta baibayeshi,

Sanye cikin jeans da T-shirt ya fito ya nufi masallaci duk da lokaci ya kure,bayan ya gama sallan zama yayi cikin Masallacin yana yin azhkar d'in yamma,bayan ya gama yana fitowa daga cikin Masallacin wayarsa dake ruke a hannunsa ta fara ringing,duba mai kiran yayi kafin ya d'aga,tun kafin yayi magana on the other hand akace"Kana ina ne naje part dinka baka nan,nazo na Hajiya ban samu kowa ba",

"Ina a masallaci gani nan fitowa",daga haka yayi rejecting kiran,yana fitowa kopan masallacin ya hango Abbas tsaye agaban part din hajiya,juyowa Abbas yayi ya kafe Haisam d'in da ido ganin yana dangyashi hakan yasa Abbas din k'arasawa wurinshi,hannu ya bashi suka gaisa kafin yace" What happened, naga kana dangyashi

"Na samu rauni ne a kafan",
"rauni,wane irin rauni"Abbas ya tambaya,
"Na taka kwalba ne" ya bashi amsa a takaice,cike da mamaki Abbas yace"kace shiyasa jiya na tambayi ko kana wurin aiki kace man a'a kenan?"
"Yeah,bana zuwa sai na samu sauki sosae"
Cike da jimami Abbas yace"wai garin yaya?A ina ka samu kwalba har ka taka?" bai bashi amsa ba sai cewa yayi"Muje ciki mana"ya kai hannu ya kamo hannun Abbas d'in daga haka suka nufi part d'in haisam,

Lokacin da suka shiga cikin parlon atare suka ja suka tsaya suna bin shi da kallo,gaba daya Fatuu ta harmutsa shi,sam Haisam bai lura ba d'azun don yanata sauri yaje yayi sallan la'asar da ta wuce shi,Flower vases d'in dake a bakin corridor ta kinkimo su ta jara su a kan carpet d'in falon,yayi mamakin yadda ta iya daukko su don ba karamin nauyi ne dasu ba,ta d'aukko telephone da lamps d'in dake akan desk ta maido su kan C-table,haka Sound systems d'in falon ta rarraba su wasu dogaye ta jajjerasu a bayan kujera L-shape,
Kallonshi Abbas yayi"Waye yayi wannan gyaran,ko duk gwaurancin ne yasa baka iya gyara falo ba" fuskar haisam d'auke da Murmushi ya nufi kujera ya zauna yana fad'in"kasan dae nafika iya komae na cikin gida Abbas,wani yarinyane tayi gyaran"cike da mamaki Abbas ya maimata abunda haisam d'in ya fad'a yana kokarin zama kan armchair,
"Yaushe ka fara shiga harkar yara ko ince yaushe yara suka fara shiga harkar ka?"
"Wannan tafi karfi na ne"

"Tafi karfin ka,wannan wace Yarinyace haka da har tafi karfin ka?"da tsananin mamaki Abbas yayi tambayar idonsa akan haisam d'in,kwantar da bayanshi yayi ajikin kujeran a takaice ya fara bashi labarin Fatuu sai dae ba komae ne ya fad'i masa ba kaman kango da taje har ya taka kwalba duk bai fad'i masa ba,Dariya sosae Abbas ke yi,lokacin da haisam ya gama bashi labarinta yace"kai gaskiya yarinyar yar bala'e ce gashi ta cika abun dariya,amman fa wllh da ni ta fasa ma glass bazan yarda ba" wani kallo haisam yayi masa"what u would hv done,zaka ce a biyaka ne,or what?",

"Ai inma nace a biyanin ba laifi bane kuma ko ba ni ba adai halin da ake ciki yanzu kowa tayi ma hakan wllh cewa zai yi sai an biyasa,ta dae ci sa'a kawae da kaine ta fasa mawa",
Wani kallo haisam ke bin shi dashi ya d'an ta6e baki"in kuma basu da halin biyan naka fa Abbas?"
A d'an harzuke yace"to kuwa jikinta zai gaya mata wllh,don har gidan nasu zan je in zaneta "sosae yaba haisam dariya don yasan da gaske yake maganar don shima Abbas d'in dan balae ne,

"U Know what Abbas,irin yaran nan duka bai masu sai ma k'ara masu rashin ji,yanzu da ban taking wani action kan hakan ba,ba gashi ta canja ba har ta zama Mom d'ina" ya k'arasa maganar yana ta dariya,
Jinjina kai Abbas yayi"U'r right,amman shima gayen daya fad'a mata kudin glass d'in ya iya zuka karya koda yake d'an shaye shaye ne abunda yafi hakan ma zai fad'i,just abunda ba zai wuce 50k ba yace wai 1 million,amman shima ya taimaka tunda yasa ta tsorata har tayi alk'awarin ta daina rashin jin"ya k'arasa maganar shima yanata daria,

"Ina My boy" haisam ya tambaya,
"yanzu haka na baro shi yanata kuka wai sai nazo dashi"
Haisam yace"baka kyauta ba ai da ka kawo man shi mun gaisa yaga babanshi daya dade bai gani ba",

"rabu dashi kawae rigima zai zo yayi maka ba wani abu ba"

"Why? haisam ya tambaya a takaice,
gyara zama Abbas yayi kafin yaci gaba"kagane wani toy ne that looks exactly like a real laptop da ake talla a mbc,shine yasa rigima sai an siya masa ya takura man,so ganin toy d'in zai yi amfani wurin taimaka ma yaro ya koyi abubuwa,don akwae educational apps da cartoons sannan yaro zai iya yin typing kuma za'a iya tura masa wasu apps din kaman islamic haka,so na neme shi anan ban samu ba gaskia,sai nayi ma wata colleague d'ina lecturer magana da yake tana ordern kaya daga waje ko zata samo masa,tace zata bincika man,nace amman in ansamun ta fara fad'a man price d'in kafin tasa akawo,aikuwa kaman yadda nayi zaton zai yi kudi sai gashi tace man ansamu price din zai kama 40k,ai sai kawai nace ta barshi yayi ta rigimar in ya gaji ya daina,aikuwa yaron nan ya kaunaci Allah ya hana man zaman lpy dole na samo mashi wani karami dan 5k ai koda nakai mashi sai yayi wurgi dashi wai shi bai son shi har ya d'an fashe da yake roba ne,ya ban haushi na zane shi,aikuwa sai na k'ara tado ma kaina rigima dole na koma lallashin shi nace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login