Showing 162001 words to 165000 words out of 212491 words

Chapter 55 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

1009

zasu je, gaba d'aya Fatuu ta baje kayanta saman gado sai faman ruwan ido take ta rasa wanda zata sanya har saida taje ta tambayi gwaggo tace tasa Jallabiyarta bak'a mana aikuwa cike da murna ta nufi d'akinta don sam bata yi tunanin sanya taba kuma tasan inta sata ba sai tasa wata hijab ba, k'arfe bakwai saura gaba d'aya sun gama shiryawa Amadu ya shigo cikin shadda ruwan madara kafafunshi sanye da bakin takalmi da agogo sai hula kalar shaddar ya matuk'ar yin kyau sai k'amshi yake saki haka gwaggo ma atamfa tasa da sabuwar hijab kalar zanen atamfar tayi fess da ita sai kuma Hajiya Fatuu ikon Allah mai jallabiya ta had'u harta gaji, takalmanta golden masu tsini da haisam ya siya mata ta sanya hakan yasa jallabiyar tai mata daidai don dama ta d'anyi mata yawa kad'an, sarka da yan kunnan da gwaggo ta siya mata ta sanya sai agogo Wow abun dae sai Mutum ya gani da idonshi dama bak'ar jallabiyar adon sak'a golden gareta da stones sai tayi kamar yar balarabiya, hotuna Amadu ya fara yi masu cike da farinciki kowa bakinshi a washe suna cikin yin hotunan Hajiya ta kirasu a waya tace su fito, bayan sun fita gwaggo ta rufe gidan suka nufi Jeep d'in hajiya dake fake ita da Saude ne a baya sai Tk dake tuk'a Motar sun sha adonsu suma Hajiya na sanye da rantsattsar lifaya sai salki take, baya tace gwaggon ta shigo shi kuma Amadu tace ya zauna gaba gefen Tk ita kuma Fatuu tace mata taje wurin Yayanta sai ya taho da ita daga haka tk yaja suka tafi, gidan Hajiyar ta nufa a nutse take tafiyar idonta akan kafafunta kaman mai counting steps dinta, tana gab da zuwa kwanar gate Mercedes Benz d'in Haisam ta karyo kwanar hakan yasa ta ja gefe da sauri, tsayawa yay saitinta ta bud'e gaban ta shige, tana shiga suka hada ido da Haisam ta sakar mashi murmushi yana sanye da wata kwankwatsetsiyar, dakakkar, bugaggar hadaddar kuma rantsattsar farar shadda wadda ko makaho ya shafa sai ya gane mai kudi ce sosae, shigar komae white yay ya fito a balarabenshi sak ga wani fitinannan kamshi mai cika hanci na tashi cikin Motar hadi da ni'imtaccen sanyin Ac mai ratsa sassan jiki, barka da salla tace mashi ya amsa ta hanyar jinjina mata kai yaja Motar suka tafi suna dab da lungun su Haulat sai gata ta fito tanata sauri don tun jiya Fatuu ta gaya mata ta shirya su bi su Hajiya sallah, sam bata gane su ba don ba'a gane wanda ke cikin Motar,

"Lah ga Haulat gidanmu zata mutafi idi tare" Fatuu ta fad'a da sauri, burki yaja ya tsaya tana niyyar kai hannu ta bud'e kopar taga ya sauke mata glass d'in hakan yasa ta lek'a kanta ta kwala ma Haulat d'in kira, koda ta juyo taga Fatuu bud'a ido tai tana kallonta cike da mamaki, da hannu tay mata alamar ta taho hakan yasa ta nufo Motar, alamar ta shigo tai mata ta kai hannu ta bud'e kopar baya ta shiga, har sai da ta lumshe idanunta kafin ta daidaita zamanta yaja suka tafi, gaidashi tay tayi mashi barka da sallah ya amsa mata a hankali, bayan sun isa a waje can gefen Masallacin ya parker Motar don Area d'in wurin dankam take da Motoci bayan sun shiga sashen Mata suka nufa anan kuma suka hango su gwaggo don suma basu dad'e da isa ba, Alhamdulillah anyi salla an gama lafiya sai gaishe gaishe Mutane keyi suna yima juna barka da sallah da kuma fatan anyi ibada karbabbiya yayin da wasu suka fara daukar hotuna ciki harda su Tk da Amadu Fatuu na hango su taja hannun Haulat don suje suma ai masu hoton, Hajiya kam tuni Jama'a suka zagayeta suna ta yimata barka da salla, sosae take farinciki cikin fara'a take amsa ma Mutane don yin sallar anan ba k'aramin nishadi ta samu ba yayin da wadanda basu san wacece ba ke tambaya ana fad'a masu matar tsohon Ministan tsaro ce mahaifiyar Senator Ali Adamu Zakee kuma Mamallakiyar HAZ FOUNDATION, gidauniyar tallafa ma Marayu da gajiyayyu da kuma koya sana'oi, bayan masu kawo mata gaisuwar sun lafa ne Tk yazo yace bari yay masu hotona, sosae sukae Hotunan harda wanda Masu daukar hotuna wato photographers dake cikin Masallacin Hajiya tasa suyi masu, ganin anata hotuna ba Haisam ne yasa Fatuu wawwaigawa ko zata hangoshi amman sam bata ganshi ba hakan yasa ta fita daga cikin masallacin ta nufi Motarshi aikuwa sai gashi a ciki ya d'an kwantar da kanshi kafarshi guda ya zurota waje don kopar a bude take yanata latsa wayarshi, ba komae ne yasashi dawowa cikin Motar ba illa kallonshi da ake tayi shi kuma ya tsani kallo ba kamar Mata wasu har nunashi suke suna fad'in da gani ba d'an Nigeria bane, cikin Masu kallonshi harda Boss Bature can na hangota ta saki baki tana kallonshi har tana fadin " bala'i kuji wani wanda yaci uban Baby Junaid kyau🤣,

Koda Fatuu tace mashi yazo suje ana yin hotuna girgiza mata kai yay alamar bazaije ba don shi baison yan d'auke dauken hotuna hakan a wurinshi ma kauyanci ne shiyasa in ba dole ba bai tsayawa ai ta yi mashi hotuna barkatai, jin bazaije bane yasata cewa to yayi masu ita dashi, da farko ki yay ta fara mashi magiya sannan ya shiga Camera d'in yay mata alamar tazo, ida fito da d'ayar kafarshi yay taje gefenshi ta d'an kwanto da kanta ya daukesu gaba d'aya sun d'anyi Murmushi, rok'onshi tay ya mik'e ya daukesu ta d'an jingina dashi tana dariya gashi tayi can k'asa ba tsawo amman dai ba k'aramin kyau hoton yay ba, ba kamar daya kasance sunyi shigar fari da bak'i ne,

( duk mai buk'atan ganin hotunansu yay ma Munah Bature Magana don a Masallaci d'aya sukai sallar wato Banu Commassie Masjid dake a GRA, can na hangota ta la6e ajikin wata bishiya tana d'aukarsu ba tare da saninsu ba, kwalelenki dae😹).

**** **** ****

Bayan sun bar Masallacin saida suka biya gidan Sarki, bayan sun fito daga gidanne gwaggo tace ma Amadu ya hau keke napep yaje ya amso mata aikin abinci data bada sai ya iskesu gida, Hajiya na jin haka tace to ba a Mota suke ba miyasa bazasu biya su amsa ba kawae gwaggon tace ai kada a 6ata masu lokaci Hajiyar tace ai ba wani abu bane suje kawae, bayan sunje sun amshi abincinne suka nufi gida lokacin tuni su Fatuu sun koma don suna baro gidan sarki Haisam ya wuce dasu gida ana sauke Haulat itama ta sauka tabita gidan nasu don tayi ma innarsu barka da Sallah, sosae Innarsu haulatu ta yaba da wankan Fatuu har barka da salla ta bata Haulat ta zubo masu abinci suka ci, su gwaggo na komawa gida ta zuba dukkan abincin tuwo, waina, Alkubus acikin Manyan Warmers taba Amadu ya kaima Hajiya, lokacin da ya kai mata sosae tai farinciki da abincin ba kamar Alkubus d'in ya burgeta don yayi kyau ya tashi sosae nan da nan tace ma Saude ta zubo masu su ci, kan kace mi gidan hajiya ya cika da yan yawon salla duk wanda yazo aka bashi barka da salla sai ya ruga ya fad'i ma abokanansa, haka iyaye mata duk wadda taji cewa Hajiya anan tayi Sallah sai ta zuba abinci tace akaimata nan aka cika hajiya da abinci sai faman farinciki take tana sawa ana daukarta hotuna da yaran unguwa daga baya kuma iyayen suka rinka shigowa suna yi mata barka da shan ruwa da fatan anyi salla lafiya.

( zaka kasance acikin farinciki matukar kaima kana sanya Mutane farinciki kuma Allah yana cigaba da taimakon bawansa matukar bawan na taimakon na kasa dashi)

Ana yin sallar Azahar Fatuu ta canja kaya tasa fitted gown dinta don kuwa da gwaggo ta amshe tace bazata sakasu ba sai taje takai kararta wurin hajiya tace gwaggo ta amshe mata kayan da Ya Handsome ya dinka mata tace wai bazata sasu da salla ba hakan yasa Hajiyar kiran gwaggon a waya ta tambayi dalilin amshe kayan gwaggo tayi mata bayanin irin dinkin da fatun tasa akayi mata, karshe dae Hajiyar tasa gwaggon ta bata kayan tace tunda an riga an dinka ba yadda za'ai sai hakuri, wurin gwaggo taje ta d'aura mata kallabi, da tace bata d'aurawa daga baya kuma ta amsa tana d'aura mata tana k'orafin yadda rigar ta kamata, d'auri mai kyau tayi mata ga gashinta ta faka shi ya sauka abayanta don ma gwaggo ta lankwashe shi, tana komawa d'akinta tasa takalmanta ta dauresu ta kuma sanya sarkar da Haisam ya siya mata wadda tamkar gold haka take, d'aura gyalenta tay akan kafad'a ta d'auki yar jakarta mahadin takalman daga haka ta fito ta nufi gidan Hajiya, ta k'aramar kopa tabi ta nufi part d'in Haisam, tana shiga cikin falon taja ta tsaya a bakin kopa tana bin Mutanen dake a cikin Falon da kallo wad'anda maza ne guda ukku kowannensu yaci gayu cikin sabuwar shadda gaba d'aya falon ya k'ara hadewa da wani irin hadaddan kamshi mai bugun zuciya, wurga ido taci gaba da yi tana son hango Haisam saidae babu shi acikinsu,

"Welcome Mom Zarah ki shigo mana" taji wani cikinsu ya fad'a hakan yasa takai idanunta da sauri kanshi, Abbas ne yana sanye cikin galleliyar shadda ash ya d'an kishingida ajikin kujera dama gaba dayansu suna akan L-shape ne ga kayan abinci birjik kan c-table da alama basu dad'e da gama ci ba don duk ga lemu nan acikin glass cups an rage, koda tay arba da Abbas sai kawae ta sakar mashi Murmushi don yanzu sun saba dashi sosae, mayar mata da martanin Murmushin yay ya nuna mata armchair alamar taje ta zauna saida ta duk'a ta cire takalmanta kafin ta nufi kujerar don ta zauna yayin da sauran Mutum biyun suka bita da ido, gaishe dasu tai gaba d'aya bayan ta zauna suka amsa banda Mutum d'aya da shi jinjina mata kai kawae yay fari ne don duk yafi su haske saidae sam bai kai Haisam ba yana sanye da farar shadda ya aje hularshi gefe kaman dae sauran suma duk sun cire hulunansu hakan kuma ya bayyanar da yalwatacciyar sumar kansu, d'ayan kuma za'a iya kiransa da Chocolate yana sanye da Brown shadda wadda ta hau fatar jinkinshi sosae har sun so sajewa, gaba d'ayansu ba mummuna kuma kallo d'aya zakai masu kasan yan hutu ne don shi mai farar Shaddar wato Saleem babanshi ne Deputy Governor na yanzu sai mai Brown shaddar wato Najeeb shi babanshi ba mai mukamin gwamnati bane saidae shahararren mai kudine a Katsina wanda idan za'a lissafa masu kudi a Nigeria to tabbas za'a fade shi, gaba d'ayansu Abokan Haisam ne tun yarinta don shi Saleem d'in ma tare su kae karatu akasar waje.

"Mom Zarah ina barka da Sallah na?" Abbas ne yay Maganar, juyawa tai ta kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta rufe bakinta da tafin hannunta tana dariya,
"Ba Dariya na tambayeki ba, ko bazaki bani bane?"
girgiza mashi kai tayi alamar zata bashin yace to ta bashi, mik'ewa tay ta nufi inda yake ta fiddo yan d'ari biyu guda biyu sabbi dama yanzu Tk ya bata su ta mik'a mashi, mik'o hannu yay ya amsa yace ya gode har zata juya yace ta tsaya shima ya bata, sabbin yan d'ari biyar guda hudu wato 2k ya miko mata, da tak'i Kar6a yace to shima ga nata baiso hakan yasa ta amshi nashin tace ta gode tana niyyar sake juyawa taji ance "Mu don ba'a sanmu ba kenan baza'a bamu ba",
da sauri takai idonta kan sauran Mutum biyun nan take ta gane wanda yay Maganar wato Najeeb saboda shine ke kallonta shi Saleem wayarshi yake daddannawa, mik'a mashi wanda Abbas ya bata kawae tayi don wani irin kallo yake binta dashi,

"No ba nashi nike so ba, muma naki zaki bamu" ya fad'a yana wani lumshe mata ido dama kuma haka yanayin idonshi yake sai yaso yake waresu, murya na d'an rawa tace "ai ba sauran irin wanda na bashi yan k'anana ne suka rage"
"No problem muna so" ya fad'a, hannu na rawa saboda kwarjinin da yay mata ta bud'e cikin jakar ta fiddo naira hamsin guda biyu da yan ashirin suma biyu naira d'ari da Arba'in, mik'a mashi su tayi duka sai ya cire hamsin d'aya da ashirin wato naira 70 ya bata sauran yace taba Saleem d'in da kanta, d'an matsawa tay ta mik'a mashi ganin bai kalleta ba yasa tace "gashi" a wani slow ya d'ago da kyakkyawar fuskarshi yabi kud'in da take mik'o mashin da kallo kafin ya d'aga manyan idanunshi ya kalleta,

"Barka da salla ne aka baka kaima" Najeeb ya fad'a, wani kayataccen Murmushi ya sakar mata kafin ya d'an girgiza mata kai alamar a'a kaman an masa dole kuma ya furta "thanks" sak abubuwan shi shigen na Haisam ne ita kanta Fatuu hakan take ayyanawa aranta, juyawa tai ta mik'a ma Najeeb kud'in tace "gashi to ka had'a shi bai so" Murmushi ya sakar mata yana d'an motsa madaidaicin bakinshi ya kai hannu ya kar6a, har zata juya ya tsaidata da fad'in "nima bari in baki tawa Happy sallan" dakatawa tai ta tsaya tana kallonshi ya kai hannu cikin Aljihun rigarshi sai gashi ya fiddo sabbin yan dubu dubu zasu kai dubu goma in ma basu fi ba ya mik'a mata, zaro ido Fatuu tay lokaci guda ta fara girgiza mashi kai alamar a'a,
"Abun wayo ne kenan, ke kin bani ni bazaki amshi nawa ba?" ya fad'a had'i da d'age mata gira,

"Ai naka sunyi yawa sosae ni yan kad'an na baka" ta fad'a tana yamutsa fuska, d'an ta6e baki yay ya gyara kishingidar da yay kafin yace "abunda kike dashi kika ban nima kuma wanda nike dashi na baki ko" tana niyyar k'ara cewa wani abu taji Abbas yace ta amsa juyawa tai ta kalleshi ya jinjina mata kai alamar ta amsa d'in, ba don taso ba ta kai hannu ta kar6a saboda ita tsakaninta da Allah kud'in sunyi mata yawa bata san ya zata yi dasu ba, godiya tayi mashi tana juyawa Haisam ya fito daga Bedroom dinshi ya canja kaya zuwa shadda Navy blue an mata fav dinkinshi wato Sen style kanshi ba hula sumar nan tasha gyara sai salki take just Ma sha Allah, yana shigowa cikin Falon ya k'ara karad'ewa da wani kalan kamshi na daban, d'ayan 6arin L-shape d'in yaje ya zauna idanunshi akan fatuu da itama shi take kallo tunda ya fito tana ganin ya zauna ta nufeshi a lokacinne kuma Najeeb ya waiga yana tambayar Abbas wai wacece ita yana murmushi yace mashi Mom d'in H,zakee ce a gidajen makwabta take, jinjina kai Najeeb d'in yay kawae, tsaye tay agaban Haisam fuskarta da d'an Murmushi nuna mata gefenshi yay alamar ta zauna, tana zama ta mik'a mashi kud'in dake hannunta wanda suka bata,
"Na miye ne?" ya tambaya idonshi akanta,
" Barka da salla ne wai suka ban",
jinjina kai yay "naki ne ai"
"To ai sunyi yawa bansan ya zanyi dasu ba" shiru ya d'anyi sai kuma yace "ki kaima Grandma d'inki",
d'aga mashi kai tayi alamar toh, ganin ta ruk'e su ahannu yace mata ta saka cikin bag d'inta, tana kokarin sakawa jakar ta kufce mata sai ga kayan kwalliya sun zubo waro ido tay ta d'ago ta kalleshi ganin kayan shafan yake kallo yasa ta rufe fuskarta alamar kunya, d'an ta6e baki yay ya kai hannu k'asa ya d'aukko lip glow d'in daya fad'a kan k'afarshi ya mik'a mata ta amsa tana sussunnar da kai, bayan ta saka komae cikin jakar ta d'ago ta kalleshi yasa hannunshi guda ya d'an shafi gaban kanshi can k'asan makoshinshi ya furta mata " Kije wurin Hajiya" yadda yay Maganar in ba ita dake kusa dashi ba ba wanda yaji abunda yace dama kuma duk Maganganun da Fatun tayi mashi k'asa k'asa da murya tai mashi su, d'aga mashi kai tayi alamar to kafin ta mik'e, k'ara yima su Abbas da Najeeb dake kallonta Godiya tai kafin ta nufi bakin k'opa tasa takalmanta daga haka ta bud'e kopar ta fuce........


ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,

ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUH📲*_
~(Oumm Imam)~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


6️⃣2️⃣

.......Tana fita Najeeb ya maido idonshi kan Haisam yace "Zakee wannan Mom en naka gaskia am in",
kafin Haisam ya bashi amsa Saleem ya d'ago ya kalleshi da expression na mamaki akan fuskarshi yace "Are u ok Najeeb, wannan abun ne zaka ce kana ciki?" ware ido

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login