Showing 63001 words to 66000 words out of 212491 words

Chapter 22 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

973

sauri tace"au na manta kuna da su da yawa,to amman fa gwaggota da hajiyanka basu san abunda ya faru ba,kar kuma su zo su sani,dama yau da na dawo daga makaranta na iske Ladidi mai waina tana ba gwaggo labarin anzo an kama Gaye wai jiya wani mutum ya gansu suna k'okarin yima wata fyade,baka gan yadda hankalin Gwaggota ya tashi ba fa" ta k'arasa had'i da rike ha6a,
"Don't worry bazasu sani ba,amman akwae abunda zan fad'i maki yanzu shima yana cikin sharadinmu na glass indai baki kiyaye ba you know what would happen" kasak'e tayi tana kallon shi,d'agowa yayi daga jikin kujeran ya d'an duk'u hadi da linke hannuwansa asaman cinyoyinsa,ganin hakan yasa itama ta goyo hannayenta saman kirjinta ta yi masa kuri da idanu,

On a serious note ya fara magana"I don't want u to repeat same mistake u made yesternight" da sauri tace"ba zan k'ara ba Allah kuwa" tayi maganar tana girgiza kai,Haisam ya ci gaba"kowa da kike gani zai iya cutar da ke,including your own blood brother..." zaro ido fatuu tayi tasa hannu ta rufe bakinta alamar mamaki,haisam yace"yeah.."cire hannun tayi tace"to amman ai ni yayana fa ba anan yake ba yana can garinmu sai dai kawu Amadu harshi kenan zai iya cutar dani din?" nodding kai yayi kafin yace"baki ji nace ko d'an uwanki na jini ba" shiru ta d'an yi alamar tunani can tace"kenan yanzu da kawu Amadu ya kara rike man hannu in gaya ma gwaggo?" girgiza kai ya yi"ba irin wannan ba,ai shi d'an uwanki ne zai iya rike ki..." shiru yayi don bai san taya zai mata bayani ba,fatuu dake ta kallonshi ganin yayi shiru tace"ko kana nufin ta6a cikin jiki?" kai kawae ya d'aga mata,da alama ta kashe bakinshi,jinjina kai tayi alamar ta fahimta can ta d'ago tace"HAR KAI.......?"

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story._


_*BY ZAINAB LALUH📲*_


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


*3️⃣3️⃣*


".....Har kai in kayi man hakan in fad'i ma hajiyanka ko gwaggotah?" komawa yayi ya jingina da kujeran yasa hannu ya rike gemunsa da bakinsa, kallonta kawai yake,fatuu ta wuce duk yadda yake tunani,tai mashi zuru da idanu da alama amsa take jira,ganin haka yasa ya daga mata kai alamar eh,can kuma ya cire hannunsa daga bakin gently yace"But i will never do dat..." da sauri ta katseshi"dama nasan kai baza ka cutar dani ba,kai mutumin kirki ne ai" shi dai kallonta kawae yake kaman yana nazarin wani abu.

"Kin ta6a yin ciwo aka kai ki asibiti?" ya jefa mata tambaya,

tace "A ina?can garinmu ko nan" yace"ko ina" dan langa6ar da kai tayi"acan garinmu ba'a ta6a kaini asibiti ba in ma ban lafiya jik'a man magani ake in sha ko asaman a abinci,kuma ma ni ina dad'ewa banyi ciwo ba fa,yauwa na tuna kaka na yana sawa ana man turaren magani,ba na fad'a maka yace wai shedanu ne su kai man fitsari aka ba,to fa yana nufin wai aljanu gareni"

"da gaske kina da su?" haisam ya tambaya,girgiza kai tayi tace"nidai wllh bani da wasu Aljanu amman sai aita cewa su gare ni ko a makarantar bokonmu ma kowa kallon mai aljanu yake yiman tun daga wata rana da displine master ya bugan man kai na fad'i ina bori shikenan akace aljanu gare ni kuma wllh ina sane nayi borin,to fa haka nan ya tsaneni ko laifi mukai mu da yawa ko bai bugi kowa ba sai ya buge ni,ni kuma shiyasa nayi masa bori dama kuma banson a bugan man kai ai kai ma kasan baida dadi ko?" daga mata kai yayi alamar eh,

ta ci gaba"amman kasan mi,tun daga lokacin wasu malamai suka daina buguna ma ajiki sai a hannu su duk atunaninsu aljanun gare ni harda sauran yan makarantar ma tsoro na ake,sai su rika cewa wai k'arfin da ke gareni ba nawa bane na aljanun ne" ta k'arasa maganar tana ta dariya,shima d'an murmushi yayi sai kuma yace"to ita grandma d'in taki bata fad'a maki ko da gaske kina dasu ba?" gyara zama tayi tace"ai ita dama bata cewa inada su,ko da na fad'a mata abunda ake cewa a makarantar cewa tayi k'aryane in rabu dasu,amman kuma tana cewa zata kaini asibiti wai a binciki kwakwalwata wai banda cikakken hankali,ba kaman in na siyo mata rigima"ta k'arasa maganar tana tikar dariya had'i da sussunar da kai k'asa,shi dae kallonta kawai yake,

"ko kaima kana ganin banda cikakken hankalin ne?" fatuu ta jefo mashi tambaya,girgiza mata kai kawai yayi alamar a'a tace"nifa wllh zafin marin da kayi man ne yasa na jefan maka gilashi kuma nayi zaton in ya fashe kawai za'a walde shi ne kaman yadda ake walde kofa,ashe shi wai sai dai a canja,Allah yaso ni mai kudi kuma mai kirki na jefan mawa ai da kuwa an kai ni asibitin mahaukata mai dalili na gidan yari"ta k'arasa tana dariya hadi da jinjina kai,shi dai d'an ta6e baki yayi baice mata komae ba,
jin kafarsa mai ciwo ta sage masa yasa ya d'agata yana k'okarin d'aura ta saman kujerar,ganin haka yasa fatuu cije baki tana yin d'an sauti"shiiii.." juyowa yayi ya kalleta bayan ya d'aura kafan da sauri tace"sannu,da zafi ko?"yar harara ya wurga mata ba tare da yace komae ba ganin haka yasa ta sake cewa"kayi hakuri Yaya handsome,kaji ciwo ta dalili na" ta k'arasa maganar tana turo baki hadi da langa6ar da kai,

d'an daure fuska yayi"ban yin hakurin,kin zaunar dani a gida ban je aiki ba ke gashi kin je school" yar dariya ta yi tace"nama san wasa kake ai,kai da nayi ma asarar million amman ka yafe balle wannan" cike da mamaki yace"kenan ita asarar kudin yafi wannan?" tace"eh mana,million fa kudi ne da yawa",

"to kuma in k'afan ya lalace fa saboda ciwon?" tace"da million ai za'a iya yi mata magani har ma arage canji" jinjina kai kawai yayi yana kallonta underneath his breath ya furta"this's serious!", wayarsa ce ta fara ringing ya kai hannu ya d'auka yana duba mai kiran Henry shine sunan da ya gani,d'aga kiran yayi kafin ya kara a kunne cikin harshen turanci ya fara magana daga ji wanda yake wayar dashi bature ne don slang english yake yi,ita kuwa fatuu k'ura masa idanu tayi kaman mujiya baki bude,yana cikin yin wayar yayi dariya har hakoransa suka bayyana a lokacin kuma wani abu yaja hankalinta a fuskar tashi,k'ara kura masa idanu tayi cike da mamaki ta ke bin fuskarsa da kallo har d'an kwantar da kanta take yi tana lek'o d'ayan 6arin fuskarshi,duk abunda take yana lura da ita ta wutsiyar idonsa,juyowa yayi ya kalleta bayan ya gama wayan fuskarshi ad'an d'aure tana ganin haka da sauri ta kama kanta tace"naga kana da irin abuna anan amman a dayan 6arin ban ganshi ba"tayi maganar tana nuna masa dimples d'inta bayan ta yake baki tana dariyar yak'e wai don yaga dimples din",

still yayi yana kallonta kafin yace"d'ayan kike nema kenan?" d'aga masa kai tayi alamar eh,ya jinjina kai kaman bazai ce komae ba sai kuma yace"to babu" da sauri tace"kenan kai guda d'aya kayi gado?",
d'age gira yayi"meaning?"
"ina nufin wurin mamanka ko babanka ka gaje shi,kasan fa in mutum guda d'aya gareshi to cikin iyayenshi guda ke dashi,kaga ita hajiya nasan bata da shi,to kenan a wurin babanka ka gada" jinjina kai yayi yace"ko?" tace"eh mana" can kuma ta rik'e baki da sauri "kai,to ai nima babana bai dashi wllh gashi kuma biyu gare ni,to ya akai hakan ta faru?" ta jefa mashi tambaya,watsa hannuwa yayi yace"how do i know" d'an tunani ta yi kafin tace"nifa dama wata kawata ce itama tana dasu ta fad'i man hakan,amma yanzu na ma gane yadda take nufi,in cikin iyayen mutum guda d'aya na dashi duka biyun to sai mutum ya gaji duka shima,in kuma cikin iyayen d'aya nada guda d'aya to sai mutum ya gaji guda d'aya shima kaman kai kenan" tana maganar tana d'aga hannu kaman malama na bayani,

Gyara zama yayi yace"what if duka iyayen na dasu kuma guda biyu kowa,ya kenan za'ai? dage idanu tayi sama alamar tana nazarin tambayar tashi can ta kalleshi tace"sai mutum ya gaji guda hudu kenan" jinjina kai haisam yayi cike da son jin yadda hakan zata faru yace"ta ya ya?" yatsun hannuwanta manunai tasa ta nuna saitin da dimples d'inta suke tace"kaga nan biyu,sai kuma asamansu ko ak'asan su wasu biyun su fito" shiru haisam yayi yana imagining yadda dimples hudu zasu fito ma mutum a fuska,can yace"ke kin ta6a ganin mai su haka?" shiru tayi tana zare idanu can ta fashe da dariya tace"wllh ban ta6a gani ba,kam yo mutum ma ai kaman Aljani zai koma" dariya shima haisam din yayi har fararen hak'oransa suka bayyana, yace"kawae kin zauna kina shirya man k'arya... " da sauri ta katse shi tana turo baki "wayyo Yaya Handsome wllh bafa k'arya nike ba,baka ji nace wata kawata ce ta fad'i man hakan ba,kaga ita ce ke yin karyar ba ni ba ko",

Sigh yayi ya shafi gefen fuskarshi,ita kuma sai sussunar da kai take alamar taji kunya,d'an Murmushi yayi yace"is okey na fahimta ba k'arya kikai ba" da sauri ta kalleshi tayi yar dariya,shima har lokacin da Murmushi a fuskar tashi "What's ur name?" ya tambayeta,tace"Fatuu,baka ji jiya ina fad'a ba a labarin dana baka",dage gira yayi yace"I mean your real name"

"Fateema"ta bashi amsa,

jinjina kai yayi kawae,shiru sukae na wani d'an lokaci,tana ta wasa da yatsun hannunta, remote haisam ya dauka yai turning tv on,da sauri fatuu ta juya jin sautin tv din,
ganin yadda take ta d'age kai tana yin kallon don a k'asa ta ke zaune haisam yace"Zarah..." shuru bata waigo ba da alama bata ji shi ba,d'an daga murya yayi ya kara kiran nata aikuwa da sauri ta waiwayo tace"ni kake kira da Zarah?"

"yeah,ko ba sunan ki bane?" dariya tayi tace"sunana ne,Fateema zahra,amman fa ba wanda ke kira na da haka" tayi maganar tana jaddada mashi da kai,hannu yasa ya shafi beard d'insa kafin yace"nima sunan da kike kirana dashi ba wanda ke ceman haka" kyalkyacewa tayi da dariya tace"ka rama kenan" bai ce mata komae ba,
"ka kira ni to" fatun ta fad'a,

yace"just to say u can have a seat,naga kina ta d'age kai zai iya maki ciwo" jin haka yasa ta mik'e tana d'an yake baki"wllh fa harma naji kaman ya fara zafi,to a ina zan zauna wannan ko wanccan" ta nuna d'ayan 6arin kujerar da yake zaune da kuma armchairs d'in dake a d'ayan bangaren "duk inda ya maki" ya bata amsa,yar dariya tayi tace"to bari in zauna can gefen kujeran nan naga kafi zama asamanta nasan tafi dadi ne ko?" dan ta6e baki yayi fuskarshi a sake kaman zaiyi murmushi"in kin zauna zaki ji" tace "to"daga haka ta nufi dayan 6arin L-shape d'in ta zauna ta daidaita zamanta sosae kafin ta juyo tana dariya tace"taushi wllh"d'an Murmushi yayi yasa hannunsa na dama ya shafi forehead dinsa,ita kuma ta juya taci gaba da kallon,

Juyowa fatuu tayi bayan wani d'an lokaci ta yamutsa baki, "yaya handsome wai baka da Arewa24 ne,nifa wllh wannan bangane abunda suke cewa" haisam dake daddana wayarsa ba tare da ya kalleta ba yace"ba kina fahimtar turanci ba" tace"ai nifa irin namu na nan nike dan ganewa ba irin wannan suri surin ba" ta k'arasa maganar tana turo baki,sai lokacin ya d'ago ya kalleta"to ai duk abu d'aya ne.." ta katse shi"to ai nasu gudu yake ban ganewa kai naji ka iya d'azun kana yi,ni sam ban iya ba,in dai akwae Arewan ka maida man" nodding kai yayi yace"baza'a rasa ba sai dai bansan a ina yake ba,let me search" searching Arewan ya fara "kenan kai baka kallon Arewan?"fatuu ta jefo masa tambaya,kai kawai ya d'aga mata alamar eh,tace"tabb kai yan turancin kenan kawai kake kalla shiyasa ka iya kaima,zaka koya man?" nan ma kai ya d'aga mata alamar eh,"to yaushe zaka fara koya mun?" sai lokaci yayi magana ba tare da ya kalleta ba yace"ba yanzu ba,sai ansamu enough time yanzu ina busy" jinjina kai tayi tace"zan jira kuwa,haulat ta bani dani in na iya har malaman makarantarmu ma sai na nuna masu su basu iya turanci ba...." da saura ta juya ta kalli tv jin ana magana da hausa lokaci guda ta washe baki tace"yauwa ga inda muka fi wayo nan...." juyowa ta sake yi a kalli haisam rai adan 6ace tace"wllh su Arewar nan sai suyi ta maimaita film" d'ago kai yayi ya kalli tv din sai kuma ya maida kan akan wayar da alama wani abu yake da ita,
"Don Allah yaya handsome ka maida Tauraruwa ko Hijira suma duk hausa ake yi" ba tare da ya dago ba yasa hannu ya dauki remote din ya mik'o mata,bin shi tayi da ido ba tare da ta taso ba,hakan yasa ya dago yace"ki zo ki amsa mana" tashi tayi ta nufesa tsayawa tsaye tayi a gabansa bayan ta kar6i remote d'in tace"nifa ban san ya ake yi ba,bamu da dish agidanmu" dagowa yayi da d'an mamaki ya kalleta,to in basu dasu ya akai duk tasan channels din da ta fadi mashi yanzu,kaman tasan mi yake tunani tace"dama a makwabtanmu nike zuwa yin kallo,mu yar tv garemu da vedio to daga baya aka saida vedion aka siyo DVD muna kallon cassette,kuma sai tv din ta lalace aka kaita gyara bayan ta gyaru munci gaba da kallo kuma wai rannan sai aka maido wuta da karfi ta sake lalacewa da aka kai gyara sai aka ce ai ta kone ne,tun daga lokacin ne bamu da kayan kallo,ita kuma banzar Naja'atun da nike zuwa gidansu kallon rannan muka yi fad'a har na falleta da mari shine tayi man gori tace karna k'ara zuwa gidansu kallo,ni kuma sai na daina zuwa don banson inje ayi man wulakanci don ba kyalewa zanyi ba ko innarsu ce tayi man sai na rama ehe,ai dai arziki na Allah ne suma ba finmu sukai ya basu ba" ta k'arasa ranta a 6ace ta kumbura baki da alama abun yayi mata ciwo,ganin haisam din yayi shiru yana kallonta yasa da sauri tace"ina nufin fa ada lokacin da banjin magana shine ba zan kyalen ba,ni yanzu bama ruwana dasu,anan gidan nike yin kallo in na zo wurin hajiya,kuma kai naga abun naka ba irin nata bane shiyasa bansan ya zanyi amfani da shi ba",

Sigh haisam yayi Calmly
yace"kome ta maki laifin ki ne miyasa zaki mare ta,ke komae aka yi maki sai bugu" ya k'arasa maganar ya dan 6ata fuska,ganin haka yasa fatuu marairaicewa tana nannok'e kai muryarta kaman zata yi kuka tace"to ai ita ta ja ni fa,raina man wayo tayi ni kuma naji bazan iya hakuri ba,kai ma rannan dana yi maka ba daidai ba ai mari na kayi ko amaimakon kayi hakuri",

"Oh kinma san ba daidai ki kai man ba har na mare ki,amman still kika jefan man glass" ganin kaman ransa a 6ace yayi maganar yasa da sauri tace"Don Allah kayi hakuri,na fa gaya maka wllh marin ne mai zafi kayi man,amman yanzu ai na bari ko"har kwalla sun taru a idonta,ga rashin ji ga saurin kuka,

Jimm ya d'an yi kafin ya mik'a mata hannu alamar ta bashi remote din,da sauri ta mika masa ba tare da ya kalleta ba yace"matso ki ga yadda ake,if u want to change another channel ba sai kin tambaye ni ba,tace to had'i da matsowa gabanshi tana k'okarin dukar da kanta taga yadda zai yi d'an gyalenta ya silalo ya fada saman hannun shi,

Dagowa yayi ya kalleta tana tsaye daga ita sai riga da wando na uniform da sauri tasa hannu ta d'auki gyalen ta fara k'okarin yafawa,tun d'azun yana lura da yadda gyalen keta zamewa hakan yasa shi cewa"ki rolling din shi mana" tace"ai ko nasa bai zama,gashina ne ke da sul6i shiyasa" shiru yayi da alama bata fahimci mi yake nufin tayi da gyalen ba,kaman ance ya kalli tv ya hango wata mata tayi rolling gyale a film din da ake hakan yasa haisam mik'a yatsansa yace"ki yi yadda tayi" da sauri ta juya ta kalli in da ya nuna kafin ta juyo tace to,cuku cukun laga gyalen ta shiga yi sai dai sam ta kasa saboda bata iya ba,ga gyalen ba wani babba bane,ganin yadda take ta fama yasa haisam fara nuna mata yadda zata yi da hannu,can tace"to tunda ka iya ka nad'a man mana,daga nan kagan sai in koya" wani kallo yayi mata, ganin hakan tace"ai shi ba ta6a ni kayi ba ko" shiru yayi ya duk'ar da kansa yana kallon k'asan parlon da alama nazari yake don al'amarin Fatuu saida nazari kam😹.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story._


_*BY ZAINAB LALUH📲*_


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


*34⃣*

D'agowa yayi yai mata alamar ta duk'u da dogayen yatsun hannunshi,kneel down tayi a gabanshi ahankali yace"ki bud'e gyalen ki d'aura shi asaman kanki" tace "to" yin yadda yace tayi,hannu yasa ya kama ha6ar gyalen ta gefe guda ya janyo shi ta yadda zai fi d'ayar ha6ar tsawo,ba tare da ya ko kalleta ba ya shiga nad'a mata shi,daga k'asan wuyanta ya dan d'aure gyalen don in ba d'aurewar akayi ba bazai tsaya ba,har ya gama hannunshi bai ko ta6a gashin kanta ba,

cikin cool voice d'insa yace"U can get up now,an gama" bata mik'en ba sai ma washe baki da tayi tace"Yaya handsome ya akai kai ka iya kana namiji amman ni ban iya ba,kuma dai ai baka da k'anne balle ace awurin su ka koya" komawa yayi ya jingina bayansa da jikin kujeran fuskarshi a sake yace"ko" tace"eh mana ai kai kad'ai ne anan gidan baka da k'anne,Aunty Saude kuma yar aiki ce...." dan dakatawa tayi alamar tunani kafin taci gaba"ko a wurin ya'yan yayanka Senator ka koya" nodding kai yayi alamar eh, tace"ashe shi yasa ka iya,

to nayi kyau?" ta tambaya tana d'age idanu,hannu yasa ya dauki wayarsa ya shiga camera,mik'o mata wayar yayi "ki duba" kar6ar wayar tayi ta fara kallon kanta aciki lokaci guda ta kyalkyace da dariya"wllh nayi d'an banzan kyau sai kace irin larabawan nan da ke yin wak'a a wata tasha a tv d'in hajiya suma haka kumatunsu ke yi in suka nad'a gyale

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login