Showing 3001 words to 6000 words out of 212491 words
ji dadin nemo man fitina,Kullum cikin daukko man magana kike nikam na fara gajiya wllh kuma zan yi maganin ki indai baki bari ba tunda na lura sam duka bai maki" ta k'arasa maganar lokacin da ta iso bakin kofar dakin da ke a bangaren dama, d'aga labulan kofar tayi ta shige harda butar da ke a hannunta,ita kuwa fatun labulan kofar da ke kallon wadda gwaggon ta shiga ita ma ta daga ta shige,dakin baida girma sosae, akwae Gado irin na karfe mai spring yana da bakin fenti da katifa wadda aka rufe da tsohon zanin gado,A bangon dake kallon gadon kuwa wardrobe ce mai gida biyu da kananun gidaje a kasa suma guda biyu,ta dan ji jiki sannan yar madaidaiciya ce ba mai tsawo ba,a samanta akwae jakunkuna,daga gefen ta kuma dressing mirror ne kalar ta shima karami ne wanda hannuwan drawers din jikin shi wasu duk sun balle haka mirror din jiki dan guntu ya rage,akwai leda shimfide a dakin wadda ta ji jiki don duk wasu wurare sun farfashe,Saman gadon ta fada hadi da fadin "Washh" sai kace wadda tayi wani uban aiki banda neman rigima,tunani taci gaba da yi "ko sai yaushe zasu kawo kara tan..." k'wafa tayi a fili tace"Allah yasa su kara sawa a doke ni wllh nasan abunda zan yi masu...."Muryar gwaggon tace ta katse ta"fatuu fito ki tankade man garin can na cikin kicin yamma tayi in samu in daura girki......,Fatuu ko bakya jina ne wai? cikin d'aga murya tace "Ina ji fa,gani nan fitowa.." mik'ewa tayi ta nufi k'ofa sai faman k'unkuni take tana jujjuya kai alamar bata son yin abunda aka sata yi.
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
*STORY*
&
*WRITTEN*
BY
*OUMMU IMAM*
*Free page3️⃣&4️⃣*
Da d'an gudu gudu ta shiga gate din gidan wanda Babban gidane irin na masu hali wata yar hanya dake a gefen tank'amemen Flat din ta bi sai gashi ta 6ullo bayan gidan,gini ne dan dogo mai dauke da dakuna biyu a jere sai kuma kofofi biyu dake opposite da juna k'ananu,akwae baranda da ta lullu6e d'akunan kana kallon yanayin ginin zaka fahimci BQ ne da ake yi a gidajen masu kudi,BQ din yadan ji jiki saman Ceiling din barandar duk yadan farfashe haka fentin ginin duk ya k'oke,ga damsa kuka duk tayi baki-baki a k'asan bangon ginin,
Yara ne bi da bi a tsakar wurin suna ta wasa,yayin da wata mata ke can gefe ak'ark'ashin ginin da ake daura tankin ruwa tana ta faman hura wuta wurin duk yayi baki da gani a nan suke yin girki,yarinyar na isowa wurin wani Yaro ya buda murya yana cewa "Lah inna ga Jamila har ta dawo daga tallan" da sauri uwar ta su ta waiwayo daga cikin inda take ganin jamilar rungume da bokiti ga awara a saman shi da gani 6arin ta tayi,yasa uwar fitowa ba shiri tana fad'in "Jamila mi zan gani haka badae 6arar da awarar kika yi ba..."Salati ta shiga yi lokacin da ta k'araso taga awarar saman marfin duk k'asa cikin tsananin tashin hankali tace"yanxu jamila abunda kika yi man kenan kina sane da cewa ko kudin kayan da akayi awarar nan ba'a biya ba shine kika........" Jamilar ce ta katse ta da cewa "Wllh innarmu bani na zubar da awarar ba" "to ubanwa ya zubar da ita kuma kina aikin mi" ta tambaya a hasale "Fatuu ce ta 6arar man da ita wai don kin kai k'ararta an buge ta" nan ta bata labarin yadda ta bita har ta zubar da awarar,
Kwafa Innar tayi a hasale tace "to wllh bazata sa6u ba bindiga a ruwa,dole a biyani awara ta,yarinya ta bi ta addabi kowa to wllh bazan d'auki asara ba dole a biya ni" ta karasa maganar tana shirin juyawa ta daukko Hijabi bata karasa juyawan ba sakamakon kudin da jamilar ta miko mata sabbi fil,zaro ido uwar tayi lokacin da tasa hannu ta kar6i kudin tana jujjuya su "Wannan kuma na miye?"ta tambaya da mamaki a fuskarta "kudin awarar ne inna" jamilar ta bata amsa, "kudin awara kuma,da mamaki innar tasu ta tambaya lokaci guda kuma ta fara kirga kudin,da sauri ta d'ago ido a waje tace "na shiga ukku ni Saratu,jamila ina kika samu kudi haka da yawa? Jamilar tace "Mutumin da abun ya faru agaban sa ne yabani ya....."bata k'arasa maganar ba innar ta katse ta"ya baki kamar ya ya? hakanan bai sanki ba kawai don an 6arar maki da awara ya dauki kudi har dubu biyar ya baki a wannan halin rashin da kowa ke fama,ke jamila ki gayan gaskia kodae wani ya miki wayo ya baki,shine kika tsara man karyar Fatuu ta zubar maki!"ta karasa maganar idanu a waje tana cikin tsananin fargaba,hannu tasa ta fizgo yarinyar har awarar dake a saman marfin bokitin na zubowa tace "gaya man ina kika samu kudin nan ko in yanka ki a wurin nan" jin ance za'a yanka jamilar yasa sauran yaran tasowa suka yi cirko cirko suna kallonsu,da sauri jamilar tace"a'a inna wllh ba wanda yayi man wayo mutumin dana gaya maki anyi a gabansa ne ya bani kuma ma sai da na tambaye shi wa zance maki ya bani in kin tambaya....da sauri uwar ta katseta ta hanyar tambayar"to waye shi yace maki? Har lokaci tana rike gam da hannun yarinyar "cewa yayi ince maki dan gidan HAJIYAR SANATA"yarinyar ta fada cike da kwarin gwiwa don tasan gaskia take fada,
"Hajiyar Sanata! Innar ta maimaita lokaci guda kuma ta saki hannun jamilar da mamaki a fuskarta sai maimaita sunan hajiyar sanatan take "to ke kinsan shine dama" ta tambayi Jamilar "a'a Innarmu ni yau ma na fara ganin shi wllh"nan ta shiga fadi mata yadda sukayi dashi bayan an 6arar da awarar,innar tace "To waye wannan mutumin mai kirki haka,lokaci guda ta rike ha6arta da alamar tunani take...... taci gaba"Ni dai a tunani na Hajiyar sanata bata da wani d'a ko d'iya a gabanta gaskia,sai dai danginta da ke yawan kawo mata ziyara da kuma mutanen gari tunda gidanta gida ne na al'umma ko don taimakon da take ma mutane tunda mace ce mai kirki ga taimako gashi kuma d'anta babban dan siyasa ne shiyasa gidan bai rabuwa da mutane kala kala,Oh to shi wannan ko waye?"ta k'arasa maganar da sigar tunani,
Jamila ce ta katse ta da cewa"gaskia nidai ce man yayi dan gidan ne shi,kuma da gani haka ne,don baki ganshi ba innarmu Kyakkyawa ne sosae wllh wani irin fari mai kyau gare shi,ga gashin kanshi kaman na yan kasan waje ni wllh innarmu banyi zaton ma ya iya hausa sosae ba sai da yana man magana nayi ta kallon shi,kuma kin san mi inna? "A'a" innar ta bata amsa a inda take tsaye Sototo "Kalar kayanshi irin kalar motar da ya hawo ne,ina irin kayan nan na turawa masu igiya a wuya...tasa hannu tana kwatanta ma innar,ita kuma ta gyad'a kai alamar ta gane kayan"to sune a jikinshi kinga takalmanshi irin rufaffun nan ne masu kyaun gaske kai wllh Mutumin mugun dan gayu ne innah" ta k'arasa maganar tana yarfa hannu,
Ajiyar zuciya uwar tayi tace"to kam ina tunanin daya daga cikin jikokin hajiyar ne,don jikokinta tubarkallah akwae kyau sosae wllh don kwanaki can da dadewa munje kar6ar tallafi a gidan naga wani Matashin Saurayi mai kyaun gaske har muka gaida shi ya amsa mana kamar baison amsawar..."inna wllh kilan ma shine,shima wannan fa kamar dan dole yake maganar baki gani ba yana wani haka,ta d'an yamutsa fuska ita ala dole yadda yake magana take kwaikwaya gaba daya suka sa Daria harda Kannenta,Innar ce tace"hakan duk cikin gayu ne ai,kinsan su yan gayu komae nasu na daban ne wllh,kai Allah muma yayi mana arziki mai Amfani" ta d'an daga hannayenta sama, "Amman anya shine kuwa wannan fa anyi shekara biyu koma fi dana ganshi kilan dai dan uwan shi ne,kai koma dai waye nagode kwarai wllh Allah ya taimakeni ta silar shi,da bansan ya zanyi in biya kudin Waken nan da Mai ba dama sai da aka ja man rai aka bani,kai Allah ya taimake ni wllh",hannu ta daga tana k'ara gode ma Allah cikin tsananin farinciki,gaba daya yaran suma suka dauka"Allah mungode ma² suna yi suna tsalle ganin Mahaifiyarsu na farin ciki,kar6ar bokitin awarar tayi tana dubawa"Kai yarinyar nan anyi yar....ko da yake inma na zage ta kanmu abun zai k'are,don ba'a son mutum yana abu ana aibata shi da mugayen kalami,to kara lalacewa yake kuma mutanen da ke tare da shi su abun ke shafa,Allah ya shiryata dai damu baki daya" "Amin"yaran suka amsa da karfi" amman duk da haka ji nake kaman inje in fadi ma gwaggon tata don abun Yarinyar yayi yawa wllh" jamila tace"innarmu ki kyale ta kawae shima Mutumin daya bada kudin cewa yayi kar in bita gidansu don in an kara dukanta zata kara 6arar mani tunda bata jin Magana" hakane gara mu kyaleta tunda ma sanadin abunda tayi mana ji bi abun arzikin da muka samu" ta kara sa maganar tana k'ara kirga kudin,
wani yaro ne cikin yaran yace "Inna muzo mu karbi sauran mu cinye tunda an samu kudi" yayi maganar yana d'an noke kai gami da yar daria da sauri Innar tace"ehh maza kuzo ku kar6a" tsalle yaran suka fara yi suna murna,marar k'asar ta babbasu Jamila ce tace "Inna don Allah tunda ansamu kudi zaki ban in siyo hoda mai madubin da na tambaye ki kwanaki kika ce sai kin samu kudi" ta karasa maganar tana sussunna kai kasa,da fara'a a fuskar innar tace "Kwarai kam zan ba ki tunda Allah yasa ansamu kudin,ko dama can abunda yasa ban baki ba kudin ne ba isa suke ba sam kina dai ganin yadda ake ta fama,kinga da kika yi hakuri ba gashi Allah ya kawo ba, shiyasa in aka ce ma Mutum yayi Hakuri to yayi din don mataki ne na nasara rashin yin hakurin kuma ba abunda yake ja ma Mutum face asara da dana sani" cikin washe baki jamila tace"Eh hakane Inna" "to sakamakon hakurin da kika yi harda na siyan jan baki zan baki sai kije ki siyo harda sabon bokitin tallan" tsallen murna jamila ta fara yi tana ta faman daria tana shima dan gayu mai mota daya bata kudi Albarka,itama Innar tasu Albarkar take sa ma mai motar yayin da ta nufi daki don adana Kudin.
* * * * * * * * * * * * * * * * *
Wani irin Katafaren Gida ne mai tsananin kyau wanda da ka kalla zaka gasgata kyawun gidan,Fentin gidan ya matukar kayatuwa wanda Peach colour ne mai dan duhu had'i da milk colour,Katangar gidan na dauke da peach din fenti yayin da Pillars din dake a jikin katangar ke dauke da Milk din fenti,gaba daya katangar na zagaye da hadaddan Fence wanda ke dauke da farin fenti,daga saman fence din yadan yi tsini kamar mashi anyi mashi adon fenti Golden mai salk'i,cikin fence din kuwa shukan Flowers ne masu kyau da gani suna samun kulawa sosae,gasu a tsare mai tsawo sai ta gabanta gajera haka suke jere gwanin sha'awa,can saman katangar ma zagaye yake da Electric fence bak'i,A k'arshen katangar gidan gaba daya kuwa Masallaci ne mai kyau da girma komai nasa kalan na gidan ne ga Tankunan ruwa manya har biyu a sama da kan Famfuna a jikin ginin da aka d'aura su Yara nata dibar ruwa.
Gate din gidan kuwa ya d'an shiga lungu ta yadda in mota ta taho daga bangaren katangar gidan ta dama ko hagu zata shiga gidan sai andan karya kwana,
A daidai gidan mutumin ya juya kan motan ya tunkari Dank'areren Gate din gidan wanda shima yake da farin fenti daga saman shi anyi design irin na fence din,ajikin bangon da ke kallon hagu in an shigo kwanar gate din kuwa wata dakakkiyar Kofa ce a rufe itama da farin fenti mai salk'i da kwalliyar irin design din fence din wanda akayi ratsi da golden paint mai daukan ido.
Wasu Jami'an tsaro ne guda biyu dake zauna a saman bencin karfe shima da farin fenti suka mike ganin motar ta tunkaro gate din kowannansu na sanye da Uniform,daya uniform din yansanda ne jikinsa dayan kuma na civil defence had'i da Bindigu rataye a kafadunsu,daya ne ya kama gate din yana Sliding din shi right yayin da dayan ya matso kusa da motar yana washe baki,a hankali gilashin motar ya dan bude "Welcome sir" jami'in ya fada baki washe.
Mutumin ya juyo fuska adan sake yace"Thanks Officer,how work" cikin sauri officer din yace"Aiki Alhamdulillah gamu a cikinsa,har lokacin bakin shi a washe yake,"Ok,Allah ya taimaka" mutumin ya fadi a lokacin kuma yaja motar fuuu don angama bude masa gate din,da sauri dayan Jami'in ya daga masa hannu alamar sannu da zuwa lokacin da motar tazo saitin da yake a tsaye,Horn na cikin motar ya latsa alamar ya amsa,Parking Spot ya shiga wanda ke dauke da karafa masu farin fenti anyi masu design mai kyau yayin da saman wurin ke rufe da Alminium roofing sheet yana da girma don yana da wurin parker mota shidda,akwae motoci guda hudu a ciki akwai Hilux mai dauke da tambarin NGO,sai Vibe,peugeot 406,da kuma wata Had'addiya wadda na kasa gane sunanta,a kusa da ita ya parker motar a can karshe kuma wani hadaddan k'aton bak'in Bike ne ajiye, daga gaban parking space din wani dan daki ne wanda ba'a sa kofa ba,daga saman wurin shiga an rubuta GENERATOR ROOM,a gefen ginin wata kofa ce ta k'arafa wadda zata kaika cikin masallacin dake jikin gidan.
Wani matashin saurayi ne rik'e da tiyo yana ba Flowers ruwa yana sanye da wani kodaddan Crazy Jeans da bakan T-shirt itama dai ba sabuwa b,kanshi anyi mashi aski irin na gayu,yana ganin motar ta tsaya ya saki tiyon ruwan ya nufo ta da yar sassarfa ya tsaya a gefe yana ta faman washe baki sai da aka dauki wasu seconds kafin na cikin motar ya bude yana kokarin fitowa,da sauri saurayin dake a tsaye ya kama k'opar ya idasa bude ma Mutumin,fitowa yayi a hankali yasa hannu yana gyara necktie din dake wuyansa,saurayin ne yace "Barka da zuwa yalla6ai "yana ta faman washe baki, fuska adan sake ya kalli saurayin daga sama zuwa kasa da alama shigar da yayi yake kallo kafin ya tsaida fuskarsa akan tasa yace " Yauwa T.K Babban Yaro,yayi maganar ta sigar tsokana,
Cikin dan jin kunya T.k din ya sunkuyar da kansa yana murmushi yace "Ah haba yalla6ai wane mu Almajirai".Murmushi mutumin yadan yi kafin ya bude back door din motar yadan zura hannu ya fiddo da Briefcase din sa,da sauri T.K ya mik'o hannu ya karbi jakan shi kuma yayi gaba,T.k yasa hannunsa daya ya rufe duka kofofin motar ta gaba da ta bayan kafin yabi bayan mutumin.
Wata corner suka shiga wadda ke a bangaren dama inda gate din gidan yake, tafiya Mutumin yake cikin corridorn a nutse, yayin da T.k ke binsa a baya rungume da jakar har suka iso wata kofa ta karafa wato Fence door daga can gaba kuma akwae bayan wata kofa wadda ke a rufe tana kallon bangaren da fence door din da suke k'okarin budewa take da alama bayan hadaddiyar kofan nan ne dake a waje kusa da gate,hakan na nufin in kabi ta kofan zaka fito wajen gidan kwanar da gate yake.
T.k ne ya dawo gaban Mutumin da sauri yasa hannu ya zare kubar da ke rufe jikin Fence door din yasa hannu ya tura kofan ciki ya dawo gefe ya tsaya saida mutumin ya shiga sannan ya bi bayansa,dan Flat ne mai kyaun gaske wanda kasan ke malale da Interlocks ga Flowers jere masu kyaun gaske girman su daya,gaban flat din na rufe da fence mai dauke da glass wanda ke dauke da zanen flowers ajikinsa hakan ya bada area din da ake kira da Bolcany.
Sai da Mutumin ya wuce saman wurin kafin T.k ya bi bayansa da sauri T.k ya murd'a handle din Dakakkiyar kofar shiga flat din ta bude ya dan ja gefe guda yaba mutumin wuri ya shiga kafin yabi bayansa,Ya Allah!ba karamin had'uwa Parlorn yayi ba wanda gaba daya Fentin cikinsa fari ne mai salk'i,haka Tiles din da ke malale a kasa ma fari ne kar da ratsin baki,kujerun ciki kuwa Leather chairs ne L-Shape bakake wanda ke kewaye a tsakiyan parlorn a samansu akwae Throw pillows Red color masu kyau a jere,daga gefen dama kuwa in ka shigo akwae Armchairs guda biyu suma leathers ne amman red color saman kowacce akwai T-pillow bak'i,daga bayansu kuma wani Had'addan Desk ne manne da bango wanda ke dauke da Drawers gefe da gefe fari ne kal sai faman salk'i yake a samansa akwai Table Lamps (fitilu) guda biyu jajaye kowacce a k'arshen desk din,a tsakiya kuma bakin telephone ne ajiye daga dan gaban desk din tangamemiyar Window ce wadda ke rufe da farin Blinds (irin labulen nan mai yanka yanka,wanda aka fi yawan amfani dashi a office),A tsakiyan kujerun parlon dakakken Carpet ne mai laushin gaske baki dauke da ratsin kwalliya ja da fari a samansa kuwa wani hadaddan Center Table ne na glass fari mai kaurin gaske,daga can bangon dake kallon inda jajayen kujerun suke wata Window dince itama rufe da bak'in blinds,a bangon dake kallon duka