Showing 147001 words to 150000 words out of 212491 words
ne, daidai lokacin da suka bud'e Motar ta k'araso tana ta faman washe baki cike da girmamawa tace ma haisam " U'r welcome sir, Nana told me about ur coming" jinjina mata kai yay ta shiga gaidashi tana ce mashi ya ibada, dama itama musulma ce amman bayerabiya ce, bayan sun gama gaisawa ne yay mata bayanin yadda yake son gashin yayi amman bai son asaka mata relaxer, da sauri tace mashi kar ya damu hakan aikinta ne zata yi mata yadda yake so insha Allahu, kallon Fatuu tayi dake tsaye jikin kopa tace su shiga ciki, saida ta gaidata kafin ta bar jikin kopar ta rufeta har zata bita ta juyo ta kalli haisam tace " Ya Handsome kai bazaka shigo ba?" girgiza mata kai yay yace "kije zan jiraki cikin mota" jinjina mashi kai tayi ta juya matar na tsaye ta kama hannunta suka nufi shagon, komawa yay cikin motar ya rufe, kwantar da seat din yay ya d'an kwanta yana cigaba da sauraron karatun Alqur'anin da dama tunda suka taho ya kunnashi, Bayan kaman minti goma sha biyar da shigar su Fatuu cikin shagon kawae sai gata ta fito da gudu kanta duk an nad'a mata rollers yayi kaman an kifa mata d'an kwando, tana fitowa matar ma ta biyo bayanta da yar sassarfa don bata iya yin gudu saboda kiba a yadda ta biyotan sai kace giwa ta biyo yar akuya, side d'in driver ta nufa lokacin idanun Haisam na a lumshe saidai yaji ana kokarin bude kopar, da sauri ya ware idanunsa koda yay arba da Fatuu ba arziki ya tashi zaune ya fara kokarin fitowa daga cikin motar don har ta bud'e kopar, tun kafin yace wani abu matar ta riga cewa "Sir, she refuses to stay in d dryer" maida idonshi yay kan Fatun dake ta hura hanci ta kumburo baki lokaci guda takaici ya rufeshi, kallon matar yay yace taje kawae ta amsa mashi da okey kafin ta juya, kallon kallo suka shiga yi da ita yama rasa mi zaice kawae sai ya juya ya tada seat d'in motar ya shige tare da jawo kopar ya rufe, tsaye tayi awurin can kuma sai ta zagaya a d'arare ta bud'e kopar ta shiga ba tare da ta rufe ba, shiru tayi tana binshi da ido ya d'age kanshi sama ya lumshe idanunshi, bayan wani lokaci ganin bai tanka mata ba yasa ta kira sunanshi "Ya Handsome" shiru bai amsa ba hakan yasa ta k'ara kiran sunanshi sai lokacin yace mata taje su cire rollers d'insu tazo su tafi, jin hakan yasa tace " Fushi kai....." tun kafin ta k'arasa a fusace ya juyo yace "A'a ba fushi nayi ba tunda ni dutse ne, an gaya maki bani da abun yi ne da zaki sa in kawo ki wuri and ki k'i yarda ayi maki, ko kuwa ance maki bana jin azumin bakina ne da zaki sa in wahalar da kaina, tell me did i brought u here ba tare da amincewarki bane da zaki nemi tozarta ni!!" zaro ido tai jin yadda yake mata Magana a kausashe daga ji ranshi ya matukar 6aci sosae don ko lokacin da ya mareta bata ga irin bacin ran dake fuskarshi ba ayanzu,
" U are wasting my time Kije su cire abubuwan su don inada abun yi" ya sake fad'a a fusace aikuwa sai ta rushe mashi da matsanancin kuka acikin kukan ta fara fad'in "to ai ba hakanan nak'i yarda ba ko, ba ji nayi abun yana da zafi ba ni kuma ina tsoron kada ya guntile man kai tunda ai ban ta6a shiga irinshi ba ko, shine za kai ta man fad'a", still yay yana kallonta sai kuma da ta yi Magana ya tuna da wacece ya kawo wurin hakan yasa ya daidaita yanayinshi calmly ya kira sunanta cikin muryar kuka tace " Na'aamm",
" look at me Zarah" a hankali ta d'ago ta kalleshi fuskarta sha6e sha6e da hawaye, hannu yakai ya bud'e glove box ya ciro mata tissue yace ta goge fuskar, amsa tayi ta fara gogewa tana sakin ajiyar zuciya,
" Do u think zan kawo ki inda za'a cuceki ne?" ya tambaya bayan ta tsagaita da goge fuskar, girgiza mashi kai tayi alamar a'a,
"Then miyasa kike tunanin dryer d'in zai cire maki kai ne or what?" cikin disashshiyar Murya tace " to ai kai Namiji ne baka san ya abun yake ba" d'an girgiza mata kai yay yace "Nima ina dashi ai, amman nawa na hannu ne, yana busar da gashi ne kawae bai cire kai" d'an yamutsa fuska tai irin bazaka gane d'innan ba tace "to ai kace naka na hannu ne kaga ba irin wannan k'aton bane, shifa wani iska mai mugun zafi yake busowa" d'an Murmushi yay yace "Zarah duk d'aya ne ai, kawae iskan zai drying gashi ne ba zai cutar dake ba, kuma ko ni bansan irinshi ba ai Sisters d'ina na zuwa ana yi masu amfani dashi kuma bai ta6a cire ma wani kai ba saidae ya gyara gashin ya koma irin yadda kike so",
" A can Abuja" ta tambayeshi ya d'aga mata kai alamar eh, shiru tayi ta kafeshi da runannun idanu hakan yasashi cewa " in baki so kije su cire rollers d'in sai mu tafi kawae" jin haka yasa tace "to amman ai fushi zakai?" tayi Maganar fuska a kwa6e,
" bazanyi fushi ba but bazanji dad'i ba saboda kin nuna kina sone na kawo ki and bazaki k'ara nuna kina son abu ba inyi maki" yay Maganar ba alamun wasa, ta6e baki ta fara yi tace "to bari inje ayi man" shiru bai tanka mata ba saidae idonshi na akanta,
"Kaji" ta fad'a ganin baice komae ba, jinjina mata kai kawae yay ta juya zata fita sai kuma ta juyo tace " zafin bazai man komae ba dae ko" gyad'a mata kai yay ta sake juyawa ta fita daga cikin motar, shima fitowa yay ya d'aura hannuwanshi asaman Motar yana kallonta, nufar shagon tayi tana yi tana waiwayenshi ahaka har ta shige.......
ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,
ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
5️⃣8️⃣
.…...Yana ganin ta shige cikin shagon yay wani murmushi dama tun farko yadda ta fito da kan yaso bashi dariya ta wani bangaren, komawa yay cikin Motar yaci gaba da jiranta,
Bayan wasu tsawon Mintuna sai gata ta fito gyalenta a hannu da gudu ta isa gaban Motar tasa hannu ta bud'e kopar gefen driver ta shige lokacin idanun Haisam na a lumshe,
"Ya Handsome!" ta kirashi da karfin gaske dama yaji shigowarta kawae dae bai kalleta bane, a hankali ya ware eyes dinshi akanta, cike da farinciki ta juya masha bayan kanta tana nuna mashi gashinta daya sha gyara ya sauka sosae don har ya kai tsakiyar bayanta da gani harda stretching akai mata sai faman salki gashin yake, gyara zaman shi yay sosae fuskarshi d'auke da murmushi ya furta "yayi kyau" washe baki tayi sam ta kasa Magana saboda tsabar murna sai faman janyo gashin take ta gaba, suna cikin hakan Maman Abdul d'in ta k'araso bakin Motar, Haisam na ganinta ya bud'e kopar tun kafin yace wani abu tana ta fara'a ta tambayeshi gashin yayi yadda yake so ya amsa mata da yayi kafin ya tambayi kudin service d'in da sauri tace komi ya bada yayi, ba tare da ya k'ara cewa komai ba ya koma cikin Motar, glove box ya bud'e ya k'irgo kudi dubu goma Fatuu nata binshi da ido ya juya ya fita, a rude ta karbi kud'in lokacin da ya mik'a mata har da d'an duk'awa, sosae ta shiga yi mashi godiya tana fad'in "Thank u sir, May Almighty Allah increases ur wealth, May God bless u....." sai faman duk'awa take don ita kanta tasan bawae kudin aikinta bane ya bata kawai kyauta ce yay mata, shi dae jinjina mata kai kawae yay ya koma cikin Motar, kafin ya rufe ta lek'a da fara'a tace ma Fatuu tana jiranta ta k'ara zuwa tunda yanzu tasan Dryer d'in bai cire kai, kai fatun ta d'aga mata kawae ta juya ta nufi shago tana yi masu bye bye, yana Niyyar tashin Motar yaga Fatun na k'okarin bud'e mota ta fita ya tambayi lafiya,
" zanje in daukko abunne",
"Wani abu?" ya tambaya cikin rashin fahimta,
"Shi abun yin, dryer sunanshi ko?"
Bin ta da ido yay kafin yace "is it ur own?"
" ai naga ka bata uban kudi ba siya kayi ba?" yar harara ya wurga mata ba tare da yace komai ba ya tashi Motar suka sauka kan titi yaja Motar suka tafi,
Tunda suka bar wurin ta kasa natsuwa acikin motar, gaba daya ta aje gyalen rigar ma sai faman d'oki take tana ta6a gashinta har hannu take kaiwa ta juyo da rearview mirror bayan wani lokaci sai yasa hannu ya juya shi yadda zai ga bayanshi, da taga yana juyashi sai ta sauke glass d'in kopar da take ta rink'a lek'a madubin wajen tana ta washe baki,
"Ki rufe shi ko wanda Grandpa d'inki yace sunyi maki fitsari su k'ara" taji ya fad'a ba tare daya kalleta ba, juyawa tayi ta kalleshi tana zare ido tace "Aljanu?" kai ya d'aga mata,
" To ai banda su fa, in ma inadasu yanzu sun tafi",
"In kinbar kan a bud'e ai zasu ga yayi kyau su dawo ko",
hannu tasa ta rufe baki sai kuma ta kai hannu da sauri ta d'auki gyalen rigarta tasa ta rufe glass d'in don dama Gwaggo na yawan ce mata in bata son rufe gashinta shed'anun Aljanu zasu hau mata su shige jikinta,
A daidai wata k'atuwar Plaza ya juya kan Motar ya shiga, can gefe guda ya parker Motar bayan ya kashe yace mata ta fito, wani katon shago mai d'auke da sunan Zee's Collection ya nufa tana biye dashi sai faman kalle kalle take, suna shiga wata wayayyar mata fara mai d'an jiki ba sosae ba kuma tana da dan tsawo jikinta sanye da bakar Jallabiya tayi rolling veil dinta ta nufo su da fara'a hakanne ya bayyana hakorin makkan dake bakinta,
" The Big CoE, U'r welcome" fuskarshi da d'an Murmushi ya furta "thanks Zee" hannu ta mik'a ta nuna masu 2 seater leather sofa dake a shagon wanda yake dankam da kaya su laces, Atampopi, Materials harda dinkakku wato ready-made da kayatattun dogayen riguna, nufar kujerar yay ya zauna ta maida kallonta kan Fatuu dake ta bin shagon da kallo tace "Beauty ave a seat" kallonta tayi sai lokacin ta gaidata da fara' a ta amsa mata tace ta zaune, acan gefen Haisam ta zauna,
"H,Zakee ya ibada" ta tambaya tana ta faman fara'a, "Alhamdulillah, Ya bussiness"
" Alhamdulillah gamu munata kokartawa" jinjina mata kai kawae yay,
Kallon Fatuu tayi tace "What's ur name?"
"Zaraah" ta bata amsa
"Sannu Fateema Zahra anata Azumi balle kisha ko ruwa" da sauri tace "ai banayi" d'an bud'a ido Zee tayi tace " bakya yi why?"
"Ai bai zamar man dole ba saboda ban...." cakk ta kasa k'arasawa ta juya tana kallon Haisam da ya dan kishingida ajikin kujeran, lokaci guda Zee ta fahimci abunda zata ce hakan yasa tayi d'an Murmushi tace "to amman dae kinayi ko?" d'aga mata kai tayi "Eh, inna yi biyu sai in huta kwana d'aya" jinjina kai tayi tace gud, juyawa tayi ta kwala ma wata Esther kira sai gata ta fito yar matashiya ce da bazata wuce shekara sha biyar ba kuma tun daga kan shigarta da sunanta zaka gane ba musulma bace, tana zuwa ta d'an rankwafa ta gaida haisam da turanci ita kau fatuu sakin baki tayi cike da al'ajabi tana kallonta, abunda ya d'aure mata kai shine ganin kanta a aske kwal ga ba d'an kunne hakan yasa da farko tayi tunanin namiji ne sai kuma idonta ya sauka kan kirjinta dake dauke da breasts, Umarnin amso cake da lemu ta bata awani shago ta nufi hanyar fita Fatuu ta bita da kallo baki sake tace "kai! Wannan Namijine ko mace, kodae irin tane mata maza!" duk atunaninta acikin zuciyarta ta fad'i hakan bata san a fili tayi ta ba,
Murmushi Zee tayi "ba Namiji bane Mace ne haka al'adansu yake" bin ta da ido kawae tayi lokacin esther d'in ta dawo ruke da leda mai dauke da abubuwan da kace ta amso, d'an durkusawa tayi taba zee tace mata ta kawo plate cikin inda ta fito ta koma sai gata ta dawo rike da plate d'in ta bata, fiddo cake d'in Zee tayi ta d'aura asaman plate d'in da lemun, da d'an Murmushi ta mik'a ma Fatuu ta amsa tace ta gode, a hannun kujera ta d'aura plate d'in ta fara ci bayan ta bud'e lemun, yar hira Zee suka ci gaba da yi da Haisam don kawarshi ce tare sukae Secondary school da ita sai dae ta d'an girmeshi, jefi jefi yake tanka mata Fatuu dai nata cin cake d'inta tana kurbar lemu, bayan wani lokaci ya duba wrist watch ganin lokaci ya tafi yace ma Zee ta duba mata kayan da sukae Magana ta amsa mashi da to kafin ta kalli Fatuu tace mata tayi sauri tazo ta za6i kaya, jin hakan yasa tai saurin tura sauran cake din gaba daya ta kwankwad'e lemun da sauri ta mik'e tace ta gama, Zee na murmushi ta mik'e suka nufi bangaren laces tace mata ta zabi wanda yay mata nan fa Fatuu ta zaro idanu tana tsuke baki ta fara bin kayan da kallo zee dae na tsaye agefe tana Murmushi,
"Should i help u?" girgiza mata kai tayi tace "zan iya za6a" can ta nuna wani hadaddan swiss lace,
"Wow, gaskia kin iya za6e" Zee ta fad'a yayin da takai hannu ta ciro mata lace din, sosae Fatuu ta shiga washe baki tana juya lace din a hannunta can idonta ya kai kan price d'inshi dake manne ajikin ledan lace din, kura ma kudin ido tayi cikin rashin fahimta tace ma Zee "Wannan kudinshi ne?" kai ta d'aga mata alamar eh,
" To..Naira nawa ne naga ansa 64..,dubu shidda da dari hudu yake kenan?" tana ta Murmushi tace mata "No, ki duba sosae dai how many zeros are there?"
K'ara k'ura ido Fatuu tayi tana kallon kudin can ta dago a d'an firgice tace "zero ukku ne, kenan dubu sittin da hudu yake?"
"Yea, haka ne kin fad'a daidai" tana rufe baki ta tura mata lace d'in sai kace wani mugun abu, cikin rashin fahimta Zee ta tambayi miya faru ne tana tura baki tace " banson shi yay tsada da yawa, ace kudinshi har yayi kudin dan shanu wannan ma ai Almubazzaranci ne" sai yanzu Zee ta gano dalili kuma Maganar shanun da tayi tasa ta fahimci bafullatana ce nan take ta yanke aranta k'ilan cikin yan'uwan H,zakee ne na Daura, cikin d'an lallami tace "ai isn't an extravagance, in kana da hali ba laifi bane don ka siya abu mai kudi sosae, kuma ai kinga lace d'in is very fine and unique" turo baki tayi tace ita dae bata sonshi,
Girgiza kai Zee tayi ta maidashi kafin tace to ta za6i wani, tambayarta tayi wanda basu kaishi kud'i ba ta nuna mata gabansu, wani Golden yellow mai sak'a Coffee brown ta nuna shima yay kyau sosae amman tun kafin aciro ta tambayi nawa yake, saida Zee ta d'anyi jimm kafin tace dubu 42, shima sai cewa tai yay kudi a nuna wadanda basu kaishi ba Zee ta nuna mata, wani blue mai kwalliya golden brown ta nuna tana washe baki alamar yayi mata don dama tana son blue har saida Zee ta sauke yar ajiyar zuciya don duk atunaninta shi zata d'auka amman koda ta ciro mata taga kudinshi dubu 34 sai tace shima bata so yayi tsada, lallashinta ta fara yi tace ta daukeshi kawae tunda tana sonshi kuma shi ai baiyi kudi sosae ba tunda kudinshi ma rabin na farkonne amman ta kafe akan yayi tsada shima, jagub zee tayi tana kallonta tana ta tura mata baki can ta tambayeta kaman na nawa take so ne tace kaman na dubu goma irin wanda gwaggonta ta siya mata waccan sallar, jinjina kai tayi tace to bata da irinshi gaskiya don ita laces d'inta masu kananun kudi duk sun kai 20k, tana jin hakan ta juya tana fad'in "bari in ma Ya Handsome Magana babu wanda nike so sai mu tafi wani wuri",
Zee na jin tana niyyar yi mata asarar ciniki ta d'aga murya tana fad'in ya zatace ba wanda take so bacin duk gasu nan ta nuna, aikuwa tana