Showing 90001 words to 93000 words out of 212491 words
shaye-shaye suke ba bai kamata kije wurin wani a irin wannan lokacin ba",ta marairaice fuska kaman zatayi kuka tace"ai ni banyi tunanin zai cutar dani ba don ko hannuna bai ta6a kamawa ba shiyasa naje,amman Yaya Handsome yayi man fad'a ya kuma ce ko yayana ma wanda muke uwa daya uba daya zai iya cutar dani,yanzu bazan kara yarda da kowa ba,duk wanda ya ta6a man jiki yaya handsome yace in fad'i ma gwaggota kuma yace har shima",jinjina kai sukayi bayan ta gama,dpo yace"Gud,kuma ki daina rashin ji,in ba haka ba duk ranar da aka kawo mana ke zamu kulleki ne"a rude tace"ai na daina tuntuni wllh yanzu ba ruwana ka tambayi yaya handsome ma",
"Owk,kin kyauta,yanzu ina son zaki yi mana aiki..." zaro ido tayi"kana nufin in zama yar sanda?"d'aga mata kai yayi da sauri tace"to ai ni fa likita nike son zama ya zaka ce kuma in zama yar sanda",
"Ai lafiya lou,dama mutum zai iya yin aiki biyu,kuma ai sai kin girma zaki zama likitan shi kuma aikin yar sandar yanzu zaki yi mana shi" Sp ne yayi maganar,
Kallon Dpo tayi"to na yarda,mi zanyi?"
"Yauwa,zaki zama Jami'ar mu ta sirri ne,ina son kisa mana ido anan unguwar taku,duk wanda kika ga ya shiga kango da wata indae kinsan yarinyar to ki ruga gidansu ki fadi ma iyayenta,in kuma baki sansu ba to kije ki fad'i ma yayanki cewa kinga wani ya shiga da wata kango kar kice zaki bisu fa,sannan k'awayenki da kuke tare suma ki fad'i masu abunda yayanki ya fad'a maki game da yadda zasu kare kansu kuma kada su yarda da kowa",
"To zanyi,sai abani kayan yan sandan nima"yar dariya su kae harda haisam,
"to ai ke aikin sirri zaki yi mana,in kika sa Uniform kuma ai za'a gane ke yar sanda ce,kuma kinga masu aikata laifin zasu guji aikatawa a inda zaki gansu,wasu kuma suna iya zuwa gida suce zasu yi maki wani abun,amman kinga in babu Uniform d'in ba wanda zai sani sai iya mu kawae"kai ta d'aga mashi cike da gamsuwa,
"To Albashi fa" gaba daya suka tuntsire da dariya shi dae haisam d'an Murmushi yayi,Sp yace"ai mun zata zaki yi mana kyauta ne,to ga yaya handsome ne shi zai rink'a biyanki" zaro ido tayi"shi kuma,a'a abarshi to zanyi kyauta",had'a baki sukai wurin ce mata sun gode,
daga haka haisam ya kalli Dpo"Sir,are u done wit her?" d'aga mashi kai yayi"yes"kallon fatuu yayi gently yace"Zarah ki jirani a Mota"kai ta d'aga mashi daga haka ta mike ta nufi hanyar fita,Sp yace"ba ki d'auki gyalenki ba"sam ta manta ma da tazo da wani gyale harda yar jakarta duk suna akasa,komawa tayi ta d'aukko daga haka ta fuce su Dpo na mata sai anjima,
Bayan fitarta suka ci gaba da tattaunawa akan su Gaye,da shi haisam tunkan su zo ma ya sanar da Sp so yake a yafe masu tunda basu kaiga aikatawa ba,ayi masu horo sannan suyi rubutun cewa bazasu kara ba sai kuma ga wata babbar maganar,don haka yace ma Dpo ya bar komae a wurinsu su yanke masu hukuncin da ya dace kawae,duk hadin kan da suke bukata zai basu,daga haka suka yi sallama da Dpo din suka fito,
Atare suka nufo cikin station d'in bayan sun fito daga cikin corridorn Office d'in Dpo,
"Kawai ni a tura mu kotun zaifi don wasa da hankali zai tayi mun,tun yaushe yake cewa a k'ara mashi lokaci zai kawo amman shiru" atare Sp da Haisam suka juya inda suka ji anyi maganar,wani babban mutum ne sanye da malum malum a tsaye gaban kanta yake yin maganar daga gabanshi kuma wani dattijo ne sanye cikin tsohon yadi duk yaji jiki kanshi sanye da wata tsohuwar hula duk ta yankwane gashin fuskarshi da kanshi duk hurhura,
"Sergeant mike faruwa ne?" Sp ne yayi tambayar,
"Sir game da case din su Alhaji Ubale ne,shi wanda zai kawo masa kudin gashi nan ya zo,sai dae dubu biyar kawae ya kawo,to shine yace wai a tura su court kawae" jinjina kai Sp yayi yana niyyar juyawa su tafi muryar dattijon ta katse mashi hanzarinsa"Yalla6ai wallahi tallahi bani da halin kudinne ba irin kokarin da banyi ba don insamo su in kawo amman abun yaci tura,wannan dubu biyar din ma dana kawo wllh yar wayata ce naje na sayar,yanzu haka gidana ko abincin rana ba'ayi ba ga yarana guda biyu kwance,don su na siyar da wayar amman saboda ba yarda zanyi na kawo kudin nan"cikin karyayyar murya yake magana,yana kaiwa karshe kwalla suka fara zubo mashi yasa tafin hannunshi yana gogewa,ba k'aramin sanyi jikin Sp yayi ba,kallon Sergeant yayi"let me come back"daga haka suka fita,
tunkarar inda motar haisam take sukai bayan sun fito daga cikin station din,
"Miye case dinshi ne?" haisam ne yayi tambayar idonshi akan hanya,
"Wllh wai wannan Alhajin ne ke yin gini a unguwarsu shine yaronshi da abokinshi suka je gidan suka sace kofofi da winduna so bayan asirin yaran ya tonu an kamosu shine aka yi ma abubuwan da suka sata kudi don tuni sun salwantar dasu,to shi d'ayan yaron mahaifinshi ya biya,wannan dattijon ya rage ya biya nasu,d'azun da nazo ne na iske shi Alhajin nata korafin wai sau ukku ana mashi uzurin ya kawo bai kawo ba,lokacin dattijon bai kaiga zuwa ba" jinjina kai kawae haisam yayi a lokacin suka iso bakin motar,jingina bayanshi yayi da murfin motar ya kalli Sp,"Nawa ne kudin?"
"Gaba daya 150k ne so da aka raba kowa zai bada 70k an cire 10k" d'aga kai haisam yayi kafin ya maida idonshi kan wayarshi dake a hannunshi ya fara daddannata,
"Your Account no pls",
"U mean my account details?"Sp dake kallonshi ya tambaya,kai haisam ya daga mashi ba tare da ya d'ago ba,nan take ya fara karanto mashi acct details din,
Da sauri Sp yasa hannu cikin trouser pocket dinsa ya fiddo wayarsa jin k'arar shigowar message,duba wayar yayi da sauri ya dago ya kalli haisam"naga ka turo kudi har 200k,na minene?"
A nutse yace"kaba mutumin 150k sai ya biya kudin sauran kuma ya yi amfani dasu"daga haka ya juya yana k'okarin bude Motar,
"What about d remaining 50k,mi za'ayi da ita?",banza yayi mashi,ganin hakan yasa Sp k'ara tambayarshi don yayi tunanin ko bai ji shi bane,d'age mashi kafada yayi"i ave no idea"lokaci guda sp ya gane bashi yayi,shine ba zai iya fadi mashi hakan ba,
Girgiza kai Sp yayi" H,zakee u will never change",fuskar haisam da d'an Murmushi yace"I was born like dat"hannu Sp ya kai ya d'an bugi shoulder dinshi suka yi dariya gaba daya da alama wata sarar su ce ,godiya ya shiga yi mashi sosae shi dae bai tanka mashi ba,saima bud'e mota da yayi ya shige,
Lek'awa ciki Sp ya yi"To sabuwar ma'aikaciyarmu sai munji daga gareki ko"da fara'a yayi maganar,kai kawae fatuu dake zaune ta d'an kwantar da kanta ajikin seat ta d'aga mashi,daga haka sukayi sallama da haisam ya tashi Motar Sp na d'aga masu hannu ya jata suka tafi.
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_
_*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*_RAMADAN KAREEM_☪️*
_Allah ya kar6i ibadunmu yasa muna daga cikin yantattun bayi,Amin ya Sami'ud dua🤲_
*4️⃣3️⃣*
Lokacin da Sp khamis ya koma ciki dattijon nan nata matsar kwalla don kuwa Alhaji Ubale ya matsa akan a turasu kotu kawae,
"Ya Allah na dogara da kai,fadar kace,duk wanda ya dogara da kai ka isar masa,Ya Ubangijina kafi kowa sanin halin da nake ciki na rashi,nayi imani da jarabani da kake yi, nasan ba don baka sona bane sai don ka gwada imanina,Allah ka shirya man yarona da ya saka ni acikin wannan halin da Sauran Al'ummar Annabi(S.A.W)",
Dattijon na gama yin Addu'ar ya kalli Sergeant cike da k'warin gwuiwa yace"Ku tura mu kotun,duk da nasan ko anje banda halin biyanshi, Amman ubangijin dana dogara dashi nasan zai kawo man Mafita",ta6e baki Alhaji Ubale yayi ya juyar da kanshi gefe irin ko ajikin shin nan,
duk wannan abun akan idon Sp,yaji duk maganganun da dattijon yayi,nufar inda suke ya yi fuskarshi d'auke da Murmushi,yana isa gaban Dattijon ya mik'a masa hannu,kasa kama hannun SP yayi ya bishi da ido yana mashi kallon mamaki,hakan yasa SP jinjina mashi kai alamar ya bashi hannun,jiki na kerma ya mik'a masa hannu suka yi musabaha SP yace"hak'ika fad'ar Allah ce acikin Suratul D'alaq aya ta ukku'....Waman yatawakkalu alallahi fa huwa hasbuun....,ka dogara dashi ya kuma isar maka ta hanyar kawo maka Mafita"fuskar Sp d'auke da Murmushi yake maganar don ba k'aramin burgeshi dattijon ya yi ba,
gaba d'aya bin Sp sukayi da ido cikin rashin fahimtar abunda yake nufi,dattijon kuwa har lokacin hannunshi dake acikin na Sp sai kerma yake yi,
"Baba Mutumin da muka fita tare dashi ya baka Kud'in,ya turo su ta Account d'ina don ka biya shi" lokaci guda su Sergeant suka fara sakin Murmushi had'i da fad'in Alhamdulillah,don suma ba k'aramin tausayi dattijon ya basu ba,
Murya na rawa ya fara Magana"Yalla6ai ban fahimce ka ba,wani ya biya Kud'in kace? ko dae ba daidai kunnena suka ji ba?"
"Baba daidai kaji,ai kasan bazan zolaye kaba da magana irin wannan kuma a irin wannan lokacin" jin hakan yasa dattijon duk'awa k'asa yayi Sujjadar godiya ga Allah ,mik'ewa yayi hawaye cike a idanuwansa"Don Allah waye wannan d'an arzikin,waye mai kirkin nan haka,bai sanni ba, hakanan ya d'auki wannan uban Kud'in ya bani...."yana Maganar kwallan idonshi na zubowa ga kuma Murmushi yana yi duk alokaci d'aya,Sp shima dake Murmushi yace"Baba kada ka damu da sai kasan ko waye,don Allah ya baka",
"Nasani Yalla6ai,amman dae yakamata ai insan waye wanda yayi man wannan abun alkhairin da bazan ta6a mantawa ba asauran rayuwar data rage man",
"Ok shikenan tunda kana son sanin ko waye bari in fad'i maka,Sunan shi Haisam,shi d'an gidan Senator Ali Adamu Zakee ne" Sp na rufe baki Alhaji Ubale ya kar6e,
"ahaf d'an gidan dan siyasa ne dake kan mulki,su da ake satar kudinmu ana tara masu ai dole su rinka bada su yadda suka gadama.....",
Wata gigitacciyar tsawa Sp ya kwatsa mashi"Enough!!!kai ka tabbatar kud'in sata ne ya bada?shikenan duk wani mai mulki ya zama 6arawo?idan har cikin mutane akwae na kirki da kuma na banza to tabbas suma shuwagabannin dole asamu na kirki da kuma na banzan tunda daga cikin mutanen ake za6arsu,kuma da kake maganar wai an tara mashi,tabbas kuwa zancenka gaskiya ne an tara masa,sai dai ina son ka sani kud'in halal aka tara masa,kowa anan nasan ya san Mahaifinsa Shahararren mai kud'i ne wanda ya tara dukiyar da har su kare rayuwarsu zata ishesu yin rayuwa cikin jin dad'i,amman hakan bai hana Wannan bawan Allahn tashi ya nemi na kansa ba,injiniya ne na na'ura mai kwakwalwa,aiki yake ba dare ba rana,Kamfanoni da Manyan Ma'aikatu har ma da kananu wad'anda suka danganci aikinsa dake a Jahohin k'asar nan ake gayyatarsa yaje yayi aiki ba tare da girman kai ba ana biyansa kudin da ba komae yake dasu ba face yin aikin Alkhairin da yafi kowanne lada kamar yadda Manzon Allah(S.A.W) yace,Ka Shigarwa da Mutum Farinciki a rayuwarsa,ko ka yaye masa bakinciki,ko ka d'auke masa wata damuwa,babu aikin da yafi Wannan lada,ban tsaya ina maka wannan dogon bayanin ba don baka cancanci hakan ba,inda naso zan iya sa a kulle man kai saboda wannan maganar da kayi akanshi,amman banyi hakan ba don nasan da yawan Mutane irin wannan tunanin naka garesu akan duk wani mai Mulki,a k'arshe ina mai gargad'inka da ka rink'a kiyaye
harshen ka don Mutum irin wannan da kayi ma kazafi nada daraja ba awurin Mutane kawai ba har a wurin Ubangiji don yana daga cikin mafi Alkhairin mutane kaman yadda Manzon Allah(SAW) yace,khairun nas man yan faun nas,khairun nas anfa'uhun lin nas,(Mafi Alkhairin Mutane wanda yake amfanar mutane,mafi Alkhairin Mutane wanda Mutane suke amfanuwa dashi).
Ranshi a Matukar 6ace ya k'arasa Maganar,shikam Alhaji Ubale yayi wuri wuri da ido sai faman bashi hakuri yake yana fad'in su6ul da baka ne,banza yayi mashi,ganin yanayinshi yasa su Sergeant had'a baki wurin fad'in"Sorry Sir," shima Dattijon Mutumin hakurin yake bashi,sai da ya d'auki d'an lokaci ba tare daya tanka masu ba kafin yaba Alhaji Ubale Umarnin ya fad'o masa Account details d'inshi,baki na rawa ya soma fad'i mashi,ba tare da 6ata lokaci ba Kudin suka shiga yace mashi ya duba,dubu 70 cuf ya gani ya d'ago ya fadi mashi cewa sun shigo,shiru Sp yayi mashi don ba k'aramin kule shi yayi ba,ba don ya kai Zuciya nesa ba da sai ya hukunta shi,
k'okarin barin cikin Station d'in Alhaji Ubale ya fara,dakatar dashi Sergeant yayi"Hey,Alhaji waya baka izinin tafiya ne?"da sauri ya dawo yana fad'in"Oh kuyi hakuri pls,nazata shikenan" a rud'e ya yi Maganar,
K'aton littafin da ke abud'e saman kanta Sergeant ya duk'a ya d'an yi rubutu kafin ya d'ago yaba Alhaji Ubale Umarnin yasa masu hannu,cikin kermar hannu ya fara sa hannun bayan ya gama Sergeant ya duba sai kuma ya kalli dattijon ya nuna masa inda zai sa hannu,bayan duk sun sa hannun yaba Alhajin Umarnin tafiya,hannu ya d'aga yana yi masu Sallama ya nufi Hanyar fita buguzum buguzum,
Bayan fitarshi su Sergeant da dattijon suka shiga k'ara ba Sp hakuri,sauke ajiyar zuciya yayi yace masu ya wuce kawae,daga haka ya bukaci su zauna saman wani benci dake acan gefe shida dattijon,bayan sun zauna ne yayi masa bayanin ainihin kud'in da aka bashi,ya nuna mashi dalilin da yasa bai fadi mashi tun farko ba don yana ganin hakan na bukatar sirri ne don haka yanzu idan yana da Account ya bashi details dinshi zai tura mashi cikon dubu tamanin din,
Jin dattijon yayi mashi shiru ne yasa shi kallonshi yace"Baba kaji abunda nace?"shiru har lokacin bai ce uffan ba,hakan yasa Sp kai hannu saman kafadarshi ya d'an girgiza shi had'i da fad'in"Baba!"gaba d'aya Mutumin ya kifo jikin Sp,cikin tsananin tashin hankali ya d'ago shi yanata faman girgiza shi had'i da fad'in"Baba!Baba!!...."da alama fa kaman ba rai a jikin Mutumin,a rud'e Sp ya juya gun su Sergeant da k'arfi yace"Sergeant Bala pls come and help me!" suna jin haka suka zagayo da sauri inda su Sp suke,suma jijjiga dattijon suka shiga yi Sp dake kallonsu cikin tashin hankali yace"Sergeant ya Mutu ko?innalillahi wa'inna ilaihir rajiun....",
Sergeant dake tatta6a jikin Mutumin yace"I don't think ya Mutu sir,da alama suma yayi ne..."da sauri Sp yaba Inspector dake k'okarin k'arasowa inda suke Umarnin kawo masu ruwa,ba tare da 6ata lokaci ba ya kawo masu pure water guda daya,cikin sa'a ana yayyafa ma Dattijon sai gashi ya farfado,Sosae Sp ya shiga yin murna yana fad'in Alhamdulillah don ya d'auka Mutumin ya mutu ne saboda irin hakan tasha faruwa saboda tsabar farinciki Mutum ya rasa ransa,ganin ya farfado yasa su Sergeant tambayar dalilin sumewar nashi,Sp bai 6oye masu ba yayi masu bayani,gaba d'aya suka shiga yin dariya harda Sp d'in don sunga ba k'aramin rud'ani ya shiga ba,anan ne Dattijon ke fad'i masu cewa tsabar farinciki ne yasa shi sumewa don ahalin da yake ciki bai ta6a tunanin wani zai mashi irin wannan kyautar ba,kwalla na zuba yake masu maganar,gaba daya sun jinjina ma kirkin Haisam lokaci guda suka ji ya kwanta masu a rai,
Bayan su Sergeant sun bar wurin Sp ya sake tambayar ko yana da Account,dattijon yace eh yana da wanda ake biyansa albashi lokacin da yake yin aikin gadi,Sp yace ya bashi don ya tura masa kudin,karanto mashi Account no d'in yayi don k'arfin hali harda cewa wai Sp ya d'auki rabin kudin ya tura masa sauran,Murmushi kawae Sp yayi,maimakon ya dauki rabin sai shima ya k'ara masa dubu goma yace baza a barshi a baya ba a aikin ladan,kuka sosae Mutumin ya shiga yi yana k'ara gode ma Allah daya kawo masa Mafita ya kuma sa ya mallaki kud'i har Naira dubu 90 lokaci guda,
Mikewa Sp yayi don tafiya yace mashi yazo ya rage mashi hanya,sai da ya tura ma Sergeant da corpral dubu biyar biyar kafin suka wuce su Sergeant nata faman yi mashi godiya,tabbas zancen Sp game da Haisam gaskiya ne,ta dalilinshi Mutum hudu sun kasance cikin Farinciki,Allah ka bamu ikon sanya ma Junanmu Farinciki a koda yaushe,Amin.
Bayan sun hau hanya ne dattijon ya rok'i Sp da ya kira mashi haisam yayi mashi godiya tunda shi baida waya,Sp ya sanar dashi cewa ko ya kirashi ba lalle ya d'aga ba don yasan bai wuce ace za'ai mashi godiya ne dalilin kiran shi, kuma shi baison aita yi mashi godiya,dattijon yace a jaraba dae don yana Matuk'ar son yi mashi godiyar,kaman yadda Sp ya fad'a sau ukku yana kiran haisam d'in bai d'aga ba, a k'arshe yace ma dattijon kada ya damu da sai yayi mashi godiya ya gode ma Allah kawae,cigaba da tafiya sukae Mutumin na yima Sp yan tambayoyi game da haisam har yake ce mashi ba a Abuja Senator Alin yake bane,nan Sp ya sanar dashi cewa shi Haisam d'in a wurin Mahaifiyar Senator d'in yake anan garin wato Hajiya Hauwa Adamu Zakee,
A bakin titi Sp ya sauke shi don sauri yake ya koma Headquater,kafin dattijon ya sauka Sp ya tambayeshi sunanshi yace mashi Sunanshi Malam Garba,
"To Baba ina son in d'an baka shawara game da kudin nan daka samu in ba damuwa" baki na rawa yace"Ah haba yalla6ai ai ko Umarni ne kaban zan bi wllh",
Murmushi Sp yayi"dama so nike in baka shawarar ka nemi Sana'a duk da bansan ko kana da wadda kake yi ba,amman nasan yanayin rayuwar yanzu ko sana'ar mutum ke yi in ba wata babba bace nan da nan sai kaga ta durkushe",
"Hakane wllh,tabbas ina sana'ar yin faci tun bayan dana bar yin gadi kuma ba laifi ina samun yan kudaden yin hidindimun rayuwa,Allah cikin ikonsa kwanakin baya sai injin d'in da nike yin sana'ar ya lalace dama ya tsufa sosae haka ma kompressor din,koda na kai wurin gyara