Showing 171001 words to 174000 words out of 212491 words

Chapter 58 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

981

sai daddad'an kamshi da sanyin da yake saki kamar ko yaushe, kware baki tayi ta rafka uwar sallama amman shiru bata ji ko motsinshi ba hakan yasa ta nufi bakin Corridor ta k'ara d'aga Murya tayi wata sallamar nan ma dai shiru ba'a yi Magana ba tana shirin yin ta ukku taji an bud'e kopar Bedroom d'in, sanye cikin Maroon din jallabiya mai gajeren hannu ya fito fuskar nan tai wani fresh ai koda tai arba dashi gaba daya hannuwanta tasa ta rufe bakinta tana dariyar farinciki, tsaye yay a gabanta cikin Corridor d'in ya goya hannuwanshi a kirjinshi yana Murmushi don ta tare mashi hanyar da zai fita cikin falon, sosae farinciki ya lullu6e Fatuu har tama kasa Magana ji take kaman ta ruga ta kankameshi don bata ta6a tunanin zai dawo yanzu ba saboda Hajiya in ta tafi salla sai tayi sati ukku bata dawo ba wani lokacin ma har wata don daga can tana biyawa Lagos, ganin tayi mashi tsaye yasashi yi mata alamar zai wuce da hannu da sauri ta matsa gefe ya fito ta jera dashi suka nufi cikin falon, nuna mata armchair yay alamar ta zauna shima ya zauna a inda ya saba zama, maimakon ta zauna kan kujeran sai kawae ta zauna akan carpet gabanshi tana ta faman sakin Murmushi,

"Duk Murnan ganin Ya Handsome d'in ne yasa kika kasa Magana" ya fad'a had'i da d'age mata gira, d'aga mashi kai tay alamar eh sai lokacin tace "Ya Handsome ashe yau zaka dawo?" shima kai ya d'aga mata,
"Tare da Hajiya kuka dawo?" girgiza mata kai yay alamar a'a,
"To ya akai kai ka dawo?" fuska a sake yace "aiki" jinjina mashi kai tay tana dae ta dariyar hakan kuma ya bayyanar da tsantsar farincikin da take ciki shidae sai kallonta yake da d'an Murmushi saidae acan kasan zuciyarshi yaji dadin ganin yadda take ta farinciki saboda dawowar tashi,

"Amman Ya Handsome ya akai baka gaya man zaka dawo yau ba kuma ko jiya fa munyi waya" ta fad'a ta d'an turo baki,
"Nayi laifi ne?"
"Eh mana daka fad'i man ba sai in dafa maka abinci ba" ta fad'a a shagwa6e, Dariya Maganar tata ta bashi yace "ai bana jin yunwa"
"Amman dae ai daga tafiya kake yakamata kaci abinci ko" d'an kwantar da kanshi yay jikin kujeran idonshi akanta yace "Don't worry naci abinci kafin na taho kuma tafiyan baida tsawo so bana jin yunwa yanzu"
"To anjima fa da daddare ina zaka samu abinci tunda Hajiya bata nan?"
"Zan siyo a restaurant" ya bata amsa,
"A'a gaskiya ka bari sai in kawo maka kawae" d'age gira yay ya bud'e ido ganin hakan yasa tace "ko bazaka ci na gidanmu ba?"
Shiru kaman bazai bata amsa ba can yace "to ai bada ni akai ba kar in cinye maku"
"Ni dai ko nawa ne sai na kawo maka" ta fad'a tana turo baki,
"Ke kici mi kenan?"
"Yo ko garin kwaki sai in sha" waro ido yay alamar mamaki yace "zaki ci wannan ki kwanta zai saki ciwo ai"

"Ai ina sha in banson cin abincin" d'an ta6e baki yay kawae can kuma ta ruk'e ha6a tace "kai na manta wllh tuwo miyan busassan ku6ewa gwaggo tayi kuma ansa daddawa fa"
d'an Murmushi yay "kinga dole ki bar ni in siyo kenan" da sauri tace "to sai in dafa maka indomie",
"Da indomie d'in kika ce zaki sha wannan abun ki kwanta?" da alama Maganar shan garin kwakin ta tsaya mashi, d'an sosa kai tayi tace "ai indae akwae abinci nace banci to ko nace zan amso indomie din wurin kawu Amadu na dafa gwaggo hanawa take tace in banci in bari amman yanzu tunda kai zan dafa mawa nasan zata barni na amso" girgiza mata kai yay "ki k'yale kawae"
Magiya ta fara yi mashi tana rantsuwar ta iya dafawa ko kawu Amadu ita yake ba ta dafa mashi ganin yak'i amincewa tace "Allah in baka yarda ba kuka zan maka kuma bazan ci abincin dare ba nima" dariya yay har fararen hakoransa suka bayyana yace "You can start now akwae tissue da yawa" tana jin hakan ta d'age kafafunta sama ta tura kanta ciki, kallonta kawae yake yana Murmushi sanin halinta na saurin kuka yasashi kiran sunanta ta d'ago aikuwa abun mamaki sai ganin kwalla yai sharere a fuskar, ta6e baki ta farayi alamar kukan zata yi sosae, girgiza kai yay cikin cool voice d'inshi yace to zai ci indomie d'in kawae sai ta kyalkyace da Dariya tana fad'in dama tasan ai data yi kuka zai amince tunda baison kukanta shi dae Murmushi kawae yake yana kallonta,

"Ya Handsome kaga hotunan sallan da tk yace ya tura maka?" d'aga kai yay yace "yea sunyi kyau yan mata" rufe fuskarta tay alamar kunya adaidai lokacin aka fara kiran sallar Magrib, kokarin mikewa ta fara yi tace bari taje tayi salla sai ta dafo mashi indomie din, ce mata yay sai bayan sallan isha zai ci ta bari sai lokacin ta dafa kar ya huce don bai iya cin shi in ya huce, amsa mashi tayi da to har zata tafi kuma yay tunanin bayan isha dare yayi bai kamata tazo kawo mashi ba a wannan lokacin hakan yasashi tsaidata yace ta bari zaizo gidan bayan isha prayer sai ta dafa mashi lokacin, cike da murna ta amsa mashi da to ta nufi kopa tana jaddada mashi da an gama sallar ya taho fa ya d'aga mata kai daga haka ta fuce shima ya mik'e ya nufi Bedroom don yin Alwala........



ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,

ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUH📲*_
~(Oumm Imam)~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*



*6️⃣4️⃣*


.......tana komawa gida ta iske gwaggo ta dawo dama makwabta ta shiga, cike da zumudi ta sanar mata game da zuwan haisam cin indomie gwaggon tace to tayi sallar magrib sai taje ta amso wurin Amadu ta amsa da to,bayan ta gama sallar ta tambayi gwaggo guda nawa zata amso tace to kuma ba'a san nawa zata ishe shi ba ko abari yazo sai ta tambayeshi Fatun tace to, mikewa tay ta nufi kitchen ta fiddo d'an gas d'insu da zatayi amfani dashi ta aje acan gefen kicin d'in, komawa tayi ta fiddo tukunya da sauran abubuwan da zatayi amfani dasu duka ta aje, attarugu da albasa ta de6o bayan ta wanko su ta daukko d'an turminsu zata jajjaga gwaggo tace karfa ta cika tunda ba'a san ko yana son su ba tace ai kad'anne dama haka take masu in zata dafa ma Amadu saboda bai son ganinsu zak'o zak'o ba kaman Albasar, bayan ta gama ta kwashe su acikin wani d'an bowl ta rufe ta aje awurin sauran kayan ta koma kusa da gwaggo ta zauna ana fara kiran sallar isha ta mik'e tayi, tun bayan data gama ta zuba ma kopar shigowa ido tana dakon zuwan Haisam shiru shiru har bayan wani d'an lokaci bai zo ba hakan yasa ta fara mita can dai tace bari taje taga miyasa bai zo ba har yanzu, tana shirin mik'ewa gwaggo ta dakatar da ita tace ta kyaleshi tunda yace zaizo ai zaizo ne k'ilan wani uzurin ya tsaidashi, tana rufe bakinta Amadu ya lek'o ta cikin zaure yace ga Yaya Haisam nan zai shigo zumbur Fatuu ta mik'e ta nufi hanyar zauren tana fad'in ya shigo kawae mana, atare da shi suka shigo tana gaba yana biye da ita a nutse yake tafiyar jikinshi sanye da riga turtle neck da jeans sai faman juyawa take tana kallonshi bakinta a washe suka karasa ciki, fitowa gwaggo tay hannunta ruke da k'atuwar darduma tana mashi maraba ta nufi can gefen d'akin Fatuu ta shimfida mashi, bayan ta gama tace ya zauna saida ya cire takalmanshi a gefe kafin ya hau kan dardumar, gaisawa suka shiga yi gwaggo na mashi an dawo lafiya da tambayar ya ya baro sauran yan gidan da Hajiya, a nutse ya rinka bata amsa Fuskarshi a sake,

"Ya Handsome indomie nawa zan dafa maka?" Fatuu da tay tsaye k'erere a gefenshi ta tambaya,shiru bai bata amsa ba hakan yasa ta k'ara cewa "kaji Ya Handsome guda nawa zata ishe ka?" kallonta yay da d'an Murmushi ya d'aga mata dogon yatsansa alamar guda d'aya tana ganin haka ta zaro ido tace "d'aya kuma, amman dae babba ko?" girgiza mata kai yay a hankali ya furta "small pack" bud'a baki tay sai kuma ta tura shi cike da shagwa6a tace "kam ya za'ai k'araman indomie ta ishe ka" gwaggo dake d'an Murmushi ta amshe da fadin "adai dafa babba ko d'ana Haisam k'arama d'aya ai bazata kosar da Mutum ba...." da sauri Fatuu ta katseta "kuma ma tun Abuja fa bai k'ara cin wani abu ba nidai Allah manya guda biyu zan dafa maka ka ci ka koshi" tana kai Maganar ta nufi hanyar fita, har ta shige zaure sai kuma ta lek'o da d'an d'aga murya ta tambayeshi harda kwai ya daga mata kai alamar eh sai kuma tace "to guda nawa kwan?" kafin ya bata amsa cikin harshen fulatanci gwaggo tace ta amso ukku Fatun tace to tare da juyawa ta nufi waje shagon Amadu, bata d'auki wani dogon lokaci ba ta dawo ruk'e da bak'ar leda ta aje gefen sauran kayan kafin tasa hannu ta cire hijab d'in jikinta ta kaita can gefen tabarmar da gwaggo ke zaune ta aje tana niyyar komawa wurin da zata yi girkin gwaggo tace ahaka kai ba kallabi zata yi dahuwar, da sauri tace au ta manta ta nufi d'akinta ta dauro kallabi, bayan ta fito ta d'auki tukunyar taje ta debo ruwa ta kunna gas d'in sannan ta daura, cike da nuna kwarewa take dahuwar nan da nan k'amshi ya gauraye wurin lokacin data kusa gamawa,
"Ya Handsome ka fara jin kamshi ko?" ta juya tana tambayarshi da yake tsakan gidan fayau yake da hasken globe mai caji, kai ya d'aga mata yana Murmushi gwaggo ma dake zaune tana mashi fira jefi jefi itama Murmushin tayi, tunawa tayi bata dafa kwan ba hakan yasa ta tambayeshi ta soya mashi ko yafi son dafaffen yace ta soya, bayan ta dahu ta shiga kicin ta daukko plate mai kyau tana fitowa gwaggo tace ta sake wanko shi kafin ta zuba, ba 6ata lokaci ta wanko shi tazo ta juye indomie d'in ta nufi inda haisam yake tace ya fara ci kafin ta soya mashi kwan kada ta huce ya jinjina mata kai, mik'ewa gwaggo tay don yafi sakewa yaci ta nufi d'akinta, kicin Fatuu ta shiga ta d'aukko fraying pan da duk abunda zatayi amfani dashi saida ta daurayo su kaman yadda gwaggo tace tayi d'azun sannan tazo ta fara had'a kwan bayan ta zuba ta juya ta kalli haisam ganin baici yasa tace yaci kada ta huce mana, aje wayar yay gefe guda ba tare daya ce mata komae ba ya d'auki fork d'in cikin indomin ya d'ebo yar kadan ya kai baki ya fara ci a nutse,
"Ya Handsome ya kaji, da dad'i ko?" maimakon ya bata amsa sai ya mik'a yatsanshi yana mata nuni da kwan da take soyawa da sauri ta duk'a ta juya bayan kafin ta d'ago tana k'ara tambayarshi da dad'i indomie d'in jinjina mata kai yay ta washe baki ta shiga kod'a kanta tana cewa ai ta iya dafawa don kawu Amadu ma inta dafa mashi har santi yake shidai haisam jinjina mata kai kawae yake yana d'an cin indomie din can suka fara jin k'auri alamar kwan na k'onewa, a rud'e ta juya gun kwan koda ta juyashi har bayan ya yi bak'i amman ba sosae ba, kashe gas d'in tayi da sauri kafin ta juyo a sanyaye tana kallon haisam da shima kallonta yake fuskarshi a sake kaman zai dariya,

"Chef Zarah kin k'ona man egg ko" ya tambaya had'i da d'age gira, d'aga mashi kai tay alamar eh adaidai lokacin gwaggo ta fito hannunta ruke da buta zata bandaki ganin Fatuu tsaye sototo ga haisam na Murmushi yasa ta tambayeta lafiya tace mata kwan ne ya kone,
"Dama komae Mutum zai yi bai sa kula ba dole yaga ba daidai ba,sai ki maza kije ki amso wani kizo ki soya kafin ya gama" ta fad'a da d'an 6acin rai ta nufi hanyar toilet, tana niyyar juyawa taje ta amso Haisam yace ta barshi, kallonshi tay a sanyaye tace "amman ai bayan ya k'one fa" d'aga mata kai yay yace "sai ki cire wurin",
"Inda ya k'one d'in?" kai ya d'aga mata alamar eh, da sauri tace to ta kwashe acikin plate ta kawo mashi, duk'awa tayi zata cire inda ya konen yace taje ta wanko hannunta tana zuwa wurin gwaggo ta fito ganinta yasa ta tambayeta ta amso wani kwan ne tace mata ai yace ta barshi sai ta cire inda ya k'one d'in wucewa tayi ta nufi cikin gidan tana zuwa inda yake tace mashi miyasa ba zai bari a soya mashi wani ba yace lafiya lou abar wannan daga haka ta shige d'aki, bayan ta dawo ta cire inda ya konen tass ta d'ago tana kallonshi da d'an Murmushi,
"Go bring another fork" taji yace, mik'ewa tayi taje kitchen ta d'aukko wani cokalin mai yatsu kaman yadda ya mata umarni, tana mik'a mashi yace ta zauna taci indomie d'in, da mamaki ta kalleshi kafin tace wani abu ya rigata cewa "kinsan ai ya min yawa kika yi shi haka so da kanki dama kika yi" rantsuwa ta fara mashi wai shi kadai ta dafa mawa yace to ta zauna taci, zaunawa tayi ya juya plate d'in sukae facing juna, suna cikin ci gwaggo ta fito daga cikin d'aki don d'aukko ma Haisam d'in ruwa da lemu don yanzu Amadu harda manyan lemuna yake saidawa, tana ganin Fatuu na cin indomie d'in cikin harshen fulatanci tace ya ta dafa mashi abu kuma zata zauna ta cinye mashi, kafin Fatuu ta bata amsa Haisam d'in yace ba wani abu shi yace taci yayi mashi yawa, ba Gwaggo ba har Fatun saida tayi mamakin jin ya gane abunda gwaggon tace basu san guessing kawae yay ba daga yanayin yadda gwaggon tayi Maganar, Fatuu na ganin ta nufi inda freezer take da karfi tace "Gwaggo Coca cola zaki d'aukko mashi" tana juyowa suka had'a ido tasa dariya tana fad'in ai tasan kalan lemun daya fi sha kenan, ba laifi yaci sosae kafin ya aje fork d'in alamar ya koshi tana niyyar aje nata yace yasan bata koshi ba ta cinye, dariya tayi kafin taci gaba da ci shi kuma yaci gaba da latsa wayarshi, saida ta cinyeta tass ta tsiyaye sauran lemun daya bari mai yawa ta shanye sai lokacin ya d'ago ya kalli plate din kafin ya kalleta aikuwa da sauri ta sadda kanta tana dariya,
"Acici kawae" taji ya fad'a da sauri ta kalleshi ta turo baki tace "Kai Ya Handsome bakai kace in cinye ba" dan ta6e baki yay kafin yace wani abu wayarshi ta fara ringing kai idonshi yay kan screen d'in kafin yay picking call din fara magana a nutse, sanar da mai kiran yay cewa zai kirata in ya koma gida on the other hand aka tambayi yana inane yace yana gidansu Zarah,
"Oh Zarah where is she, let me speak wit her" wadda yake wayar da ita fad'a, mik'a ma Fatuu wayar yay ta amsa tana tambayar waye daga cikin wayar taji ance "is ur Sis Fanan" washe baki Fatuu tayi tace "Aunty Fanan ashe kece, ya India" amsa mata tayi da lafiya lou,
"Ai ina ce ma Ya Handsome ya gaida man ke in naga kuna waya yana fad'i maki?" amsa mata tayi da eh,
"To rannan nasa ya d'auki hoton kayan dana ce ki siyo man ya turo maki?" nan ma amsa mata tayi da eh ya tura mata,
"To kin siyo?"
tace "No, na bari sai zan dawo kinga in an siya yanzu zai iya maki kad'an lokacin"
"To shikenan,amman fa in suna da tsada ki barsu kawae kar ki kashe kud'inki kuma ki rasa na dawowa" har saida ta bata dariya kafin tace "Don't worry sis Zarah, i will definately buy it for u ko don yadda kike kulawa da Ya Handsome d'inki" jin hakan yasa Fatuu washe baki cike da gwaninta ta shiga bata Labarin indomie din data dafa mashi yanzu ya ci saboda Hajiya bata nan, sosae Fanan d'in ta nuna jin dad'inta tay mata godiya, hira suka shiga yi har saida Haisam yaji ya gaji da zaman ya mik'e sannan Fatun tayi sallama da ita tace Ya Haisam din zai tafi, d'akin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login