Showing 105001 words to 108000 words out of 212491 words
Bus ta wuce baki ji takaicin dana ji ba dole na hawo mashin koda na iso har an fara taren yan makara,a bakin gate d'inne naji prefects nata Maganar Motar da aka kawo ki suna kuma zuzuta Mutumin da ya kawo kin,kinsan fa A.Sp Asma'u Kabeer har tambayata tayi wai ya kuke dashi.....", katseta Fatuu tayi da sauri,"ya kika ce mata muke dashin?",
Dariya haulat tayi"Yo cewa nayi Yayanki ne",
"Yauwa Allah gwara da kika ce masu hakan yan sa ido kawae,wai kinga yadda aka rink'a bin Motar da ya kawo nin da ido sai ma da ya fito zai gaisa da Principal ashe ya santa innalillahi!ke kinga kuwa yadda ake kallonshi",
"Ai naji ance wai har kud'i yaba masu gadi,Binta Musa duk ta rud'e wai yadda ya kira Baba maigadi mai kirki ya bashi abun kaman a film..." da sauri fatuu ta amshe"Wllh baki ga uban kud'in da ya mik'o mashi ba,dafa inaga Maigadi Masifaffen hana shi yaso yayi wanda aka bashi aikau ashe Ya Handsome d'in na kallo shine ya kira shi shima ya bashi",
"Ai in gaya maki suna can sun rud'e sai faman santinshi suke yi anga Mijin Novel,Labour Prefect Binta Musa ma wai zata zo kamun k'afa a wurinki,kinsan ma lokacin da aka samu a layi za'a kaimu muyi punishment ita tasa ni in gudo wllh sauran na can suna shara wasu na wankin toilet,ke hardae Sp Ni'imatu Abdullahi da take miskila saida ta tanka akanshi wllh",Wata Mahaukaciyar dariya Fatuu tayi,
"Ƙyale banzar tazo d'in,yama za'ai Ya handsome ya sota da fuskarta kaman an ƙona baƙar leda",hannu Haulat ta kai ta d'an bugi kafadarta"wllh baki da kirki fatuu,aikam tana da kyawunta daidai gwargwado kawae don dai tana bak'a sosae ne,kuma ba ita kadai ke son nashi ba Asma'u Kabeer ai ba laifi tana da kyau kuma wankan tarwada ce...."
"Allah yasa wankan kada ce wllh Ya Handsome ba abunda zaiyi da ita,ce man fa yayi shi baida budurwa",
ita dae haulat dariya kawae tayi tace"wai bazamu fita break bane sai an dawo",
"Wane break ai yau a aji zamu yi break d'inmu basai munsha wahalar fita ba"Fatuu tayi Maganar yayin da ta kai hannu ta d'aukko jakarta ta zage zip, fiddo abubuwan dake aciki tayi ta d'aura su saman desk,bin yoghourt da fruit da k'aton biscuit d'in haulat tayi kafin tace wani abu Fatuu ta fara bata labarin kayan dubiyar daya kai mata jiya da daddare da biscuit had'i da kud'in daya bata lokacin da ya kawota,
"Kai Amman Mutumin nan yana da Mugun kirki wllh...." katseta Fatuu tayi"Mugun kirkin ma,ba kinga kayayyakin daya siya man ba lokacin da kika zo gaida ni",
"Gani kai,nida har na samu rabona,da wani ne kika ma laifin da kikai mashi tun farko ko kallonki ma zai sake yi ne in ma bai d'au mataki akanki ba kenan,amman shi ji abun arzikin da ma yake maki wllh yaji dadi,ga kyau ga kudi ga kirki ko nayi rantsuwa bazan yi kaffara ba samun irinshi a wannan lokacin zaiyi Matuk'ar wahala wllh", Murmushi kawae fatuu ke saki ta bud'e masu biscuit da yoghourt d'in suka fara ci,
Suna cikin yin break d'in sai ga prefects su biyar sun shigo,su Binta musa ne,Asma'u Kabeer,Amina Aminu,Halima lawal,sai Sp,dama mate dinsu ne suma duk Js 3 suke itama Fatun lokacin da suka shiga aji ukkun harda ita cikin wad'anda aka za6a za'a basu prefect d'in Displine master ne ya hana a bata don cewa yayi in aka bata watarana sai ta kashe wata tunda kaman yar dambe take bunu bunu an kai k'arar ta bugi wata harta raunata ta,gashi kuma lokacin sam bata da wani tsawo yar k'arama ce kan sauran da aka za6an,
tana ganin sun shigo ta wani sha murr,saman Desk din wasu suka zauna wasu kuma suka tsaya a tsaye,tambayarta sukae wai haulatu ta gaya mata sak'onsu tace masu eh,nan suka shiga zuzuta haisam din suna fadin basu ta6a ganin mutum mai irin kyawun shi ba a Nigeria,tambayoyi suka rink'a yi mata cike da rainin wayau take basu amsa wani lokacin kuma ta 6a66ake masu da dariya ganin yadda duk suka susuce kan Ya Handsome,ba kamar Binta Musa da Asma'u Kabeer su da gaske sonshi suke sai faman rokonta suke wai ta shigar dasu wurinshi da taga dae bilhakki da gaske suke sai tace masu ita bata iyawa don bai wasa da ita duk wadda ke sonshi in ya k'ara zuwa taje da kanta ta fad'i mashi,nan take duk suka ce gaskia bazasu iya ba,bai yi wasa da ita bama ita dake yar'uwarshi balle su, kuma sunga yasan principal kar su ja ma kansu,fatuu tace to sai suyi hakuri kawae,k'arshe dai atare suka idasa cinye kayan break d'in su Fatun kafin suka tafi.
Kallon Haulat Fatuu tayi fuska a tur6une"banzayen sun zo sun cinye mana abu gashi ma ban k'oshi ba",
d'an Murmushi tayi tace"rabonsu ne ya tsaga suma",
ta6e baki tayi"to sai kiyi sauri ki taso muje mu siya wani abu kafin adawo",tayi Maganar had'i da mik'ewa tsaye itama Haulat d'in ta tashi suka fita daga cikin class din.
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching love story._
_*BY ZAINAB LALUH📲*_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*4️⃣7️⃣*
Lokacin da suka tunkaro gate d'in,Discipline master na tsaye awurin masu gadi sunata yi mashi zancen Haisam,sai faman yaba kirkinshi suke,Dariya Malam Mahadi yayi yace"ai kufa dama kunfi kowa shaida kirkinshi tunda ya cika maku Aljihunanku,amma dae nima na yaba da kirkin shi gaskiya",
adaidai nan su Fatuu suka k'araso bakin gate d'in,kallon masu gadin Malam Mahadi yayi"to ga wadda tayi maku sanadin Alkhairin da kuka samu nan sai kuyi mata godiya" ya yi Maganar yana nuna Fatuu,atare suka kalleta da mamaki Maigadi mai kirki kaman yadda suke cewa ya furta"Dama Fulani ce ya kawo?",sunan da yake kiran fatuu dashi kenan saboda sun sa6a sosai da fulatanci ma yake mata magana duk in tazo bakin gate d'in kuma dayake shi yana a toilet lokacin da fatun ta fito daga Motar Haisam shiyasa baisan itace aka kawon ba,
"Eh Yayanta ne" Malam Mahadi ya fad'a,aikuwa nan suka shiga yima Fatuu godiya gaba d'ayansu suna fad'in Allah ya k'ara Arziki shi d'ayan da fulatanci yake mata godiyar ita dae sai faman sakin Murmushi take ba tare data ce masu komai ba,
"Ku sai yanzu zaku je Break d'in an kusa dawowa"Malam Mahadi yace,
turo baki tayi"to ai da a aji zamu yi break d'in bazamu fito ba sai kawai......"da sauri Haulat ta tari numfashinta tace"munci kayan break din tare da wasu ne to sai muka ji bamu k'oshi ba shine zamu je mu siyo wani abu mu k'ara" kai ya jinjina masu daga haka suka wuce,
Bayan sun fita gate d'inne Haulat tace"kefa yanzu yakamata ki zama mai aji don d'an gidan Hajiyar Sanata ya kankaro maki girma,shiyasa na katseki da kina ma Malam Mahadi magana don nasan halinki sarai shima kina iya ce mashi banzayen prefects ne suka cinye mana abun break d'in wanda hakan ba girmanki bane kina dangin Senator",ta k'arasa tana tik'ar dariya,itama Fatun kyalkyacewa tayi da dariyar tace"Dangin Senator masu shanu ba,sufa duk sun yarda baki ga yadda Malam mahadin ma ke man magana ba cikin mutunci inda da ne wllh kora mu zaiyi ya hana ni fita break d'in tunda bamu fito da wuri ba",dariya suka ci gaba da yi Haulat nata tsokanarta tana fad'in dangin Senator.
__________
Misalin karfe 4:30 na ranar,Haisam na zaune a falon hajiya saman Sofa 2 seater yana cin abinci,jikinshi sanye cikin Sportswear da gani gym zai tafi,
"Wai wace yarinya ce yau ka kai Wtc ne?" hajiya ta jefo masa tambaya,sai da ya cinye abincin dake acikin bakin kafin yace"Wani abu?",
"A'a,dama principal ce ta kira ni muka gaisa shine tace man yau ta ganka a Makarantarta kun gaisa har kake ce mata sister dinka ka kawo shine nike ta tunanin wacece ka kai Makarantar ne?"
"Zarah" ya bata amsa ba tare daya kalleta ba,
"Dama saida nayi tunanin itace ka kai", shiru yayi baice mata komae ba,ganin yana k'okarin mik'ewa tace"halan har ka k'oshi?",
Kai ya d'aga mata"Yea,i ate too much food at work"d'an ta6e baki tayi"ka dae ci abunda ka saba ci ba dae abinci ba,ni da nasan hali ai saidae ka fadi ma wani hakan ya yarda badai ni ba",
d'an murmushi yayi"Am serious yau naci abinci,Zarah tasa nayi alk'awarin zan ci abinci in k'oshi"fuskar Hajiya d'auke da tsananin mamaki tace"Fateemar ce tasa ka yin hakan?"kai ya d'aga mata alamar eh,ganin tana ta binshi da ido har lokacin da mamaki akan fuskarta yasashi fad'i mata yadda akai tasa shi yin Alk'awarin,Lokaci guda tayi Dariya ta furta"Ina ruwan Fateema,ta man daidai itama tasan ba yadda za'ai tarkacen su biskit su ruke Mutum kamar ka",
daga haka ya nufi Dining area ya kuskure bakinsa had'i da wanke hannayensa a Washbasin duk da badasu yaci abincin ba,hanyar fita daga parlon ya nufa ya d'aga ma Hajiya dake kallonshi hannu alamar bye bye,itama hannun ta d'aga masa tace"A dawo lpy,Allah ya tsare.
Yana fita parking space ya nufa ya fiddo bike dinsa cikin harabar gidan,jakarshi dake rataye ajikin bike d'in ya curo ya goyata a bayansa daga haka ya tasheshi bayan yasa helmet ya nufi gate da tuni an bude masa shi ya fuce.
**** ***** *****
Bayan Sallar isha'i Haisam ya shigo gidan,parking space ya shige ya parker bike din,jakarshi rataye a hannunsa na hagu ya nufi part d'inshi,yana niyyar shiga cikin corridor wayarsa ta fara ringing alamar ana kiransa,hannu yakai cikin Aljihun wandonsa ya fiddota, tsayawa yayi ganin hajiya ce ke kiran nasa,picking call din yayi ya kara wayar a kunnansa,
"Naji ka shigo ka d'an lek'o nan kana da bak'o", amsa mata yayi da"Ok" daga haka ya cire wayar,yaso ya isa part d'in nasa don ba abunda yafi buk'ata ayanzu face yayi wanka to amman baisan wane bak'o bane kuma baisan tsawon lokacin da ya d'auka yana jiransa ba hakanne yasashi aje jakar anan bakin corridor din ya juya ya nufi part d'in Hajiya,
Da sallama ya shiga cikin falon lokacin daya isa,Hajiya na zaune tana opposite da wani dattijo sanye cikin manyan kaya riga da wando kanshi sanye da hula harda rawani,amsa mashi sallamar sukayi ya nufi sofa one seater dake kusa da wadda hajiya ke azaune ya zauna,gaida mutumin yayi cikin girmamawa ya amsa mashi,
"Yauwa Mahaifin Ashiru ne yazo yana son ganinka" hajiya ta fad'a,shiru haisam yayi yana son ya tuna waye ma Ashirun,kallon Dattijon hajiya tayi"Malam bismillah kuyi magana",
Amsawa yayi da toh ya d'an matso daga kan kujeran kafin yayi gyaran murya ya fara Magana "Dama naje can caji office ne don in dubashi to ananne nasamu labarin kaine ashe ka kai case d'in..."d'an dakatawa ya yi,sai yanzu Haisam ya gane Ashirun da ake nufi wato Gaye,
d'agowa Malam Tanimu yayi cikin sanyin murya ya d'ora da fad'in"tun bayan da al'amarin ya faru banyi niyyar sa baki ba saboda babban laifi ne sukayi niyyar aikatawa ba don Allah ya kiyaye ba,kuma yakamata dama arinka bada goyon baya wurin hukunta masu aikata irin wannan laifin ta hakanne za'a samu saukin al'amarin,amman ina kowa baison a hukunta nashi,sai mutum ya aikata mummunan laifi amman kiri kiri kaga danginshi sun shiga sunyi yadda sukai an sake shi ba tare da an hukuntashi ba yadda yakamata,shiyasa kullum k'ara samun yawaitar masu aikata munanan laifuka ake tunda sunga ko an kama ma saki ake ba tare da anyi wani tsattsauran hukunci ba,Allah ya kyauta ya rabamu da son zuciya" gaba daya suka amsa da Amin,
Gyaran murya ya k'ara yi kafin ya sake d'aurawa"Yau da naje tasani gaba yayi yanata kuka yana rok'ona akan kar na bari wai akai shi gidan yari shi wllh yasan yana shaye shaye da yan d'auke d'auke amman bai ta6a yunkurin aikata fyade ba,na nuna masa komae ya faru dashi shi yaja ma kansa da ya za6i yin irin wannan rayuwar har yayi abokai gur6atattu irinshi,bayan an maidashi cikine muka tattauna da wani d'an sanda nan mai kirki har yake nuna man ya tausaya ma yaron don ya jefa kanshi cikin matsala gashi yanzu da kyar ne in ba'a kaisu gidan yari ba,kuma matsalan wasu in aka yanke masu hukunci kan laifin da basu aikata ba in suka fito sai kaga sunzo suna aikata laifin saidae wanda Allah yasa yana da sauran imani,wasu kuma sukan had'u da manyan masu laifine sai kaga sun koyo mugayen laifukan da sunfi wanda suke aikatawa muni da sauransu dai..."dakatawa yayi yana maida numfashi kafin yaci gaba"atak'aice dai ni Uba ne,duk yadda naso k'arfafa zuciyata saida tayi rauni,maganganun d'an sandan nan sun tsaya man araina,kullum bani da fata da burin daya wuce inga Ashiru ya shiryu,shin yanzu in aka kaishi gidan yarin ya halayyarsa zata koma kuma?wannan tambayar ita ta tsaya man arai ta kuma saka ni jin tsoron zuwansa can d'in don bazan so yafi hakan lalacewa ba tunda dai ba'a ta6a canja ma tuwo suna,shi d'in d'ana ne ni na haifesa hakan bazai ta6a canjawa ba,ba komae ya bani kwarin gwuiwar zuwa gareka ba face furucin da ya rink'a yi yana kuka na ya yarda zai koma Jos in dae na ku6utar dashi lokacin da za'a maidashi cikin cell....",
"Wani abu ake a Jos d'in?" Hajiya ce ta katseshi da wannan tambayar,
"Eh akwai wani Yayana acan babban malamin tsangaya ne,ana tura mashi kangararrun yara ba kamar masu irin halin Ashirun wato masu yin shaye shaye da kuma sata kuma akan dace su shiryu,da farko lokacin da ya jefa rayuwarshi cikin wannan halin nayi tunanin zan iya gyarashi amman ina,ganin abun nashi yana yin gaba ne yasa nayi ma yayan nawa magana akanshi yace in kaishi can,wllh banfi sati guda da kaishi ba sai gashi ya gudo,bayan wani lokaci na sake d'aukarshi na maidashi amman sai ya sake guduwa kuma abunda ya tada man hankali shine da ya gudun ba nan gida ya dawo ba gaba yayi bamu san inda ya nufa ba,hankalinmu ya matukar tashi don ba irin neman da bamu yi mashi ba amman shiru ba labarinshi,haka muka hakura kuma muka dukufa da yin Addu'ar Allah ya bayyana shi kwatsam, wata rana sai gashi kamar an jefo shi,nayi Matuk'ar farincikin dawowarsa duk da canjin dana gani atattare dashi,wai ashe lagos ya tafi bayan ya gudun,to tun dagananne na hak'ura da turashi jos d'in duk da halin nashi saima abunda yayi gaba bayan yaje lagos d'in", sauke ajiyar zuciya suka yi gaba dayansu,
"Yanzu mi kake bukata a wurina ne?" Haisam ne ya yi Maganar,shiru yayi ya d'an sadda kanshi k'asa kafin ya d'ago yace"idan zai yuwu ina neman alfarmar ayi mashi duk hukuncin da ya dace amman don Allah kar akaishi kotu don daga can ne za'a iya tura su gidan yari,na dad'e ina mashi Addu'ar shiriya watakil lokacinne yayi don tabbas naga nadama a idanuwanshi kuma sanin basu kaiga aikata laifin bane yasa nayi karfin halin zuwa nema mashi wannan Alfarmar,wallahi tallahi kaji arantse da ace yau sun aikata laifin koda shi Ashirun bai yin ba bazan ta6a nema masa sassauci ba duk kuwa yadda raina zai sosu zan bada goyon baya d'ari bisa d'ari akan ayanke masa hukunci",
Jin ya dakata yasa Haisam fara Magana"at first munso ayi masu afuwa ne tunda basu kaiga aikatawa ba so bayan munje can da Yarinyar ne kuma ta kawo wani issue wanda yasa dole aka fasa yi masu afuwan da akai niyya bansan ko kasamu labarin hakan ba",da d'an rud'u Malam tanimu ya girgiza mashi kai"bansan wani abu ba bayan abunda ake tuhumarsu dashi,dayake tunda aka kamasu ni banje ba sai yau,yan uwansa dae na zuwa Mahaifiyarsa ma taje",jinjina kai Haisam yayi nan take ya fad'i masa dalilin da yasa aka fasa yi masu afuwar,cike da tashin hankali ya saka salati yana tafa hannuwa,a razane, a kuma firgice yace"Wllh sam bansan hakan abun yake ba da ban fara ma zuwa nema masa afuwa ba,ashe rashin hankalin Ashiru har yakai haka,yanzu ace saboda kayan maye zai goyi bayan wannan aika aikar da suka so yi ba don Allah ya takaita Al'amarin ba",lokaci guda idanunsa suka cuccuko tab da kwalla,girgiza kai hajiya tayi cike da takaici ta fara magana"nima dai na Matuk'ar girgiza wllh da jin hakan,sam Ashiru bai yi man wayo ba,yadda bai goyi baya ba tun farko kamata yayi jin wannan Mummunar niyyar tasu yasashi bujire masu ta hanyar tona masu asiri amman ina,saboda tsabar rashin hankali ya za6i ya jefa kanshi cikin matsala ta hanyar goya masu baya duk da yasan mummunan kudirinsu ",
"Ai Hajiya ni yanzu ma wllh na cire hannuna daga lamarinshi daman rashin sani ne,duk hukuncin da ya dace ai mashi ai mashi kawae shi ya ja ma kanshi" yana kai Maganar kwallan daya taru suka zubo mashi sharrr ya sunkuyar da kan k'asa,
Sigh Haisam yayi gently yace"We should thank Allah da bai basu nasarar aikatawa ba gaba daya,lamarin zai fi zuwa da sauki,in sha Allah zanyi ma wanda case din ke ahannunsu Magana za'a duba ayi abunda zai yuwu",
Hajiya ce ta shiga bashi baki tana cewa kar yasa damuwa aranshi yaci gaba da yi mashi Addu'a kawae don ita kadai ce magani inda rabon shiryuwa wataran komae zai zamo tarihi.
Mik'ewa Haisam yayi ya kalli Hajiya"is that all?"ya tambayeta,kallon Malam tanimu dake ta matsar kwalla tayi tace"Malam ko akwae wani abu?"da sauri ya girgiza mata kai"Babu komae hajiya Nagode kwarae,Allah ya k'ara girma",jin hakan yasa Haisam yi mashi sallama ya nufi hanyar fita daga falon don duk a takure yake bazai ta6a samun natsuwa ba har sai yaji saukar ruwa ajikinsa,d'an k'ara tattaunawa sukai kan halin da yara matasa ke jefa rayuwarsu daga bisani Malam Tanimun yayi mata sallama ya tafi.
____________
Washegari da Safe misalin k'arfe 7:30 Fatuu ta fito kopar gida jikinta sanye da kayan makaranta,tsaye tayi gefen kiosk d'in Amadu tana d'an tunanin ko Ya Handsome ya wuce,zuciyarta ce ta raya mata wani abu hakan yasa ta mik'i hanyar zuwa gidan Hajiya,tana karya kwanar Gate aka zuge gate d'in,tsaye tayi tana kallon Motar da ta fito wadda suka je Police Station da itace,adaidai inda take tsaye Motar ta tsaya glass d'in ya fara sauka ahankali tana had'a idanu da Haisam ta sakar mashi