Showing 126001 words to 129000 words out of 212491 words
mai kyau badai jan hankali ba), jin baice mata komae ba yasa ta sake maimaita mashi cewa guda daya fa ya isa,
"Ba kinada Friend ba,ki bata" taji yace ba tare daya kalleta ba, shiru tayi sai yanzu ta gane ashe harda Haulat ya siya, da itama ance ta siyo littattafan harda ita zai saimawa kenan ta ayyana aranta, bayan an d'aukko su yace a bashi bandir d'in littafin rubutu,kwalin biro dana pencil da eraser da sharpener, wata zabura tayi ta zaro ido tana kallonshi shikam baima san tana yi ba, ganin duk an d'aukko mashi yasa a rud'e tace"Ya Handsome wannan ai sunyi yawa sosae duk ina zan kaisu?" banza ya mata ganin hakan yasata ta d'an buga k'afa tana jujjuya kai irin na shagwababbun yara hakan yasa Mutane yin Murmushi harda Alhajin yace "ai abun amfani bai yin yawa, in aka siya da yawa kinga zaki dade baki nema ba, ko baki son ayi mana ciniki ne" tura mashi baki tayi batace komae ba,
bayan duk an d'aukko komae aka zuba masu acikin katuwar leda mai tambarin shagon ya basu card suka cire kudinsu daga haka suka yi sallama da Alhajin har sun juya zasu tafi ya kira Fatuu ya bata kyautar jotter mai cover din frozen had'e da dan bironta in ana rubutu dashi da daddare yana sakin haske kala kala, fuska a tur6une tace ta gode ta nufi hanyar fita ita ala dole anyi mata laifi gashi ma Ya Handsome d'in yaki tanka mata hakan ya kara fusata ta,
Har suka hau hanya tana ta tura baki tana d'an satar kallonshi, duk yana kallonta ta cikin mirror can ya d'an juyo suka had'a ido tayi narai narai da idanu kaman zatai kuka,
"In kana da abu har yayi maka yawa wasu basu dashi suna bukata sai ka basu" taji ya fad'a bayan ya maida idonshi kan hanya,
Kallonshi tayi don bata fahimceshi ba,ci gaba da magana yayi" duk abunda kike ganin yayi yawa ki nemi wanda basu dashi ko kuma suke bukatar k'ari sai ki basu",shiru tayi tana ta kallonshi hakan yasashi sake kallonta ya d'age mata gira yace"Understand? " da sauri ta jinjina mashi kai don yanzu ta fahimci dalilin dayasa ya siya da yawa, yana cikin driving d'in ya yanke shawarar zuwa Electronics Empire (E.E) da ita don wurin suna da park na yara sai kawae ya siya mata ticket ta shiga wurin kafin ya gama workout dinshi, lokacin da suka k'arasa wurin Babban ginin bene ne mai girman gaske, duk wani abu mai amfani da wutar lantarki ko mai samar da wutar zaka samu a wurin bama su kad'ai ba akwae katon shagon wayoyi da abubuwan da suka danganceta wato accessories,akwae internet cafe wato inda mutum zai shiga ya hau yanar gizo a Computer, wannan duk ak'asan benen suke, acan sama kuwa nan Gymnasium d'in yake wato wurin motsa jiki, k'aton wuri ne shaqe da kayan motsa jiki, daga can bangare guda glass ne mai dishi dishi irin wanda ba'a ganin abu sosae akayi amfani dashi wurin fitar da bangaren mata saidai zaka d'an iya hango kawunansu don glass din baida tsawo sosae, bayan gym d'in akwae wani babban parlor koparsa na kallon ta gym d'in an k'awata shi sosae da kujeru na alfarma ga had'addun Flowers da frames masu d'aukar hankali, ba komae ake aciki ba face Electronic games iri iri, bayan su kuma akwae Cold Store wato wurin kayan sanyi mai d'auke da freezers kala kala komai zaka samu nau'in kayan sanyi awurin har kayan itatuwa ana matsewa ayi ma mutum juice in yana bukata, shima dae ya kawatu wurin,
Bayan yayi parking motar a wurin da aka fitar don aje motoci atare suka fito da ita yace ta biyo shi, bangaren da park yake daga can gefen benen ya nufa,ticket ya siya mata kafin ya shigar da ita don an sanshi sosae a wurin, park d'inma ya kawatu sosae, akwae lilo kala kala aciki da abubuwan da zasu dauke ma yaro hankali, lilon da yasan inta hau su baza'a samu matsala ba ya biya mata daga haka yace mata shi zai shiga ciki ta tsaya tayi wasa in ya gama zai dawo sai su tafi, tana jin abunda yace ta turo baki tana yamutsa fuska ganin hakan yasashi cewa "any problem?"
A shagwa6e tace "to ni bazaka je dani wurinku ba sai kace wai in tsaya nan inyi wasa kaman wata k'aramar yarinya" d'an bud'a ido yay jin abunda tace yace "to ke ba Yarinyar bane?"
"Eh mana ni yanzu ba yarinya bace matashiyar budurwa ce" d'an guntun tsoki yayi ya d'an girgiza kai,
"Wurin namu to Matashiyar budurwa bata zuwa sai Babba,in bazaki tsaya anan ba to kizo in maida ki gida kar ki wasting time d'ina" tana jin hakan tace to zata tsaya, dama wurin ya burgeta Sosae kawae rigimar tace saida yaga ta hau lilo sannan ya tafi bayan ya gargadeta kan babu ruwanta da kowa da komae tayi wasanta kawae tace mashi to,bayan ya fita saida ya koma wurin motarshi ya d'auko jakarshi sannan ya nufi cikin wurin.
Sosae Fatuu take jin dadin wurin tana ta nishadi, in ta hau wannan lilon sai ta sauka ta hau wannan har abokai tayi harda yan yara anata yi masu hotuna tare hakan yasa tayi tunanin zuwa ta amso wayar Ya Handsome don itama ayi mata hotunan da wayarsu,lokacin data zo fita hanata akai akace inta fita shikenan sai dae ta sayi wani ticket d'in in zata sake shigowa ita kuma tace wllh ba wani ticket d'in da za'a k'ara siya daga zata je ta amso wayar yayanta ayi mata hoto sai ace sai ta k'ara wani biyan kudi wannan ai salon sata ne ma,k'arshe dae dole aka barta ta fita ba kamar dayake ansan wanda ya kawota, tana shiga entryway din benen ta tsaya a wurin tana yan kalle kalle wai ko zata ga wurin exercise d'in amman bata ga an rubuta a ko ina ba hakan yasa ta tsaida wani mutum daya fito daga cikin internet cafe ta tambayeshi inda ake motsa jiki yace Gymnasium kenan ta hau saman bene zata ga wurin an rubuta asaman kopar shiga tace mashi to ta gode, tana hawa ta kalli kopar bangaren dama taga an rubuta Game Zone asama hakan yasa ta juya hagu ai kuwa sai gashi taga an rubuta yadda Mutumin nan ya fad'i asama da sauri ta nufi babbar kopar shiga wurin saidai tana zuwa mai tsaron wurin ya hanata yace masu register da wurinne kadai ke shiga, turo baki tayi tace to ai wurin yayanta tazo, yace saidai ta kirashi awaya ya fito,rokonshi ta fara yi akan ya barta ta shiga,don daga inda take tana d'an hango cikin wurin ganin yadda ya had'u ne yasa taji ta matsu ta shiga ciki har d'an d'agyel take tana k'ara hango cikin,hakuri ya bata yace haka dokar take ne ba laifinshi bane amman ta fad'i sunan yayan nata sai akira mata shi,tana niyyar fad'i mashi kaman ance ta d'aga kanta ta hango Haisam d'in ya bullo wuyanshi rataye da farin short towel yana goge zufa da alama motsa jiki ya gama ga headphones asaman kanshi sai dae ya cire kan speakers d'in daga jikin kunnanshi,
da sauri tace "yauwa gashi can yayan nawa" juyawa mutumin yayi don ya ganshi daidai Haisam d'in na niyyar shigewa aikuwa fatuu na ganin haka ta kware murya ta kwala mashi kira"YA HANDSOME!" da sauri ya juyo don bai tsammaci jin muryarta ba a wurin,hannu ta d'aga mashi tana d'an tsalle wai don ya ganta,yana hangota ya nufo kopan cikin tafiyarshi ta kasaitacce kuma maji karfi,da d'an mamaki yake kallonta lokacin daya fito inda take ita kuma sai faman washe mashi baki take,
"What are u doing here Zarah?" ya fad'a ya d'an 6ata rai, ganin haka yasa ta marairaice fuska ba tare da ta ce mashi komai ba,
"Ba nace ki tsaya acan ba!" ya k'ara fad'a idonshi a kanta da d'an yanayin bacin rai a fuskarshi,
" To ai ba hakanan nazo ba fa" ta fad'a tana kyakkyafta ido ta d'an yamutsa fuska, jin hakan yasa ya d'an sassauta d'aure fuskar da yayi ya fara tunanin ko wata matsala ce ta kawo ta,
"What's d problem?" ya tambaya,
" Dama wayarka nazo ka bani za'a man hotuna, duk mutane yan uwansu nata dauk'arsu banda ni" ta k'arasa tana tura baki, bud'a ido yayi ya d'an jinjina kai " Wayana zan baki?" kai ta daga alamar eh,
" waye zai maki hoton?"
"Ai akwae mutane awurin zan samu wani sai in bashi yayi man kuma harma nayi abokai fa" ta k'arasa tana Murmushi shima murmushin yayi amman nashi na mamakin maganarta ne,
"Yanzu idan na baki wayana aka gudu dashi fa? baki san ana satan waya sosae ba a irin wurinnan" zaro ido tayi jin bunda yace sai kuma tace" to muje tare kai sai kayi man" d'age mata gira yayi yace "Zarah bazaki barni nayi exercise d'ina ba ko",
Langa6ar da kai tayi tana dariya tace "ai yanzu zaka dawo" gyad'a mata kai yayi kafin yace bari ya d'aukko wayar tana ciki,tana jin hakan tace don Allah ya shiga da ita taga yadda wurin yake,sosae take mashi magiya har saida ya shiga da ita,daga baki bakin kopa ya tsaya da ita bai shige da ita can ciki ba,baki bud'e take bin wurin da kallo don ba k'aramin haduwa yayi ba kaman a kasar waje,ko iya haduwar wurin tasa mutum ya ringa kwakwar zuwa kullum,kayan motsa jiki kala daban dabanne a wurin an jerasu a tsare ga maza nan masu k'irar karfi sanye cikin workout outfits iri daban daban nata yi gwanin burgewa, ga sanyin Ac ya karad'e wurin sai kace ba wurin fidda zufa ba, ga wak'a an kunna sautin kid'an na tashi a sifiku ji kake wani dudum dudum abun dai sai wanda ya gani, nuna mashi d'ayan bangaren tayi tace nan kuma inane yace mata wurin mata ne tana jin hakan tace bari ta d'an leka ta gani, kafin yace wani abu tuni tayi gaba,tana lekawa cikin wurin da sauri tasa hannu ta rufe bakinta, cike da al'ajabi ta dawo wurin Haisam dake tsaye tace "amman dai Ya Handsome wad'anccan matan ba musulmai bane ko suke sanya irin wannan kayan na jikinsu,wai kaga wata,wllh wandon jikinta da kad'an ya wuce girman d'an pant gashi bata da riga sai....." kasa k'arasa abunda zata ce tayi ganin kallon da yake mata,
"Tunda kin shigo kin gani ki koma waje ki jirani ina zuwa" amsa mashi tayi da toh tana juyawa daidai wata mace ta shigo wurin dama kopar daya ce tanan kowa ke shigowa sai ya nufi bangarenshi, tana ganin Haisam ta nufo shi tana murmushi, sanye take da tight long sleeve shirt irin rigar nan mai kama jiki mai dogon hannu purple colour kuma bata rufe mata cikinta ba duka sai bak'in wando pant irin dogon wandon nan roba shima mai kama jiki don har shaidar pant d'inta na can ciki ana gani tasa hular gashi baka har tsakiyar bayanta ta d'aure da ribbom purple, kafafunta sanye da kambas farare ba laifi tayi kyau kuma kayan sun fitar mata da shape dinta sosae amman dai da ganinta ba musulma bace,
"Hi zakee" ta fad'a tana ta faman washe mashi baki,
kasa kasa ya furta"Anah",kallon Fatuu tayi dake ta faman bin ta da ido tana mata kallon k'urulla tunda ta shigo tayi kafin ta kalli haisam tace "is she ur sis?",kai ya d'aga mata alamar eh, tambayar sunanta tayi yace mata Zarah,jinjina kai tayi ta kalli Fatuu tace "kina lafiya?" mamaki ne ya kama Fatun don bata yi tunanin ta iya hausa ba tace "Lafiya lau",
"Gud,tunda kin kawo mana ziyara yakamata kiyi exercise kema" ta fad'a still da fara'a a fuskarta, ita dai Fatuu bata ce mata komae ba, sai ta kalleta sai kuma ta kalli haisam da ta kasa gane yanayin fuskarshi, hannun Fatun ta kamo tace ma Haisam zata je da ita wurinsu don ya samu yayi workout dinshi,
"No Anah, she's going now" ya fad'a fuskarshi ba yabo ba fallasa,
"Don Allah Ya Handsome ka barni in bita ina son nayi nima" Fatuu ta fad'a kaman zatayi kuka, girgiza mata kai yayi yace ba'a yi da irin kayan jikinta,da sauri tace "to ai sai in nad'e rigar sama" wani kallo ya bita dashi jin wani shirme data fad'a,
"Don Allah Ya Handsome ka barni ko irin wannan wanda akeyi mai kaman tafiya ne inje in danyi, wllh dama ina ganin Hajiya Rabi Bawa mai kada na shirin kwana cas'in na hawa irinshi yana burgeni sosae" ta k'arasa tana d'an hade hannu alamar rok'o,
" Tana nufin treadmill kabarta sai in rage mata Speed din k'arshe" Anah ta fad'a,shiru ya danyi kaman bazai ce komai ba da alama nazari yake acikin ranshi, kallon Fatun yayi da ta kafe shi da ido da gani tana Matuk'ar son taje duk tayi kalar tausai, d'an lumshe ido yay yai mata alamar taje, sosae ta saki dariyar farinciki tace mashi ta gode, hannunta Anah d'in ta kama suka nufi bangaren matan bayan Haisam yace mata ta kula da ita sosae don bata ta6a yi ba,
Suna shiga aka fara tambayar Anah wacece ita tace masu sister d'in zakee ce, nan da nan suka shiga d'aga ma Fatuu hannu suna mata welcome don suna yin Haisam, da yawansu sun fada tarkon sun shi sai dae ba fuska, ita kanta Anah din bala'en sonshi take har haisam din ya gane mata don tafi kowa shishshige mashi acikinsu shiyasa bai sakar mata fuska, ita dae Fatuu sai faman binsu take da ido tana ganin yadda suke motsa jikin,Anah da kanta ta tattare ma Fatuu rigar sama dama rigar nada mad'auri ta d'aure mata ita sannan ta cire mata mayafin rigar ta aje shi gefe, dama yar jakarta tunda suka zo ta barta a mota, wurin wani treadmill da bakowa ta nufa da ita, saida ta fara hawa ta nuna mata yadda ake amfani dashi ta tabbatar ta gane sannan tace ta hau bayan ta rage gudunshi karshe yadda zata yi kaman tana tafiya a hankali, sosae Fatuu ke sakin Murmushi tana tayi dad'i duk ya kamata abunda take gani a tv anayi yau gashi itama ta hau tanayi, kallon Anah tayi dake gefenta tace ta d'an k'ara mata gudunshi,ganin tana yi ba wata matsala yasa ta k'ara mata gudun kad'an,tana cikin yi aka kira Anah din waya tace ma Fatuu zata yi waya kar ta ta6a komae ta amsa mata da to, dan matsawa kad'an tayi tai picking call d'in saidai bata ji sosae saboda k'arar kid'an dake tashi a wurin hakan yasa ta nufi can bakin kopar shigowa wurin taci gaba da yin wayar, Fatuu na cikin yi hankalinta ya tafi kan wasu tanata kallon yadda wasu ke yin nasu har bata san ta d'aura hannunta kan malatsin dake d'auke da alamar + ba, wato k'ara gudu saidai taji gudun ya k'aru hakan yasa ta rud'e ta daddafe kan abun ashe tanata k'ara gudunne bata sani ba,lokaci guda ta rud'e ta kidime ta gigice gaba d'aya taga duniyar na juya mata hakan yasa ta saki wata gigitacciyar k'ara ta kwala ma Haisam kira "YA HANDSOME.......!!!" duk tabi ta daddafe kan machine d'in sai falla uban gudu take,k'arar data saki ce ta jawo hankalin Mutane kanta harda masu sanye da earpiece saida suka ji don ba k'aramar k'ara tayi ba, a gigice Anah ta saki wayar ta nufo ciki da gudu sai dai ko kafin ta kai wurin wata wadda ke kusa da fatun tayi kukan kura ta kai ma fatun d'auki cikin zafin nama ta kasheshi, Anah na isowa wurin fatun tayi baya luuu zata fad'i kasa da sauri ta tarbota ta riketa gam adaidai lokacin kuma Haisam ya fado cikin wurin don yana jin k'arar yasan Fatun ce, akasan wurin ta kwantar da ita tanata faman girgizata sai dai ko motsi bata yi ba hakan kuma ba k'aramin tada mata hankali yayi ba har ta fara zubda kwalla,
" Zarah, Can u hear me? Open ur eyes please!" haka Anar keta fad'i tana ci gaba da zubar da kwalla, shidai Haisam tsaye yayi yana kallon Fatuu dake yashe a k'asa bata motsi,tsananin tashin hankali ne yake ciki sai dai ba lalle ka gane hakan ba, yama kasa yin tunanin takamaimai abun yi gashi duk matan sunyi mata rumfa hakan ne yasa bai k'arasa wurin Fatun ba,ko wurin ma don baida zabi ne dole tasa ya shigo saboda maza basa shigowa, a hankali ya matsa kusa dasu yace su d'an matsa duk suka dare ya kasance yana kallon fuskar Fatun, dagowa yay ya tambayi ko akwae ruwa awurin da sauri wasu suka amsa da eh don duk basu yi tunanin ma su samata ruwan ba, bayan wata ta kawo bottle water Haisam d'in ya amsa ya duk'a gaban Fatun ya zuba ruwan ahannunshi dama a bud'e aka bashi robar, yayyafa mata a fuska yayi nan da nan taja wani dogon numfashi don ruwan nada dan sanyi,
"Zarah" haisam din ya kirata, a hankali idonta ya fara motsi,Anah na ganin haka ta ci gaba da kiranta tana cewa ta bud'e idonta, bud'e idon ta fara yi tanayi tana lumshe su,
"Zarah look at me" haisam ya fad'a, a hankali ta d'an ware idon akanshi, kura mashi ido tayi kamar bata sanshi ba can kuma sai ta fashe da kuka tana wani dashe baki dama haka take kukanta kamar yar k'aramar yarinya,
Sai lokacin ya kalli Anah fuska a d'aure yace "how does it happened?" baki na rawa ga kwalla a fuskarta ta kora mashi bayani, tana kaiwa karshe yay ma Fatun wani kallo hakan yasa cikin sheshsheka ta fara mashi bayanin yadda abun ya faru "Wllh Ya Handsome bani na k'ara gudun ba, bansan na d'aura hannuna kan abun k'ara gudun ba, da naga gudun na karuwa shine na rurruke kan abun ashe na k'ara latseshi ban sani ba" shiru yayi don yama rasa abunda zaice,wad'anda suka ji abunda tace sai faman yi mata sannu suke yayin da wad'anda basa jin hausa suka shiga tambayar abunda tace aka fad'a masu suma suka shiga ce mata sorry,
"Zan sha ruwa" ta fad'a da disashshiyar murya, sauran ruwan dake hannunshi ya mik'a mata Anah ta d'an d'ago kanta ta