Showing 144001 words to 147000 words out of 212491 words
aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,
ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
5️⃣7️⃣
.......tun kafin ya k'arasa ta fara girgiza mashi kai da sauri Murya na rawa tace "a'a baka takura man ba zan rink'a yin yadda kace bazan k'ara cewa komae ba wllh",
Shiru yay yana dai ta kallonta dama yafi son tasama ranta yin azumin ta hakane kadae zata daina jin wuyarshi sosae, jin baice komai bane yasa tace "kaji ya Handsome, zan rink'a yi",
Dan d'age kafad'a yay ya furta " Is Ok" daga haka ya fara kokarin wucewa,
" To bakai dariya ba" cakk ya tsaya ya juyo yay mata wani kallo kafin yace " kin raina ni ko!" zare ido tai gudun kada ta kara wani laifin da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a,
"Dama ina wannan ne?" tanata zare ido tace " eh wani lokacin kana yi sai ka juyar da kanka amman kana yin haka..." ta dan jirkice bakinta ita ala dole irin murmushin da yake yi na gefe ta kwaikwaya aikuwa baisan lokacin daya d'aga hannu zai rankwashi kanta ba ta janye da sauri tana dariya, dan Murmushin gefen dai yay ya girgiza kai daga haka ya juya,
"Masallaci zaka?" ta tambaya jin ana kiran sallar isha, kai kawae ya d'aga mata alamar eh ba tare daya juyo ba,
"In zo mu tafi tare?" sai lokacin ya juyo ya kalleta ya saki fuskar sosae,
"Ba kina cin abu ba" da sauri tace "a'a zan barshi inna dawo sai inci" jinjina kai yay ya tambayi ta rufeshi ne tace a'a umarnin taje ta rufe ya bata ta juya da sauri tana ce mashi ya jirata fa, Sauke ajiyar zuciya yay bayan ta shige cikin falon a fili ya furta "Zaraah Rigima", bada jimawa ba ta fito suka tafi.
Bayan angama sallar asham atare suka dawo parlon hajiyan, haisam ya d'an kishingida saman 3 seater ita kuma ta nufi dining ta daukko abincinta da ta rufe, a gefen Haisam d'in ta aje kafin tasa hannu ta cire hijab dinta, ba tare data ji komae ba ta zauna daga ita sai yar shimin jikinta ga gashinta dama atsafe yake yayi wani tum abaya hakan kuma yasa ta k'ara kyau, fuskarta da d'an Murmushi tace mashi su ci, girgiza mata kai yay alamar bazai ci ba, ta langa6ar da kai tana ce mashi don Allah, yasan in ba cin yay ba haka zatai ta faman yi masa magiya shiyasa yace mata yafi son abu mai ruwa, tana jin hakan ta mik'e tace bari taje ta amso mashi abu mai ruwan ta nufi kitchen da sauri batare data jira mi zai k'ara cewa ba. Bada jimawa ba sai gata ta dawo hannunta ruke da bowl d'in Fruit Salad da spoon ta mik'a masa idonsa akan Tv ya dan kalleta ya furta " Thanks" tana ta Murmushi tayi gwaninta ta koma ta zauna, a hankali yake d'ebowa yana kaiwa bakinshi itama tana cin nata suna yi suna kallon tv, ganin dare nayi yasashi cemata tayi sauri ta gama taje gida tace to, bayan ta gama ta mik'e don kai Plate da bowl d'in data yi amfani ya mik'a mata nashi yace ta kai duk da bai k'arasa shanyewa ba, bayan takai kitchen ta aje ta fito ta nufi d'akin Aunty saude tayi mata saida safe kafin ta nufi Bedroom d'in Hajiya don itama tayi mata saida safe lokacin da taje har ta fara bacci saidae baiyi nisa ba, saida safe tayi mata tace taje wurin Saude tace ta zuba mata tuwo ta kaima Dije ta amsa mata da to, bayan ta gaya ma Saude atare suka je kitchen d'in ta zuba mata tuwon acikin bakar leda wanda na semovita ne an nad'e shi a farar leda, bata dade da gama yinshi ba don Hajiya tafi son cin tuwo da Asuba, a yar madaidaiciyar warmer ta zuba mata miyar Alaiyahun mahad'in tuwon suka sake yin sallama ta nufo cikin falon, tana zuwa gabanshi ya mik'e yay gaba tabi bayanshi rungume da warmer d'in, jerawa tai dashi bayan sun fita tana ta faman zuba shi dai sai dai ya jinjina mata kai ko kuma ya bata yar gajerar amsa in ta matsa mashi da tambaya.
Saida suka gaisa da Amadu yayi mashi ansha ruwa lafiya kafin ya wuce da ita har cikin gidan don yana son yi ma gwaggo barka da shan ruwa, a zaure ya tsaya yace mata ta shiga ta fad'i ma gwaggon zai shigo, cike da zumudi ta shiga cikin gidan lokacin gwaggon na kwance a tsakar gida tayi shimfida ga maganin sauro ta kunna agefe don ba wutan Nepa, a gefenta ta aje tuwon tana sanar mata cewa tare da Ya Handsome take yana zaure yace zai shigo, da sauri gwaggon ta tashi zaune tace mata tace ya shigo don a kimtse take, da gudu taje tace ance ya shigo, a tare suka shigo tana gaba yana baya lokacin gwaggo ta fito daga d'akinta ruk'e da darduma ta shimfida mashi tana ce mashi sannu da zuwa, bayan ta gama ta nuna mashi alamar ya zauna saida ya cire takalmanshi agefe kafin ya hau ya zauna ita kuwa Fatuu can gefe inda sauran kayan bud'a baki suke ta nufa ta fara bubbud'awa tana fad'in " Gwaggo Allah yasa dae baki cinye komai ba kin rage man" har saida Haisam ya d'an kalli inda take sai kace ba yanzu ta gama cin abinci ba, shuru gwaggon tayi mata suka shiga gaisawa da Haisam tace bari akawo mashi abun ta6awa, tana k'okarin mik'ewa ya dakatar da ita yace yanzu ya gama cin abu tace to ai ko ruwa yasha nan ma yace ya gode tace to ta kyaleshi yanzu amman dole yazo shan ruwa kafin agama azumin, d'an Murmushi kawae yay kafin ya d'an d'aga kai ya kalli Fatuu dake can gefe sai ta tsakura wannan ta ci wannan acikin ranshi kuwa mamakin yadda take cin abinci yake yanzu ya gano dalilin dayasa ta tashi hankalinta daya sata yin azumi dole, godiya gwaggo ta fara yi mashi game da azumin dayasa Fatuu take yi tace ita sam bata san rashin hankalin da take yi kenan ba da tuni ta tsawatar mata don duk atunaninta in tayi azumi cikakkene, nan ma dae d'an Murmushi yayi ita kuwa fatun tana jin abunda gwaggon ke cewa ta taso tazo inda suke, agefenta ta zauna tace,
"Gwaggo ni ce banda hankali?",
" ina kika ganshi fa" ta bata amsa cikin harshen fulatanci, turo baki tayi da hausa tace "Wllh Allah inada cikakken hankali kuma ga Ya Handsome nan ki tambayeshi kiji don shi yasan inada hankali" jinjina kai gwaggo ta shiga kafin tace " dama ai yanzu yana daga cikin wad'anda zasu fad'i rashin hankalinki Fatuu" jin hakan yasa ta fara kukan shagwa6a tana d'an tuttura kafa, girgiza kai gwaggo tayi tace "yanzu shi wannan abun da kike ai duk cikin hankalinne ko, ke sam ba ranar da zaki girma ne?" turo baki tayi ba tare data ce komai ba idonta akan Haisam daya d'an sadda kai yana kallon k'asan gidan, d'agowa yay ya d'an kalleta suka hada ido ya d'an girgiza kai kafin ya kalli gwaggo yay mata sallama yana kokarin mik'ewa, atare suka rako shi gwaggon na k'ara yi mashi godiyar dawainiyar da yake masu, suna zuwa bakin zaure ta koma ciki ita kuma Fatuu ta rako shi har waje dama bata cire hijab d'in jikinta ba, suna fitowa kan hanya yace ta koma tayi tsaye bakin hanyar tace sai ya tafi zata koma, har ya d'an wuce shagon Amadu ta kwala mashi kira,
"Ya Handsome",tsayawa yay ya juyo ya kalleta,
" ai gobe dae ba Azumi ko?" shiru ya danyi da farko sai kuma ya d'aga mata kai alamar eh, kawae sai gani yay ta fara yin rawa, bud'a ido yay alamar mamaki aikuwa tana ganin hakan dayake akwae haske ta ruga tana ta dariya, girgiza kai kawae yay daga haka ya nufi gida.
Washe gari da bata yin azumi sam bata yarda taji yunwa ba,duk wani abun ci data gani sai taci, tunda safe kafin ta tafi makaranta ta cinye duk abunda suka rage haka bayan antaso data je gidan Hajiya bunu bunu taci wani abu wai daga yau sai bayan kwana biyu Saude nata mata dariya, da yamma data koma gida ma tana taya Gwaggo aiki tana cin abubuwan da aka fara na bud'a baki ba tare da ta 6oye ba kamar yadda take yi da don yanzu gwaggon tasan yau ba ranar yin azumi bace har gwaggon nace mata wannan kafin asha ruwan ma ai saita cinye komae sai da tayi da gaske ta hanata. Haka taci gaba da yin azumin duk in tayi biyu sai ta huta kwana d'aya kuma bata k'ara yima Haisam korafi game da azumin ba gudun kada yay fushi da ita sai dae in yana bata wuya tai ma su gwaggo ko Saude korafin, ana saura kwana takwas agama azumi bayan gama sallar asham yace mata ta shirya gobe karfe 10 na safe zai kaita inda za'a gyara mata kai, lokacin zai rakata gida kaman yadda kusan kullum yake rakata don yanzu da angama sallar saita koma part d'in hajiya daga baya ya rakota sa6anin da tare da Haulat suke tafiya gida da angama sallar yanzu kuwa tun a Masallacin suke rabuwa suyi ma juna saida safe, cike da murna ta amsa mashi da to sai kuma ta tuna goben ranar yin azumi ce hakan yasa ta rokeshi akan ya barta ba sai tayi gobe ba tunda fita zasuyi, da farko k'in yarda yay ganin yadda ta marairace mashi ne kuma ba wuri daya yake son suje ba yasashi ce mata in ta yarda zata rama shi next tayi ukku sai ya amince, cike da zumud'i tace to ta yarda ahaka suka rabu,
**** **** *****
Washegari tunda sassafe ta tashi don fitar da zasuyi na ranta shiyasa da tayi sallar Asuba ta kasa komawa, kuma dama tunda ya gaya mata tana isa gida ta sanar ma gwaggo tace karta tada ita sahur don bazata yi azumi ba, tana tashi shaf shaf ta share tsakar gidan tayi wanke wanke don indae bata azumi ita ke yinsu in tana yi kuma gwaggon ke kama mata wani abun kaman wanke wanke sai suyi tare in tana gida wani lokacin ma ita kad'ai ke yi ita Fatun sai ta share duka gidan don tuni anyi masu hutun Islamiyya, tana gamawa ta fad'a bandaki tayo wanka bayan ta gama ta nufi d'aki don ta shirya, Misalin k'arfe 9:30 saura ta gama shiryawa cikin jar jallabiyarta harda su makeup ga jan janbaki tasa abakinta tayi kyau sosae ba kamar yanzu da skin d'inta ta canza saboda mayukan da take amfani dasu sun fito da ainihin kalarta don bana bleaching bane, koda ta lek'a yi ma gwaggo sallama isketa tayi tana bacci hakan yasa ta fito ta tafi don tasan ta sanar da ita tun jiya, lokacin da ta fito wajen wayam ba kowa duk anata baccin safe ko kawu Amadu ma bai tashi ba dama yanzu bai bud'e shago da wuri wani lokacin ma yan kawo kud'in kankara ne ke tada shi dole, ta Gate tabi don k'aramar kopar arufe take har Officer na zolayarta cewa da ganin wannan kwalliyar bata azumi tace mashi tana yi daga haka tai wucewarta don a k'agare take da su tafi, da sallama ta shiga cikin falon nashi don abud'e ta iske kopar sai dai koda ta shiga bai acikin falon hakan yasa ta zauna don ta jirashi tunda tasan lokacin daya dibar masu zasu fitan bai idasa ba kuma koda wasa bata ta6a shiga Bedroom dinshi ba don bata ma ga fuskar yin hakan ba a wurinshi, shiru shiru har bayan wani lokaci bai fito ba hakan yasa ta gaji da zaman ta d'an kwanta a d'ayan 6arin kujerar, nan da nan sanyin Ac ya bugeta ta fara d'an gyangyadi dama jiya bata samu isasshen bacci ba saboda zumudin yau tayi, jin sanyin Ac d'in yayi mata yawa don har kafafunta sun fara rawa yasa ta mik'e ta daukko throw pillows d'in dake akan kujeran ta rufe kafafunta dasu ta linke hannuwanta akirji nan da nan ba tare da ta ankare ba bacci mai karfi yai awon gaba da ita,
Karfe goma daidai ya fito cikin falon jikinshi sanye da rantsatstsen Voile Coffee Brown haka takalmanshi da agogon hannunshi ma duk Coffee ne, Ma sha Allah shine abunda na fad'a yayin da yake nufo cikin falon da tafiyarshi ta kasaita, tsaye yay d'an nesa da ita yana kallon fuskarta fuskarshi d'auke da d'an Murmushi don ganinta da yay yasashi k'ara fahimtar yadda take son agyara mata gashin, kai idonshi yay kan kafafunta da ta jera throw pillows lokaci guda ya fadada Murmushinshi had'i da d'an girgiza kai, juyawa yay ya koma Bedroom dinshi, bada jimawa ba ya fito hannunshi d'auke da lallausan farin Duvet, saida ya cire pillows d'in sannan ya lullu6a mata shi har zuwa cikinta daga haka ya juya ya nufi dakin lab d'inshi ya fito hannunshi ruke da wata bak'ar laptop ya zauna a inda ya saba zama ya fara operating dinta bayan ya daurata kan c-table,
Bacci sosae Fatuu take yi, duk in tayi motsi sai ya d'aga idonshi ya kalleta sai kuma taci gaba, saida ta d'auki kusan awa kafin ta fara motsi sosae, a hankali ta fara bud'e idanunta kafin ta idasa ware su sosae, kuri tayi tana kallon Haisam dake ta daddana computer da mamaki tace "Ya Handsome" gira ya d'age mata kafin ya d'aga ido ya kalleta, mik'ewa tayi zaune idonta akan duvet d'in dake jikinta tace "Ya Handsome kai kasa man wannan abun?" kai ya daga mata alamar eh sai kuma yace " kina jin sanyi ne",
" to munje wurin gyaran gashin ne?",
shiru yay jin wata tambaya mara kan gado, can kuma tace "Wai ashe bacci nayi, to mun fasa zuwa ne" jinjina mata kai yayi ba tare daya kalleta ba yace "Yea, time d'in ya wuce yanzu ina abu ne",
kaman zatayi kuka tace "to ai ba laifina bane tunda da sassafe nazo kaine baka fito ba ka ganni ba har bacci ya kwashe ni",
" Yanzu laifi nane kenan tunda ni nace kiyi bacci ko?" ya d'ago ya kalleta tai narai narai da idanu har kwalla ta fara taruwa,
" Saboda ba sayar da su ake ba shiyasa da kin so sai ki zubosu without any strong reason, baki tsoron su k'are?" yay Maganar idonshi akanta aikuwa kaman tana jira kawae sai tasa mashi kuka harda shashsheka, bud'a ido yay alamar mamaki sai kuma ya mik'e ya d'auki laptop d'in ya maida ita dakin daya daukkota bayan ya fito wurin tv ya nufa ya daukko tissue box yazo gabanta, yagowa yay ya mik'a mata bayan ya kira sunanta ta d'ago idanunta sun d'an yi ja gashi duk ta 6ata kwalliyarta, fuskarshi a sake cikin cool voice dinshi yace "Wipe ur tears, ina maki wasa ne ai yanzu zamu tafi dama am just waiting for u to wake up" hannu ta mik'a ta amshi tissue ta fara goge idonta tanayi tana d'an kallonshi ganin ya kafeta da ido,
" Zan sha ruwa" ta fad'a a sanyaye,
" Owk " ya furta kafin ya aje box d'in kan c-table ya juya ya nufi inda fridge yake, bottle water da lemu fanta ya d'aukko ya dawo ya mik'a mata ta amsa tace ta gode, bud'e ruwan tayi ta d'an sha har zata aje yace su tafi dashi ko zata bukata ta amsa da to, daga haka yace zasu iya tafiya ta mik'e tabi bayanshi, yana gaba tana biye dashi suka fito harabar gidan, bata yi tunanin zuwa gaida hajiya ba don tasan ba lalle inta tashi ba, bayan sun hau mota sun fitane ya kira wata mai suna Nana a waya ya tambayeta wurin salon mai kyau tace zata turo mashi Address d'in mai yi masu yay rejecting call d'in bayan yace mata thanks, ba wani 6ata lokaci ta turo mashi ya duba dama bai aje wayar ba tana hannunshi, aje wayar yay ya dan juya ya kalli Fatuu da tunda suka fito batai magana ba ta kwantar da kanta tana ta kallon hanya ta glass d'in kofa, maida idonshi yay kan hanya yaci gaba da driving bayan wani d'an lokaci suka k'araso wurin wanda bene ne dauke da jerin manyan shaguna a sama da kasa, acan gefen benen ya hango shagon da aka turo mashi mai dauke da sunan MAMAN ABDUL BEAUTY SALOON, hayewa yayi sama ya parker motar acan gaban shagon tun kafin ma ya kashe sai ga wata mata mai kiba tana sanye da doguwar rigar atamfa mai gajeran hannu kanta daure da kallabi ta nufo Motar da sauri fuskarta dauke da fara'a da gani an sanar mata game da zuwan su