Showing 60001 words to 63000 words out of 212491 words
wani lokacin dole ai uzuri yasa ka makara kaman yadda wani lokacin kaima ba'a zuwa a amshe ka da wuri saboda wani dalilin haka dai ake ta fama" yar dariya ladidi tayi"hakane kam rayuwan gaba daya sai da uzuri,ku kunma ji dadi kunata aikin ku wllh kai bawa kullum sai fama da wuta kake" gwaggo tace"to ya za'ai kowa da hanyar da Allah ya tsaga masa cin abincinsa,Allah dai ya kara rufa mana asiri duniya da lahira" ladidi ta amsa da Amin yayin da suka nufi hanyar zaure a tare,
Da sauri fatuu ta koma gefen d'an gadonta ta zauna daga inda ta la6e tana sauraron hirarsu gwaggo,hannu tasa ta ruke ha6arta a fili tace"kai,wai yaya handsome har yasa an kama su gaye kenan" kwafa tayi ta sake cewa"ai maganinsu kenan mugaye kawai,kilan ma su za'a kai gidan yarin ba ni ba,wayyo har naji tausayin Gaye wllh shi baiso ba amman abokanansa sun ja masa" idasa fadawa tayi saman gadon ta kwanta tana kallon sama ta ci gaba"yakamata inje in gaida Yaya handsome tunda saboda ni yaji ciwo,ko yama akai yasan naje kangon nan,kilan yagan sanda na juya nabi lungun ne,ashe dai haka yake da mugun kirki ni wllh farkon dana fara ganinshi nayi tunanin baida mutunci ba kaman daya falla mun marin nan" kyalkyacewa tayi da dariyar farinciki kafin tace"ai da har naji tsoron ko yana can bai iya tafiya ne shiyasa ban ganshi da safe ba,ashe har wurin yan Sanda yaje ya kai kara,ohooo shiyasa yace kar na fadi ma kowa abunda ya faru nagano dalilin...,Oh da ansan nice da sai aita nuna ni wasu ma su ki yarda ba ai man fyaden ba,gwara ma da ba wanda yasan ni ce"ta k'arasa maganar tana ta faman watsa hannuwa kaman da wani take maganan,
"Fatuu" gwaggo da ta dawo daga rakiyar da tayi ma ladidi ta kwala mata kira,da sauri ta saukko daga gadon ta nufi kopa tana amsa kiran,d'aga labulan tayi ganin gwaggon a bakin kopan yasa ta tsaya tace"gani" kallon kanta gwaggon tayi wanda ke bude ba dankwali ta d'an girgiza kai tace"wai ke don Allah fatuu sai yaushe ne zaki hankali,kisan abunda ya dace ne iye?yanzu wannan kan naki tun yaushe yake a tsefe ne,kudi fa kawai zaki dauka kije a kitse maki amman abun duniya ya gagara so kike sai na kama hannunki naje na kaiki ne?" turo baki fatuu tayi"Allah gwaggo bazaki gane ba fa,wllh balaraban nan mugun zafin hannu gare ta,kitson da tayi man na karshe fa har dan guntun fitsari sai da nayi fa" ta6e baki gwaggo tayi tace"wannan kuma ai kin saba in dai sakin fitsari ne,kullum mutum bazai yi abu lokacin da yake jin sa ba sai ya matse shi ba dole ya zubo ba,ke dai kika sani,gashin ma naki bai da zuciya ne yadda baki gyara shin nan kamata yayi ace zuwa yanzu duk ya zube ya bar ki da kwaikwaidon kai",
Langa6ar da kai tayi tana turo baki"kai gwaggo harda mugun fata,to ke ki mun ko kalaba ko kuma ki man na fulani da kike man" gwaggo tace"Uhmm sai ki ta jira na ai har in samu lokaci,nasan hakan ba matsala bane a wurinki,kinga ni zan wuce wurin aiki nama rigada na makara,ga abinci nan a kicin in Amadu ya dawo ki dau nasa ki kai masa,sannan kema in kin ci kiyi wanka sai ki share tsakan gidan da kuma kicin din don duk ya 6aci ban samu na gyara ba" daga haka ta juya can kuma sai ta sake juyowa tace"fatuu na roke ki don Allah ki zauna agida kar kije ko ina da lokacin islamiyya yayi ki tafi ana tasowa kuma ki dawo gida kinji?,
d'an sosa kai tayi"to,amman zan dan je gidan hajia in nagama abunda kika sani kafin lokacin islamiyyar yayi" wani kallo gwaggon tayi mata kafin tace"wai mi kike yi ne a gidan hajiyar ba jiya kinje ba kuma ma da dare,to mi kuma zaki je yi yanzu?anya fatuu ba wata rigimar kike shirin jawo man ba kike fakewa da zuwa gidan hajia?" da sauri ta girgiza kai tace"Allah ni ba wani rigimar da zan jawo maki,yaushe rabon ma da kiji an kawo karata,kawai banson in zauna ni daya shiru tunda kinga shi kawu Amadu da ya dawo ya dan huta shago zaije ya bude" ta6e baki gwaggon tayi"ai jin shirun ba'a kawo k'arar taki ba kwana biyu yasa ni nike zullumi don in kikai kwance kwancen nan to ba k'araman rigima za'a jawo man ba",
kyalkyacewa da daria fatuu tayi tace"to ki kwantar da hankalinki kakus ba wani rigiman da zan jawo na bari na shiryu ba ruwana yanzu" gwaggo tace"da nafi kowa farin ciki,sai dai nasan a iya baki ne don nasaba jin hakan" daga haka ta juya ta nufi hanyar fita fatuu ta d'an daga murya"inje ko? batare da gwaggo ta juyo ba tace"ai sai kita zuwa ko na hana ma nasan sai kinje" fatuu da ke ta dariya da karfi tace"si to a warti kakus" hannu gwaggon ta d'ago mata lokacin kuma ta idasa ficewa daga gidan,fatuu na ganin ta fice ta koma d'aki da sauri don daukko gyalenta dan gado ta tafi gidan hajiyar Sanata.
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching love story._
_*BY ZAINAB LALUH📲*_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*32⃣*
Fitowa tayi da sauri tana yafa gyalen saman uniform din jikinta,a daidai zaure suka had'e da kawu Amadu ya dawo daga Makaranta shima,wani kallo yayi mata yace"yawo ko?" Da sauri ta girgiza mashi kai"a'a gidan hajiya zani kuma na tambayi gwaggo ma yanzun nan ta fita" gyada kai yayi yace"eh na hadu da ita,mashin d'in da ya kawo ni ma ta hau,yanzun je ki kawo man abinci na sai kita tafiya" to tace ta juya don daukko masa abincin,
Yana zaune agefen yar katifarsa yana cire safar kafarsa ta shigo,aje masa yar kular abincin da cokali asamanta tayi a gabansa tace"gashi nan" tana k'okarin juyawa yace"ruwa fa?"wani kallo tayi masa tana turo baki "kai kawu wai ruwan ma baka iya zuwa kasha in ka gama don kawai ka wahalar dani" harararta yayi cikin d'aure fuska yace"Imi fijirma(ina wasa dake)!zaki kawo man ruwan ko sai na tattaka ki anan,kin iya jin wahalan asa ki yin abu amman baki jin wahalan yawo"tana ta faman turo baki ta koma ta d'ebo masa ruwan ta kawo masa,yar harara ya watsa mata kafin yasa cokali ya fara cin abincin,juyawa tayi zata fita ta hango kwali d'auke da su biscuits dasu sweet aje a jikin bango, d'an juyowa tayi ta saci kallonsa taga hankalinsa na kan abincin da sauri tasa hannu ta rarumo sweet jin karar ta6a kwalin yasa shi dagowa da sauri yace'Fatuu...."da gudu ta fice daga gidan.
________________
Haisam zaune a parlornsa hannunsa ruke da wayarsa yana karatun Al'qurani a hankali ta cikin app d'in Vmuslim,tun bayan da suka dawo shi da Officer direct part din hajiya ya nufa don yin breakfast yasha magungunan da aka bashi,anan ne taga raunin daya ji a kafan,ba k'aramin tashi hankalinta yayi ba taita faman tambayan shi yadda ya samu rauni bacin jiya lafiya lou suka rabu,bai 6oye mata ba ya fad'i mata kwalba ce ya taka amman a part d'in sa yace mata bai fad'i mata ainihin yadda akai ya samu raunin ba,aikam ba k'aramin jimami ta shiga ba mamaki ya cikata na yadda akai akasamu kwalba apart dinsa har ya taka don tasan ko lemun kwalba basu amfani dashi haka dai taita faman jajanta al'amarin,da kanta ta had'o masa breakfast har yunkurin bashi a baki tayi ya hanata yana ta faman dariya,tsare shi tayi sai da ta tabbatar yaci sosae sannan ta 6allo masa magungunan yasha,ci gaba su kai da hira har ya tambayeta miyasa bata je aiki ba,ta sanar mashi cewa tana aikin wani project ne sai ta gama gaba daya sannan zata je,bayan wani lokaci ne hajiyan tayi bak'i hakan yasa haisam din baro part din hajiar,har cewa tayi yaje dakinta ya kwanta yace mata baijin bacci zai koma part d'insa.
A hankali fatuu ta kama handle din kopan ta tura ta d'an leka ciki,hango shi tayi zaune yaba kopan baya ta yadda duka kafafunsa na asaman kujeran ya mik'ar dasu,k'ira'ar karatun da yake na tashi a hankali,
Shiga tayi da yar sallama a bakinta gabanta na d'an faduwa ta nufi can gefen c-table ta durkushe,bai kalleta ba amman yaji shigowar mutum,cigaba yayi da karatunsa ita kuma tana ta kallonshi tana wasa da yatsun hannunta,sai da yakai karshen surar da yake karantawa ya aje wayan a gefensa,tsawon wasu seconds ya d'auka kafin ya juya ya kalleta fuskar nan ad'aure tamkar bai ta6a dariya ba,lokaci guda fatuu tasha jinin jikinta ta shiga motsa baki gabanta na bugawa da karfi da karfi,tana son ta bud'a baki ta gaishe shi amman sam ta kasa saboda ganin yanayin shi,yadau d'an lokaci yana kallonta
"Dama ke yar iskace" ya jefo ma fatuu tambaya,a gigice ta zaro idanu tana kallonshi jin abunda yace,girgiza kai ta fara yi a tsananin rud'e tace"A..a...a'a wllh ni ba yar iska bace,na rantse da Allah ban ta6a iskanci da kowa ba kaji na rantse maka...." ta6e baki ta fara yi nan da nan hawaye suka fara zubowa daga idanunta,
Juyar da kanshi yayi gefe sam ba abunda yaso fada ba kenan, it was just an unfortunate slip of the tongue,shi kanshi yaji nauyin abunda yace d'in,kuka sosae take yi tasa hannu tana murzar idanunta sai faman rantse rantse take na ita ba yar iska bace,
"Tashi ki tafi" haisam daya juyo yana kallonta yace har lokacin fuskarshi a d'aure,kallonshi tayi tana niyyar magana ya daka mata tsawa"just leave!" da sauri jiki na kerma ta yunkura zata mike gocewa tayi ta bigi c-table d'in dake gefenta sosai ta bugu har sai da haisam ya d'an yamutsa baki,kopar fita ta nufa tanayi tana waiwayenshi tana kuka a tunaninta ko zaice ta tsaya amman bai ko juyo ba balle ya kalleta har ta fita, bakin kopar ta tsaya kaman bazata tafi ba sai shesshekar kuka take yi,
A hankali ta fara tattaka stairs din balcony"yanzu shikenan kin 6ata masa rai zai fasa yafewar da yayi hajiya da gwaggo duk zasu sani kuma sannan gwaggon zata san ke ce wadda su Gaye suka kusa yima fyade a kangon su....."zuciyarta ce take raya mata hakan,cikin tsananin rudewa ta juya ta koma jikin kopan kama handle d'in tayi ta dan tura ta kad'an ba tare da ta lek'a kanta ba ta fara magana"Don girman Allah yaya handsome kayi hakuri don darajar Annabi,in kana kaunar maman ka hajiya,wallahi tallahi ni ba yar iska bace kowa ya sani a unguwar nan,wllh ko Bello na gidansu Umar makwabcin mu kwanaki da ya rike man hannu sai da na daddage na falle shi da mari kuma ko haulatu zaka tambaya zata fad'i ma hakan,ko gwaggota ma tasan anyi hakan don har cewa tayi na kyauta dana mare shin" dakatawa tayi taci gaba da kuka tana shessheka,
Duk maganganun nan da take haisam din na jin ta,don tun bayan da ta fita yake zaune still,bai motsa ba ko wayarsa ma bai d'auka ba,gaba daya tun bayan da fatuu tazo wurin shi he felt distubed,shi mutum ne da baison hayaniya,ji yake gaba daya ya takura,
Tsam ya mike ya nufi hanyar fita,fatuu najin an kama kopan za'a bude taja baya da sauri sai faman zare ido take,tsaye yayi a bakin kopan bayan ya bud'e yana kallonta ya goya hannayenshi a kirji,itama shi take kallo da kumburarrun idanu fuskarta tayi jage jage da hawaye ganin yana ta kallonta baice komai ba kuma har lokacin fuskarshi a tamke take yasa ta sunnar da kai k'asa had'i da sa gefen gyalenta tana goge hawayen fuskarta hakan kuma yasa gyalen sa6ulowa daga saman kanta,jin shiru bai yi magana ba yasa ta d'an saci kallonshi ta kasan ido suka hada idanu hakan yasa ta d'ago ta marairece fuska ta fara motsa baki kaman zata yi magana amman ta kasa cewa komae saboda kafetan da yayi da ido,
Sauke Ajiyar zuciya yayi calmly yace"ki tafi kawae,in don laifin da kika yi man ne na fasa glass I hv forgiven u already,so karki damu bazan tada maganan ba,kije ki ci gaba da yin rayuwan ki the way you want" yana gama maganar ya juya zai koma cikin parlorn da sauri tace"to don Allah kar kayi fushi dani..."juyowa yayi ya d'an kalleta,ta langa6ar da kai taci gaba"Don Allah,wallahi ni ba yar iska bace,kawai zuwa nayi in fad'i ma gaye ka yafe man shida yace bazaka ta6a yafewa ba shine..."bata k'arasa ba ya juya ya shige,
Matsowa tayi jikin kopan wadda bata idasa rufewa ba,ta kama handle din ta ci gaba"Don Allah kayi hakuri kar kayi fushi dani,wllh ko gwaggota da haulat in naga sun yi fushi da ni banjin dad'i" Haisam dake a zaune tun bayan da ya shige yana jinta sai faman ta6a kopan take tana yin yar k'ara,hannun daman shi yasa ya dafe forehead d'insa,wannan shi ake kira da karfen kafa😂.
A hankali ya zame hannun daga kan goshin ya juya ya kalli kopan"Come in" ya fad'a da wata irin dishasshiyar murya,turo kanta tayi jin kaman yayi magana sai dai batasan miya ce ba"kira na kayi"ta tambaya ta inda ta sak'o kan,a hankali ya cira kai ya kalleta,yadda tayi yaso ya bashi dariya amman ya share ya d'an daga kanshi alamar eh,aikuwa da sauri ta idasa shigowa ta nufi inda ta tashi dazun ta durkushe gaba daya gyalen ma ya dawo a hannu daga ita sai Uniform riga da wando ga gashinta yayi wani tumm a d'aure,
Shiru sukai na wani lokaci shi yanata kallonta ita kuma sai faman murzar idanu take da gyalen hannunta,a hankali ta saci kallonsa ganin ita yake kallo yasa ta dakata da abunda take yi itama taci gaba da kallonshi tana kyakkyafta idanu hadi da motsa baki, hannu yasa yana shafa beard dinsa cikin cool voice yace"ga ki kaman zaki wayo ashe baki da shi" kya6e fuska tayi tace"wllh ina da wayo fa" d'an ta6e baki ya yi"da kina dashi ai bazaki je can wurin ba at dat time,da banje in a right time ba baki san mi zai faru da ke ba....",
"Nasani,fyade zasu yi man"ta fad'a tana sussunar da kai,still yayi sai dai sam baiyi mamakin jin haka daga bakinta ba,don yarinyar da bata kaita bama yanzu zata san kalmar fyade koda bata san ainihin abunda yake nufi ba saboda yadda ake fadakarwa game da aikatashi a kafafen sadarwa irinsu tv,radio da sauransu,gashi a jiya tace yima yarinya k'arama kamarta aure is a child abuse,yana ganin tasan miye ne auren shiyasa har ta fad'i hakan don inba haka ba ai a garinsu ya tabbatar ana ma yaran da basu kaita bama aure,
ci gaba da magana tayi"ai shima a makaranta anyi mana bayani akanshi kuma an fad'a mana abubuwan da zamu yi don mu kare kanmu,ance in wani da bamu sani ba ya kira mu yace zai aike mu wani gida da bamu sani ba to kar muje,ko ya kira mu a wani wuri kaman kango yace zai bamu wani abu nan ma kar muje,ko kuma mu ga wani yana ta6a mana jiki to mu hana shi in bai bari ba muje gida mu fad'i ma iyayenmu,shiyasa da Bello na gidansu umar ya kama man hannu na felle shi da mari" ta kai maganar tana gwada yadda ta mare shin har sai da Haisam ya dan juya fuska,
Juyowa yayi yace"to ai ba gwaninta kikai ba tunda jiya da kafafunki ki ka kai kanki inda za'a cutar da ke" da sauri tace"ni fa wllh kawai zuwa nayi in fad'a ma gaye cewa ka yafe d'in,shida yace wai bazaka ta6a yafewa ba,shine fa abokansa suka ce wai k'arya nike hada cewa wai kai kanin babanane ko mamata da zaka yafe man hakanan wai zuwa nayi ka da....." da sauri ya d'aga mata hannu"shikenan,since they've been arrested duk wannan bayanin zasuyi acan ne ba sai kin maimaita man ba",
Jinjina kai tayi tace"za kau suyi bayani mai dalili,duk sai sun yabawa aya zakinta tunda su yan iska ne,amman kasan mi yaya handsome?"Girgiza mata kai yayi alamar a'a tace"wllh shi fa Gaye ba ruwanshi baiso ayi man abun ba,har cema su yayi su kyale ni inyi tafiyata don Allah,don abunda zasu yi man babban laifine hukuncin sa d'aurin rai da rai,amman wannan banzan abokin nashi gago ne ko gogo oho ni ban iya sunan ba,ya ki ya kyale ni wai suma sai na basu abunda na baka,har rantsuwa nayi masu ba abunda kai man don Allah ka yafe man kace kawae in daina rashin ji,amman katoton banzan yaki yarda..."d'an dakatawa tayi tana maida numfashi kafin taci gaba"harfa cewa yayi wai rabon da ya samu irin wannan daman tun akan wata ko hajara,kenan kaga dama sun saba yima yaran mutane fyade ko?"
Haisam da yayi still yana saurarenta tamkar ya kunna radio,ya dan ta6e baki kafin yace"whatever dai zasu yi bayani acan,ke ma in kika je sai kiyi masu duk wannan bayanin" wata zabura tayi ta kwalalo idanu"ni kuma!to ni mi zanje yi police station?nifa ba laifin da nayi Allah,kuma abunda yasa naje wurin gayen da dare saboda banyi tunanin zai cutar dani ba saboda shi wllh ko hannuna bai ta6a rukewa ba,kawae dai in ya ganni yana tsokana na yana ce man wai Aljana",
D'an kankance idanu yayi yace"aikam dole zaki je can...." tun kafin ya k'arasa ta fara kokarin rage tsawonta har idanunta sun kawo ruwa alamar zata fara kuka,d'agowa yayi yana mata nuni da hannu yace"No,yi zamanki zaki je ne don akwae bayanai da suke so daga gare ki,yadda incident d'in ya faru,dat's all" komawa tayi ta zauna had'i da yin dan murmushi lokacin kuma kwallan da ta taru ta zubo sharrr,haisam dake kallonta ya dan girgiza kai calmly yace "kuka bai maki wuya ko" tsayawa tayi da goge kwallan da take da gyalen tace"wllh hankalina ne ya tashi,nayi zaton nima kulle ni za'ai,amman kaine zaka kai ni can din?" d'aga mata kai yayi alamar eh,tace"A motar mai fasassan gilashin?" banza ya mata yana mata kallo mai kaman harara,da