Showing 30001 words to 33000 words out of 212491 words

Chapter 11 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

958

fara fadin haka ba,kuma ko kun 6ata da kanku dai kuke shiryawa don keda haulat sai Allah.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

*Mallakin*
⬇️
*ZAINAB LALUH*🌹
*(Oummu imam)*


Free Page1️⃣8️⃣

Gwaggo ce ta fito daga cikin kitchen lokacin ba'a dade da gama sallar isha ba,hannunta d'auke da d'an kwanon silver madaidaici rufe da murfinsa asaman shi kuma bakar leda ce dauke da wani abu an kulle, tsayawa tayi ta fara kwala ma fatuu kira "Fatuu,fatuu,Worei mi lilma", leko kanta tayi ta jikin labule tace" ina zaki aike ni?" hajia zaki kaima tuwon nan nasanta da son tuwon dawa" da sauri ta fito jin za'a aiketa wurin Hajiyar Sanata,hannunta rik'e da k'aramin bak'in gyale ta fara k'okarin cire hijab d'in islamiyya dake jikinta tana fad'in "dama kwana biyu banje ba wllh...."

Gwaggo tace"to miye na cire hijab d'in kuma,kibarta mana" turo baki tayi tace"ni nafi son in sa gyalen kinga na fi shan iska ma",
gwaggo tace "A daren nan zaki sa wannan figaggen gyalen da iyakarsa kafad'a,to bar aiken ni bari in mik'a mata da kaina..." da sauri tace "a'a to yi hakuri nabar hijab din" tayi maganar tana d'aga hannu alamar ban hakuri,
gwaggo ta mik'a mata kwanon tace "kiyi maza ki kai mata kidawo,sauran kuma ki tsaya shiririta sai tsakan dare ki dawo" dariya tayi ta amshi kwanon ta rungume tana fad'in yanzun nan zan dawo kakus, Gwaggo tace "to ki d'aura akai mana salon miyan ta zubo ta 6ata maki hijab din",
fatuu tace "bazata zubo ba zan kula" abunda gwaggo bata lura ba fatun ta 6oye gyalen da ta hanata sawa a kasan hammata shiyasa tak'i daura kwanon aka don kar ya fad'o ta gani,

A zaure ta aje kwanon k'asa ta cire hijab din ta sagale ta jikin windon d'akin kawu Amadu tasa gyalen kana ta nufi gidan Hajia.

A daidai gate ta tsaya wurin Officer dake zaune shi kad'ai tace"Sannu da gadin gate Officer" ya d'ago ya kalleta yana daria,don maganar tata ta bashi dariya yace "Yauwa kema sannunki yar fillo" tace "kai kad'ai a zaune ina d'ayan Officern yake? Rausayar da kai yayi yace ya tafi yin wani uzuri ne" ta ta6e baki tace "ba wani uzuri wayo yayi maka yanzun haka zance ya tafi wurin Budurwarshi ya barka kai d'aya kana ta aikin tsaro,wllh kada ka yarda ya maida kai sakarai kaima ka rama atoh" jinjina kai yayi yana d'an murmushi jin abunda tace,sam baiji komae ba don yasan ta sam ba datsar k'umba gareta ba duk abunda yazo bakinta fad'i take yace"to yar fillo ya zanyi in rama d'in? turo baki tayi tace "nifa ka daina ceman yar fillo" kyalkyacewa da dariya yayi don dama yasan bata son sunan yace "to ke ba yar fillon bace? tace "to nidai banso ka kira ni da Fatuu na kawae" yace "to shikenan hajia fatuu na bari,sai a fad'i man yadda zan rink'a ramawa nima" tace "yo kaima budurwar zakayi sai ka rink'a tafiya tadi....." katseta yayi yace "to ni ina zan samu budurwa nida kullum ina nan zaune ina tsaron gate" tace "Yo yadda yayi shima ya samu zaka yi" ta juya tana k'okarin shiga gidan yace "to ko ke kizama budurwar tawa kawai ma...",
A fusace ta juyo bayan ta tsaya ta bishi da wani kallo,shi kam sai daria yake,tace" God forbid! ni bazan zama budurwar kowa ba yanzu sai na zama likita,kuma lokacin ni nafi karfin mai gadin gate,tana gama fad'in hakan ta shige sai kuma ta sake lek'owa ta cikin gate din tace "in budurwa ka ke so kaje wurin kawata Haulatu don ita ban ji tana da burin zama koda malamar makaranta ba,kuma nasan zata so ka don sakarya ce" daga haka ta shige tana ta tik'ar daria,shima Officer dariyar yake yana girgiza kai.

A corridor ta tsaya ta cire takalmanta sannan ta d'an lek'a cikin parlon a hankali ta hango hajia dake zaune saman 2-seater ta d'aura takardu saman sofa table tana rubuce rubuce idanuwanta sanye cikin gilashi,cikin d'aga murya Fatuu tace"Assalamu alaikum ga bak'uwa,ga bakuwa daga makkah" hajiya ta d'ago ta kalli entrance tana daria,fatuu ta k'ara maimaita abunda tace,Hajia ta girgiza kai tasan in ba amsa mata tayi ba,haka zatai tayi tace"Maraba da bakuwa mutan makkah shigo" shigowa fatun tayi tana ta kyalkyalar dariya itama hajiyar dariyar take tace "ja'ira",
kusa da ita fatuu taje ta zauna tace"Hajiyar Sanata ina wuni" Hajia tace "lafia lou yar gidan hajiar sanata,kwana biyu baki zo kika gaida hajiyar taki ba, jiya juma'a inata zuba ido banga kinzo yiman barka da juma'a ba" Fatuu ta d'age kai ta kwanta jikin kujerar tace "Ai jiya ban je ko ina ba a d'aki na wuni kamar maijego" ta kai maganar tana ta daria,hajiya dake kallonta tace "hala rigima kika janyo?", "a'a" Fatuu tace tana kunshe daria,
Hajia ta girgiza kai tace"habawa,nida nasan hali,hakanan ba ciwo ba mi zai sa ki wuni a d'aka,har yanzu dai kin k'i daina yin rigima da mutane ko Fatima? dago kanta tayi daga jikin kujerar ta d'an turo baki tace"wllh hajiya mutane ne ke tono na..." hajiya dake kallonta ta katseta"ke kuma ba hakuri ko" dariya kawai fatuu tayi,hajiya tace "gaya man abunda yasa kika wuni a daki" sosae gaban fatuu ya fadi a ranta tace "tabb wllh bazan fadi mata na fasa ma wani glass ba" a fili tace "wata yarinya ce muka yi fad'a na fasa mata hanci da baki" ta kai maganar tana nok'e kai,hajia dake kallonta ta girgiza kai tace "kai jama'a! Yanzu ina amfanin haka fatima,aita gaya maki magana baki ji,ke sam baki da hakuri to kuwa kwanan nan zamu 6ata wllh,6atawa kuma ta har abada kar ma kiyi tunanin zaki ban hakuri in hakura...."da sauri Fatuu ta saukko daga kan kujerar ta duk'a gabanta tace "Don Allah Hajiar Sanata kiyi hakuri wallahi tallahi ita taja ni kinji na rantse,daga nace ta matsa man wuri a Bus din makaranta in zauna bayan an tashi,ta fara gaya man maganganu nai shiru na kyaleta,hakan bai isa ba da muka sauka taci gaba har tana fad'a ma abokanta wai ni daga k'auye aka kawoni..." tayi narai narai da idanu kaman zata yi kuka,
Ajiyar zuciya hajiya ta sauke tana ta kallon fatuu da har kwalla sun cika idanunta, tasan dama hakan sai ya faru don bata son taji tace zasu 6ata,tace"shikenan tashi ki zauna,amman don Allah Fatima ki rika hakuri kinji,yawan fad'an da kike da mutane shiyasa suke tsokanarki ai,ki koyi kauda kai akan abunda bai kai ya kawo ba kinji yar gidan Hajiya" ta k'arasa maganar ta sigar lallashi,
Gyad'a kai Fatuu tayi ta koma kan kujera ta zauna tana murmushin jin dadi,hajiya ta kalli kanta da gyalen ya d'an zame tace "wai har yanzu baki je an kitse kan nan ba? ko rannan ba saida nayi maki magana akan kije ayi maki kitso bane?"
Ta marairaice fuska tace "wllh Balarabar ce zafin hannu ne da ita hajia,in tayi man kitso kaman kan zai tuge gaba d'aya,ni shiyasa banson zuwa" hajiya tace"ba wani zafin hannu,nima ai tana man kitson ko,kawai dai baki son kitson ne,don ma Allah ya taimakeki gashin mai kyau ne ai da tuni ya lalace yadda baki kula dashi d'in nan,bari in Balarabar tazo yiman kitson ai nasa tayi maki shi a gabana kuwa",

ta juya ta kalli kwanon da fatuu ta aje saman carpet da ta shigo tace"mina samu da daren nan haka" Fatuu ta d'ago tace "tuwon dawa ne,Gwaggo tace na kawo maki" fuskar hajiya d'auke da murmushi tace"Aikam nagode wllh,dama kwana biyu banci tuwon dawa ba,gashi Dije badai iya tuwo ba....." Fatuu tace"nikam dai ai ta kusa ta kashe ni da shi" Hajiya tayi daria tace "A ina ki ka ta6a ganin tuwo ya kashe mutum fatima?" Shiru tayi tana ta turo baki,hajia dake ta daria tace"to kinga tashi kidau kwanon miyan nan kije kitchen kisamu bowl mai kyau ki juyo man miyan sai ki daukko man plate in saka tuwon inci abuna yanzu yabi jiki kafin in kwanta,sai ki wanke kwanon ki zubo abinci na nan a kicin d'in kije kici tunda ni dai bazanso tuwon ya kashe ki ba" ta k'arasa maganar tana ta tik'ar daria,

Mik'ewa fatuu tayi ta dau kwanon miyan da ledan tuwon ta nufi kitchen,Hajia tace"ki fara zubo man ruwa a roba in wanke hannuwa",
juyo miyan tayi ta warware tuwon a plate ta kawo ma hajia,har ta juya zata koma kicin don zubo abincin ta waiwayo tace"Hajia ina Aunty Saude ne? Hajiya da har ta fara cin tuwon tace "tana a backyard taje ba su d'awisu abinci" fatuu tace "aikuwa bari inje bayan,dama kwana biyu ban gaisa da mutumina Aku ba...." hajia ta katse ta "A'a kar kije bayan nan,kije ki d'ibo abincin kizo ki tafi kinga dare yayi,na tabbata kika je wurin Aku kuma ai sai an biyo sawunki,ki bari gobe in Allah ya kaimu,ana tasowa islamiyyar safe sai kizo kusha fira dashi,yanzu je ki zubo abincin ki ciko kwanon" Fatuu ta gyad'a kai taje ta zubo abincin wanda dafa dukan couscous ne yaji uban kifi sai k'amshi ke tashi,ta dawo parlon ta aje kwanon akan carpet ta nufi kujerar dake kusa da telephone ta zauna lokacin Hajia har ta kusa cinye tuwon,Fatuu tasa hannu ta dau kan telephone din ta kara a kunnanta ta d'aura kafa d'aya kan daya tana murmura idanu,tace"Hajia" hajiya da ta tura tuwo a baki tace "Uwun" tace "wllh in nazama likita sai na sayi irin wannan telephone d'in kuma har a Office dina na wurin aiki zansa" hajia tace "to Allah ubangiji ya bada ikon zama likitan,amman a Office dinma gwamnati zata sa maki ba sai kinsha wahalan siya ba.....",
Saude ce ta shigo cikin parlon ta kofar baya hannuwanta rik'e da wata roba mai d'an fadi,tana hango fatuu ta aje roban a bakin kofar kicin ta nufo cikin parlon da fara'arta tace "Ah Fatuu yar gidan hajia yaushe ki ka shigo" Fatuu tace "tun d'an dazun,ai naso inzo bayan hajiya ta hana" ta d'an saci kallon hajia tana turo baki,ita dai Saude Murmushi kawae take,
Hajia ta girgiza kai ta kalli saude tace "to wai wurin Aku fa zata da daren nan" Saude ta jinjina kai tace"lallai kam gara ki bari sai gobe don in ki ka je yanzu har sai an biyo ki nasan" Hajia ta gyad'a kai alamar atoh, tace"Saude kije bedroom a bedside din hagu da kin jawo drawer d'in farko akwae kudi ki daukko yan ashirin guda biyar ki kawo man" Saude ta amsa da "to" ta juya don cika umarnin hajiyan.

Hannunta ruk'e da kudin ta dawo dan russunawa tayi ta mika ma ta,hajia tace tsaya ina zuwa,ta juya kan fatuu da ta yi mitsi mitsi da idanu ta d'age baki tana kallo tace "to taso ki tafi kinga har tara saura,yau dai banda wani abun ci,amman gashi kije ki siya ko biscuit ne" Fatuu ta mik'e tana fadin"to ki bashshi mana" Hajia tace "a'a,ai yaba kyauta tukwuici,na yaba da tuwon naji dadin shi kwarae,kice mata nagode Allah yabar zumunci,ya kara zakin hannu" takai maganar tana murmushi, Saude ta mik'a mata kudin,ta duk'a ta dau kwanon tace "Sai da safe Hajia" ta juya kan Saude tace "zanzo gobe da safe in antaso islamiyya Aunty Saude",
Saude da fara'a tace "to Allah ya kaimu" daga haka ta rungume kwanon a 6arin hannunta na dama ta nufi hanyar fita.......

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

*Mallakin*
⬇️
*ZAINAB LALUH*🌹
*(Oummu imam)*

_GARGADI!_
_Wannan littafin ni na kirkire shi,komae kaji yayi daidai ko shige da rayuwar ka/ki ko wani/wata to arashi ne ba da nufi bane kuma ina mai bada hakuri,Don haka kasantuwar littafin nawa ne,ban yarda wani/wata su canza mun littafi ba ko daukar wani bangare daga cikinsa ba tare da izini na ba,Haka ban amince ba,ban yarda ba,ban lamunce ba a yada man shi ba a wata kafa ba misali,YouTube da makamantansu,ba tare da an tuntube ni ba,ni mai littafin don neman izini,Don haka a kiyaye! kuma idan ka ko kin san ba wani muhimmin abu bane Don Allah kar ayi man magana don bazan kula mutum ba,Don haka mu mutunta kanmu_🤝

*Free Page1️⃣9️⃣&2️⃣0️⃣*

Fatuu na fitowa harabar gidan aka bud'e ma Haisam gate ya shigo,parking space ya shige ya parker bike din,ya fito jakar shi rataye a 6arin hannunshi na hagu,hannunshi na dama rike da Bottle water ya d'aga yana d'an sha a hankali ya nufi part dinsa, Fatuu kuwa tsaye tayi a tsakiyan harabar ta rike k'ugunta da d'ayan hannunta da ba komae,a fili tace "Kai! waye wannan kuma da ya shigo a saman waccan dirkeken babur d'in dana gani rannan a ajiye? Ko bak'o akayi bansani ba" yadda tayi maganar kamar irin gidan ubantan nan.

Fatuu bata ta6a ganin haisam cikin gidan ba,don bai dade daya dawo ba weekend dinshi na biyu kenan,dama kuma tafi zuwa gidan ranakun da ba islamiyya Alhamis da juma'a saboda Working days ba lokaci da safe taje boko da yamma kuma islamiyya haka Weekends ma Safe da Yamma tana islamiyya sai dai ko da dare in an aikota kaman yanzu da aka aiko tan shima aiken akan kwana biyu ba'a aiko ta ba,Wani lokacin kuma tana cema gwaggon zata zo ta gaida Hajiar in dare bai yi ba sosae,kuma da tazo suka gaisa hajia zata ce ta tafi gida dare yayi.Ranar Alhamis da ta wuce tazo gidan da yamma kaman yadda tace ma Gwaggo bayan ta fito ne ta biyo Jamila suka yi fad'a har ta zubar mata da Awara a lokacin ne kuma ta fara ganin Haisam d'in.
Ganin haisam na niyyar shigewa corridor yasa ta bi bayanshi da sauri tana fad'in "Aikuwa sai naga ko waye" daidai lokacin da ta iso bakin fence door d'in shiga part d'inshi,shi kuma yana taka matattakalar hawa balcony,jin kaman motsi a bayansa yasa shi dan juyowa,da sauri Fatuu ta koma gefe ta la6e,a hankali ta lek'o da kanta lokacin ya kama handle din kofa zai bud'e ya sake waiwayowa nan take ta gane fuskarsa don gaba daya hasken fitilu ya haske wurin kaman da rana,da sauri tasa tafin hannunta ta rufe bakinta ta juya da d'an gudu gudu tabar wurin,ko amsa saida safe da Officer ke mata bata yi ba,ta yanki hanyar gida tana yi tana waiwayen bayanta,har tana yin tuntu6e,
tana zuwa daidai kiosk din kawu Amadu yace"Ke,daga ina ki ke? Cikin rawar murya tace "d..daga gidan h..hajiya tuwo na kai mata" Yace"miye a cikin kwanon nan" bata bashi amsa ba sai kawai ta bud'e masa kwanon,da yake akwae wuta nan take yaga abunda ke ciki yace "Ah nima kam zanci in kin shiga ki d'an zubo man a plate" tace "toh" daga haka ta shige gidan da sauri,har lokacin hijab d'in da ta d'aura jikin window na nan,tasa hannu ta ciro ta wuce ciki,a bakin kofar kicin ta aje kwanon ta shige d'aki,

fad'awa tayi saman Gado ta takure wuri d'aya sai faman zare ido take cike da fargabar Mutumin nan da ta gani,a ranta kuwa sai maimaita abu d'aya take "dama a gidan hajiya yake...!" a fili tace "Innalillahi,to ko ya gaya ma hajia..!!! Can kuma tace "to amman da ya gaya mata ai da tayi man magana" ta rik'e ha6a alamar tunani,
Ta ci gaba"to ai bai san ni ko wacece ba,kai kilan ma ya fad'a mata fa" ta shiga yarfa hannuwa tace"Aikuwa in hajia tasani ta kuma gane ni ce...." shiru tayi saboda wani bugu da kirjinta ke yi sai zaro ido take,
Gwaggo ce ta fito daga d'aki hannunta rik'e da buta zata band'aki,daidai kitchen ta tsaya tana kallon kwanon da Fatuu ta aje a ranta tace "Ah wannan ba kwanon dana aiki fatuu dashi bane,yaushe ta shigo gidan? hannu tasa ta bud'e kwanon k'amshin couscous din ya bugi hancinta,tace"tabbas fatuu ta aje shi" d'agowa tayi ta kalli bakin kofar d'akin Fatun bata ga takalmanta ba don dasu ta shige d'akin hakan yasa tayi tunanin ficewa ta sake yi kenan,kwafa tayi a fili tace "zata dawo ta same ni,saita fad'an inda taje a daran nan" daga haka ta wuce band'akin.

Shiru shiru gwaggo nata jira taji shigowar fatuu,har bayan wani lokaci bata ji ta shigo ba hakan yasa ta fito ta nufi kofar gida ta lek'a ta wawwaiga ko zata hange ta amman bata ganta ba,
wani yaro ta hango tsaye a bakin shagon Amadu tace "Kai yiman kiran Amadu don Allah" tunkan yaron yayi magana Amadu yace mashi "naji", bayan ya sallami yaron ya bud'e kofan kiosk din ya fito ya nufi inda Gwaggo take tun kafin yace wani abu gwaggo tace mashi "Fatuu fa? Da mamaki ya maimaita sunan fatu yace "ba tana a cikin gidan ba? tace "a'a bata nan" shiru yayi yana tunani can yace "gaskia nadai ga sanda ta dawo daga gidan Hajiyar Sanata tace ke kika aiketa,harma naganta ta dawo da abinci nace ta d'an zubo man"
Gwaggo tace "to ta kawo ma abincin? Yace "a'a,tunda ta shiga banga ta fito ba gaskia,kin duba d'akinta? Tace "ai ko takalmanta babu a kofar d'akin,shiyasa ma ban duba ciki ba,don nasan in tana nan zan gansu a bakin d'akin" Amadu yace"ki dae duba cikin kilan ta shiga dasu don dama kaman a firgice take ta shiga gidan",
Gwaggo ta ta6e baki tace " wannan daman ai koda yaushe ma a firgice take,bari in duba d'akin to" har ta nufi ciki ta juyo tace"ka shigo ga abincin can a kofan kicin sai ka d'iba ka rage mata" yace "toh" daga haka ta nufi d'akin Fatuu,tsayawa gwaggo tayi cike da mamakin ganin fatuu kwance saman gado ta duk'unkune wuri guda,ta nufeta ta d'an leka fuskarta sai taga bacci take,gwaggo tace "bacci kuma.." hannu tasa ta d'an bubbuga k'afafunta aikuwa nan da nan ta farka firgigit

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login