Showing 108001 words to 111000 words out of 212491 words
Murmushi,shima murmushin ya maida mata yana sanye cikin Suit Ash and black colour,alamar ta shigo yayi mata da kai hakan yasa takai hannu da sauri ta bud'e Motar ta shiga,rufe glass d'in yayi bayan ta rufe kopar,daga haka yaja Motar suka fara tafiya,
"Gud Morning Ya Handsome",fuskarshi asake yace" Morning,how a'r u",
"I'm fine" ta bashi amsa,jinjina kai yayi ba tare da ya k'ara cewa kamae ba,
"Ya Handsome ashe kasan Principal d'inmu?" kai ya d'aga mata alamar eh,
"Ashe shiyasa kasan Makarantar da nike"nan ma kai ya d'aga mata,ganin sun wuce kwanar gidansu Haulat yasata sakin salati "kai innalillahi...."kallonta yayi yace"What?",
"Wllh jiya mantawa nayi ban biya ma kawata Haulatu ba hakan yasata ta makara aka tareta,ranta ya 6aci har tana ceman wai tunda an kawo ni a Mota sanyin Ac ya ratsa ni ai dole in manta da ita",
d'an bud'a idanu yayi yace"baki kyauta ba" turo baki tayi cike da shagwa6a"to ai mantawa nayi ko,kowa ba yana yin mantuwa ba",d'an ta6e lips d'insa yayi sai kuma yace"to yau sai ki biya matan ko",
"To ai saidae ka aje ni sai inje in biya mata mu hau Bus" kallonta ya d'anyi "Why,ko wannan ba Mota bane?",
langa6ar da kai tayi idonta akanshi"to ai kai naga baka son ana zauna maka a bayan mota to kuma in tazo ita a ina zata zauna?"d'age mata gira yayi yace"mukai dake ba'a zauna man a bayan Mota?"
zaro ido tayi cike da mamaki"to amman jiya dana zauna ba k'in tafiya kayi ba kace sai na zauna a inda ya dace ka nuna man gaba",
"Yea,ai ni ba Driver dinki bane da zaki zauna a baya kuma gaban ba kowa" bud'a baki tayi alamar mamaki"wai dama saboda hakan ne kace in dawo gaba?'kai ya d'aga mata kafin yace"ina ne gidansu Friend d'in naki?",
"To ai mun fa wuce kwanar tana baya" gyad'a kai yayi ya fara k'okarin juya motar,kallonta yayi bayan ya juya"shi center d'in nasu yana fita titi ne?"
"Eh,amman fa bansan ko Wannan k'atuwar motar zata wuce ba don lungun nasu d'an tsukuku ne,yauwa ga lungun nan" takai Maganar tana nuna masa lungun da yatsanta,kallon lungun yayi nan take ya fahimci motan zata iya wucewa hakan yasashi kutsawa ciki,suna zuwa daidai gidansu Haulat tace "wait, wait ga gidan nan",tayi Maganar tana nuna gidan,ganin tana k'okarin fita yace"ki bari ayi mata horn mana ta fito",da sauri ta kalleshi ido waje"Haulatun za'ai ma horn,ita da ba mota garesu ba taya zata gane ita ake kira bari dae inje in kirata" yadda tayi Maganar sai kace ita Motar garesu,tana shiga cikin zauren gidan suka kusan cin karo da ita ta taho tana sanya hijabin Makaranta,tana ganin fatuu tace"ai na zata yauma a Motar aka daukeki kin manta dani..."da sauri Fatuu tasa hannu ta rufe mata baki,
"Dalla kiyi shiru da Ya Handsome d'in fa muka zo" da mamaki Haulat ta d'an bud'a idanunta"bangane ba?",
"Shi d'an gidan hajiyan nike nufi gashi nan kopar gidanku shi yace in kirawo ki zai kaimu Makarantar" zaro ido Haulat tayi ta kasa magana,ita kam Fatuu hannu takai tana gyara mata wuyan hijab d'inta da ya jirkice ta goge mata maikon kosai data gama ci agefen bakin,
"Ki taho mutafi kada yayi ta jiranmu,amman fa kada kiyi mashi hauka ko kauyanci da kin shiga motan ki gaidashi sai kija bakinki kiyi shuru don shi baison Surutu" daga haka tayi gaba Haulat da tayi sototo tana saurarenta tabi bayanta,har zata fita ta juyo da sauri"ki saka wannan jakar ledan taki cikin hijab ki 6oyeta har muje class don kauyanci ne ki shiga wannan had'addar Motar da Jakar leda",kai kawai ta gyad'a mata tayi yadda tace daga haka suka fita,nuna mata kopar baya Fatuu tayi tace"ki bud'e ta ki shiga,in baki iya ba in bud'e maki kuma in kin shiga ki kulle da karfi don kar taki rufuwa" d'an Murmushi kawai Haulat tayi takai hannu taja Door handle d'in sai gashi kopar ta bud'e fatuu na ganin ta shiga itama ta bud'e gaban ta shige,
"Ya Handsome gata nan na kirata" kai ya d'aga mata yana k'okarin jan motan Haulat data kame kanta agefe guda tace"ina kwana",kai kawae ya jinjina mata daga haka suka tafi,tunda suka hau hanya Fatuu keta faman zuba kaman burkakkar radio,cike da mamaki haulat ke kallonta ita data gama mata hud'ubar taja bakinta tayi shiru baison surutu amman ita ji yadda ta cika su da surutun,ita dai saidai ta d'an girgiza kai kawae kai kace bata acikin Motar ma.
Yauma har gaban Administrative Block ya kaisu,yana tsayawa Haulat ta rasa yadda zata bud'e Motan ta fita hakan yasa tayi zugudum kirjinta na bugawa,
kallon haisam Fatuu tayi tace"Yauwa Ya Handsome inata son in tambayeka wai jiya kuwa ka cika alkawarin daka yi man?"
Kwantar da kanshi yayi jikin headrest ya d'aga mata shi alamar eh,
"To kaci ka koshin?" daga yadda yake ya d'an juyo ya kalleta"Yea,sosae naci i can't even remember when last dana ci abinci haka",kyalkyacewa tayi da Dariyar farinciki harda d'age kai sama,shi dae sai kallonta yake yana d'an Murmushi, kallonshi tayi bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"to yauma ka d'aukko biscuit d'in?"kai ya daga mata alamar eh,
"To ka bani shi sai mu sake kulla Alkawarin yauma" yar harararta yayi"nak'i wayon yau ni zanci abuna in kina so sai ki siya",
Magiya ta fara yi mashi tana jujjuya kai wai ya bata ai anan ba'a saida irinshi,Haulat dake baya batasan lokacin da ta fara sakin Murmushi ba ga mamaki tanayi yadda ya sake ma Fatun sai kace dan'uwanta da gaske,
"Zarah bafa zan baki ba,in kuma na bakin i won't promise u zanci wani abinci a wurin aiki"turo baki tayi ta kai hannu ta d'aukko jakarta dake ajiye akasan seat ta juya zata fita,
"Zarah" ya kirata,juyawa tayi ta kalleshi fuska a d'aure alamar tayi fushi,d'an Murmushi yayi ya girgiza kai daga haka yakai hannu baya gefen haulat ya d'aukko jakarshi,budeta yayi ya fiddo biscuit har yafi na jiya girma,mik'o mata biscuit d'in yayi ganin tak'i amsa yace"take it!" tana tura baki tace"to ai baka yi alkawarin ba" shiru ya danyi yana kallonta,karfin halinta na bashi mamaki,sigh yayi"to zan ci wani abu in naje wurin aiki shikenan?"
"Abinci ko mi?"
"Duk abunda na samu zanci kedai ba so kike in ci in koshi ba?" da sauri ta d'aga mashi kai,
"Owk zanyi hakan,ki amsa kina sani ina makara fa", da sauri takai hannu ta kar6i biscuit d'in tasaka acikin jakarta tana d'agowa ya sake mik'a mata N500 yace su samu drink su had'a batare da musu ba ta amsa tayi mashi Godiya, Haulat dai nata bin ta da ido,so take kawai taga yadda zata bud'e kopar,aikuwa tana ganin yadda Fatun tayi itama tayi sai gashi kopar ta bud'e,wani irin sanyi taji aranta dama bata son agane bata iya bud'ewarba ba kamar Fatuu yanzu tayi mata surutu,
tsaye Fatuu tayi tana mashi bye bye yayinda aketa faman binsu da ido saida ya gama juya kan Motar ta kalli Gate sannan ya sauke glass d'in side din da Fatuu take tsaye,alamar tazo yayi mata da kanshi,mik'a ma Haulat jakarta tayi ta nufi Motar,tsaye tayi abakin kopar tace"gani" hannu ya kai cikin jakarshi dake a gefe sai gashi ya fiddo wani Biscuit d'in irin wanda ya batan fuskarshi d'auke da k'ayataccen Murmushinshi yace"I ave another biscuit,so shi zanci in naje aikin tunda ban yi alkawarin cin wani abu daban ba" zaro ido tayi tasa tafin hannun damanta ta rufe baki alamar mamaki,ganin yanata Murmushi yasa ta cire hannun rai a 6ace kaman zatai kuka tace"ni za kaima wayo Ya Handsome?"d'an harararta yayi"ke kika so yi man wayo bare ni,C'mon Go Class Yar Yarinya",
daga haka glass d'in Motan ya fara rufewa sama a slow yana gama rufewa yaja motan ya tunkari gate,yana zuwa gate masu gadi suka fara d'aga mashi hannu don sai yanzu suka gane ko waye ganin Fatuu da sukai,tsayawa yayi ya sauke glass d'in side d'inshi yana amsa gaisuwar da suke mashi har wani d'an russunawa suke,ganin ya tsaya yasa Fatuu tsallakawa side d'in masu gadin taci gaba da kallonshi fuska atur6une ita ala dole ya 6ata mata rai yayi mata wayau,ta cikin side mirror ya hangota hakan yasashi d'an lek'o da kanshi suna had'a ido da ita ya saki Dariya ganin yadda ta cika fam kaman zata fashe,Sauran Mutanen dake kallonshi suma basu san lokacin da suka fara yin dariyar ba duk da basu san tak'amaimai dalilin yin dariyar tashi ba kawae ya burgesu ne,Wohoho mai kyau ya huta(Allah sarki,sarar kawayena na sec skul😍),maida kanshi yayi yaja motan ya fuce daga cikin Makarantar.
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
4️⃣8️⃣
.......tsallakowa Haulat tayi inda take tsaye ganin tak'i tahowa su tafi aji,
"Mu tafi" tace mata,
k'wafa tayi "Wllh Ya Handsome sai yasan ni ya yi ma haka" Murmushi Haulat tayi tace"wai mi yayi maki ne?" tana tura baki ta fara bata labarin rashin cin abincinshi da Hajiya ta fad'i mata da yadda suka yi jiya daya bata Biscuit d'in da sukai break da kuma yadda yau yayi mata wayo ya bata ashe yana da wani,
Dariya sosae Haulat ke yi,ita mamaki ma fatun ta bata wannan k'arfin hali har ina,
"To kema in banda abunki ga abunda ya saba ci sai kice lokaci guda sai ya canja ya rink'a cin abunda kike so" a harzuk'e tace"To Wannan biscuit d'in abinci ne,ta ina Mutum zai wani k'oshi da biscuit ",
"To ai tunda ya saba cinsu yana k'oshi dasu ne,kinsan kowa da kalar halittarshi akwae Mutane da yawa da basu son cin abinci gara ma shi yana d'an ci kuma duk da ba sosae yake ci ba zaki ga ahakan yana k'oshi halittarsa ce shima haka",
ta6e baki tayi "sai yaje yai ta cin su in Ulcer ta kamashi ba shi ya sani ba"daga haka suka iso bakin class d'insu ta shige ita kam Haulat girgiza kai tayi cikin ranta ta ayyana"Fatuu ta cika rigima,ko ina ruwanta da wani cin abincinshi ma"daga haka itama ta shige cikin ajin.
Bayan sun dawo daga Break Malaminsu na lissafi ya shigo,single period gareshi yana cikin yi masu bayani Malamar Basic science dake da Next period tazo ta sanar cewa bazata samu shigowa ba saboda wani uzuri daya taso, don haka in period d'inta tayi su d'aukko darasin da tayi jiya su k'ara karantawa daga haka tayi ma Malamin Maths d'in godiya ta fita,lokacin da period d'inshi ta kar'e maimakon ya fita sai yace masu zaiyi amfani da lokacin Malamar tunda bazata samu shigowa ba yana so su gama topic d'in yau gobe sai kawae su shiga sabon darasi,duk ba haka suka so ba don da har sunji dad'i zasu wataya in ya fita don period din Malamar Double ce,
Tun yana masu bayani suna ganewa har abun ya gundiresu dama kuma mafi akasari ba son lissafin suke ba don ba kowa ke ganewa ba,juyawa Fatuu tayi tana k'arema sauran yan ajin kallo ganin kowa ya tur6une fuska da gani sun gaji yasa ta juyo ta kalli malamin rai a6ace,can taja d'an guntun tsoki a hankali,da sauri Haulat ta kalleta,hannu biyu tasa tayi tagumi ganin Malamin baida niyyar tsayawa da alama duka double periods d'in yake son yin amfani don har ya shiga sabon Darasi,
"Malam gaskiya mun gaji fa" Fatuu ce tayi maganar,a fusace ya juyo don lokacin da tayi Maganar yana cikin yin rubutu a board ne,
"Who said that" ya tambaya, gaba d'aya yan ajin suka yi tsit kamar bada su yake ba,
"Wacece tayi wannan Maganar" nan ma shiru kowa yayi suna jin tsoron su nuna Fatun,aikuwa nan take ya harzuk'a cikin tsawa yace"U're Very Stupid!baku ji mi nace bane,ko ku nunata ko kuma ku ja ma kanku ku duka wllh,
"Sir ni ce" Fatuu ta fad'a fuska a d'aure,wani kallo ya bita dashi cike da mamaki ya furta"kece!" kai ta d'aga mashi alamar eh,
"Ke mara kunya ko?" turo baki tayi "a'a ba rashin kunya bane,duk mun gajine kuma ko ganewa ma bama yi yanzu,kace so kake ka gama topic d'in gashi har ka fara wani",still yayi yana kallonta da alama ta d'aure mashi kai,can yace"su yan Class d'inne suka ce maki sun gaji kuma basu ganewa?"kai ta d'aga mashi alamar eh,
jinjina kai yayi ya kalli sauran yan ajin fuskarshi a murtuke"Class ku kuka ce mata kun gaji baku ganewa?"tsiit suka yi kowa ya kasa tanka mashi saboda sabon Malami ne d'an bautar k'asa ne shima kanshi rawa yake gashi ya cika zafi,
tsawa ya daka masu"baku ji mi nike tambayarku bane!"gaba d'aya suka had'a baki wurin cewa "a'a",
"To mara kunya sunce basu suka ce maki ba,dama na lura kinfi kowa rashin kunya aduk classes d'in da nike d'auka to zan cire maki duk wani rawar kanki,i will definately deal with u,fito gaban allo ki kama kunnanki" wani kallo tayi mashi kafin ta fito d'in,tana zuwa gaban allon tayi tsaye k'erere tana turo baki,a fusace yace" baki ji mi nace kiyi bane!",
kallonshi tayi"to ai ni ban yin kamun kunne" da mamaki ya maimaita abunda tace,
"Miyasa baki yin kamun kunnan?" shiru ta mashi hakan yasa yan ajin had'a baki wurin cewa"Malam bata lafiya"
juyawa yayi"mike damunta?"ya tambayesu,
"Aljanu gareta in tayi kamun kunne ko aka bugar mata kai tashi suke" wata mai zazzak'ar murya daga can baya ta fad'a,juyowa yayi ya kalli fatun lokaci guda kuma ya yarda da aljanun gareta,
"Ki rage tsawonki anan" ya fad'a yayin da ya koma gaban Allon yana ci gaba da yin rubutun,su kuwa gaba d'aya yan ajin idanunsu na akan Fatuu data kumbura kamar zata fashe,tafi jin haushinsu fiye da malamin,ganin anata kallonta ne yasa tayi kwafa da karfi tace"Wllh in dae aka bugeni bazan k'yale ko wacce banza ba,duk sai na rama tunda baku san abun arziki ba" ta k'arasa tanata huci,Malamin na jinta yayi shiru bai tanka ta ba,hakan yasa ta k'ara cewa"dallah kowacce banza ta daina kallona duk baku kuka ja man ba,matsoratan banza da wofi kawae....."
"Keep quiet!" Maths teacher d'in ya daka mata tsawa yayin da ya juyo yana kallonta fuska a murtuke,turo baki tayi tana kallonshi k'asa k'asa,tsoki yayi ya juya yaci gaba da rubutun duk da hakan bata kyalesu ba kasa kasa ta rink'a yi masu Masifa tana yarfa d'an yatsanta manuni alamar zata kamasu,
Juyowa yayi bayan ya gama rubutun yace"kuyi copying wannan,tomorrow i will explain it",amsa wa sukai da"Ok sir" nuna dayan 6arin board d'in yayi ya tambayesu sun gama kwafar rubutun suka ce eh,hakan yasa ya goge wurin ya rubuta Assignment,a Wayarshi ya ringa kallo Question d'in yana rubutawa a Allo,bayan ya gama rubutawa suka tambayeshi suyi copying Assignment d'in yace masu a'a ba nasu bane,kallon Fatuu yayi yace nata ne Assignment d'in ta tabbatar gobe tayo shi ta kawo mashi kuma a Allo zata yi ma yan ajin bayanin yadda ta fidda shi in kuma ta kasa to duka filin dake gaban classes d'insu ita zata share shi ta kuma wanke duka toilets dinsu har tsawon sati guda sannan ya k'ara mata da bugu,k'ank'ance idanu tayi tana kallon Assignment d'in da ya batan kafin ta kalleshi tana tura baki tace"ai baka yi mana irinshi ba",
"Eh nasani,kece zaki yo shi kiyi ma sauran yan ajin bayani,ga amsar da nike so ki samo nan na rubuta a k'asa in dae amsar da kika samu bata yi daidai da ita ba to baki yi shi daidai ba" cike da isa yana wani shan k'amshi yake mata Maganar daga haka ya kwashe kayanshi da yayi amfani dasu ya kalli sauran yan ajin yace"Till we meet tomorrow" ya fuce abunshi,
Mik'ewa tsaye Fatuu tayi tana k'are ma Assignment d'in kallo,sam bata san ta ina zata fara yinshi ba bare har ta gano amsar daya rubuta a k'arshen,lokaci guda ranta ya k'ara 6aci ta harzuka juyawa tayi tana kallon yan ajin da suma ita suketa kallo tun bayan da malamin ya fita nan take ta fara zuba masu ruwan bala'e tana yi tana buga desk ta kuma ci alwashin indae har bata yo Assignment d'in daidai ba yasata yin abunda yace wllh kowa sai taci ubanta,tun tana masifar a k'asa har abun yakai ga hawa saman desk yadda zata ji dadin ganin kowa kuma kowa ya jita,gaba daya kowa yayi tsit ba wanda ya tanka mata don sun san halinta sarae bata iya fad'an cacar baki ba sai nakai bugu kamar yar dambe da mutum ya tanka mata yanzu ta hau shi da bugu koda kuwa ya girme mata haka zatayi suka kan mutum ta mak'alkale shi kaman biri,Haulat dai girgiza kai kawae take don tasan in tayi irin wannan zuciyar bata jin lallashi,saida tayi mai isarta don kanta ta hakura ta saukko daga saman ta zauna saman seat taci gaba da kwafar rubutun tana yi tana kwafa had'i da tsoki,
sai bayan da aka tashi ne lokacin da Bus ta saukesu Haulat ta fara bata hakuri ta nuna mata duk laifinta ne da batayi Magana ba tunda ba ita kadae ta gaji ba kuma ba wanda yasata tace mashi hakan dama dole zai ga tayi mashi rashin kunya ne data k'yaleshi yai tayi har ya gama ya fita,shiru tayi bata ce mata komai ba,
"Yanzu to shi Assignment d'in daya bakin kin iya ne?" Haulat ta tambayeta,nan ma shiru tayi mata kaman bazata ce komae ba can kuma tace"ko ban iya ba sai na dage nayi shi ko don in bashi kunya,mugu kawae ai da biyu ya bani shi bacin yasan bai mana shi ba,baki ga ma a wayarsa ya kwafe shi ba" kai Haulat ta d'aga"Eh nagani,Allah ya taimake ki kiyi shi daidai",a hankali ta amsa da Amin,adaidai nan suka rabu da Haulat d'in, Fatuu tayi gaba ita kuma ta shige kwanar gidansu.
Tun bayan data koma gida ta baje a tsakar d'akinta tanata faman kokarin yin Assignment d'in,saidae sam ta kasa,har wani textbook d'inta na maths ta duba wai taga ko zata ga irin tambayar amman ina ko mai kama da ita bata gani ba gashi