Showing 138001 words to 141000 words out of 212491 words
tace mata ta tashi tayi salla ta amsa da to saidae har ta idar Fatuu bata da niyyar tashi, kiranta ta k'ara yi tace ta tashi tayi sallar inta gama sai ta kwanta, tana tura baki ta tashi zaune, koda ta saukko daga kan katifar ta mik'e tsaye sai taji d'an jiri ya kwasheta, da sauri ta koma ta zauna tanata faman k'unci hannunta guda dafe da cikinta ita dae saude tana ta lazimi bata tanka mata ba, saida ta dau d'an lokaci kafin ta sauka k'asa ta fara yin rarrafe ahaka ta isa kopar toilet din, Saude data saki baki tana bin ta da ido bata san lokacin data saki dariya ba tana girgiza kai tace Allah ya shiryeki Fateema, koda tayo Alwalar matsar da abun sallan tayi can jikin bango ta jingina dashi ahaka ta kwa6a sallar tana gamawa ta baje awurin, da Saude ta lek'o d'akin wurin karfe biyu har kwalla tayi mata wai mutuwa zatayi sauden tace mata bazata mutu ba don da ana mutuwa suma da suke yi duk shekara kuma duka ai da tuni sun mutu, tace wannan zaman d'akin da take yi ne yake sata jin wuyar azumin da zata d'aure ta fita tayi wani d'an aiki zata rage jin wuyarshi, tana jin hakan tace tabb wllh ita ko mik'ewa ma bata iyawa,
Ana gab da kiran sallar la'asar Hajiya na zaune a falo tana kallon tafsir aka aiko wata yarinya kiran Fatuu, da mamaki Hajiya tace anya Fateema na gidan nan kuwa, k'wala ma saude kira tayi ta fito daga cikin kitchen tun kafin ta k'araso cikin falon hajiya tace "wai Fateema na gidan nan kuwa?",
Murmushi tay tace "tana nanl" da mamaki Hajiya ta maimaita tana nan kafin tace "yaushe to tazo gidan ban sani ba?" Saude na dariya tace " Azumi take yi yau tun safe tana cikin dakina kwance" da mamaki Hajiya ta k'ara maimaita maganar Sauden kafin tace "to dama sauran ranakun da take cewa tana azumi bayi take ba?"
" Eh wai wuya yake bata shine take karyawa wani lokacinma wurina take zuwa in bata abinci to jiya na aiketa ta d'aukko Basket a part d'in yalla6ai haisam shine ya kamata tana ci ",
Salati Hajiya ta saka ta ruke ha6a cike da mamaki tace "yanzu dama duk marairaicewar da take tace tana yin azumi k'arya ne bata yi ko d'aya ba, kai Fateema Allah dai ya shiryata wllh, ke kuma ya da haka Saude ya zaki rink'a goya mata baya tana karyawa?" Hajiya ta kafeta da ido hakan yasa ta dan sunnar da kai kafin ta d'ago tace "ta ce man wai bata fara jinin al'ada bane kuma a islamiyyarsu ance sai Mutum ya fara azumi ya zamar masa dole kuma nima haka nasani shiyasa",
jinjina kai Hajiya tayi tace " to ai koda bata faran ba tunda alamomin balaga sun fito mata ya wajaba arinka sata tanayi amatsayin ladabi shiyasa ma Dijen ke sawa tana yi, kuma in bata saba da azumin ba taya zata rinka yi inya zamar mata dolen, aikuwa ya kyauta daya sata dole tayi in ba haka ba to kuwa ba ranar da zata yi azumin, kema kuma kar ki k'ara goya mata baya ta hanyar bata abinci abarshi a yadda Haisam d'in yace ta rinka yi" jinjina kai Saude tayi cike da ladabi tace "insha Allahu bazan k'ara ba",
Umarnin tado Fatun Hajiya taba sauden, lokacin da taje dakin tana nan dae malale a k'asa kaman ruwa tana ganin sauden ta fara juye juye tana fad'in wayyo cikinta,
" Sannu Fateema, ki daure ai ankusa ma shan ruwa tunda la'asar ta kusa",
wani kallo tayi ma Sauden tace "wai har yanzuma bata yi ba kenan, Aunty saude kodae lasifinkan masallacin ne ta lalace shiyasa baki ji ankira ba" ta k'arasa Maganar tana ta nishi, yar dariya tayi tace lafiyar lasifikan masallaci lau kawae lokacinne bai idasa ba, lokacin da ta sanar mata Hajiya tace akirata don an aiko kiranta cewa tayi ita wllh bata iya tashi sauden tace to taje ta fad'i ma hajiyan hakanne tace a'a ta kamata sai suje, kamar wata mai jinya haka Saude ta kamota suka fito hajiya na ganinsu ta saki baki tana kallon ikon Allah, a tsakiyar falon ta zauna tana gaida hajiyar da kyar,
"Yanzu duk azumin ne haka Fateema?" kai ta d'aga mata kawae,
"To sannu, ki tashi kije Dije ta aiko kiranki"
Yamutsa fuska tayi kaman zatayi kuka ta kalli saude tace don Allah ta k'ara kamata suje gidan, Hajiya ta hana tace ta daure ahaka zata saba, da k'yar ta tashi ganin hajiyar ta d'an d'aure fuska ta tafi tana layi kaman wata yar maye, tana fita waje ta dawo cikin falon kamar wadda wani abu ya biyo har saida hajiya ta d'an tsorata takai idanunta kopar shigowan, can gefen Hajiyar taje ta zauna ta jingina da kujerar da take zaune idanunta cike tab da kwalla, ganin hakan yasa hajiya tambayarta lafiya,murya kaman zata yi kuka tace "Wllh Hajiya rana yayi yawa baki ji ba dana fita kaman an watsa man wuta a fuska, ban iya zuwa gidan cikinta" tana kai Maganar kwalla suka zubo mata sharr, jinjina kai Hajiya tayi tana kallonta tace "to yanzu ace ma Dijen baki zuwa kenan duk da tun safe baki gidan?" shiru ta d'anyi sai kuma tace "A'a zani amman don Allah ki ara man lemarki" waro ido hajiya tayi bata san lokacin data sa dariya ba tace "lema kuma fateema" kai ta d'aga mata tana ci gaba da zubda kwallah, kwala ma Saude kira tayi tace ta aro ma fateema lemarta wai bata iya zuwa gida cikin rana, Saude nata dariya ta d'aukko mata lemar, dakyar ta mik'e tun acikin falon ta bud'eta ta d'aga saman kanta daga haka ta fita sunata mata dariya hajiya na fad'in yau Manya na Azumi.....
( A daidai wannan gabar zanyi karin bayani dangane da wajibci ko rashin wajibcin azumin Fatuu, ni ba malama bace ta wannan fannin daliba ce, hakanne yasa nayi amfani da ilimin da aka koyar dani kan hakan, Fatuu bata balaga ba saboda bata fara jinin haila ba saidae alamomin balagar sun fara bayyanar mata kaman fitowar mama wanda wannan ba ainihin balaga bace, a ka'ida na cika azumin mace da namiji, shi namiji sai ya balaga ma'ana yayi mafarki shine malamai suke cema iza balagal luhuma, ita kuma mace sai ta fara jini, su abubuwan da zasu fara fitowa ajikinta wato canjawar jikin anace masu alamun balaga amman ba ainihin balagar ba, a ka'ida ta musulunci da malamai suke badawa shine wanda hukunci ya fara hawa kanshi wanda in baiyi abu ba na wajibi za'a bashi zunubi in kuma yayi za'a bashi lada shine mace ko namiji su balaga, wato cikakkiyar balaga ga mace takai lokacin da zata fara yin jini, in kuma kaman aka samu matsala mace tazo da lalura cewa ita bata jini, to malamai suka ce akwae abunda ake cema,'addaruriyati tud'id' iful ma'azurat, shine lalura tana kauda duk wani abu da yake na uzurine to sai a kiyasta shekarunta aga sun kai nawa, ko kuma a duba wanne ne karshen shekarun da mace take kaiwa ta fara jini in dai lafiya lafiya to sai ace ta fara cika azumi tana da matsala kilan tana daga cikin matan da basu jini,
Kaman Fatuu da alamomi suka bayyanar mata amman bata fara jini ba to azumi bai zama wajibi akanta ba sai ajira har sai tafara sai kuma ayi mata ladabi kaman yadda Manzon Allah (S.A.W) ya fad'i cewa ku hori yaranku suyi sallah suna yan shekaru bakwai, idan suka kai goma basu yi ba ku bugesu, ba ana nufin idan sun kai shekara goma basuyi sallah ba suna tare da zunubi, ana so akoya masu yin sallar ne sai sunkai lokacin da zasu balaga ne in basu yi ba za'a rubuta masu zunubin wannan anayi masu ladabi ne don akoya masu su saba, to haka yarinya in bata balaga ba bata fara jini ba ana koya mata ta cika azumine saboda in yazamar mata wajibi ta saba, anan nike son jan hankalin wasu Iyayen da suke goya ma yayansu bayan kin yin azumi saboda basu balaga ba basu fara jini ba duk da alamomin sun bayyana wai don yana basu wuya, wannan kuskurene ba soyayya bace in dae wuyar ba lalura take zamar masu ba ya kamata ayi masu dole su rinka yi don in basu saba ba ko ya zamar masu wajibi zasu iya su rinka karyashi ba tare da sanin kowa ba, yakamata ayi ma yaro ko yarinya ladabi su saba kaman yadda ake yi masu na salla, Allah yasa mu dace Amin,
Ga wadanda fahimtata su ba haka bane agare su, ba haka aka koyar dasu ba, Wannan kuma sa6ani ne na malamai, Wallahu a'alamu).
ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,
ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
5️⃣6️⃣
......dakyar ta fito daga gidan don ko tanka ma su Officer dake tambayarta lafiya ko duk azumin ne batayi ba, har saida ta zauna gaban fence d'in gidan hajiyan ta d'an huta kafin ta samu ta mik'e da kyar ta k'arasa gidan tanata had'e hanya don ko kawu Amadu baiga sanda ta wuce ba saboda ta kifa lemar asaman kanta don ruk'on ma lemar aiki ya zamar mata, koda taje gidan bata iya tsinana ma gwaggon komae ba don tana shiga ta kwanta a k'asa ta aje lemar gefe tana ta nishi dayake yamma tayi ba rana a tsakar gidan, a d'an rud'e Gwaggo ta rink'a tambayarta lafiya kafin ta iya bata amsa wayarta ta fara ringing hakan yasa ta juya ta d'aukkota asaman window, ganin sunan Hajiya yasa ta d'auka da sauri don tasan k'ilan Maganar da ta shafi Fatun zata yi mata, aikam bayan sun gaisan hajiyar tayi mata bayani dangane da yanayin da fatun take ciki ta nuna mata karta sare tace zata sata ta karya ta kyaleta inba haka ba bazata ta6a sabawa ba, cike da girmamawa tace mata in sha Allahu bazatayi hakan ba, sosae ta shiga yi masu godiya ita da haisam, bayan sunyi sallama ta aje wayar, bin fatun tayi da kallo cike da mamakin ashe duk azumin da tayi ba cikakku bane ita ta mayar shashasha, kyaleta tayi nan yashe taci gaba da ayyukanta saboda taga tana jin jiki sosae don tasan dama bata da jumurin yunwa,
MAGRIB
Lokacin da aka sha ruwa jiki na kerma Fatuu ta d'auki Jug d'in ruwan sanyi ta kafa baki gwaggo na karta sha da yawa amman ina saida ta shanyeshi tasss sannan ta dire jug d'in aikuwa nan da nan ta fara kwara amai anan tsakan gidan gwaggo na fad'in maganin mara jin Magana kenan, sosae jikinta ya mutu ta kwanta asaman tabarmar da daddumar da gwaggo ta shimfida sam tama kasa cin komai gwaggo nata faman yi mata sannu, lokacin da Amadu ya shigo shan ruwa yana ganinta ya hau tambayar lafiya ko bata lafiya ne gwaggo ta bashi labarin abunda ya faru, sai can bayan Magrib d'in ta samu ta iya cin wani abu, duk burin da take dashi na taci uban abinci in ansha ruwa yatashi abanza tana niyyar k'ara kwanciya gwaggo tace ta tashi tayi wanka zata ji k'arfin jikinta sai tayi sallah in ma kwanciyar zatai sai ta kwanta, da farko cewa tayi bata iya yin wankan gwaggo tace ta dai daure bari ta kai mata ruwan band'aki, aikuwa tana yin wankan sai gashi taji ta dawo daidai har saida ta k'ara cin wasu abubuwan sannan ta had'a Magrib da Isha tayi, anan kan sallayar ta sake bajewa sai bacci don da lokacin kwanciya yayi saidae gwaggo ta kaita cikin d'akin dakyar,
Da Asuba lokacin da gwaggo ta tada ita sahur kuka ta saka mata wai in ta k'ara yi yau mutuwa zatayi don Allah ta rokar mata ya Handsome ya kyaleta ba sai tayi ba tunda bai zamar mata dole ba aikuwa nan ta tok'alo gwaggo dama yanayinta a jiyan yasa bata tanka mata ba akan karya azumin da ta rink'a yi har bata yi ko d'aya ba, fada sosae tayi mata tace waye yace mata don bata fara Al'ada ba shikenan bazata rinka yi ba ai dole zata rink'a yi don Al'adar na kan hanya, tana kuka a haka ta rink'a tura Abinci ranta ajagule sai dai bata yi irin cin da tayi jiya ba abinci d'an daidai ta ci harda fura gwaggo ta bata tasha don ita tafi sha da yawa lokacin Sahur sai abinci kad'an anan kuma taci alwashin da gari ya waye zataje ta bashi hakuri akan ya kyaleta ko dayan ne ta rink'a yi, bayan ta gama tana niyyar kwanciya gwaggo tace ta tsaya tayi sallar asuba sai ta kwanta in ba haka ba da ta kwanta cikinta na iya 6aci tace ta d'aukko Alqur'ani ta karanta, lokacin da tayi sallar asubar har Addu'a tayi wai in taje ba Ya Handsome hakuri Allah yasa ya yarda ta rinka yin daidaya kuma Allah yasa ta daina shan wuya harda su kwalla da tana yin addu'ar.
Karfe takwas da rabi Gwaggo ta tada ita don tayi shirin islamiyya don yanzu da safe suke zuwa karfe 9 saboda anyi hutun boko kafin itama islamiyyar abasu hutun ranar Laraba, lokacin da ta shirya ta fito cikin Uniform direct gidan hajiya ta wuce, tana zuwa part d'in haisam ta iske kopan shiga falon a kulle lokacin da ta tura, shiru tayi tana tunanin k'ilan bai tashi ba, ko ta tafi sai anjima sai kuma ranta ya bata yau ba lalle Aunty Saude ta kyaleta ba batare da ta tafi islamiyya ba kuma lokacin da za'a taso rana ta fara gara ta bashi hakuri in ya yarda sai ta karya azumin kawae, Knocking kopar ta fara yi ahankali, jin ba'a da shirin bud'e mata yasa ta k'ara sautin bugun amman shiru har ta fara tunanin ko dai ya tafi aiki ne, har ta juya taji an bud'e kopar hakan yasa ta waiwayo da sauri, tsaye yay jikinshi na sanye da sleeping dress riga da wando Army green ba k'aramin fito mashi da farinshi kayan sukai ba, da ka kalli fuskarshi zaka gane daga bacci ya tashi, kallonta ya rink'a yi daga sama har k'asa fuskarshi a d'aure hakan yasa tayi saurin sunnar da kai k'asa, juyawa yay ya koma cikin falon ya zauna kan kujera had'i da d'age kanshi sama don har ya fara sara mashi, a rayuwarshi ya tsani yana bacci a tasheshi, bama wanda ya ta6a gigin yi masa hakan, ko Hajiya take da bukata awurinshi indae tasan yana bacci bata tadashi ko acan Abuja ma indae ba abu na gaggawa ne ya taso ba wanda dole dole sai ya tashin shine aka tashinshi, in kau ba haka ba duk wanda ya tasheshi sai ya fuskanci bacin rai, shi kanshi yasan yana d'aga ma Fatuu kafa sosae don a yadda ya taso da wani ne tabbas sai ya fuskanci bacin ranshi koda da dalili duk da itama fuskarshi ta nuna,
Tsaye tayi awurin ta kasa shiga ciki saboda yadda taga ya daure fuska tunani ta rink'a yi kodae ta tafi amman kuma tana bukatar rokonshi don lokacin da za'a taso islamiyya tasan rana tayi kuma indae tana azumin tasan sai tasha wahalar dawowa gida, wannan tunanin yasa ta fara tafiya ahankali kaman mai yin sand'a ta shiga cikin falon, ganin yadda ya d'age kai sama yasa taji tsoron k'arasawa ciki tai tsaye daga gaban kopan tana kallonshi,
Bayan wani d'an lokaci taji yace "Just to interrupt my sleep?" da wata irin murya mai kaushi yay Maganar, shiru tayi tana kyakkyafta ido, jin bata amsa mashi ba yasa ya d'ago kan ya kalleta, ganin kallon da yake matanne yasa ta matsa zuwa gefen kujerun ta tsugunna, yar sheshsheka ta fara yi kafin ta fara magana,
" Ya Handsome da..dama..don Allah zuwa nayi in rok'eka ka kyaleni in rink'a yin azumi kwana daidaya, wllh jiya kusan mutuwa nayi ko islamiyya ma banje ba saboda ban iyawa a d'akin Aunty Saude na wuni lokacin da aka sha ruwa kuma har amai nayi" ta k'arasa cikin karewar murya tana goge kwalla da hijab dinta,
Sigh yay ya d'an gyara zamanshi kaman bazaice mata komai ba idonshi akanta tana ta nannok'e kai,
"Kinsha ruwan da yawa next time sai kisha kad'an, ko ki fara shan something warm in zaki iya and karki k'ara zama baki je skul ba saboda kina fasting " ya fad'a bayan ya daidaita temper dinshi, d'agowa tayi ta kalleshi still tana murzar ido cikin marairaicewa tace "to zan rink'a yin hakan kuma bazan kara kin zuwa islamiyyar ba amman in rinka yin d'ayan?" girgiza mata kai yay