Showing 156001 words to 159000 words out of 212491 words

Chapter 53 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

988

ko sallar data wuce haka tay masu d'inkakkun kaya saidae wanccan karon atamfa tayo masu Amadu kuma yadi ne mai kyau kuma dama ko ba salla ba tana yi ma Fatuu d'inki lokaci zuwa lokaci, wata k'arar murna Fatun ta saki tana fad'in tafi kowa kayan salla wannan sallar gwaggo dai nata faman dariya, lissafi ta shiga yi Ya Handsome yayi mata kala hudu ga bakar doguwar rigar data aje kala biyar kenan sai ga biyu hajiya tayi mata bakwai kenan sai kuma baffanta da yazo ya kawo masu atamfofi ita da gwaggon anyi mata dinki kala biyu Amadu kuma ya kawu masa yadi mai kyau mai matsakaicin kudi dama ita gwaggo bata da niyyar yi mata d'inki wannan sallar tunda baffanta ya kawo mata kuma tasan hajiya dama zata yi mata ga kuma jallabiyar da ta aje, sam bata ma sa ran na Haisam ba iyaka dae ta siya mata gyale da takalma dasu sarka harda sabbin pants da undi da vest sai gashi kuma Haisam din shima ya siya mata, lallae da alama su Fatuu canjin wardrobe za'ai, cike da murna ta ruga waje ta fad'o ma Kawu Amadu suka dawo tare, sosae yay farinciki da ganin kayan, koda lokacin kwanciya yayi Fatuu tasa dukkan kayan tayi gabanta ahaka tai bacci..........


ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,
ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE๐Ÿ‘ฐ,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWAโญYAR LELE AGUN MIJINTA๐Ÿ˜ SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI๐Ÿค

*๐Ÿ’–A SANADIN MAKWABTAKA๐Ÿ’–*

_A heart touching story of Love and Destiny_ ๐Ÿ’”


*Mallakin*
โฌ‡๏ธ
*๐ŸŒนZAINAB LALUH*๐Ÿ“ฒโœ
_~(Oummu imam)~_


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

6๏ธโƒฃ0๏ธโƒฃ

Washe gari da Safe suka d'unguma gaba d'aya suka tafi yin godiya, ana saura kwana ukku salla bayan la'asar lokacin gwaggo da Fatuu suna cikin aikin kayan shan ruwa Amadu ya shigo cikin gidan da sallama, nufar Fatuu yay dake jajjagen kayan miya aturmi ga kuma dankali na soyuwa kan gas agefenta,
"Gashi nan in ji Ya Haisam" ya fad'a yayin da ya aje babbar ledar da ya shigo da ita daga haka kuma ya juya don ya baro Mutane a shago, cike da zumud'i ta janyo ledan ta bud'e, koda ta yi arba da kayanta da aka kai d'inki sai ta saki dariyar farinciki ta fara kwala ma gwaggo kira tana fad'in tazo taga dinkinta gasu an kawo, fiddo kayan ta fara yi tana dubawa nan take tsananin farinciki ya lullu6eta ganin yadda dinkin sukai bala'en kyau, a atamfar akai mata fitted gown d'in lace din kuma sai akai mata riga da skirt, sunkutar gown d'in tayi ta nufi d'aki don ta gwada, bayan shigarta da d'an lokaci gwaggo ta fito daga cikin kitchen tana fad'in taga dinkin, ganin ba Fatun a wurin yasa takai hannu cikin ledar ta fiddo rigar lace d'in ta d'aga sama, waro ido gwaggo tayi gannin dinkin rigar ba arziki ta d'aurata a saman kafadarta ta curo skirt d'in shima ta d'aga tana k'are mashi kallo bata gama al'ajabin d'inkin da akai masun ba sai ga Fatuu ta fito cikin fitted gown d'in ta kamata tayi mata d'as ajiki daga k'asa ta bud'e sosae yayin da hannuwan ma suka wani kumbura anyi masu wani kalan design d'in dinki da wani abun kwalliya mai kyau, nufo gwaggo tayi tana faman washe baki tana fad'in bari tazo ta idasa zuge mata zip d'in, cakk taja ta tsaya sakamakon jin salatin da gwaggon ke rafkawa hannu a baki, tsaye tayi ta kwalalo ma gwaggo ido,

"Yanzu Fatuu wannan d'inkin akai maki sai kace wata kifi, waye yace ai maki shi ne?" ta tambaya rai a 6ace, shiru tayi tana ta zare ido ganin yanayin fuskar gwaggon, har saida ta kwatsa mata tsawa sannan cikin en ina tace "n..nice na za6a" cike da takaici gwaggo ta maimaita abunda ta fad'an kafin tace "saboda baki da hankali ko shine bazaki za6i d'inkin arziki ba sai wannan duk da irin fad'an da nike maki akan matsatstsun kaya shine don kin raina ni baki jin maganata kika za6i wannan dinkin na rashin arziki duk an matse halitta ta bayyana, to naga yadda za'ai ki saka su da sallar in Allah ya kaimu sai dae ki kallesu kuwa",
yamutsa fuska ta fara tana jujjuya kai kaman zatai kuka tace " ni dae don Allah ki barni nasa abuna ai dae ajikin Mutane naga anyi nima na za6a ko"
"To ni bazan bari kisa ba sai in ga ta tsiya" bubbuga kafafu ta fara tana k'unk'uni tana fad'in " Wllh nidae sai nasa abuna tunda ai bake kika siya man ba ko kuma....." cakk ta tsaya da yin Maganar ganin gwaggon na dube duben k'asa da alama abun bugu take nema, hannu takai cikin robar da fatun ta yanka dankali ta curo wuka, a rud'e Fatuu ta zaro ido tace "Gwaggo wuk'a ne fa!"
"Wukan ne don kazan ki, in na illata ki ba sai inga yadda za'ai kisa su da Sallar ba" ta bata amsa lokacin da take d'agowa hannunta ruke da wuk'ar aikuwa Fatuu na ganin haka ta juya fatal fatal don ta kasa yin gudu sosae, maimakon ta jefa wukar saitinta sai ta jefata can gefe guda kafin ta duk'a da sauri ta curo slipper d'in kafarta ta jefa mata daidai fatun ta shige ya d'an sameta a gefen jikinta, tana shigewa d'akin ta rufo kopar, ita kuwa gwaggon cigaba da d'aga riga da skirt d'in tayi tana ta zabga uban tsoki don da gani suma kayan matseta zasuyi sosae gashi lace d'in ya Matuk'ar burge Gwaggo don ya had'u sosae kuma ko ba'a fad'a ba da an kalleshi an san mai kudine sosae, k'arshe dae da takaicin ya isheta sai ta jawo ledar kayan ta cusa su ciki ta ajeta can gefe taci gaba da aikinta cikin ranta kuwa takaicin Fatuu ne k'unshe,

(Gwaggo ai ba laifin Fatuu bane ita kadai, harda haisam da ya goya bayan ayi mata shima yakamata kije ki hukunta shi gaskia๐Ÿคฃ)

A ranar bayan gama sallar asham atare da haisam suka nufi falon hajiya kamar dae kusan ko yaushe, basu dad'e da shiga ba itama Hajiyar ta fito jikinta sanye da hijab ta zauna suka ci gaba da yin fira sai dae tafi yi da Fatun, suna cikin yin firar ne Hajiyan ta juya tana ma Haisam zancen tafiyarsu Abuja jibi wato daren salla, har saida gaban Fatuu ya fad'i duk da tasan dama indae Hajiyan bata je Umrah ba to k'aramar sallah a Abuja take yinta babbar salla ce take yi anan, gaba d'aya jikinta yay sanyi jin harda Ya Handsome d'in za'a tafi lokaci guda walwalarta ta dushe, koda ya rakota lokacin zata tafi gida shiru tay mashi sa6anin yadda ta saba suna tafe tana mashi surutu, daren ranar dae cike da kunci ta kwanta har bacci ya kwasheta ba kuma komae yaja hakan ba sai don tunda tasan Haisam bai ta6a tafiya ba, ko lokacin baya kafin azumi daya tafi lagos shida Abbas sam bata san bai gari ba don in taje bata iske shi ba sai tai tunanin ya fita ne saida ya dawo ranar Monday da yamma taje bayan an taso su daga islamiyya ya bata tsaraba anan ne tasan tafiya yayi yanzu kuma tasan in suka tafi sai sun dade don in hajiya taje sallar tana dadewa bata dawo ba,

Washe gari ya kama saura kwana biyu salla, tunda ta farka ba walwala a tare da ita komae sukuku take yinshi don Maganar ta tsaya mata arai, taci burin cin gayu suyi yawan salla tare dashi ya kaita wurare, gwaggo ta lura da yanayinta kaman akwae abunda ke damunta ba kamar data zauna gida bata je gidan hajiya ba hakan yasa ta kirata a d'aki ta tambayeta mike damunta ne (har an shirya kenan๐Ÿฅฐ) da farko ce mata tayi ba komae gwaggon tace ai in ba komai bazata ta6a ganinta haka ba dole akwae abunda ke damunta hakanne yasa ta fad'i ma gwaggo Hajiya ce zasu tafi Abuja ba anan zasu yi salla ba,
"To dama wannan karonne ta fara tafiya Abuja salla" gwaggon ta tambaya da mamaki,
"A'a nasan tana zuwa, amman wai fa harda Ya Handsome za'a tafi kuma da shi naso ya kaini yawon salla" ta fad'a fuska a kwa6e, jinjina kai gwaggo tayi jin wani karfin hali awurin fatun tace "to tunda bawanki ne ai sai ki hanashi tafiya gidan babanshi yin salla ya tsaya ya bauta maki tunda ke shashasha ce" turo baki tayi kaman zatayi kuka, can bayan wani lokaci a marairace tace ma gwaggon wai ko tace ma Hajiya zata bisu, aikuwa tun kafin ta rufe baki gwaggo ta hau zazzaga mata fad'a tana fad'in ahirr dinta karta sake taji hakan in ba haka ba ranta zai 6aci ne, duk da da hajiyar ke tafiya da ita dama ake zuwa ne, sosae ta 6ata ma gwaggo rai k'arshe ma tace ta tashi ta bata wuri kuma da taji ance za'a Abuja da ita to tasan ita tayi Maganar atafi da ita kuma wllh daga can tana dawowa Yola zata tafi tunda ita komae sai tasa rashin hankali, lokacin data koma d'aki kan gadonta ta fad'a tana share kwallar da suke zubo mata ita dae hakanan bata son yin salla ba tare dasu ba. Da rana Wuraren karfe sha biyu Hajiya ta kira waya tace Fateema tazo ga Balaraba nan ta kusa gama mata kitso sai ayi mata itama, lokacin da gwaggo ta sanar mata tana tura baki tace ita dae bata son ayi mata kitso tunda an gyara mata gashi gwaggo na jin hakan tace to taje da kanta ta fad'i ma hajiyan hakan, lokacin da ta shiga falon Hajiyar har angama mata kitson tana ganin yanayin Fatun ta tambayeta lafiya ko duk azuminne tace mata a'a bata jin dad'i ne, hajiya na jin hakan ta yarda don duk ranar sai lokacin taje gidan wanda lafiya lafiya tasan bazata k'i zuwa ba, tace to anma yi mata kitso kuma bata jin dad'i fatun tace a'a abarshi tunda Ya Handsome ya kaita an gyara mata gashin, daga haka tayi mata sallama ta nufi hanyar fita hajiyar nayi mata Allah ya sawak'e harda Saude dake jiran itama ayi mata kitson da Balarabar ma,

_____________

"Zaraah" taji an kirata lokacin har ta kai gate d'in gidan tana niyyar fita, a hankali ta juya ta kalli haisam dake fitowa daga cikin corridor d'in part d'inshi da alama Masallaci zaije don an fara kiran salla, d'an matsawa tayi kafin taja ta tsaya ya k'araso gabanta yana kallonta,
"Ina wuni" ta fad'a asanyaye, shiru bai amsa ba sai cewa yay "mike damunki ne" ya tambaya ganinta sukuku kuma yasan ba azumi ne yasata hakan ba don yanzu sam ta daina korafin azumi har ukku ukku take yi ma,
"Am i not talking to u?" ya fad'a da d'an d'aga Murya, maimakon tayi mashi Magana sai kawae tasa mashi kuka hakan kuma yasashi Fahimtar tabbas akwae abunda ke damunta,
"Kije part d'ina ki jira ni" ya fad'a yayin da yake wucewa ya nufi Masallaci,
"Baki ji bane" ya sake fad'a bayan ya dakata ganin bata tafi ba, a hankali ta wuce part din nashi, ana gama sallar ya dawo yana shiga falon ya isketa tana yin salla dama hijab ce ajikinta kuma d'akin da ta ta6a zuwa yin fitsari taje tayo alwala, zama yay kan kujera ya d'auki remote ya fara canja Channel, zaune tayi kan Carpet bayan ta gama ta sunkuyar da kanta kasa,

"Unhum am all ears, miye ne?" taji ya fad'a idonshi akan tv, shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta don tsoron fad'i mashi take saboda gargad'in da gwaggo tayi mata, aje remote d'in yay ya maido hankalinshi kanta a hankali ta d'ago suka had'a ido ganin kallon da yake mata ne yasa ta fara motsa baki amman ta rasa mi ma zata ce mashi,
"Kina sani abubuwan da bana so Zarah, i think i ave told u since banason maimaita mgn right?" ya d'age mata gira, d'aga mashi kai tayi alamar eh,
"Ok ina jinki"
Cikin en ina ta fara Magana "da..daman naji ba anan zakuyi salla ba Abuja zaku tafi"
Shiru kaman bazaice wani abu ba sai kuma yace "yea, akwae matsala da hakan?" girgiza mashi kai tayi "a'a, kawae dai nayi zaton anan zakuyi saboda ina son muyi yawan salla tare da kai",
bud'a ido yay jin wata Magana mai nuna tsantsan yarintarta, d'an Murmushi yay gently yace "ni ai bani yawon salla Zarah"

"Eh ina nufin ka kaini wurare dama, don duk salla ba inda nike zuwa in ba nan cikin Unguwar ba sai gidan wasu yan uwanmu yan kad'an" jinjina kai yay "Ko zaki bi mu Abujar ne?" ba zato ba tsammani taji ya fad'a aikuwa arud'e ta d'ago tana girgiza mashi kai alamar a'a, ya lura da razanar da tayi da jin abunda yace hakan yasashi tambayarta dalilin k'in bin nasu, farko shiru tayi sai kuma ta tuna da baison maimaita Magana hakan yasa kaman zatayi kuka ta fad'a mashi yarda sukae da Gwaggo harda rantsuwar da tayi na daga can tana dawowa sai Yola, shiru yay yana nazarin Maganar tabbas bai kamata ya gifta rantsuwar da tayi ba don yasan tana da dalilin hakan wanda bai wuce k'ok'arin da take yi na saita Fatun,

"Owk tunda ta rantse shikenan ba sai kin bimu ba but ki daina damuwa kan yawon sallan zan sa akai ki duk inda kike so in ma ta hana i will talk to her" d'agowa tai ta kalleshi ya d'age mata gira "are u Happy now?" jinjina mashi kai tayi alamar eh,
"To baki smile ba" ya fad'a fuskarshi a sake, da bud'ar bakinta sai cewa tayi "dama ina wannan ne?" wato abunda yace mata rannan itama ta fad'i mashi aikuwa ya jefo mata throw pillow yana fad'in kin raina ni da yawa Zaraah, duk'ewa tayi tana dariya hakan kuma ba k'aramin dad'i yay mashi ba don shi sam bai son yaga Mutum na k'unci duk sai yaji ya damu shiyasa in dae yana da iko yin yadda zai sa Mutum farinciki sai yayi, shiru su kai na wani lokaci can ta kalleshi idonshi akan tv,
"Naga an kawo man dinkin jiya" kai ya daga ba tare da ya kalleta ba,
"Nagode"
jinjina mata kai yay sai lokacin ya kalleta tana ta wasa da yatsun hannunta,
"Baki yin kunshi ne da salla" taji ya fad'a,
Turo baki tay "da gwaggo ke yi man irin na hausa nan da ake d'ansa Salatef ni kuma yanzu banson tayi man irinshi nafi son irin wanda ake yayi a yayyanka salatef d'in ayi design mai kyau da kuma bak'i da ake zanawa" ta k'arasa tana kwatanta mashi wanda take nufi a hannunta, d'aga mata kai yay alamar ya fahimta ya maida idonshi kan tv, bayan wani d'an lokaci ya d'auki wayarshi yai dialing kira ya karata a kunne, wadda ya ta6a kira mai suna Nana lokacin da zai kaita saloon ita ya k'ara kira, yar wurin aikinsu ce zatayi tsararshi sai dae bata yi aure ba har yanzu amman ba zaune take ba tana ta aikinta da bussiness kuma tana jiran Allah ya kawo mijin (da duk masu neman mijin aure Allah Ubangiji ka albarkace su da mazaje na gari masu wadatar zuci wadanda zasu sosu su kuma ruke su saboda Allah ba don wani abu ba haka ma mazan, masu aure kuma ka kara zaunar damu lafiya da mazajenmu ka k'ara rufa mana asiri ka Albarkaci zuri'armu, Amin ya hayyu ya kayyum, ban mance da masu neman haihuwa ba Allah ubangijin samai da kasai mai ikon akan komae wanda da yace kun faya kun (kasance sai ya kasance (wani al'amari) ka albarkace su da samun zuria d'ayyiba Amin),

suna mugun yin good time dashi dama kuma ita d'in yar barkwanci ce tana d'aya daga cikin Mutanen da ke sashi dariya ba tare daya shirya yin ba, kai tsaye take fad'i mashi itafa Mugun sonshi take ya taimaka mata ya shige da ita mana wato ya aureta, bayan ta d'aga kiran sun gaisa yace yana son ai ma Sister nashi henna ne tace ba matsala in zai yuwu ya kawota gidansu da safe mai kunshi zata zo yi masu sai ayi mata, amsa mata yay da owk daga haka yai rejecting call d'in, kallon Fatuu yay da ta k'ura mashi ido bayan ya aje wayar yace ta tambayi Grandma d'inta zai kaita k'unshi gobe da safe around 10 tace to, mik'ewa yay yace mata yana jin bacci ta d'aga mashi kai ya nufi Bedroom dinshi ita kuma ta koma kan kujera ta d'auki remote ta canja channel zuwa Bollywood ta kishingida tana yin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login