Showing 177001 words to 180000 words out of 212491 words

Chapter 60 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

997

kallo itama kallonshi take tana Murmushi, d'aga kai yay ya kalli haisam yace "Wannan yar k'aramar ce mamanka?" kai ya d'aga mashi alamar eh da mamaki ya k'ara kallon fatun sai kuma yace "kodae matarka ce baba zakee" gaba d'aya suka sa dariya Abbas yace "wato tayi k'arama ta zama mamanshi kenan saidai matarshi ko, to sister d'inshi ce" dariya Abdul d'in yayi yace "kenan yayata ce ita?"
"Mamanka dae" Abbas ya bashi amsa, cike da rashin yarda yace "kam ni ba mamata bace wannan yar karamar ga mamata nan babba" Feenah dake dariya tace "zata iya zama mamanka mana,ba Hafsa mamanka bace itama kuma ai yar k'aramace ko" turo baki yay yace "ai ita mamata ce ta k'arya ko wannan ma ta k'arya ce?" ya tambaya yana nuna Fatuu, girgiza kai Abbas yayi yana dariya yace "No ka barta a yayar taka dai" mik'ewa Feenah tayi ta kawo masu abun sha ta zuba ma kowa kafin ta koma ta zauna suka shiga yar hira harda Haisam d'in, tambayar Abbas tayi ko a shirya table yace no ta bari sai sun dawo salla tunda lokaci ya kusa tace to, juyawa tayi ta kalli Fatuu dake ta faman binsu da ido bata cewa komae tace "wai dama Mom Zarah bata magana ne?" d'aga ido haisam yay ya kalli Fatun suka hada ido tayi Murmushi Abbas yace "Magana kai,kawae dai k'ilan bakunta take maki ne"
tace "Ah Mom Zarah kada muyi haka dake gaskiya,inata murna za'a kawo man ke musha fira kuma sai kizo ki man shiru alhalin kina magana" hannu tasa ta rufe bakinta tana dariya jin abunda Feenah din tace,
"Ba dariya zaki man ba bud'a baki zaki muyi fira" cire hannun tayi ta amsa mata da to, saukkowa Abdul yay daga kan cinyar Haisam yaje gaban fatuu yace "zo muje dakina kiga Computer d'ina da Baba zakee ya siyo man a k'asan waje" amsa mashi tayi da to ta mik'e zata bishi Feenah tace ta cire Abayar mana ta sha iska, sa6ule rigan tayi ta daurata kan kujera harda gyalen rigar ta bi bayanshi suka nufi wani Corridor, bin ta da ido sukae gaba d'aya har ta shige kafin Feenah ta juyo suka had'a ido da Abbas tayi dan Murmushi kawae don shima Murmushin yake yi, basu jima ba suka fito Fatuu na ruk'e da computer d'in Abdul na biye da ita, akan carpet ta ajeta duk suka zauna suka cigaba da yin game d'in da suka fara yi anan Feenah ta fara jin muryarta wurin yin gardama da Abdul sai kace wani tsaranta sudae dariya kawae suke yi masu, bayan wani lokaci ta fita daga game din ta shiga wani app na koyon karatu nan ta fara koya mashi da turanci sosae ta burge su Abbas don daga yadda take koya mashin zaka fahimci tana da k'ok'ari da abun ya nisa ma duk sai suka kwanta akan carpet, kiran sallan da aka fara ne yasa Abbas da Haisam mik'ewa don zuwa masallaci Haisam yace ma Abdul ya taso suje suyi salla,mik'ewa yay yana cema Fatun sai sun dawo ta d'aga hannu tana yi masu bye bye, bayan sun fita itama Feenah mik'ewa tayi tace ma Fatuu ta taso suje suma suyi sallar ta amsa mata da to, atare suka nufi Bedroom dinta taba Fatun hula tace ta rufe kanta kafin ta nuna mata toilet tace ta shiga tayo Alwala ita kuma ta nufi d'akin Abbas ta d'auro Alwalar, atare sukayi sallar suna gamawa Fatuu ta koma Falo ta cigaba da abunda take ita kuma Feenah tana fitowa Kitchen ta nufa don shirya abinci kan Table, Fatuu na hangota tana fitowa da kayan abinci ta mik'e taje tace bari ta taya ta suka cigaba da shirya table d'in suna cikin yi su Haisam suka dawo Abbas na hangota ya d'an d'aga murya yace "Mom Zarah an saki jiki kenan har ana taya Feenah aiki" ya yi Maganar yana dariya Feenah tace "aikuwa dae ta zama yar gida dama haka yakamata ai" Abbas d'in yace gaskiya yayin da yake zama kan kujera, bayan sun gama Feenah tace su taso table yazama ready Abdul ya fara rugowa ya zauna kusa da Fatuu don ita tuni ta zauna, atare suka nufo Dining area d'in da Haisam kowa yaja kujera ya zauna Feenah ta hau serving nasu bayan ta gama Abdul yace "kowa yayi Addu'a kada yaci da shedan" gaba d'aya suka jinjina kai suna dariya, a nutse suka fara cin abincin baka jin komae sai k'arar cokulla hankali kwance Fatuu ke tura abinci har ta k'ara abunda bai yi mata ba, Haisam ne ya fara mik'ewa alamar ya koshi Feenah ta d'aga kai ta kalleshi tace"badai wai har ka koshi ba?" kai ya d'aga mata alamar eh,
tace"amman fa baka ci wani na kirki ba, har yanzu dae kana nan da rashin cin Abincin ka kenan" d'an Murmushi yay ba tare daya ce komae ba ya fara kokarin barin wurin Abbas dake kallonshi yace "ki rabu dashi lokaci na zuwa da zai rink'a ci hannu baka hannu kwarya in har yana son samun kuzarin yin noma yadda ya kamata" shiru bai tanka mashi ba bai kuma kalleshi ba yabar wurin amman sarae yaji abunda yace ita kuwa Feenah d'an runtse ido tayi ta sadda kanta k'asa alamar kunya, kusan atare suka gama Abbas ya nufi parlor Feenah kuma ta fara clearing wurin tana cikin kwashe kayan abincin da su Abbas sukae amfani Fatuu ta mik'e alamar itama ta gama ta tambayeta ta tabbatar ta koshi tace mata eh, tayata gyara wurin tayi kafin ta nufi parlor wurin Abdul suka ci gaba da abunda suke a Computer dinshi su kuma su Haisam suna kallo a tv, duba agogo yayi ganin ukku tayi yace ma Abbas suje gidan Najeeb ya amsa masa da ok duk suka mik'e a tare har zasu nufi hanyar fita yace ma haisam "bazamu je da Mom zarah ba su gaisa" shiru yay mashi kaman bai jishi ba har saida ya k'ara Magana sannan ya amsa masa da No kawae daga haka ya fuce,dariya Abbas yayi dama tsokana ce yasa yayi mashi Maganar Fatun, saida ya lek'a Bedroom ya sanar ma feenah zasu je su dawo tayi mashi Allah ya tsare sannan ya dawo falon su Fatuu dai gaba d'aya hankalinsu na akan abunda suke hakan yasa ya fuce kawae. Bayan tafiyarsu ne Feenah ta fito tayi wanka ta canja kaya zuwa doguwar rigar Material ta zauna tana kallon abunda su Fatuu keyi in sukae abun dariya tayi in kuma wani yai gwaninta ta tafa mashi haka in suna gardama sai ta rabasu sosae ta saki jikinta daga baya ta koma kan kujera suka shiga yin fira da Feenah har sata tayi ta rink'a yi mata fullanci ta kuma bata labarin garinsu,

Lokacin da su Abbas suka k'arasa gidan Najeeb dake a Gra wanda katon gidane na gaske, sosae yay farinciki da zuwan nasu haka ma Matarshi Sofeeyat wadda irin matan nan ne da suka waye over tana da kyau daidai gwargwado kuma tana da haske saidae kana gani kasan hasken harda na kanti, taci gayu cikin k'ananan kaya wando da riga sun kamata hakan ya bayyanar da d'an dirin dake gareta, kanta anyi mata kitson k'arin gashi miri miri amman yay kyau sosae ta d'aura bak'in veil ta zameshi daga gaban yadda kitson ya fito sosae haka k'umbunanta an k'ara mata dana kanti shima Najeeb d'in yana sanye da kayan shan iska armless da wando 3 quarter,suna shiga cikin tangamemen falon wanda yake shak'e da kayan alatu suka zauna asaman d'uma d'uman sofas d'in dake kewaye acikinsa set biyu, zama itama soffyn tayi tana facing d'insu cike da kisisina ta shiga gaidasu idonta akan Haisam amman Abbas ne kawae ya kalleta shikam Haisam bai ko kalleta ba ya amsa mata a takaice,
"H,zakee manyan gari ashe ka dawo nan da aiki rannan My ke gayaman" ta fad'a cike da salo, shiru bai ce mata komae ba da alamu ma bai jita bane don ya sadda kanshi yana danna wayansa, d'an ta6a shi Abbas yay yace mashi ana magana sannan ya d'ago ya kalleshi kafin yace wani abu ta k'ara cewa "da alama ta janye mashi hankali ne" kallonta ya d'anyi da d'an Murmushi ba tare daya ce wani abu ba, Najeeb ne yace tasa akawo masu drinks mana tace dama yanzu zata sa ta bari su gama gaisawa ne, mai aikinta ta fara kwalama kira "Murja,Murja" ta kirata har sau biyu sannan ta fito yar dattijuwar mata ce in a auren k'auye mane zata haifeta,
"Baki ji anyi baki bane" ta fad'a ta d'aure fuska had'i da d'aura kafa d'aya kan daya, murya na rawa Murjar tace "ayi man afuwa Hajiya ina can ciki ne banji shigowarsu ba" shiru ta d'anyi kafin cike da bada umarni tace taje ta kawo masu abun sha kuma ta shirya abinci akan table Abbas na jin hakan yace "adai bamu abun shan amman abincin dae abarshi basai an shirya ba....." katseshi Najeeb yay "kana nufin bazaku ci abincin gidana ba?" yar dariya yayi yace "ba haka bane kaima kasan by dis time mutum yaci lunch so duk a k'oshe muke" d'an ta6e baki yayi baice mashi komae ba adaidai lokacin murja ta karaso ruk'e da babban tray ta d'auro bottle water da drinks da glass cups, daurashi tayi kan c-table kafin ta kinkimeshi da k'yar don murtukeke ne ta matsar masu dashi gabansu, tana shirin juyawa ta tafi aikuwa soffy ta daka mata tsawa tace "wai ke dak'ik'iyan inane,da kika aje masu waye bawanki da zai zuba masu?" har saida ta d'an tsorata jiki na kerma ta hau bata hakuri ta juya zata zuba masu Abbas yace ta barshi zasu zuba shidae haisam baima d'ago ba balle ya kallesu saidae yaji tsawar da tayi matan har cikin ranshi don ya tsani wulak'anta dan'adam don shi a wurinshi duk d'aya muke,tsaye Murjar tayi tana binta da ido ta kasa tafiya ita kuma Soffyn taba banza ajiyarta sai juya k'afa take tana wani shan kamshi, a hankali Haisam yay ma soffyn kallon kasan ido cikin sa'a suka had'a ido don dama bunu bunu sai ta kalleshi, ganin kallon da yayi mata ne yasa tasha jini jinkinta ta kalli murjar tace taje amman karta shirya table d'in ta kawo masu abunda zasu ta6a ta amsa da to harda dan rissinawa tayi mata godiya soffyn ta d'aga mata kai kafin ta juya ta tafi, bada jimawa ba ta dawo d'auke da wani hadaddan trayn ta d'auro plates d'in soyayyan naman kaza da kuma na snacks ta aje masu gefe tayi masu aci lafiya gaba daya harda haisam suka d'aga mata kai, fira suka shiga yi ganin haisam bai ta6a komae ba yasa Soffy yunk'urawa tana fad'in "kunsan fa H,zakee saraki ne bari nai serving nashi" dakatar da ita yayi ta hanyar d'aga mata hannu kafin yace ba yanzu zai ci ba, bata san shi k'yamar k'umbunan hannunta ma yake ba, tana zama wayanta ya fara ringing alamar ana kiranta mik'ewa tayi tace masu "excuse me" Abbas ne ya d'aga mata kai ta nufi ciki tana wani karairaiya jiki ba kunya ba tsoron Allah, suna cikin hiran Najeeb ya kalli Haisam yace "H,zakee ina Mom d'inka bafullatana?? Kafin ya bashi amsa cike da tsokana Abbas yace "aikuwa kasan tana gidana ya kawota da har nace mashi mu taho tare ku gaisa" Najeeb yace "halan yak'i ko?" dariya Abbas d'in yasa yace "nidae ai baka ji na fad'i haka ba" d'an ta6e baki kawae yay baice komae ba, hira suka cigaba da yi har aka kira sallar la'asar sukaje masallaci suka yo salla suna dawowa suka ce bazasu shiga ciki ba zasu je wurin Saleem ne Najeeb na jin haka yace su jira su tafi tare ya nufi cikin gidan yana fad'in bazasu yi sallama da soffy ba Abbas yace ya gaya mata sun wuce, bayan wani lokaci ya fito sanye cikin jeans da t-shirt hannunshi ruke da wayarshi yasa bak'in glass ya fito a d'an madararshi, yana k'arasawa wurunsu suka shiga cikin Motar suka fuce, Bayan sunje har wurin Mahaifiyar Saleem d'in sukaje suka gaidata kafin suka shiga part d'inshi sai karfe biyar da wani abu suka baro wurin Saleem d'in Abbas ya tambayi Najeeb gida zasuyi dropping nashi ne dayake shi ke tuk'a Motar Haisam na gefenshi sai Najeeb d'in a baya, ce mashi yay su wuce gidanshi ya gaisa da Feenah, Murmushi kawae Abbas yayi don yasan ba wata Feenah kawae Zarah yake son gani, lokacin da suka isa bakin gate d'in gidan Abbas d'inne ya fita ya bud'e gate kafin ya dawo cikin Motar ya kutsa cikin gidan, suna shiga ciki daidai lokacin Abdul ya fito da gudu sai kuma ga Fatuu ta biyo bayanshi da gudu gaba d'aya gashinta a tarwatse ya zubo mata gefe gefe da kuma bayanta, tun kafin su tsaya Najeeb ya zuba mata idanu, suna yin parking suka firfito da gudu Abdul ya nufi bayan Haisam ya 6oye yana fad'in "Baba zakee kaga Aunty Zarah zata bugeni" d'agowa yay ya kalleta tayi tsaye agabanshi ba damar ta kamo Abdul d'in cikin cool voice d'inshi ya tambayi abunda yayi mata tana tura baki tace "ba game mukeyi ba duk wanda yay winning ya bugi mutum tun d'azun nike cinyeshi amman sai yak'i bari in bugeshi kuma ni da shi yay winning na tsaya ya bugeni har ma ya cire man ribbom" still yay yana kallonta Abbas kuma sai dariya yake Najeeb ma murmushi yake don ba k'aramin burgeshi take ba ba kaman yadda ya ganta a yanzu gashi tana Magana cike da sangarta,
"Baki ga yaro ne ba kiyi hakuri" Haisam ya fad'a, tura mashi baki tayi alamar bata yi hakurin ba, ruk'o hannun Abdul d'in yayi ya dawo dashi gaba yace mashi "Say sorry to her" da sauri yace "Aunty Zarah Sorry" yayi Maganar yana dariya, harararshi tayi kawae haisam yace taje ta d'aukko Abaya dinta su tafi tace to, tana shirin juyawa Najeeb yace "yar bafullatana ba gaisuwa" dakatawa tayi ta juya ta kalleshi sai lokacin kuma tama ganshi don da duk bata lura dashi ba,ganin yana mata Murmushi yasa itama tayi mashi don ta ganeshi ta gaidashi ya amsa mata bayan ya cire glass d'in fuskarshi, nufar cikin gidan tayi Abdul yabi bayanta yana tambayarta tafiya zata yi tace mashi ehh, bada jimawa ba ta fito Feenah da Abdul na biye da ita suka k'araso wurin Motar, gaida Najeeb Feenah tayi tana cewa shine yazo gidan amman bazai shiga su gaisa ba Abbas yace kuma dama wurinta yace zai zo Najeeb d'in yace to yaga ya tafi bai shigan bane ita dae dariya kawae tayi ta mik'a ma Fatuu yar babbar ledar data ruk'o a hannunta, amsa tayi ta lek'a ciki kafin tasa hannu ta fiddo wani Material mai kyau tare da veil d'inshi can k'asa kuma kayan shafa ne wai sai ta rungume Material d'in ta mik'a mata ledar kayan shafan tace "Aunty Feenah ki bar wad'annan na d'auki wannan" d'an waro ido Feenah tayi tace "saboda me ki tafi dasu duka" tace "ai inada su da yawa Ya Handsome yana siya man" kafin tace wani abu Abbas ya riga cewa"ai na Ya Handsome daban wannan daban Mom Zarah don haka ki tafi dasu" kallon Abbas d'in tayi kafin ta kalli haisam ta d'age gira tace "in tafi dasu??" har saida tasa ya d'anyi murmushi yadda tayi mashi tambayar, ganin tayi mashi tsuru tana jiran amsa kuma kowa shi yake kallo yasa ya d'aga mata kai alamar eh, maida Material d'in tayi tace mata ta gode ta nufi Motar da sauri Abdul ya nufi Haisam yace "Baba zakee zaka k'ara kawo man ita?" kai ya d'aga mashi alamar eh ya juya gun Fatun ya kama hannunta yana tambayarta yaushe zata dawo tace sai Ya Handsome ya kara kawota daga haka ta nufi gaban Motan zata shiga Najeeb yace ta shiga baya zasu tafi tare tace to ta shiga bayan shi kuma ya shiga gaban Haisam ya zagaya side din driver ya shiga, lek'awa Abbas yay yana yi masu sallama yace ma Najeeb sai sunzo rakiya Airport, tada Motar yay su Feenah nayi ma Fatuu bye baye Abdul kamar zaiyi kuka suka fuce daga gidan........



ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,

ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUH📲*_
~(Oumm Imam)~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


*6️⃣6️⃣*

......Suna komawa cikin parlon Abbas ya fad'a kan 3 seater Abdul ma ya haye saman jikinshi yana mai rigimar shidae adawo mashi da Aunty Zarah d'inshi Abbas d'in ya shiga rarrashinshi yana ce mashi zata k'ara zuwa, zama Feenah tayi gefenshi tana dariya kafin tace "kasan mi Dear?" girgiza mata kai yay alamar aa, tace"wllh ni kaina yarinyar ta shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login