Showing 21001 words to 24000 words out of 212491 words

Chapter 8 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

955

da ita ya zauna yad'an kwantar da kanshi yana sauraren k'ira'ar ta a cikin suratul kahf,bai jima da shiga ba ta kammala,d'aga hannuwa tayi tana Addu'a lokaci guda suka shafa ita da Haisam wanda ya d'ago yana kallon ta da murmushi a fuskarsa bud'e baki tayi zatayi magana... ya rigata da cewa "Na karanta a Office" gaba d'aya sukai daria tace "wato har kasan abunda zan tambaya kenan" yace "yeah" d'an ta6e baki tayi tace "ai kwadayin falalar nike maka shiyasa nike tambayar ko ka karantan" "I knew" yace, hajiya taci gaba"To ya wurin aikin,Amman kad'an jima baka dawo ba don har nayi tunanin ko acan zakai sallan juma'ar" shiru yayi ya koma ya d'an jingina yana tuna abunda Fatuu tayi mashi,hajiya ta lura da yadda yanayinsa ya canja da sauri tace"lafia dai ko?? d'agowa yayi ya kalleta yace "Yes,kawai motan ce ta samu matsala",
"Wace irin matsala kuma" Hajia ta tambaya da yar damuwa a fuskarta,shiru Haisam yayi baima san mizai ce mata ba,don shi kunya ma yake ji yace wai wata yarinya ta jefar masa mota har ta fasa glass,kuma yasan in har ya fad'i mata abunda ya faru tabbas bazata bari ba sai taje gidan su yarinyar ko ta aika a taho mata da iyayen yarinyar ma don Hajia tana da kirki amman akwae fad'a ba kamar kuma kan abunda ya shafi d'an lelenta Haisam tabbas bazata bari ba,duk da bawai don a biya ba,so bai ma son abun yazama wani big issue,don shi a tunaninsa yarinyar is Abnormal don abubuwan nata sun wuce hankali "Kayi shiru" hajia ta katse shi,d'agowa yayi da d'an murmushi yace"bafa wata babban matsala bace kawai it was faulty lokacin da zan dawo,amman nasamu na k'araso tana waje and I called Iro zai zo ya tafi da ita" sauke numfashi mai karfi hajia tayi don tayi tunanin ko had'ari yayi duk da ta ganshi lafia lau,tace"K'arfen nasara ba tabbas,duka yaushe Iron yazo yayi masu service da ka dawo" d'an ta6e baki Haisam yayi yace "ko kuma ba'a so na ara ba" wani irin kallo hajia tayi masa tace "Eh din,ai kaima kana da taka bama daya ba,karka k'ara daukar man tawa" gaba d'aya sukai daria a daidai lokacin kuma aka fara hud'ubar hausa bayan angama ta larabci a Masallacin gidan,da sauri Hajia ta mik'e tana fad'in kai yau dai mun taushe hannu wallahi,na dawo a gajiye bacci yai awon gaba dani....."ba kince yau ba zaki Aiki ba?" Haisam ya tambaya,"Eh wani abu ne ya taso dole naje, amman ba wani dad'ewa nayi ba don ko tafiya ban bar T.k yayi ba 11:30 muka dawo" ta k'arasa maganar lokacin har yayi gaba ita kuma ta fara kwala ma saude kira"Saude,Saude" fitowa Sauden tayi tana amsawa jikin ta sanye da dogowar hijab brown,hajia tace"Yauwa to mutafi" Saude ta juya tana gaida Haisam wanda ke k'okarin fucewa ya amsa ba tare daya juyo ba suma suka rufa masa baya.

Jin an tada sallar juma'a yasa Fatuu lek'owa daga inda ta 6uya,wani gini ne wanda ba'a ida ba,cikin sauri take tafiya tana yi tana waiwayen bayanta kaman zata tashi sama har Lokacin hijabinta na d'aure a k'ugu ga kanta da yayi wani tum da gani kan a tsefe yake duk tayi bud'u bud'u saboda tumurmusar da suka yi a k'asa ita da murja,ta cikin lungun dake tsakanin gidan hajia da nasu ta 6ullo,tsayawa tayi bakin lungun tana lek'en kofar gidansu wanda yake wayam ba kowa shagon kawu Amadu ma a rufe yake don shima yaje makaranta kuma bai dawo ba dama gashi yau juma'a daga can kasuwa yake wucewa ko lokacin da su Fatuu ke yin fad'a sai da wasu yara suka zo kawo sheda suka tarar gidan a rufe.
Ganin ba kowa yasata fitowa daga cikin lungun da sauri ta shige gidan farko wanda daga shi sai nasu har tana yin tuntu6e wurin shiga,a cikin zauren gidan taci karo da wani yaro ya fito da sauri da sallaya a hannunsa,tace "kai Umar je ka amso man makulli" yaron yace "kije ki kar6a man nifa sauri nike masallaci zani kuma har an fara...." tsawa ta daka mashi tace" dalla je ka amso man ba yanzu aka fara sallar ba ta d'aure fuska tana harararsa" juyawa yaron yayi rai 6ace yaje ya amso mata makullin don yasan mi zai biyo baya in bai amso ba,
Da sauri ta bud'e gidansu ta shige ta maida kofar ta rufe had'i da sa sakata.

Ita kuwa Murja bayan Mutumin ya kaita Chemist,aka duba ta ba wani rauni mai yawa bane ha6o ne tayi a hanci saboda bugun hancin da Fatuu tayi sai le6enta na k'asa daya fashe aka yi mata dressing sannan aka bata magani pain reliever,duka ko d'ari biyar dinma ba'a kashe ba,bayan sun fito daga Chemist din Mutumin ya bata naira dubu yace gashi itama ta rik'e,sannan yayi mata nasiha sosai kan rashin dacewar suna ya'ya mata su rink'a yin fad'a haka, ya kuma roketa da tayi hakuri kar tace zata d'auki fansa,kuma ko taje gida kar ta fad'i don ita fitina a kwance take Allah kuma ya La'anci mai tado ta,Murja ta tabbatar mashi da tayi hakuri bazata k'ara yin fad'a da ita ba,Ya k'ara mata naira d'ari yace ta hau mashin ya k'arasa da ita shi kuma ya tura nashi ya tafi yasha mai,bayan ya tafi ta kama hanya k'asa bata hau mashin d'in ba tana ta farin ciki ta samu Naira dubu harda d'ari daya a fili tace"Ko ba komae na rage zafi,wannan mahaukaciyar yarinyar wama zai k'ara fad'a da ita".

Bayan angama Sallah Hajiya suka fito daga 6angaren da mata ke yin sallah nan da nan mutane suka kewayeta ana ta kwasar gaisuwa,har d'an rankwafawa wasu keyi in zasu gaidatan,Saude na tsaye a gefe,Haisam ne ya k'araso wurin, ganin yadda hajiyan keta gaisawa da mutane yaji bazai iya jiranta ba ya wuce,Part d'inta ya koma ya kishingid'a saman 3-seater bayan ya cire hular kansa dama duk ta damesa don in yasa dinki irin wannan bai cika sa hula ba,yau ma don yana friday inma baisa ba,hajiya zata matsa masa ne dole sai ya sa,
Sai bayan wani dan lokaci su Hajiyan suka shigo,tana shigowa Parlon ta fara kokarin cire jalbabar jikinta tana fad'in "Alhamdulillah,Allah ka nuna mana wata juma'ar cikin k'oshin lpy" Saude ta ce "Amin" ta mik'a ma Saude jalbabar, jikinta na sanye da doguwar riga cotton mai gajeren hannu gaban rigan anmashi wata irin sak'a mai kyau har zuwa k'asa kanta daure da kallabin rigar,ta idasa shigewa cikin parlorn ta zauna kujerar dake kallon wadda Haisam yake kwance yasa pillow a bayansa ya d'an d'ago yana kallon T.V tace "Shine ka k'i jira na mu dawo tare kaman yadda muka tafi a tare" tayi maganar tana cire glass din fuskarta ta aje a saman hannun kujera,d'an murmushi yayi ba tare da ya juyo ba yace"Ina zan iya tsayawa ki gama da wannan mutanen da sukai circling d'inki sai kace kece Senator din" ya karasa maganar da sigar tsokana,daria sosae hajia tayi tace ai ni nafi Senatorn tunda ni na haife sa..." Saude ce ta k'araso ta cire hijab d'in jikinta sanye da riga da zani na atampa tsaf tsaf da ita ta d'an dafa kujera tace"Hajia na gama jera Abincin" hajiya tace "to sannu" daga haka Sauden ta juya,Hajia ta kalli Haisam tace "Oya Food is ready,tashi muje" sai lokacin ya kalleta yace "kije zanzo" harararsa tayi tace "Zaka tashi ko kuwa" hannu ya mik'o mata,tace"mi kenan? Yace "ki dauke ni tunda dole sai tare zamu" kama hannun tayi tana k'okarin kado shi k'asa da iya karfinta,ganin haka yasa haisam janyo hannun da karfi sai gata ta fad'o saman shi gaba d'aya suka sa daria a tare suka mik'e yana fad'in "tsohuwa ba k'arfi".
Dining area d'in suka nufa a tare suka zauna bayan kowannansu ya wanke hannunsa a Handbasin d'in da ke gefe,Saude dake tsaye bakin k'ofan kitchen tana dariyar yadda Haisam yaja hajiyar dama kuma sun saba,ta k'araso don yin serving d'insu,wasu Luxury warmers ne guda ukku kai da gani kasan zasu yi kudi ba sai an fad'a ba,Milk color ne,yayin da handle d'insu da kasan su da saman marfin inda za'a juya a bud'e akayi masu wani irin design mai kyau golden,K'atuwar ta fara bud'ewa wadda cikinta ke d'auke da tuwan shinkafa da kuma sakwara kowanne a gefe guda sunyi fari tas an nad'e su da faran leda gwanin burgewa, Plate ta janyo zata fara zuba ma hajia ta dakatar da ita da fad'in "Zuba mashi" "to" Saude ta amsa,wani plate din ta ciro ta warware tuwo guda ta d'aura,ta d'aukko sakwara zata bud'e Haisam yace"Wannan ya isa..." Hajia dake kallonshi tace "Pounded yam ce fa,kuma nasan kana sonta" Shiru yad'an yi yana tunanin anya zai iya cinye su,gashi yana d'an son abinci swallow,ganin haka yasa hajia cewa saka mashi "To" Saude tace,ta saka masa sakwarar sannan ta bud'e warmer ta biyu wadda ke d'auke da had'addiyar miyar Egusi wadda taji ganda da kifi tarwad'a tayi kauri kitif ta d'aukko plate mai gida biyu ta zuba miyar a gidan farko sannan ta bude warmer ta ukku wadda ke dauke da Liver pate wato miyar hanta wadda itace ta sakwarar duk da za'a iya ci da ta agushin ma,ta zuba mashi a dayan 6arin plate din ta turo plate d'in gaban shi tace "gashi" Alamu yayi mata da taba shi cokali da hanzari ta ciro cokalin had'i da fork don in zai d'auko nama ta saka masa a plate d'in tuwon,ta janyo wani Glass jug mai kyau cikinsa d'auke da Kunun Aya fari k'al mai kauri tana k'okarin zuba masa a glass cup ya dakatar da ita da fad'in "Let me finish" hajia tace ni zubo man,tayi maganar bakinta cike da Abinci don tuni tayi serving kanta bata jira Sauden ba,"to,saude tace ta cika mata cup da kunun ayar ta tura a gabanta,juyawa saude tayi ta nufi freezer wani d'an babban Acryclic bowl ta fiddo mai marfi d'auke da fruit salad ta aje masu ta koma ta daukko bottled water shima ta kawo masu tace"Aci lpy" hajia ce ta amsa da"Allah yasa" har Saude ta juya zata tafi hajia ta tsaida ta da fad'in "Kin dai zuba naki ko,nasan ki da duminiya" murmushi Saude tayi tace "na zuba hajia, "to kin zuba nasu Officer?" Saude tace"Eh yanzu zan kai masu" d'aga kai hajia tayi sai kuma ta cigaba"Wai ni ina T.k ne ko a masallaci fa ban ganshi ba,ban kuma ga yazo ya d'auki Abinci ba...kafin Saude tace wani abu T.k d'in ya shigo da sallama sanye da dogayen kayan yadi ya nufi dining d'in ya tsaya daga gefe yana gaida hajia,tace "Ina ka shige ne wai tunda muka dawo ban k'ara saka a ido na ba ko a masallaci ma ban ganka ba" T.k yace "nad'an lek'a makaranta ne acan nayi sallah",
"Au dama zaka makarantar baka gaya mun ba muka fita?" d'an murmushi T.k yayi yace "Ai dama duka lectures biyu gare ni yau,kuma Lecturer d'in safen yace bazai samu zuwa ba,ta biyun ce naje" cikin girmamawa yake maganar,hajia tace "Amman duk da haka dai ka makara gaskia,sai fa 11:30 muka dawo,kuma har kayi wanka sannan ka tafi, wace lecture kasamu,ka je dai yawo kawai" ta tura ganda a bakinta,
T.k yace "dama dai attendance nike son inje insamu kuma na samu nayi" tace"duk da haka daga yau in kasan zaka makaranta na bukaci mu fita ka gaya man sai insa Officer ya kaini,amman banso kana wasa da karatu sam" T.k yace "In sha Allah" sannan ya maida kallon shi kan Haisam wanda duk maganganun da suke ko kallon su baiyi ba,yace "Yaya Haisam barka da juma'a" hannu haisam d'in ya d'aga masa saboda akwae abinci a bakinsa daga haka ya wuce kitchen don amsar Abincinsa.

Ajiyar zuciya Haisam yayi wanda ya kusa cinye abincin saura tuwo d'an kadan a cikin plate din,ya yago tissue acikin kwalinta dake saman table din yana k'okarin goge bakinsa, d'an tura kujerar yayi baya yad'an kwantar da kansa Hajia ta d'ago tana kallonsa tace "Sai kace wanda yake wani uban aiki,to wannan guntun da ka rage fa? ai dai ba wani ya matsa maka cin biyun ba kai ka ga zaka iya don haka sai ka idasa cinyewa" d'an ta6e baki yayi yace "dama nasan sai kin tanka..."da sauri hajia tace "eh d'in,inma bayaga abun ka wannan guntun ai shine Albarkar" d'agowa yayi ya kalleta da d'an murmushi yace "kika sani ko yau ma wani zan samu ya idasa man shi...."da sauri Hajia ta d'aukko wuk'ar yanka bread daga cikin cutlery set din dake saman table din tace "Bismillah" daria sosae haisam yake yi yace "Wannan abun fa da kika rik'e? tace "na kare kai ne" gaba d'aya suka sa daria,Hajia tace "don Allah idasa mana",dan lumshe ido yayi yace "Owk tunda kince Allah,amman fa na koshi in cikina ya fashe you will see the consequences" yayi maganar yana jaddada mata da spoon d'in da ya d'auka,tace "Eh naji" ta jawo Jug din kunun ayar ta cika mashi cup ta tura gaban shi.

Mik'ewa yayi bayan ya idasa cinyewa ya d'au cup d'in kunun ayar ya nufi cikin parlon hajia na fadin "Fruit salad d'in fa? Hannun da ba komai ya d'ago mata ba tare da ya juyo ba yace "bansan ina zan sa shi ba" ya idasa shiga cikin parlon ya kishingid'a saman kujera 2 seater yana d'an kurbar kunun ayar yana kallon T.V,bayan wani dan lokaci itama hajia ta mik'e bayan ta zuba fruit salad din acikin d'an bowl tasa cokali ta nufo cikin parlon tana kwala ma Saude kira,da hanzari sauden ta fito tace "gani hajia" hajia ta juya tace mata"Je ki clearing dining din mungama" "to" Saude tace ta nufi Dining area din ta kwashe duk abubuwan da sukayi amfani ta kai Kitchen banda Warmers d'in Abincin don gidan hajia bai rabuwa da bak'i manyan mutane,ba kamar yau da yake Friday ta tabbatar wasu zasu zo a buk'aci ta basu Abincin,tasa towel ta goge wurin yayi fess kaman ba'a zauna anci Abinci ba.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

*Mallakin*
⬇️
*ZAINAB LALUH*🌹
*(Oummu imam)*

*Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp banda phone call,Thanks🤝*


*Free page1️⃣4️⃣&1️⃣5️⃣*


Saman kujerar dake opposite da wadda Haisam ke kishingid'e hajia ta zauna tana shan fruit salad d'in da ta d'ebo tana yi tana kallon American film din da Haisam d'in ke kallo,
"Dad called me when I was in office" Haisam yace ba tare da ya kalli Hajiyar ba,d'an ta6e baki tayi tace"Ai nima dai ya kira ni tunda safe,yayi man barka da juma'a" yar daria Haisam yayi yace "Jealous Old Woman" itama dariyar tayi tace "ai don kasan yafi ji dani" gyad'a kai yayi yace "I knew,shiyasa ma koda ya kira ni maganar ki yayi man" da sauri Hajiya tace "Maganata kuma? Kai ya d'aga alamar Ehh,tace "to wace magana ce da ni bai man ba da ya kirani sai kai zai yi mawa,ko dai gulmata ku ka yi?" ta dakata da shan fruit salad d'in tana kallon shi alamar shi take jira ya bata amsa,
sai lokacin ya juyo da kanshi yana facing d'inta yace "gulma kuma,No kema kinsan baza muyi hakan ba" ya d'an dakata,sai kuma yaci gaba "Ya tambayi yaushe zan kai mashi ke ne" wani irin kallo tayi mashi tace "Ka kaini kuma,da can da nike zuwa lokacin baka k'asar kai ke kaini? Yar daria yayi yace "to ai yaga kin dade baki je bane shi kuma yana son ganin ki" d'an ta6e baki tayi tace "to tunda yana son ganina sai yazo ya ganni,haka itama waccan ta lagos d'in last week ta kira ni tana ce man wai don Allah inje ta na son ta ganni na...." Haisam ya katse ta "Aikine yayi masu yawa they're always busy" hajia tace "To ni ban aikin ne?" murmushi yayi yace "Kina yi amman ai ba kaman su ba,ke You are less busy kuma Aikin naki is voluntary ke kika sa kanki...."katse shi tayi da cewa "Ai dai duk aiki aiki ne" tayi maganar a harzuk'e daria yake yace"ni daman ai baki ji nace aikin ki ba aiki bane Celebrity" da d'an murmushi tace "Ni ce celebrityn? Yace " Yeah,anata son ganinki kina wulakanci" yayi maganar cikin wasa,dariya Hajiya tayi tace "Miye abun wulak'anci don nace duk mai son ganina yazo inda nike" dan ta6e baki yayi yace "I think suna son kije kid'an kwana biyu ne" tace "Ai ina zuwan ko,kawai ni haye-hayen jirgin ne ba so nike ba wllh" ta k'arasa maganar fuskarta dauke da damuwa,ta aje bowl din saman sofa table kusa da cup din kunun ayar da Haisam ya sha ya rage kad'an,Sannan ta maida Kallonta kan hoton Sojan mutumin nan ko kyaftawa ba tayi.

Ganin yadda ta k'ura ma hoton ido yasa Haisam d'an juyar da kanshi shima ya kalli hoton,girgiza kai ya d'an yi ya juyo da duban sa kan Hajiyar yace "Ba lalle silar ajalin ya zama d'aya ba Sweethrt" "I know" hajiya tace,ta kauda kanta gefe har lokacin da damuwa a fuskarta,
"In bakya son hawan jirgin ne ki fad'a ma Dad sai asamo k'wararran Driver da zai rink'a kai ki",
Uhmm tace batare da ta waigo ba,ya cigaba"Ita kuma lagos d'in in zakije sai ki rink'a hawa luxurious Bus...." da sauri ta juyo tace"Waye zaije lagos a Bus?" Yace "Ke mana tunda bakya son hawa jirgin ko" yayi maganar yana dariya,itama Hajia dariyar tayi tace "tabb inje lagos a mota,aikam in na isa saidai k'ilan a kwashe ni a Wheelbarrow" gaba d'aya suka sa dariya "Saboda me? ba bakya son hawa jirgin ba" tace "Eah amman hakan ba yana nufin zan daina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login