Showing 201001 words to 204000 words out of 212491 words

Chapter 68 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

975

"I said leave before i......." tsit tayi bata k'arasa ba sakamakon jin k'arar bud'e kopar Falon Haisam ta d'aga ido ta kalli saitin kopar, shine ya fito cikin shirin zuwa gym bin su yayi da ido yana tunkaro su ya tsaya a yar matattakalar ba tare daya idasa saukkowa k'asan ba, kallon Fatuu data sadda kai yay kafin ya d'ago ya kalli Farha data tamke fuska hakan ya tabbatar mashi da akwae abunda ke faruwa,
What's happening here?" ya tambaya idonshi akan Farhar, shiru tayi ta d'an kauda kai tana tura baki, maida idonshi yay kan Fatuu yace "Zarah" da karyayyar murya ta amsa mashi yace "mike faruwa ne" girgiza mashi kai tayi alamar ba komae sam bai yarda ba ya sake tambayar Farha itama tace ba komae, shiru ya d'anyi yana nazarinsu gaba d'aya, a kausashe yace "Zarah tell me miye ne!" aikuwa kaman tana jira ta fashe da matsanancin kuka wanda daga jin sautinshi zaka fahimci tana cikin bacin rai, d'agowa yay yayi ma Farha kallon tuhuma kafin ya idasa sauka ya tsaya agaban Fatun ya kirata ta amsa yace ta d'ago ta gaya mashi abunda tayi mata, d'agowa tayi idanunta sunyi jawur cikin kuka ta fara fad'i mashi aikuwa tun kafin ta k'arasa ya juya yana ma Farha wani kallo fuska a matukar d'aure yace "Why, Why Farha!" tana tura baki tace "this is not their House so ta tsaya a gidansu mana zatai ta zuwa ma Mutane gida" takaici ne ya turnuke shi har baisan lokacin daya daka mata tsawa ba yace "shut up and leave my sight" wani kallo ta bishi dashi ya kara daka mata tsawa yace "i said leave else i will slap u!" d'an zaro ido tayi da alamun mamaki tace "u will slap me Ya Haisam because of dis pauper?" wani Murmushin takaici yayi ya jinjina kai had'i da maimaita kalmar pauper data kira Fatun da ita kafin yace "then isn't she a human being?" ya tambaya had'i da d'age gira jin tayi mashi shiru yasa ya fara moving inda take yana maimaita abunda yace mata "ki gaya man ita ba Mutum bace saboda talaka ce?" ganin yadda yake Maganar cike da 6acin rai yasa ta fara ja da baya kafin ta juya gaba d'aya ta nufi hanyar fita shi kuma yaja ya tsaya yana kallonta tana zuwa bakin fence door ta tsaya ta juyo tayi mashi wata magana da shi kad'ai yaji mi tace daga haka ta fuce, d'an guntun tsoki yaja jin abunda tace sai yanzu ya gane dalilin da yasa tayi ma Fatun haka juyowa yay ya kalleta ta fara kokarin bi ta gabanshi zata wuce yace mata su shiga ciki, d'agowa tayi ta kalleshi ya jinjina mata kai hakan yasa ta wuce gaba yana bayanta suka shiga cikin Parlon, armchair ya nuna mata yace ta zauna ta zauna sai faman sheshsheka take, wucewa yay ya nufi frigde ya d'aukko lemu fanta da cup ya dawo shima ya zauna akan d'ayar armchair d'in ta kusa da ita ya bud'e lemun ya tsiyaya acikin cup ya mik'e ya ajiye robar kan c-table kafin ya dawo ya mik'a mata, d'agowa tayi ta kalleshi ya d'an lumshe mata idanu alamar ta amsa maimakon ta amsan sai kawae ta k'ara fashewa da kuka tana Fad'in "wllh na rantse da Allah Ya Handsome ni ba kwad'ayi da kwakwa nike zuwa ba" d'an cije baki yay sam baison jin Maganar ma don yasan tana yi mata ciwo sosae saboda bai manta da labarin wadda tayi mata gorin kallo ba da ta ta6a bashi tun lokacin ya fahimci irin hakan na mata ciwo, shiru yay yana kallonta tana ta faman kuka fuskarta tayi jaga jaga da hawaye ga idanunta sunyi ja, Calmly ya fara Magana idanunshi akanta "i know who's Zarah, so i will never think of dat, ki daina damun kanki akan hakan ki manta kawae ita haka halinta yake ne kawae don ta 6ata maki rai tayi maki wannan Maganar but ni nasan ba haka halinki yake ba" da sauri ta kalleshi da jajayen idanu murya na rawa tace "to su sauran fa?" d'an Murmushi yay yace "suma bazasu yi maki kallon hakan ba don ba halinsu d'aya ba su zasu d'auke ki kaman sis nasu" shiru tayi tana kallonshi ya jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abunda ya fadan kafin ya sake mik'a mata lemun ta amsa ta d'an kur6a daga haka ta mik'e ta aje kan c-table ta kalleshi tace mashi zata tafi gida, shiru ya danyi yana kallon face d'inta kaman mai nazarin wani abu kafin ya d'aga mata kan alamar to har ta kama kopar zata bud'e ya kirata ta juyo yace "am so sorry and am apologizing on her behalf" shiru ta d'an yi sai kuma ta jinjina mashi kai daga haka ta fuce, zaune yay a wurin ya d'age kanshi sama na d'an wani lokaci kafin ya mik'e ya nufi hanyar Bedroom, ruke da jakarshi ya fito ya fita daga falon da farko da ya fito lokacin da yaga su Fatun part d'in Hajiya zaije yaci abinci amman yanzu yana fitowa Parking space ya nufa kawae ya hau bike dinsa ya fice, Hajiya na zaune a Falo hannunta ruke da Al'qurani idanunta na sanye cikin gilashi ta jiyo k'arar bike d'inshi,lokacin data kai karshen ayar da take cikin karantawa ta d'ago ta kalli Farha dake Facing dinta ta juya tana lek'en Haisam d'in ta window tace "Fita yayi kenan ba tare daya zo yaci abinci ba" juyowa Farhar tayi ta kalleta ta d'an ta6e baki daga haka ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom. Koda Fatuu ta koma gida bata gaya ma kowa abunda ya faru ba dama kuma gwaggon ta tafi aiki taja bakinta tayi shiru saidae acan k'asan ranta tana jin zafin Maganar sosae ba kamar dayake bata rama ba.

Ranar Alhamis bayan Azahar duk suna zaune kan dining suna cin abinci banda haisam da bai kaiga dawowa ba Jidderh ta kalli Hajiya tace "wai nikam hajjaju ya akai kwana biyu yar gidan Ya Handsome bata zo ba ko dama ba ko yaushe take zuwa ba?" saida ta idasa cinye abincin dake cikin bakinta ta ajiye cokalin kafin tace "wllh kin riga ni ne a baki amman abun na raina ace yau har kwana ukku bata zo ba inata so in maganta kwana biyu da ba zaune nike ba shiyasa nama yi zaton ko tazo ban nan ne" girgiza mata kai jidderh tayi alamar a'a Hajiyar tace "to Allah dae yasa lafiya" tana rufe baki Nameer yace"Lafiyarta lau ko jiya naje gidansu mun gaisa da granny dinta" sai lokacin Farha ta d'ago tayi mashi wani kallon mamaki Hajiya tace "shanshani ashe har kasan gidansu kana ma zuwa kenan" murmushi yay gaba d'aya dimples d'inshi suka lotsa yace "Ran Monday da tazo na rakata ne naga gidan har muka gaisa da Uncle d'inta mai kiosk so wurinshi nike zuwa fira shine har na shiga cikin gidan" jinjina kai Hajiya tayi Jidderh tace "to muma zamu je mu gaisa",
"haka yakamata kuje ku gaishe da kakarta har ku gano mana ita kuji ya akai bamu ganta ba kwana biyu" Hajiya na rufe bakinta Jidderh ta mike su twins ma suka saukko daga kan dining chair alamar suma zasu je kallon Farha tayi ganin yadda ta wani tamke fuska yasa bata ce mata komae ba ta nufi cikin falon Nameer na mata kwatancen gidan yace ko tayi ma Officer Magana zai nuna masu tace to, dama akwae gyale akanta don bata cika son zama ba kallabi ba suka fuce, suna fitowa bakin gate tayi ma Officer Magana ya tashi ya rako su har wurin kiosk d'in Amadu ya nuna masu gidan yayi masu adawo lafiya yana daga ma su twins hannu suma suna d'aga mashi, a bakin kiosk d'in ta tsaya ta gaida Amadu yana ganinta ya washe baki yana amsawa tace mashi sunzo gun Zarah ne ko tana nan yace eh bari ya rakasu ciki ya fito yay masu jagora yana gaba suna biye dashi har bakin kopar d'akin Fatun ya d'aga labulen baiwar Allah tana kwance kan gado tunda ta daina zuwa gidan Hajiya take jinta kaman bata lafiya ko gidansu Haulat ta daina zuwa duka sau d'aya taje shima kasa zama tayi ta dawo gida saidae taita kwanciya a d'aki har gwaggo ta gano akwai abunda ke damunta taita tambayarta amman sai tace mata ba komai,

"Ki tashi kinyi bak'i" Amadu yace mata bayan ta d'ago ta kalleshi, idasa tashi tayi zaune ya juya yace masu su shiga su twins nata faman kallon gidan, da sallama Jidderh ta shiga Fatuu na ganinta ta saukko daga kan gadon ta mik'e tana kallonta da alamun mamaki ta amsa sallamar ita kuma tana tayi mata Murmushi, nuna mata gefen gadon tayi tace ta zauna ta amsa da to kafin ta nufi wurin ta zauna tace ma su twins dake ta bin d'akin da kallo suzo su zauna a tare suka haye saman gadon ko takalma basu cire ba Jidderh tace suje waje su cire Fatun tace ta kyalesu ba komai ai,
"Zasu 6ata maki bedsheet" ta fad'a a nutse fatun tace ba komae, shiru suka d'anyi sai faman Murmushi suke ma juna can Mubeen yace "Sis Fatuu is dis ur House?" kai ta d'aga mashi alamar eh, Mubeena tace "but it's too small....." kafin ta ida Jidderh ta d'an yi mata tsawa tace "who ask u dat!" turo baki tayi Mubeen ya ta6a Fatun yace "ki dawo gidanmu babbane k'ato yana da kyau" yar dariya tayi tace "to zaku barni in zauna ko" da sauri suka d'aga mata kai alamar eh tace "amman a d'akinku zan zauna fa" a tare suka ce "to ai d'akinmu ma babba ne" suka yi Maganar suna nuna mata girman da hannu tayi Murmushi, suna zaunen Amadu ya shigo ruk'e da d'an babban plate ya d'auro masu ruwa da lemu harda Biscuits ya ajiye a k'asa kusa da k'afafun Jidderh ya d'ago da Murmushi yace mata bismillah itama Murmushin take tace mashi sun gode daga haka ya juya ya fita, kallonsu twins Fatuu tayi tace su saukko su ci atare suka mak'e Kafad'a suka ce "Abinci zamu ci bamu son wannan" wani kallo jidderh tayi masu Fatun tace "to bari in zubo maku...",
katseta tayi "ki rabu dasu yanzu fa suka ci abinci" turo baki sukae suka ce su dae yunwa suke ci ai basu koshi ba suka taho binsu tayi da wani kallo Fatuu kuma ta nufi hanyar fita har zata fita ta juyo a sanyaye tace "amman bansan ko zaku iya cin abincin ba d'an wake ne ko in dafa maku indomie ko taliya?" da sauri suka hada baki suka ce "a'a zamu ci dan wakun" har saida tayi dariya jin yadda suka fad'i sunan d'an waken wai dan waku, bada jimawa ba ta kawo masu tasa masu fork guda biyu aciki da robar yaji ba yadda Jidderh batayi dasu ba akan su saukko k'asa suci amman suka k'iya wai ai ba table su bazasu zauna a k'asa ba Fatuu tace ta kyalesu ba komae dole asaman gadon suka ci sai faman tura biyu biyu suke ita Fatuu mamakin yadda suke cin d'an waken take don bata yi tunanin sun iya cinshi ba saida Jidderh tace mata ai suna yin abincin gargajiya Dad d'insu yafi son cin irinsu,jin hakan yasata cewa bari itama ta zubo mata to tace a'a ta barshi duk da ranta ya biya saboda ta jima bata ci ba, baki cunkushe su twins suka ce taci da dad'i sosae, Fatun tace ita dae sai ta zubo mata tace to kad'an zata kawo mata don daga kan abinci ta taso, bayan ta kawo matan sama sama suka shiga d'an ta6a hira saboda rashin sabo har ta tambayeta gwaggo tace mata tana wurin aiki, sai can bayan la'asar suka bar gidan Fatun ta rako su har bakin Gate Jidderh na cewa bazata shiga su gaisa da Hajiya ba tace ta gaidata ta baro gida ba kowa in gwaggonta ta dawo zata zo daga haka sukayi sallama ta juya ta komo gida.


ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,

ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE๐Ÿ‘ฐ,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWAโญYAR LELE AGUN MIJINTA๐Ÿ˜ SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI๐Ÿค

*๐Ÿ’–A SANADIN MAKWABTAKA๐Ÿ’–*

_A heart touching story of Love and Destiny_ ๐Ÿ’”


*Mallakin*
โฌ‡๏ธ
*๐ŸŒนZAINAB LALUH*๐Ÿ“ฒโœ
_~(Oummu imam)~_

Littafin A Sanadin Makwabtaka Kashi na Farko wanda nayi shi a kyauta yazo karshe, Ga mai bukatar cigaba da karanta kashi na biyu wato Book 2 zai biya kudin karatu Naira 300 kacal ta wannan Account din๐Ÿ‘‡

1509618776
Zainab Bature
Access Bank

Za'a turo da shedar biya ta daya daga cikin wadannan Lambobin wayan ko kuma tuntu6a don neman karin bayani, 09013804524 ko 08169856268.

Thanks and i luv u as u patronize๐Ÿค๐Ÿฅฐ


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

7๏ธโƒฃ1๏ธโƒฃ


.......tunkarar gate d'in suka yi Officer na masu an dawo lpy Jidderh ta amsa mashi da lafiya lou kafin suka shige cikin gidan, suna shiga suka hango Haisam na tunkarar parking space zai tafi Gym da gudu su twins suka nufeshi ya bud'e masu hannu suna isa suka kankameshi suna murnar ganinshi, d'agowa sukai suka ce mashi daga gidansu sis Fatuu suke yace yayi kyau, lokacin Jidderh ta k'araso tana Murmushi ta gaidashi ya amsa har zata wuce ya tambayeta Zarah d'in na Lafiya tace eh har bakin Gate ma ta rako su tace gidansu ba kowa ne shiyasa bazata shigo ba, jinjina mata kai yay sam baiyi mamakin jin hakan ba su twins suka ce suma zasu je gym d'in yace ba'a zuwa da yara daga haka ya nufi parking space ya haye bike d'in ya fito su twins na yi mashi bye bye shima ya d'aga masu hannu bayan yasa helmet yaja ya fuce daga gidan.


__________________

Washa gari Friday Misalin karfe takwas na safe Motar Haisam ta fito daga gidan don tafiya aiki kamar kullum, daidai lokacin Fatuu ta fito daga gida tana niyyar hawa hanya taga Mota ta tsaya gabanta wanda ko ba'a fad'i mata ba tasan haisam ne aciki, a hankali glass d'in ya sauka fuskarshi ta bayyana slowly ya juya ya kalleta itama idonta na akanshi duk tayi kalar rashin gaskiya murya na d'an rawa tace mashi ina kwana, shiru kaman bazai amsa ba sai kuma taji yace "bana amsa gaisuwan maikarya" waro ido tay jin abunda yace ya jinjina mata kai kamar zata yi kuka tace "to ai ban yin k'arya yanzu" d'an ta6e baki yay kafin yace "ni ai kinyi man saboda kin raina ni ko?" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a idanunta har sun kawo ruwa ganin yanata kallonta yasa tace "to karyan mi nayi maka?" da kai yay mata alamar ta shigo cikin Motan jikinta sukuku ta zagaya ta bud'e Motan ta shiga, kwantar da kanshi yay jikin headrest ya d'an juya yana kallonta ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta,

"The other day bana baki hakuri ba kuma kin nuna kin hakuri miyasa kika daina zuwa?" taji ya fad'a, d'agowa tayi ta kalleshi kafin murya na rawa ta fara Magana "To ai ita wannan fa bata son ina zuwan nasan innaje data ganni sai ta karamin abunda tayi man kuma ko rannan data kada ni k'asa tace wai na taka mata k'afa wllh ni ban taka ta ba kawae bata sona ne shiyasa na daina zuwa" tana kai Maganar kwalla suka zubo mata sharrr tasa bayan hannunta ta goge, still idonshi akanta yace "bana gaya maki halinta ne hakan ba so u shouldn't mind her shit ki rabu da ita kuma a hakan zamu rayu a taren daga d'an abu har kin sare" da sauri ta kalleshi yace "ko ba ke kika ce haka ba?" ya d'age mata gira ta tura mashi baki yay murmushin gefe kafin yace "tunda kin zama matsoraciya ran Monday zasu tafi sai kici gaba da zuwa ko?" tana tura baki tace "ai ni ba tsoranta nike ji ba wllh don ko fad'a mukayi da ita bazata iya man komae ba kawai don ka hanani fad'a ne kuma banson inyi mata abu aga nayi mata rashin kunya kuma nima kamar yar'uwata na d'auketa tunda yar uwarkace" dan bud'e ido yay yana Murmushi jin tayi Maganar hankali tace "ko ba kace ni k'anwarka bace" still da Murmushin yace "Yeah sis d'ina ce Coward" cike da shagwa6a ta d'an jujjuya kai tana Fad'in"Wayyo Ya Handsome bana fad'i maka dalili ba wllh ni ba Matsoraciya bace" dariya yayi har hakoransa suka bayyana acikin ranshi kuma yaji dad'in abunda tayi, ganinta sanye da Uniform yasashi tambayar ta fara zuwa Skul ne tace a'a Registration zataje yi jiya sunje basu samu yi ba saboda akwae Mutane da yawa kai ya jinjina ya fara kokarin tashin Motar tace kaita zaiyi ya d'aga mata kai tace "to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login