Showing 51001 words to 54000 words out of 212491 words
abu ba kyau kuma kika aikata even if u ask for his forgiveness he won't forgive u,saboda kinsani kika take,so duk hukuncin da za'a yi maki is better ayi maki da ki zabi ki sa6a ma Allah saboda hukuncinsa yafi na kowa tsanani,Understand? Ya tambayeta hadi da dage girarsa sama,da sauri ta daga kai sama,tace"Astagfurrullah,Allah,Allah na tuba"ta tofa a hannu ta shafa,girgiza kai ya d'anyi ganin abunda tayi.
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching love story_
_*BY ZAINAB LALUH📲*_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*28⃣*
Haisam speaking calmly"kaman yadda nace zan yafe amman abisa sharad'i guda,shine i want u to promise me bazaki k'ara fada da kowa ba,kar in sake ganin ana fada da ke,indai kina son zama Doctor like you said to sai kin natsu don in kina rashin ji koda kina da kokari you won't be a doctor,saboda sai masu natsuwa ne ke wannan aikin"
Sakin baki tayi tana kallonshi,ganin hakan yasa shi dage gira yace"is too harsh for u ko,nasan bazaki iya bari ba..." da sauri tace"a'a wllh,nifa mamaki nike,wai iya abunda zanyi kenan ka yafe miliyan din,kuma bazaka fadi ma hajiyanka ba da gwaggotah?" d'aga mata kai yayi alamar eh,cike da farinciki ta washe baki tana fadin"wllh,wllh,kwarankwatsi kaji na rantse nayi maka alkawarin na daina,kam yo wannan abun mai sauki ai ko cin tuwon gwaggo yasin yafi shi wahala" ta k'arasa maganar sai faman daria take dimples dinta duk sun lotsa,shi dai sai kallonta yake ya dan ta6e baki,
ta ci gaba"Uhm nasan gaye sai yayi mamaki sosai idan yaji ka yafe man,shida yace wai ko dan gidanmu ne kai bazaka yafe man ba,dole sai an biya ka ko kuma akaini gidan yari,aiko sai na fad'a masa to ka yafen in na ganshi,nasan yanzu haka suna can kangon da suka saba zuwa yin shaye-shayensu,Allah dai ya shirye su",
ganin yadda take ta faman farinciki yace"kibar wani murna i know u can't maintain,kin saba rashin ji,nasan sai kinci gaba" da sauri tace"ai wllh na bari fa,kam gidan yari fa za'a kai ni ko aman aure ai nama bari baruwana da kowa yanzu komi aka man zanyi hakuri, daman haulat tace Allah yana tare da masu hakuri kuma in aka cuce ka kayi hakuri shi zai saka maka ta hanyar da baka yi zato ba" dan murmushin gefe yayi yace "we shall see,ai inma kika kara ina zaune zan gani so karma kiyi tunanin yiman wayo kiga ai ban gani,kuma da kin breaking promise din zan tada maganar glass din don akwai camera a motana tayi recording lokacin da kika fasa glass din kinga dole a biya ni and I will not forgive again" a nutse yake maganar,
Baki sake take kallonshi har ya gama maganar sannan tace"ai fa ko kare mai bak'in baki ne ya cije ni bazan k'ara fad'a da kowa ba,kwarankwatsi kaji na rantse kuma zaka gani" ta k'arasa tana daga hannu sama alamar rantsuwa,haisam dake kallon abunda tayi yace"miye wannan din da kike fad'i? tace"kwarankwatsi?" daga mata kai yayi alamar eh,tace "rantsuwa ce,in dai ka rantse da ita kuma ka karya to fado ma mutum take ta kashe shi" hannu yasa ya rike beard dinsa kafin calmly yace"to ba kyau ki bari,is a kind of shirk,kinsan miye shirka?" ya tambayeta,zaro idanu tayi a rude tace"shirka!hada Allah da wani kenan,malamin islamiyyar mu yace kaman kayi mashi kishiya wurin bauta masa"
Yace "haka ne,kinga ke yanzu wannan abun da kike fadi kaman kishiyan ki ka masa tunda kina rantsewa dashi,kuma ba'a rantsewa da ko wani abu bayan Allah don komai a karkashin ikonsa yake,
Hannuwanta ta d'ora asaman kai tace"na shiga ukku,wllh ni ban san ba kyau ba fa tun a garinmu nike rantsewa da ita,kuma malam yace babban laifine shirka,shine laifin da Allah bai yafewa in aka mutu ba'a tuba ba"tayi narai narai da idanu zata fara kuka,
ganin hakan yace"ai shirkan iri iri ne,wannan tunda kince baki sani ba sai ki tuba ki bari,in kuma kika ci gaba kinga kinsani kin take like i told u before,
Da sauri ta daga hannu sama tace"Allah,Allah na tuba ka yafe man,bazan kara rantsewa da ita ba,ban san shirka bane,daga yanzu da kai kadae zan rinka rantsewa" ta tattofe a hannu ta shafa,girgiza kai kawai yayi ganin wata bidi'ar kuma.
Shuru sukai na wani d'an lokaci,ita dai sai faman murmushi take,
"daman haka ake barin ki kina fita da dare ki dade batare da an neme ki ba? taji ya jefo mata tambaya,daga kai tayi ta kalleshi tace"a'a Gwaggo bata bari na ina fita da dare,nan gidan ne kawae nike zuwa ina kaiwa dare,da fa har kwana ma nike amman yanzu na daina kwana sai dae inzo taya hajiyanka fira to wani lokacin sai bacci ya kwashe ni,sai ta aiko kawu Amadu ya tafi dani,yanzun ma ce mata nayi zanzo wurin hajiyar tana nemana shiyasa ta barni,da tace ma dare yayi,sai kuma tace inzo amman kar in bari har kawu Amadu ya tashi daga shago" dage gira yayi yace"k'arya ko" daria tayi tasa tafukan hannu ta rufe fuskarta tana fadin"ai gidan hajiyan nazo ko,kuma malam yace akwai inda wata k'aryar ke hallata mutum yayi,kaga da banzo ba har gobe tayi shikenan da sai gidan yari,ko kuma ka matsa abaka shanu ni kuma aman aure" ta k'arasa maganar tana turo baki,
Fuskarshi dauke da dan murmushi yace"ai ba wani abu bane in an maki auren.." da sauri ta katseshi"kam,ni d'in yar karama dani hakan ai child abuse ne(cin zarafin yara)" waro ido yayi cike da mamaki sai kuma yayi daria har hakoransa suka bayyana yana jinjina kai yace"Child abuse!waye ya fada maki hakan?" tace"malamar social studies dinmu" jinjina kai kawai yayi ya mik'a hannu ya daukko gwangwanin lemun ya idasa juye sauran ya kai bakinsa yana sha,bin lemun tayi da kallo ko kyaftawa batayi,can ya d'ago idanunsa suka hada ido,dan murmushi tayi batare da ta janye idon ba,yatsa ya mika yana nuna mata fridge yace "je ki daukko" girgiza masa kai tayi alamar a'a,
"baki shan lemu ne?"ya tambaya,tana ta murmushi tace"ina sha,amman gwaggo ta hana ni rok'o" dan guntun tsoki yayi kafin yace"kin rok'e ni ne daman,in kika roke nima bazan baki ba don ba abu ne mai kyau ba shiyasa grandma d'in taki ta hana ki,C'mon je ki daukko"mikewa tayi ta nufi inda fridge din yake,
Hannu ya kai ya dauki remote yayi turning tv on,yana cigaba da shan lemun yana kallo,dawowa tayi tai tsaye gabanshi ba tare da ta d'aukko lemun ba,kallon ta yayi"ina lemun?" hannu ta dan watsa tace "babu" da dan mamaki yace"babu,to duk ina suka tafi?? tace"a'a akwai sauran wasu irin wannan da kake sha ne babu" wani kallo yayi mata mai kaman harara"to wannan shikenan dama aciki kuma baki bukatan shi,ki daukko wani" "giya ce?" yaji ta jefo masa tambaya yana niyyar kai cup din bakinsa,da wani irin expression ya d'ago yana kallonta,sosai gabanta ya fad'i ta shiga ja da baya tafukan hannunta dafe da bakinta furiously yace"zo nan!" sosai ta tsorata da yadda fuskan shi ta canja,a hankali ta fara matsawa dan nesa dashi ta durkushe tana girgiza kai alamar yayi hakuri don ta kasa ma magana,sassauta d'aure fuskan yayi yace"nayi maki kama da mai aikata abunda kika fadi ne...?da sauri ta girgiza masa kai,yace"to miyasa kika tambaye ni? Baki na kerma tace"naga kalan shi wani iri ba irin na lemunan dana sani bane shiyasa nayi tunanin ko itace tunda ni bansan ya take ba,amman don Allah yaya handsome kayi hakuri na tuba" ta d'aga hannuwa,
Sauke ajiyan zuciya yayi ya kwantar da bayanshi jikin kujeran kaman bazai tanka mata ba,gaba daya ya gaji da magana,dama duk duniya a yanzu dai mutum biyu ne ke sa shi magana da yawa,daga Abbas sai hajia,yanzu kuma ga fatuu dama dazun Abbas ya gama nashi,ita abunda yasa ya biye mata dama don akwai abubuwan da yake son sani game da ita don dan kwana biyu da ya santa ya fahimci bata jin magana sosai kuma shi tunda yake bai ta6a cin karo da yarinya irin haka ba,haka yanzu ma da tazo wurinshi sai yaga kaman ba daidai take ba,shiyasa yayi tunanin ko tana da matsalan kwalwa ne,to amman daga baya ya fahimci kaman lafiyarta lau kawai halinta ne hakan.
"Don Allah yaya handsome kayi hakuri kar kayi fushi,wllh bansan irin wannan lemun bane" kwalla ce ta fara gangaro mata a daidai lokacin ya d'ago da kansa yana kallonta itama shi take kallo tana matsar kwalla,gently yace"is okey,amman ki rage yawan surutu mara amfani" da sauri ta d'aga kai alamar toh,alama yayi mata da hannu tazo ta mike a hankali ta tsaya gefensa ya d'aga gwangwanin lemun ya fara magana a nutse"akwai lemu kala kala,wani a roba,wani a can,wani a kwalba,wasu manya wasu k'anana,so ba iya wad'anda kika sani bane lemu kawai,kar ki k'ara ganin wani yana shan wani kalan lemu da baki sani ba kice giya,Understand?" Da sauri ta daga kai,ya ci gaba"abunda yasa nace baki bukatan sa,Energy Drink ne,kuma yana da d'an karfi ne",
bude baki tayi da mamaki tace Energy..! Yace"yea,ko baki san miye energy ba?da sauri tace "nasani,is the ability to do work" cike da confidence tayi maganar d'an murmushi yayi,hakan yasa itama tayi "mi kenan yake nufi?, Tace"karfi,karfin yin aiki,shi kake sha kenan shiyasa ka ke da power?" ta fad'a tana nuna damtsen hannunshi dake a murd'e,banza ya mata taci gaba"don dai kace in aka roke ka abu bakayi da nace kabar lemun da zaka bani yanzu sai nima ka samo man iri wannan din,wallahi aiki yawa yake man,inna dawo daga makaranta sam ban hutawa ba kaman gwaggo in tana nan,fatuu yi tankad'e,fatuu dibo ruwa,fatuu fito ki shara,komai ni",
Murmushi ya sake yi yace "wannan ai ba wasu aiki bane,and being a girl dole ki koya irin wannan aikin..." tace "to ai sai in mutum aure za'a masa sannan ni kuma fa ba yanzu zanyi ba sai nan da dadewa,ba na fada maka..." da sauri yace "yea,is a child abuse,je ki daukko wani zan kawo maki wannan din" tace "toh,ta juya,ya bita da kallo,kafin ya maida kallon kan t.v.
Lemu fanta ta daukko ta dawo ta zauna a inda ta tashi,ta rike lemun tana d'an wasa da robar sai faman murmushi take da ka kalli fuskarta zaka san tana cikin tsananin farin ciki,sai kallon haisam take wanda idanunsa ke kan tv,juyowa yayi suka hada ido kaman jira take ta d'aga lemu daya tace"Allah yaya hansome kana da kirki wllh,kafi kowa na duniyar nan kirki,wai har kudin shanu gomaa ka yafe tabb,nagode thank u so much,God bless you" ta k'arasa maganar tana noke kai,gyara zama yayi ya d'an kwanta yana kallonta,
"in kuma kika karya promise din,na dawo nace ban yafe ba sai kice ni mugu ne,nafi kowa rashin kirki a duniya,right? Girgiza masa kai tayi tace"a'a ai wannan ni naja ma kaina kuma,bama fa zan kara ba tunda nasan da nayi zaka sani,ai nagan ma abubuwan da ke fadi maka abu in akayi baka nan" yace "a ina?" Juyawa tayi tana nuna dakin da taje yin fitsari tace"a cikin dakin naga wani abu babba mai uban wayoyi ajiki,kuma ma naga wasu jajayen abubuwa manne a bango,bokayen turawa ne ko?" shiru ya mata,ya lura ta cika tambaya ta rashin kan gado ita kanta ba kan gadon gareta ba,ganin tana ta kallonshi alamar jira take ya bata amsa,ya d'age gira yace"bokayen fulani ne" da farko waro ido tayi waje cike da mamaki,can kuma sai ta gane gatse ne yayi mata don gwaggo ta saba yi mata,hakan yasa ta d'age kafafunta ta tura kanta ciki tana daria gyalenta ya zamo kasa,
Dago kanta tayi a hankali suka had'a ido dashi tana murmushi tace"ashe kaima ka iya irin abun gwaggo"banza ya mata,ganin ta rungume lemun yace"kisha mana" girgiza kai tayi tace"ba yanzu zan sha ba,dashi zanje makaranta gobe in yi break" jinjina kai yayi sai kuma yace"je ki k'aro wani" daga na hannunta tayi tace"ai wannan ya ishe ni"
"What about ur friend,bazaki bata ba,ko ba school daya kuke ba?" tace"wai haulatu,ajin mu ma daya kuma seat dinmu daya da ita,tare ma muke yin break din,ai sai mu raba" shiru yayi yana tunanin halinta ne haka bata da had'ama ko kuwa don yace bai son roko shima" je ki daukko mata wani,in nace kiyi abu just do it banson jayayya" da sauri ta mik'e tana cewa"yi hakuri yaya handsome,taje ta daukko coca-cola ta dawo tana daria ta nuna mashi tace"ita haulatu tunda bak'a ce sai in bata wannan ni kuma tunda fara ce sai in sha wannan jan" ta koma ta zauna hadi da rungume roban lemunan,shidai dan murmushi yayi kawai kafin yace"karfe nawa Uncle din naki ke kulle shagon? tace "k'arfe tara da rabi ko goma cikin sanyi amman da zafi kaman yanzu yana kaiwa har sha daya" time ya duba a wayansa yaga 9:50,yace mata "shi zai zo ya tafi dake ne? tace "a'a haka gwaggo tace dai kar na bari ya tashi,amman in ban koma ba har ya tashin zata aiko ya tafi dani" jinjina kai yayi kawae yaci gaba da kallo,can ya mike don ya gaji bacci yake son yi,gashi gobe akwae aiki,ya wuce bedroom dinsa tana ta kallon bayan shi har ya shige,tana ganin ya shige ta kyalkyace da dariyar farinciki,tana tillah robobin lemun hannunta tana cafewa.
Sanye cikin jallabiya mai gajeren hannu ash color ya fito,komawa yayi inda ya tashi ya zauna yana kallon yadda take wasa da robobin lemun,dagowa tayi suka hada ido tayi dan murmushi a hankali tace"Yaya handsome" shiru yayi kaman mai tunanin wani abu kafin yace"ba sunana haka ba" sakin baki tayi da mamaki tace"amman ai haka naga ansa a jikin riganka" yace"yeah,but wannan rubutu ne kawai",
"ya sunanka to?"ta tambaya, d'an k'ankance idanunsa yayi yace"Haitham" cike da mamaki ta rika maimaita duka sunan,haisam da handsome can tace"ai to duk d'aya ne ko wancan da turanci wannan da hausa ko"d'age gira yayi yace"koh? Jinjina kai tayi"eh mana,kuma ni nama fi iya fadin handsome din kuma ai shi ya dace da kai,baka san mi yake nufi bane?" ta fad'a tana daria,dan murmushin gefe kawai yayi baice komai ba,daman saida yayi tunanin zata iya cewa sunan daya ne.
Kallon time ya k'ara yi a wayansa lokaci guda ya mike yana fadin"it's already late,tashi na raka ki" toh tace ta fara kokarin mikewa hannuwanta rungume da lemunan,ta wuce gaba yabi bayanta daidai bakin kofan fita ta juyo da murmushi tace"in ringa zuwa ina gaida ka?"daga mata kai yayi alamar eh,daga haka suka fice.
Unguwar shiru ga duhu saboda an dauke wuta,gidaje kad'an ne gaban su ke dauke da hasken wutar generator da suka kunna wasu kuma solar saidai gaban gidan hajiyan yafi ko ina haske saboda fitulun jikin gidan da suke akunne gaba daya,ko alluran mutum ta fad'i a wurin zai iya ganinta,gaban shagon Amadu ma akwai hasken kwai mai caji ga wasu mutane biyu a tsaye suna siyayya,suna kaiwa daidai rabin bangon gidan hajiyan yaja ya tsaya agaban fence itama tsayawar tayi tana kallonshi hannu yasa ya shafi forehead dinshi gently yace"Good nyt" murmushi tayi itama tace"to good night yaya handsome" jinjina mata kai ya yi daga haka ta wuce.
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching love story._
_*BY ZAINAB LALUH📲*_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*2️⃣9️⃣*
Haisam na ganin ta kai k'arshen katangar ya juya ya nufi gida don yaga akwai mutane gaban kiosk din.
Tana gab da isa shagon Amadu taja ta tsaya tana tunanin wani abu sai kawai ta juyo ta nufi lungun dake tsakanin gidajen su da gidan hajia,daidai haisam na niyyar shigewa kwanar gate kaman ance ya juya yaga tasha kwana saboda hasken da ya haska lungun da tabi,tunani yayi a ranshi ina kuma yarinyar zata da daren nan,juyowa yayi ya tsaya yana kallon hanyar data bi,a hankali ya fara tafiya ya koma hanyar daya baro,daidai lokacin da ya kai karshen bangon ya juya yana kallon lungun lokacin ta karya kwanar dama ta shige ya daina ganinta,tsaye yayi yana ta kallon inda tabi yana cigaba da tunani,can ya ayyana kilan aikenta akai bata je ba sai yanzu,"ai kuma cewa tayi ta tambayi zata zo gidan hajiya don ta baka hakuri",wani bangare na zuciyarshi ya ayyana mashi can dai ya d'an ta6e baki hadi da d'age kafad'a daga haka ya juya ya koma gida.
A daidai gaban kofan kwangon ginin data 6uya ranar juma'a lokacin data fasa ma haisam glass ta tsaya,tura kanta tayi tana lek'en ciki wanda yake dund'um ba haske,lokaci guda ta shige ciki ko tsoro bata jiba,ta nufi wata kofa,
Zaune suke su ukku saman windunan wani babban d'aki,da gani falo ne aka fitar,suna ta busa hayaki sunyi mankas da wiwi(Allah ka shiryi al'ummar Annabi,Amin),jin motsin mutum ya shigo yasa daya daga cikinsu fad'in"kwalawa yasin...."da karfi yayi maganar duk suka dire na karshen na niyyar direwa da karfi fatuu tace "kai Gaye nice fa" jin hakan yasa shi tsayawa ya juyo yana k'are mata kallo cikin duhu,fiddo wayarsa yayi ya kunna fitila ya haska inda take tsaye,cike da mamaki da kuma fargaba cikin muryarsa ta wanda ya bugu da wiwi yace"Aljana!,kece ko kuwa Aljanar gasken ce" turo baki tayi tace"ni fa ka daina ce man Aljana banso" jin hakan ya tabbatar mashi da itace,juyawa yayi jikin windown yace"Goga,6aure ku dawo ba kwalawa bane" daga haka ya juyo ya nufo fatuu yana fad'in"ke Aljana miya kawo ki fadarmu da daren nan?",
"ba kaine kace mutumin nan ko d'an gidanmu bane bazai yafe abunda nayi masa ba,to yace ya yafe kuma ko gwaggotah bazata sani ba" ta k'arasa tana murmura idanu, Gaye yace"wai mi kike magana akai kiman gwari-gwari don ni ba fahimtarki nike sosai ba na riga na dau caji kingane ko" yana maganar ya kasa tsayar da kanshi awuri guda,bude murya tayi tace"wannan mutumin dana fasa ma glass din mota wanda kace kudin gilashin yakai miliyan kuma inba'a biyashi ba gidan yari za'a kaini..." yace "eahh hakane,to minene?",
"to yace ya yafe,yanzun nan daga wurinshi nike,naje na bashi hakuri kaga ma har lemunan roba ya bani" ta d'aga lemunan tana nuna masa,waro idanu yayi yana kallon robobin ta hasken fitilan daya kunna ya fara karanta sunansu a