Showing 117001 words to 120000 words out of 212491 words

Chapter 40 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

983

ta d'ago abun mamaki sai taga ya bud'e mata tafin hannunshi fari kwal dashi,bud'a ido tayi alamar mamaki shi kuma ya d'an lumshe nashi had'i da jinjina mata kai,washe baki tayi ta buda tafin hannunta na dama ta buga a nashin da k'arfi ji kake fasss har saida ya d'an cije baki,tana ganin abunda yayi ta kyalkyace da dariya tace"thank u,God bless u Sweethrt"girgiza kai kawae yayi tare da mikewa,
"Ki copying solution d'in Magrib ya kusa" daga haka ya fita daga cikin d'akin,da sauri ta d'aukko littafinta da tuni ya fad'i a k'asa da tana tsalle ta zauna saman kujeran ta fara kwafar rubutun kaman yadda yace mata tana yi tana sakin Murmushi,

Yana fita fridge ya nufa ya daukko bottle water mai sanyi da glass cup ya nufi kujera ya zauna inda ya tashi lokacin da Fatuu ta shigo,tsiyaya ruwan yayi kaman rabin cup d'in kafin ya rufe robar ya kai cup d'in baki ya fara shan ruwan ahankali,yana niyyar aje robar ruwan akan c-table Fatuu ta fito har ta gama kwafar rubutun dama saurin rubutu ne da ita,kan d'aya daga cikin armchairs ta zauna idonta akanshi,
"Ko zaki sha ne?" ya tambayeta bayan ya cire cup d'in ta d'aga mashi kai alamar eh, sauran na cikin robar ya mik'o mata ta mike ta kar6o kafin ta dawo ta zauna,
"Ki d'aukko cup acikin fridge" girgiza mashi kai tayi"ai shanye shi zanyi bari insha a robar" kai ya gyad'a mata shiru ya biyo baya na d'an wani lokacin,
"Wai Ya Handsome kodae kaima malami ne naga ka iya bayani fa sosae"girgiza mata kai yayi alamar a'a,ganin tana ta binshi da ido yasashi cewa" hakan is part of my work,ina yawan presentation kinsan miye hakan ko?"ya tambayeta idonshi akanta,d'aga mashi kai tayi"eh yima mutane bayani"jinjina kai yayi daga haka ya d'aura kafarsa d'aya akan c-table d'in gabanshi ya d'age kanshi yana facing saman d'akin,duk jinshi ake wani iri ya saba kaman yanzu yana gym,

"Ya Handsome" Fatuu ta kira shi,amsa mata yayi ba tare daya d'ago ba,
"In tambayeka?" ta sake cewa,shiru ya d'an yi ya maimaita abunda ta fad'an acikin ranshi,saboda duk in zata tambayeshi kai tsaye take jefo mashi kowacce irin tambaya,daga yadda yake ya d'an juyo da fuskarshi side d'in da take,
"Am all ears" ya fad'a,
"Wai don Allah da wane irin dutsen goge kaushi kake amfani ne kafanka tayi haka kaman ta jarirai sumul ba kaushi?" ta k'arasa tana nuna kafarshi da ya d'aura saman c-table, kai jama'a ashe tunda ya dauran ta k'ura ma k'afar ido tanata kallonta har ta kasa daurewa saida ta tambaya, shi kuma sam bai gane ma mi take nufi ba,ganin tanata kallonshi yasa shi ce mata"miye shi abun da kika fad'in?"idanunshi a lumshe ya tambaya,
"Dutsen goge kaushin kake nufi?" kai ya d'aga mata alamar eh,
"Wannan fa dutsen mai gurjigurji wanda ake sakawa acikin kwandon wanka ana gurje tafin k'afa dashi mai kaushi ko faso"tayi maganar tana kwatanta mashi yadda ake goge k'afan dashi da tafin kafanta da ta d'an d'age sama,still idanunshi alumshe suke ahakan yake kallonta,yanzu ya gane abunda take nufi duk da shi bai san ma dutsen ba,
"kina son abunne?"da sauri ta girgiza mashi kai "a'a bani ke so ba Kawu Amadu zan sai ma irin nakan k'ilan ya gyara mashi k'afarshi ta koma kaman taka, wllh baka ga kafarshi bafa, ina...kasan dawon fura in ya kwana,to haka k'afarshi ke komawa cikin sanyi haka zaka ga yanata dirzarta a gefen inda nike yin wanke wanke,har wani k'aton dutsen goge kaushi gwaggo ta siyo mashi a kasuwar yar kutungu yana amfani dashi,kwanaki fa cewa tayi in kafarshi nayin hakan in yayi Amarya zai rinka yaga mata zanin gado"ta k'arasa tana 6a66aka Dariya,d'an bud'e idanun yayi yana kallonta fuskarshi d'auke da dan guntun Murmushin gefen baki,
"Shiyasa na tambayekan in ka fad'i man inda ka siyo naka sai in siyo mashi k'ilan ta daina tunda ni dai banso yayi Amarya ya yaga mata zanen gado kuma in ta canja wani taga ya k'ara yaga mata ai kaga tana iya yin yaji ko?" tsakaninta da Allah take yin Maganar😂,

d'ago kan yayi gaba d'aya daga saman bayan kujeran yace mata"bani amfani da abun ina kaita ana wanke man ne" wata zabura tayi ta zaro ido tace "kafan kake kaiwa wanki sai kace kayan wanki!" tayi maganar hannunta guda ruk'e da ha6arta alamar mamaki,kai ya d'aga mata kafin yayi mata bayanin yadda ake pedicure d'in,cike da Al'ajabi take kallonshi hakan yasa ya d'age mata gira"zaki kaishi arika wanke mashi kafan ko?" a razane tace "wa!ba ruwana wllh,ban shirya zuwa gidan yari ba,haka kawae muje kafan tashi ta lalata masu inji ace sai na biya miliyoyi,ai ma yanzu ta d'an gyaru tunda zafi ake sai sanyi yazo take tsatstsagewan sosae zan dai gaya mashi in yana so to sai yaje amman ba ruwana ni dai" tana Maganar tana d'aga hannuwa sama alamar ba ruwanta,gyad'a kai yayi kawae yana niyyar k'ara kwantar da kan nashi aka fara kwala kiran sallar magrib hakan yasa ya dakata,

"kije gida kiyi salla sai ki kara duba Assignment d'in karki manta ko" kallonshi tayi ta d'an marairaice "to ai yanzu gwaggo bata isa dawowa ba, kuma wllh in na koma kakkarya ni kawu Amadu zaiyi kaman kara dama ya ta6a gota ni a hannu,kofa Gwaggon na nan yana buguna balle yanzu da bata nan"shiru baice komae ba can ya mik'e tsaye yana gyara rigarshi ta daga kai tana kallonshi,
"Ki jira in dawo" yace mata ganin bata da kallabi kuma magriba tayi bai kamata ta fita haka ba,da sauri tace mashi toh tana gyara zamanta,Bedroom d'inshi ya nufa yayo alwala,yana fitowa zai wuce tace ya kunna mata kallo,remote ya dauka asaman c-table ya latsa power daga haka ya mik'a mata ya fita.

Ana gama sallan ba 6ata lokaci ya dawo part din nashi,lokacin daya shigo parlon iske Fatuu yayi ta baje a d'ayan 6arin L-shape sai sharar bacci take,(nima inyi ta hajiya ja'ira ta gaji),dama tun agida take jin baccin amman tak'i yi saboda rashin yin Assignment,tsaye yayi tsakiyan falon yana kallonta yayinda ya shiga tunanin yadda zaiyi da ita don fita yake son yi gashi da gani tana enjoying baccin,tunanin ko ya barta yaje ya dawo ya shiga yi sai kuma yayi tunanin za'a iya zuwa nemanta wurin hajiya kuma bata san har yanzu tana wurinshi ba kuma ma is'nt proper taci gaba da zama anan wannan lokacin, yin wannan tunanin yasashi fara kiran sunanta daga nan inda yake atsaye sai dai ko motsi bata yi ba tun yana kiran ahankali har ya d'an k'ara d'aga murya amman ina tuni sanyin Ac yasa tayi nisan kiwo acikin barcin da alama ma bata Nigeria,d'an k'ara matsawa yayi gabanta ya k'ara kiran sunanta nan ma shiru,still yayi da alama baison zuwa kusa da ita ne balle yasa hannu ya tasheta,har zai juya yaga ta motsa zata gyara kwanciya da d'an karfi ya furta"Zarahh"slowly idanunta suka fara bud'ewa suna kuma d'an lumshewa duk alokaci d'aya alamar dae baccin take ji sosae, yana ganin zata juya mashi baya ya sake kiranta wannan karon da k'arfi yace"Zarah!" amsawa tayi tare da bud'e idon sosae cikin Muryar bacci tace"Na'amm",

"Tashi muje na raka ki gida" amsawa tayi da toh ta fara k'okarin tashi zaune idonta akanshi tace"wai bacci nayi?"kai ya daga mata alamar eh,
"Wllh bansan ma nayi ba,kallo fa nike yi shine ya sace ni shiyasa ma ake ce mashi 6arawo ashe"da wata irin kasalallar murya take maganar,d'an murmushin gefe yayi yace"tashi muje",
"Gidan zaka kaini" kai ya d'aga mata alamar eh,
"To amman fa gwaggon bata isa dawowa ba yanzunma kar kawun ya dokeni",

"zamu je sai ki bashi hakuri",da sauri ta jinjina kai ta fara k'okarin tashi tsaye,har zai nufi kopar fita sai kuma ya juya yace mata yana zuwa,Bedroom d'inshi ya nufa bada jimawa ba ya fito lokacin har ta zauna don jikinta ba kwari,hannunshi ruke da wani bakin abu ya nufi inda take,mik'a mata yayi"kisa wannan akan ki" amsa tayi tana dubawa,hula ce skullcap irin mai matse kai,sawa tayi akanta kuma tayi mata da yake roba ce,kallonshi tayi tana da murmushi tace"thank u Sweethrt ya handsome"d'an kya6e baki yayi da Murmushi ya nuna mata hanya alamar su tafi, saida ta d'auki littafinta data aje kan armchair kafin ta wuce yabi bayanta suka fita daga parlon.

Unguwar ko ina da haske da yake akwae wutan nepa,lokacin da suka iso bakin shagon Amadun ba kowa sai sautin waka dake tashi saidae bai k'ure sautin ba ta yadda har zai takura Mutane,Fatuu ce agaba Haisam na bayanta tana zuwan gaban shagon ta tsaya lokacin ya juya baya da alama wani abun yake nema ko zai daukko,
"Kawu" Fatuu ta kirashi, aikuwa a fusace ya juyo ya kalleta fuska a tamke yace "kin gama guje gujen naki kin dawo ko,to sai ki shiga ciki zanzo in samek...." bai k'arasa ba sakamakon Haisam da idonshi ya hango mashi a gefen kiosk d'in don da duk bai ganshi ba,washe baki yayi ya fara gaidashi,hannu ya mik'o masa suka gaisa kafin calmly yace"naji laifin da tayi maka bata kyauta ba,but u know she's still a child dat's why take behaving haka sai kana hakuri and she's here to apologize" maida kallonshi yayi kan Fatuu yace"Say sorry to him" tana jin haka da sauri ta kalli Amadun"Kawu pls Sorry,wllh raina ne ya 6aci saboda ba'a fidda Assignment d'in ba shiyasa har bansan lokacin dana fad'i ma abunda nace ba amman don Allah ba don ni ba kayi hakuri bazan k'ara ba" takai Maganar tana girgiza mashi kai,wani kallo yai mata mai kaman harara sai kuma yai saurin sakin fuskar don mugun nauyin Haisam d'in yake ji,d'an Murmushin yak'e yayi mata yace"shikenan ya wuce" Dariya tayi cike da farinciki tace"Nagode kawuna kuma yayana"yar harararta yayi cikin wasa da sauri ta bud'e mashi littafinta tana nuna mashi Assignment d'in da aka fiddan"kawu kagani Ya Handsome ya fidda man shi, ashe ya iya shi sosae baka gani ba" kai ya d'aga fuska asake yace"na tayaki murna",

"Ki shiga gida Zarah" Haisam yace mata,amsawa tayi da to ta rufe littafin kafin ta nufi gidan tana yi mashi bye bye sai lokacin da zata shige ne ya d'an d'aga mata hannun shima,bayan ta tafi ne Amadu ke ce mashi wllh Assignment d'in da aka ba Fatun shi bai ko ta6a ganin shegenshi bama anan Haisam ke mashi bayaninshi yace itama don tayi laifi ne aka bata irinshi,Amadu yace shi dama yayi tunanin hakan wllh,hira yaci gaba da yi ma haisam d'in shi kuma yana tankawa jefi jefi hakan kuma ba k'aramin dadi yayi ma Amadun ba don bai ta6a tunanin ma watarana haisam zai tsaya agaban kiosk d'inshi ba balle har su danyi fira haka,

"Yaya Haisam ko abaka wani abu kad'an ta6a gashi ma kanata tsayuwa"Amadu ya fad'a yana washe baki,
"Don't mind,zan tafi ne yanzu",
"To kad'an ci wani abu don Allah" yayi Maganar cikin marairaicewa,shiru haisam din yayi,yasan in ya amsa zaiji dad'i don da dad'i kaba mutum abu ya amsa hakan yasa yace ya bashi sweet guda d'aya duk yadda yaso ya k'ara mashi yaki amincewa daga haka yayi mashi sallama ya tafi,yana komawa gida ya fiddo bike dinsa don tafiya gidansu na GRA ko kaya bai canza ba don acan akwae wanda zai iya amfani dasu.

Tana shiga gidan cike da farinciki ta nufi dakinta ta fad'a saman gado,can kuma sai ta mik'e ta nufi gaban d'an fasassan madubin daya rage a jikin d'an Dressing mirror dinta tana kallon hular da Haisam ya bata tasa,ta Matuk'ar yi mata kyau ba kamar da igiyoyin kitsonta suka zuba gefe da gefe gashi ta fito mata da haskenta sosae kasantuwar bak'a ce hular,tana ganin yadda tayi matan ta saki kayataccen Murmushi tasa hannu tana shafa jikin hular,komawa tayi kan gadon ta bud'o Assignment d'in tana k'ara bin yadda aka fidda tana cikin hakan ta tuna ai batayi sallar magriba ba hakan yasa ta mik'e da sauri ta d'auro alwala tazo tayi salla bayan ta gama har gode ma Allah tayi acikin Addu'a ta kuma yima Ya Handsome addu'a tace Allah yashi mashi Albarka ya biya mashi bukatunshi ya kuma saka shi a Aljanna,bayan ta gama Addu'ar a saman abun sallan bacci ya sake d'aukarta ko abinci bata ci ba har saida Gwaggo ta dawo ta tasheta sannan taci abincin tayi sallan isha daga haka ta koma baccin.

Washe gari tunda asussuba Fatuu ta farka da kanta ba tare da gwaggo ta tasheta ba dama akagare take da garin ya waye ta tafi Makaranta,bayan tayi sallar Asuba ta sake daukko littafin Assignment d'in lafiya lau ta k'ara bin yadda aka fidda shi ba tare da ta kakare ba,a gurguje ta shirya ta dan ci abun kalaci kad'an daga haka ta nufi dakin gwaggo tace zata tafi,amsa mata tayi da to duk da tayi mamakin shiryawarta da wuri haka don ko bakwai da rabi bata ida ba,da ta bata kudin break ce mata tayi ta barsu jiya Ya Handsome ya kaisu ita da Haulat kuma ya basu kudi sun kuma rage canji,godiya gwaggo ta shiga yi tana fad'in shi bai gajiya da hidima ne don ranar Monday ma daya kai Fatun saida ta fad'i mata har Biscuit da kudin daya bata,tana fitowa kopar gida taga Amadu a bayan kiosk dinshi yana yin brush,Murmushi tayi tace"Gud Morning my Uncle"aikuwa wata uwar harara ya zabga mata ta kyalkyace da dariya don tasan ta mecece,jiya ba don Allah yaso taba data yaba ma aya zakinta,wucewa tayi tana fad'in"sai na dawo My Uncle"daga haka ta nufi gidansu Haulat don yau ko tunanin zuwa wurin Haisam bata yi ba burinta kawae ta ganta a makaranta don Malamin lissafin garesu farko......

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔


*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

5️⃣1️⃣

Tana shiga gidansu Haulatun ta iske innarsu acikin yar rumfar da take yin sana'ar koko,wurinta ta nufa tana zuwa tace"innarsu haulatu ina kwana"
Da fara'a ta amsa mata"lafiya lau Fateema har an shiryo yau da wuri haka" ɗan murmushi Fatuu tayi tace eh,
"Ita haulatun ma ban tunanin ta shirya don bata ma daɗe da dawowa daga kai markade ba,amman ki shiga ciki ki duba ko ta shirya" amsa mata tayi da toh kafin ta nufi dakinsu haulatun da sauri,madaidaicin daki ne fentin bangonshi duk ya kode ya kankare bazaka ma gane ainihin kalar fentin ba,kasan dakin siminti ne ba leda shima wasu wurare duk ya farfashe yayi ramuka haka saman dakin leda mai kyalkyali ce akayi rufin da ita,ba wasu kaya adakin daga yar lamusassar katifa sai wata tsohuwar wardrobe mai gida biyu taji jiki ba laifi don murfi guda ma akasa yake ya balle dayan kuma da bai ballo ba shima bai rufuwa sosae gefen wardrobe din dan tebur ne an jajjera tarkacen kayan shafa akasanshi kuma takalma ne,Haulat na zaune da daurin kirji agefen katifar tana shafa mai daga can gefenta kuma kannanta ne zaune akasa suna karyawa da koko da kosae Fatuu ta shigo da sallama,bud'a baki haulat tayi alamar mamaki k'annanta suka shiga gaida fatun ta amsa masu tana nufar inda haulat d'in ke zaune,
"Wai ba dai har kin shirya ba?" haulat ta tambaya,
"Ba ga zahiri kin gani ba" Fatuu da tayi tsaye k'erere ta bata amsa,
"Amman nayi mamakin ganinki yanzu lokaci fa bai ida ba",
" nasani so nike muje da wuri kafin banz....kafin malamin math din nan ya shiga"da har zata zagi malamin ta tuna da fad'an da Ya Handsome da Hajiya suka yi mata,

washe baki haulat tayi "kenan kinyi Assignment d'in?"girgiza mata kai Fatuu tayi alamar a'a tana wani Murmushin rainin wayo,
"Allah ban yarda ba kinyi,ai da baki yi ba bazaki doko wannan uban safkon ba,kuma gashi ma kina Murmushi" haulat tayi maganar tana dan harararta,
"Don Allah haulat ki tashi kisa Uniform d'inki mu tafi mana" Fatuu ta fad'a cike da kosawa harda d'an yarfa hannu,
"To amman fa ko karya kumallo banyi ba" tayi maganar a yayin da take kokarin mikewa tsaye,daukar uniform dinta dake aje agefen katifar tayi ta wuce dakin innarsu ta shirya,da kyar tasamu ta dan sha kokon Fatuu nata azalzalarta akan su tafi harda cewa ta bari in sunje kan hanya sai su sayi wani abu haulat tace ga dai abun kari agida kuma ba makara suka yi ba ta dae bari ta karya kumallon.

A kan hanya haulat ke tambayarta yadda akai tayi Assignment din nan take ta kwashe komae ta fadi mata harda wuyar da suka sha ita da kawo Amadu don su fidda amman suka kasa da yadda Ya Handsome ya fidda mata,Dariya sosae Haulat ke yi mata tana fadin"wllh kedai baki da dama,baki san mutunci ba,yanzu duk irin kokarin da kawu Amadun yayi maki amman shine kika yi mashi rashin kunya,ni dama ya zane ki"wata yar iskar dariya fatun tayi kafin tace"wllh da kawu ya matsa sai ya fidda Assignment din nan kilan sai ya haukace shegen wuya ne dashi,wai kinga yadda yayi uban gumi yanata hura hanci karshe daya kasa ya wurgo man shi,harda wani cewa shi dama ba kaunar lissafi yake ba"dariya sosae suke yi kafin suka tsagaita suka koma yabon Haisam,haulat ta jinjina ma basirarshi jin yadda yayi solving mata Assignment din har tana cewa lalle shi dan baiwa ne komai Allah ya bashi,Lokacin da suka iso bakin titi Fatuu hanawa tayi su jira Bus tace su hau keke napep kawai kuma hakan suka yi ba 6ata lokaci suka iso Makarantar.

Fitowa Amadu yayi jikinshi sanye da uniform ya rataye jakarshi a kafada da alama shima ya gama shirin tafiya makaranta ne,yana kokarin hawa saman hanya wata galleliyar mota fara sol kirar Hyundai ta parker agabanshi,slowly glass din motar ya dan sauka nan take fuskar mai Motar ta bayyana,Amadu na yin arba da haisam ya washe baki don da har ya dan tsorata da motar ta tsaya agabanshin,jiya da yaje gidansu na Gra ne ya taho da motar yabar Bike din acan,

"Yaya Haisam ina kwana" Amadu ya fad'a,kai kawai ya jinjina mashi fuskarshi asake kafin calmly yace"Zarah fa?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login