Showing 6001 words to 9000 words out of 212491 words
kujerun parlor din
kuwa wani irin PoP Casting ne manne da bangon mai dauke da Manyan gidaje anan kuma madaidaiciyar Plasma T.V ke manne a gidan tsakiya daga kasanta kuma gidan da Sound systems suke ne da DVD player da reciever,a gidajen dake a gafe da gefen bangon da saman inda T.V din take kuwa,Hotuna ne dasu Agogo da Frames na zane wato Artworks ba karamin kyau wurin yayi ba.A gefe kuma d'an corridorn da bedrooms suke ne,a kofan corridor din flower vases ne bakake dauke da Red flowers masu ratsi da farin kananun flowers,a Angles (sako) din dake a bangon kuwa 6arin hagu Standing A.C ce babba a angle din dama kuwa madaidaiciyar Freezer ce a wurin,a tsakiyan pop ceiling din parlon akwae chandelier babba (irin fitilar nan mai adon sarkoki) kwan fari sol yayin da sarkokin jikinta bakake ne,ba k'aramin haduwa parlorn yayi ba ga sanyin A.C hadi da kamshi mai sanyaya rai da ya gauraye ko ina,da ka shigo parlorn zaka ji gaba daya yanayin ka ya canja koda kuwa kunci kake to tabbas ranka zai yi sanyiii.
Mutumin na shiga ya nufi inda bakar kujerar take ya dan fada samanta hadi da aje wayarsa wadda take slim mai dan tsawo bayanta sai shining yake a gefensa,ya kwantar da kansa jikin saman kujerar don bayanta baida tsawo sosae,T.k kuwa yana shigowa yad'an lumshe ido hadi da jan dan dogon numfashi alamar sanyayyan kamshin ya kai masa karo,shiyasa a koda yaushe yake son abunda zai kawo sa part din Mutumin koba komae ka samu natsuwa.Wucewa yayi bayan Red Armchairs din parlorn ya daura jakar saman farin desk din dake wurin kafin ya zagayo tsakiyar parlorn ya tsaya saitin Mutumin yace"Yallabai akwae wani abu? A nutse yayi maganar,Mutumin bai dago ba yana a yadda yake yadan daga mashi hannu hadi da fadin "Thanks T.k,u can go" t.k yace "To a huta lpy" ya kama hanyar fita batare da ya jira amsar Mutumin b,don yasan ma b lalle ya kara cewa komae ba,
Yana fitowa yaji wani zafi ya bugi fuskar sa a fili T.k yace " Kai masu kudi dai sun ji dadin su,da ace part din nan yazama nawa ai wllh fitowa sai dole"Ya k'arasa maganar hadi da wurga kafa yace "qur'an kau" a daidai lokacin ya fita daga Part din Mutumin.
Ya dau tsawon mintuna a haka da alama dai ya gaji ne sosae kafin ya mike ya tunkari hanyar da zata kai shi Bedroom dinsa har zai shiga cikin koridon ya tsaya cak sakamakon karar da Telephone ke yi,a hankali ya juyo gami da kai idonsa saman desk din da telephone din yake yanata faman kara alamar ana kira,tafiya ya fara yi a hankali saida ya zauna saman daya daga cikin Armchairs din dake gaban teburin sannan ya mikar da hannunsa ya dauko kan telephone din,da murmushi a fuskarsa ya kara shi a kunnansa da alama yasan mai kiran nasa cikin murya mai tattare da gajiya ya fara magana"Hello sweetheart" dan saurarawa yayi kafin yaci gaba da magana "Ok ganinan zuwa yanzu" daria yayi har Hakoransa masu kyau da tsari suka bayyana cikin jaddada abun da ya fada ya k'ara cewa "Don't worry, I'm coming right away" yana fadin hakan ya maida telephone din ya mike har lokacin fuskansa da dan murmushi,Corridorn ya shiga kofa biyu ce a ciki daya tana kallon mutum in ya shiga wurin,dayan kuma na a bangaren bangon dake dama,sai da ya tsaya ya cire takalmin kafansa ya daura sa saman Shoe rag din dake ajiye a wurin anyi mashi design mai kyau da daukan hankali yabar safar dake a kafarsa bai cire ba kafin ya tura kofan dake a bangaren dama ya shiga,masha Allah Bedroom ne mai kyau da tsari bai da hayaniya Italian Bed ne da Bedside drawers din shi sai Dressing mirror wanda ke dauke da yan kwalaben turare da yan mayukan shafawa saidai da gani masu tsada ne don jikinsu kadai abun kallo ne,a bangon dake kallon gadon kuwa Wardrobe ce gaba daya bangon wadda ke rufe ruf a iya hangena nakasa gane yadda ake budata don banga hannun da za'a kama a bude ta ba, gaba daya Furniture din Coffee brown ne masu duhu sosai don inba ka shigo sosae ba zaka yi tunanin kayan bakake ne,haka Labulen dake a jikin katuwar Window din d'akin ma coffe ne mai kyaun gaske ga kauri wanda tsakiyan sa ke a tsage anyi hanging din bari daya,a Angles (sako) din bangon da gadon yake kuwa Floor lamps (dogayen fitilun kasa) ne dogaye ko ina an aje daya.
Gaban dressing mirror din ya tsaya ya cire agogon hannunsa ya daura a saman wurin kana yasa hannu cikin Aljihun wandon sa ya fiddo da wallet dinsa itama ya daura ta a wurin ya juya ya tunkari wata kofa dake a rufe da alama kofan Bandaki ce,kofan na budewa na tsaya kallon Ikon Allah don kuwa ba toilet bane wani dan daki ne mai tsawo sai dai bai cika fadi ba akwai Wall Cabinet (durowar bango) a jikin dogon bangon dakin wadda ke a bude ga kaya nan iri iri wasu a sagale a jikin hangers wasu kuma a ninke daga gafen cabinet din kuma madaidaicin injin wanki ne wato Washing Machine a jiye.a bangon dake kallon inda cabinet din take katon Madubi ne manne da bango daga kasan shi kuma wurin d'aura mayuka ne dasu Shampoo da sabulai kala kala da alama wurin laundry ne,wato wurin wanki dasu kayan dauda,tsayawa yayi gaban tangamemen madubin wurin yana kallon fuskarsa kafin yasa hannu ya ciro wipe daga cikin wani kwali mai kyau a hankali ya fara goge Fuskansa da ita,nikam zuru nayi ina kallon ikon Allah,ya gama goge ko ina ya jefa ta cikin dustbin sannan ya tunkari Wall Cabinet din ya fara cire kayan da ke jikinsa tun daga kan rigan saman zuwa ta cikin da safar dake a kafafunsa yayi hanging dinsu jikin hangers din Cabinet din ya rage daga shi sai Vest da Short acan sama cikin wani gida ya mika hannunsa ya dauko wani abu dake a linke fari sol cikin kayan da ke wurin da alama Bathrobe ce wato rigan wanka wadda duk jikinta gashi gashi ne mai laushin gaske daga haka ya tura kopan Toilet din dake cikin wurin ya shige.
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
*By Oummu Imam📲*
*Free Page5️⃣&6️⃣*
Sanye da Bathrobe din da ya d'auka ya fito,sai da ya cire Slippers din dake k'afar sa a bakin kofan toilet din yasa wasu flip-flops dake a waje cikin laundry din,K'arasowa yayi gaban Mirror din dake a Laundry room d'in ruwa na dripping daga cikin sumar kansa da alama wanke kan yayi,Juyawa yayi ya d'aukko d'an farin towel a cikin Cabinet din bangon ya dawo gaban mirror din yana tsane ruwan cikin sumar kafin ya jawo Stool ya zauna ya rataya towel din a wuyansa a can gefen mirror din ya mika hannunsa ya d'aukko Hair dryer wadda dama a jone take ya fara busar da sumar tasa yana dan jujjuya ta da d'ayan hannun yan mintuna ya dauka yana busar da sumar kafin ya maida dryer din inda ya d'aukko ta,Hair Oil ya matsa a tafin hannunsa ya shafa ma sumar sannan ya bude robar da Cotton buds suke ya zaro daya yana kwalkwale Kunnansa ya gama goge duka kunnuwan ya jefa abubuwan wadanda ba wani dirty a jikin su cikin Wastebin.
Daga haka ya mike ya nufi kofar shiga Bedroom din har lokacin Bathrobe din na a jikinsa,gaban dressing mirror ya tsaya ya fara matso mayuka yana shafe jikinsa bayan ya gama wardrobe d'in dakin ya tunkara wadda na k'osa inga ta yadda ake buda ta gefenta na dama ya tsaya,sak'a hannunsa gefenta yayi ya latsa sai ga shi ta fara zugewa da kanta,Iko sai Allah ashe Sliding ce,a tsakiyan murfin ta akwae tsaga wadda ta raba marfin biyu daidai,in ta daman aka bud'e sai ta zugo ta rufe ta hagun haka ma in ta hagun aka bud'e,komai dai na masu arziki na daban ne,Allah kai mana Arziki mai Amfani,Amin.
Kayan sawa ne birjik a cikin ta wasu a rataye jikin hangers,wasu a ninninke gasu nan a tsare abun gwanin burgewa. Kowane kaya da wurinsu,Jeans,Shirts,Suits,Shaddoji,Yadiddika,wasu ma kayan a cikin leda suke alamar sabbi ne,ga Underwears suma wurin su daban tsarin kayan dai kaman Boutique,fiddo kayan da zai sa yayi had'i da underwears sannan ya latsa jikin marfin daga ciki ta fara rufewa ya juya ya nufi gefen gadon ya d'aura kayan.......
Bayan ya gama sa kayan wanda T-Shirt ce coffe brown da bakin wando tracksuit wanda yad'an tsuke daga k'asa gafe da gefensa akwai zip wanda sai ka k'ura idanu zaka gani,rigan kuwa ta zauna cib ajikinsa hannun rigan ya kama cinyar hannunsa wadda take a murd'e da gani yana Bodybuilding,gaban Dressing mirror ya koma ya matso wani hadaddan mai ya shiga mutsitsika ma tafin hannuwansa,bayan ya gama ya dauko Hair Spray ya fesa ma gashin kansa sannan ya daukko turaren jiki wanda kwalbar shi kanta abun kallo ce ya faffesa ma jikinsa maida kwalbar yayi ya daukko wata itama mai matukar kyau ya fesa.....saida ya fesa turare kala ukku kafin ya dau Comb yana sharce kanshi wanda yake nad'e ko ba'a sharce ba bai yamutsewa,Drawer chest ya jawo ya fiddo da wani kwali mai kyau da k'yalli ya d'aura shi gaban mirrorn sannan ya bude,wasu irin agoguna ne masu kyaun gaske designers kala daban daban kowacce a dan gidanta ya fiddo mai fata kalan rigarsa ya daura sannan ya dauki wadda ya cire d'azun ya maida ta ciki ya mayar da kwalin hadi da rufe drawer.
A corridorn ya tsaya ya ciro takalma Slide Sandals bak'ake daga cikin Shoe rag kafin ya fito parlor a daidai nan kuma telephone din ya sake fara ringing,dan girgiza kai yayi yana murmushi bai kalli inda yake ba yasa hannu ya dauki wayarsa da ya aje dazun ya fice.
Ta Corridorn daya bi dazun ya fito cikin farfajiyar gidan mai girman gaske cikin natsuwa yake tafiya ya tunkari k'aton flat din dake a cikin farfajiyar wanda sak fentin shi kalar na gidan ne,Wani farin d'awisu ne ya fito daga bayan flat din ya bude jikin shi yana kuka gwanin burgewa,bansan lokacin da ni mai rubuto maku labarin na furta"lah kuga wani hadaddan dawisu,abun ka da ba'a saba gani ba,shi kau yalla6an ko kallon shi bai yi ba ya shige Entrance din,a wani dan corridor ya tsaya ya cire takalmansa da alama nan ake aje takalma kafin ashiga main Parlour din don akwai wasu takalman jere a gefe,shiga yayi cikin parlon wanda yake mai girman gaske fentinsa milk colour yana dauke da Royal Sofas masu kyau yadin su Maroon design din kwalliyarsu golden mai kyau ga Table dinsu aje a tsakiya daga can bayan kujerun kuwa dining area ce mai dauke da dinning table da kujerun shi irin design din kujerun parlorn, gaba kad'an da dining din kofa ce ke kallon su wadda corridor ne anan kuma kofofin bedrooms suke,Pop Casting din dake a bangaren da kayan kallo suke irin na d'akin mutumin da ya shigo ne sai dae hotunan dake wurin sunfi yawa har a sauran bangarorin bangon parlourn duk an kafe hotuna manya manya,hotunan wata dattijuwa sunfi yawa wasu tayi da family dinta wad'anda suke kyawawan gaske,wani kuma tayi da turawa akwai wanda tayi da Governor yana bata Award,da kuma wanda tayi da mutananmu na nan da alama a wurin aiki ne,akwae wanda take ita kadai ta nad'a lifaya fuskanta sanye da glasses tayi daria har hak'orin makkan ta ya bayyana daga kasa an rubuta sunanta,HAJIA HAUWA ADAMU ZAKEE,Akwae hotunan wani babban mutum wanda yayi suna gaisawa da shugaban k'asa,wani kuma tare da dattijuwar matar ya riketa fuskarsu d'auke da fara'a,akwae wanda kuma yake zaune a majalissar tarayya wato National Assembly k'asan hoton an rubuta sunan shi,SENATOR ALI ADAMU ZAKEE. Akwae flowers a Angles din parlorn da A.C manne a jikin bango,Labulayen cikin parlorn kuwa maroon ne da ratsin golden masu shegen kyau.
Zaune saman kujera 2 seater dattijuwar matar dake jikin hotunan parlon ce gafenta telephone ne ajiye hannunta rike da magazine yayin da idanunta ke cikin glasses da alama Medical glass ne,da ka kalleta zaka fahimci ta manyanta sosae sai dae yanayin hutu yasa ba lalle ka iya kiyasta ainihin shekarunta ba,tana da haske don ba baka bace,ba kaman kuma da jikin ke samun hutu sosai,
Tsaye mutumin yayi a bakin kofar shigowa ya dafa bango da hannunsa d'aya yana kallon matar da murmushi a fuskarsa.
Sarai taji shigowar shi amman ta share taki d'agowa ta kalle sa idanunta na kan jaridar hannunta.
Dan gyaran murya yayi,still tak'i dagowa ta kalle sa hakan yasa ya dan d'aga kafadarsa cikin ransa yace"Mun saba aii..." cikin parlon ya shiga ya tunkari inda take zaune yasa hannu ya dauke Telephone din dake gefenta ya maidashi adan sak'on da table dinshi yake, Zaunawa yayi gefenta ya d'an kwantar da kanshi a saman kafad'arta yace "Sweetheart fuskan shanun na miye ne? "What happen?" Ya kara tambaya,banza tayi dashi hakan yasa ya juya yana kallon fuskarta hannu yasa yana gyara mata bakin da ta turo alamun fushi,ya cigaba da magana,
"Haba Beb fushin na miye ne..? kin wani turo baki,baki gan yanda kika yi muni ba,Smile plss..." ya fad'a har lokacin hannun shi na a gemun ta yana dan jan shi.Hannu tasa ta buge hannun shi kafin tace"Wato don kaga na damu da kai shiyasa nazama abun wulakanta wa ko?
"Oh no Sweethrt ya zaki ce haka..,Am not hoping to see that day,dani zan wulakanta ki,ai ko wani nagan zai wulakanta man ke sai inda karfi na ya k'are" ya k'arasa maganar yana kara kwantar da kansa a kafad'an ta.
"To amman miya sa na kira ka kace man kana zuwa harda wani cewa right away,Amman shiru ka k'i zuwa tsawon lokaci,akarshe na sake kira kak'i yin picking" tayi maganar tana dan harararsa.
D'agowa yayi daga kan kafad'arta ya rik'e hannunta guda yace "Lokacin da kika kira I just came back and I was so tired shiyasa na bari in dan rage kayan jikina in watsa ruwa don insamu karfi" ya kai maganar da d'an murmushi, "To miyasa na sake kira baka dauka ba?" har lokacin
bata saki fuska ba,
"I was about to come here,lokacin da kiran ya shiga shiyasa naga no need in daukan"ya karasa maganar yana wani lumshe ido,
"Yanxu dama duk saboda wannan ne kike ta faman daure fuska,to Am sorr.....bai karasa ba ta katse shi da cewa "bashi kadai bane" "To,what else? Ya tambaya.
Gyara zama ta d'an yi shima ya gyara zama yana kallonta alamar ita yake jira tayi magana..."yanzu tsakani da Allah kana kyauta ma kanka,ace kullum sai nayi fama da kai kafin kazo kaci abinci,sam baka son cin Abinci..."katse ta yayi da cewa "Ni kuma,duk abincin da nike ci" Yana maganar da d'an murmushi a fuskarsa "karya kake baka wani cin abinci yadda ya kamata" ta fada tana harararsa,da mamaki yake kallonta with his eyes wide open yace "Yanzu ni da girmana kike cewa karya nike" d'an ta6e baki yayi yace "nidai nasan ina ci kawai dai rigimar kice,ko kuma so kike in rinka yin cin da ya fita Musulunci,Me I don't know" ya dan buga hannunsa guda kan kujera,
"baka wani ci,d'an wanda kake cin ma ai sai kaga dama,kullum ka dawo aiki sai ka shige part din ka kadau uban lokaci wai kana wanka sai kaga dama kazo ka tsakuri abinci ka kuma fucewa,wani lokacin ma I have to called u,just like now dai" Yar ajiyar zuciya yayi kafin yace "Nidai nasan ina cin Abinci da banci ai bama za'a ganni haka ba,ji fa uban naman dake hannu na" yayi maganar hadi da d'aga hannunsa sama yana daria,
ta6e baki tayi tace"Naman daga k'arfe ko,wllh kabi a hankali inba haka ba wataran k'arfen zai d'aga ka,ace mutum ya wuni yana zurga zurga baka nan baka can amman wai sai an matsa maka kaci abinci, da daddare ma ba wani na kirki kake ci ba da anyi magana kace wani Light food kake bukata".
"Fata kike man karfen ya daga ni kenan"ya tambaya,"Ni ba fata nike ba kadama Allah ya nuna man ranar kawai dai ina so ka rik'a cin abinci sosae don kana bukatar hakan,ka daina yaudarar kanka da wannan murd'ewar don bogi ce,kullum kana dawowa direct ka wuto nan ka cika cikinka sai kaje kayi ta bauta ma jiki uwa wata mace,ni wllh ma na dade banji ko ganin mace da take ma jiki wahala irin ka ba abun naka yayi yawa",
"Haka dai kika ce ni bana ganinsa a wahala duk abunda ya dace mutum yayi don tsaftar kansa nike nothing's too much" Yaci gaba,
"Toh why not a rik'a kaiman abincin can part dina kinga in nagama wahalar jikin kaman yadda kikace sai inci ko? "Kaji dad'in kin cin kenan,a gaban nawa ma ba ci kake sosae ba, balle ba idona".
Dariya yake sosae yace "sai kinsa man ido kenan,sai kace wani karamin yaro,You know what,in kingan nadawo na dade ban nemi abinci ba bana jin yunwa ne,kinsan bai yiwuwa in dauki wannan hours din wurin aiki ba tare da naci komai ba"
Yamutsa fuska tayi tace "Abinci! Kai dinne zaka ci abinci a waje,wanda ma aka yi cikin gidan sai kaga dama zaka ci balle wanda aka yi a waje,nasan dai kasha wannan bak'in lemun d'an gado sai ko snacks kilan,suma in kagadama kenan"jingina bayansa yayi da kujerar yace"Yanzu dai zaki sa akawo man abincin ko kuwa,don am running out of time fa,ya fada yana duba Wrist