Showing 192001 words to 195000 words out of 212491 words
bashi takaici wai ace wannan yar kankanuwar yarinyarce zata zageshi jan Motar yay ya k'ara yin gaba kafin ya karya wata kwana,
Ranar laraba tunda sassafe gwaggo tayi sallama da kowa bayan an had'a mata sha tara ta arziki su Fatuu ne yan rakiya saboda Baffanta ne zai kaita jimeta a Motarsu Hijet da suke kai kaya kasuwa daga can sai ta hau Motar Katsina ko Kano, ita da Fatuu da kamalu da Mino ne abaya sai gaba Baffanta da Amadu Fatuu harda kukanta na atafi da ita, banza gwaggon tayi da ita sai yadikko ce ke rarrashinta tana cewa tayi hakuri ta k'ara kwanan masu biyu basu gaji da ganinta ba kuma in ta tafi ai sai an k'ara ganinta ko, Bayan sun dawo daga raka gwaggo kwance tayi saman gadon tana matsar kwalla a haka bacci yay awon gaba da ita lokacin data farka ne yadikko ta nuna mata abun karin kumallonta, bayan ta wanko bakinta rai a jagule take tsakuran abincin ganin tak'i sakin jiki yasa yadikkon ce mata tayi sauri ta gama ta shirya suje cin Kasuwar babbar hanya ita dasu mino tace bari ma tayi ma Kamalu Magana don tasan duk sati yana zuwa sarin rake, tana jin hakan ta d'an ji sanyi bada jimawa ba yadikkon ta dawo tace tayi ma Kamalun Magana zasu tafi tare, wuraren karfe sha biyun rana sun gama shirin zuwa kasuwar Fatuu tasha ado da shaddar da haisam yayi mata da babbar salla sosae yadikko da k'annenta ke yaba kayan bata 6oye mata ba tace ai Ya Handsome ne yayi mata don dama kullum ne sai tayi masu firarshi kaf ta basu labarin abubuwan da yake mata sosae suke yaba kirkinshi da kakarshi Hajiya, cike da tsokana yadikko tace kodae saurayinta ne don wannan hidiman tayi yawa, da sauri ta girgiza mata kai tace a'a ita ai bata da saurayi don karatu take son yi ta zama likita kuma shima baiyin soyayya koda ma zaiyi bazai yi da ita ba tunda ita karama ce shi kuma babbane kuma d'an gayu ita yadikko dan ta6e baki kawae tayi, itama Mino kwalliyar shaddar tayi cikin kayan da aka bata gwanin sha'awa yadikko ke kallonsu inda so samu ne Fatun ta dawo hannunta saidae ita kanta tafi mata sha'awar zama acan hannun gwaggon, lokacin da suka fito tsakan gidan gaba daya wadanda ke wajen sakin baki sukae suna kallonsu ciki harda Altine da tayi ado da kayan fulani suma zasu cin kasuwan ko ta kansu Fatun bata bi ba sukae fucewarsu a waje suka samu Kamalun harda ma Amadu shima yayi gayu da kananun kaya ba 6ata lokaci suka kama hanya, tun akan hanyar ake ta faman binsu dana mujiya don ba'a saba ganin irin shigar da suka yi ba wasu mutanen da basu iya hakura har tambayar Kamalu suke wai bak'i sukae ya basu amsa da eh wadanda suka san Fatuu kuma ya gaya masu itace da al'ajabi suke kallonta koda suka isa kasuwar ma nan ma dae abun kallo suka zama sai kace ansamu tv anan kuma suka hade da Jibo Mutumin da shine sanadin komawar Fatun Katsina wato wanda ta jefar ma Akuya ta mutu, yana sanye cikin shigan Fulani riga da wando da takalma fatalo shima kasa hak'uri yay ya tambayi Kamalu bak'in binni sukae yana dariya yace ya kalli Fatuu da kyau ya santa, k'ura mata ido yay saidae sam ya kasa gane wacece har saida Kamalun yayi mashi bayani sannan ya ganeta, cike da al'ajabi yake kallonta baki bude harda cewa ai shi yaga Mata wllh a tsiwace Fatun tace mashi Allah ya kyauta ta aureshi ko maza sun k'are mi zatayi dashi yadda tayi maganan yasashi cewa da kwarankwatsa itace kuwa sudae su Kamalu nata dariya, zagayawa sukae cikin kasuwa suka danyi siyayya yawanci duk abubuwan ci ne akafi saidawa su Awara, kosai, rake, danyen nono harda madarar shanu da kuma kayan noma sai yamma liss suka koma gida don daga kasuwar zagaya garin sukae har k'oramar dake bayan gidansu suka je mai tarin ni'ima da wadatar kayan itatuwa suka yi hotuna.
_____________
Ranar Juma'a lokacin kwanansu Fatuu shidda da tafiya bayan sallan juma'a iyalan Senator harda shi sanatan da kuma Hajiya Maryam itama da nata iyalin suka sauka Katsina, Senator da Matansa guda biyu Mahaifiyarsu Haisam sai kishiyarta da suke ce ma Aunty da k'annen Haisam d'in guda bakwae don su takwas ne ya'yan Senator d'in ita Aunty bata haihu dashi ba sai dae akwae diyarta guda d'aya data Haifa da tsohon mijinta a wurinta don ba'a budurwa ya aureta ba kuma likita ce sa6anin Mahaifiyarsu Haisam ita full house wife ce bata aiki tunda Senator ya aureta da k'yar ya barta ta k'ara yin karatu anan amman tun lokacin data gama ya hanata yin aiki, k'annen haisam akwae Laila ita ke bi mashi wadda yanzu haka take karatun likitanci a k'asar Malaysia kuma ita Mahaifinsu ta biyo saidae ba bak'a bace ta d'an d'aukko hasken Mahaifiyarsu ba sosae ba sai Nameer shi yanzu ya gama Secondary skul sai kuma Hauwa'u mai sunan Hajiya suna ce mata jidderh zata yi shekara sha biyar zuwa sha shidda yanzu zata shiga s.s two sai Yasmeen dake j's 2 sai Adams mai sunan kakansu suna ce mashi Affan sai twins wanda sune auta wato Mubeen da Mubeena zasu yi shekara hud'u kusan gaba d'ayansu hasken Mahaifiyarsu suka d'ebo ba kamar Haisam Nameer jidderh da twins sun fi sauran fari sosae, a 6angaren Hajiya Maryam kuwa yaranta biyar saidae da guda hud'u tazo don cikon d'ayar wato Fanan bata k'asar sai Farha wadda ita ke bima Fanan d'in sai ibraheem suna ce mashi abraham sai muhammad da yar auta Noor itama sunan Hajiya gareta, a wata dankareriyar Hummer jeep aka je d'aukar Senatorn sai Haisam da shima yaje da Benz d'inshi sai kuma Tk da yaje da Jeep d'in Hajiya, cikin shiga ta Alfarma suka iso Arrival daka kallesu ko baka san su waye ba zaka fahimci akwae masu gidan rana ba kad'an ba a tattare dasu, Mahaifiyar Haisam wato Fateema tana sanye da wata jugunannan jallabiya da tasha adon stones sai d'aukar ido take tayi rolling veil d'in kallo d'aya zaka yi mata ka shaida balarabiya ce tun daga kan kalar fatarta da kuma suffarta don giant ce tana da tsawo da kuma jiki sai dai ba jiki sosae ba daidai, sai Hajiya Maryam ma tana sanye da dandatsetsen leshi red color mai touch din ash tasa gyale ash da takalma da jakka ash sai sarkar diamond dake wuyanta da agogo harda zobensu itama babbar macece saidae bata da tsawo sosae daka kalli fuskarta kuma zaka shaida kamanninta da Hajiyar Sanata sosae, shima mai gayya mai aikin wato Senator Alee zakee yasha farar shadda ta alfarma wanda basai na tsaya fadan kalan takalmi da hula da agogon hannunshi ba don kowa yasan na alfarma ne suma, Mutum ne mai tsananin haiba da cikar kamala ga kwarjini shima giant ne don sak Mahaifinsu shi kuma ya biyo wato Gen. Adamu zakee, su Jidderh da Laila sun ci gayu da had'addar embroidery atampa anyi masu riga da skirt kowacce ta d'aura gyalenta a kafada su kuma mazan suna sanye da jeans da t-shirt wasu rigunan polo ne sabbi dal, a 6angaren yaran Hajiya Maryam kuwa gaba d'aya yaran Mahaifinsu suka biyo hakan yasa daka kallesu zaka gane turawa ne tun daga kan kwayar idanuwansu da kuma sumar kawunansu, Farha na sanye da skinny jeans ya kamata had'i da farar top ta d'aura boyfriend jacket wadda gabanta ke hangame haka kafad'ar rigar a zame take, kaman yadda k'wayar idonta ke ash haka ma gashin kanta daya fito duk da akwae gyale bak'i akanta haka kafafunta na sanye da takalma bak'ak'e masu tsini sosae tana ruke da yar purse silver, shima Abraham kwayar idonshi brown ce kalar ta Fanan haka sumarshi ma take, Mohammed irin kwayar idon farha gareshi wato ash amman sumarshi bak'a ce sai yar auta Noor wadda ba k'aramar kyakkyawa bace tana da kwayar ido blue ga yalwatacciyar sumarta bak'a ce, suna hango haisam dake tsaye yana sanye da bak'in jeans da polo shirt yellow haka agogon hannunshi baki ne yayin da glass d'in ke bada launin yellow mai shining haka idanunshi ma na rufe da glass shima mai d'an launin yellow abun saidai ace ma sha Allah kawae, su Jidderh na hango shi suka nufo shi da d'an gudu gudu suna fad'in "Bro...." da Murmushi ya bud'e mata hannuwa ta fad'a jikinshi tana ta dariya side hug Laila tayi mashi tana murmushi, janye Jidderh yayi daga jikinshi ya janyo Yasmeen dake ta kokarin ture Jidderh don itama ta rungume Haisam d'in, yana rungume da ita ya hango su twins da sukae tsaye gabanshi sun kumburo baki alamar fushi dama gasu tubarkallah bul bul dasu da gani ba k'aramin 6arna da Madara suke ba kuma identical twins ne suna bala'en kama da juna gwanin sha'awa suna sanye da jeans da t-shirt kala d'aya wato unisex, janye Yasmeen yay ya duk'a ya bud'a masu hannu alamar su taho kawae sai suka had'e bayansu suka kalli 6angare daban daban, sanin halinsu rigimammu ne yasa ya nufesu duk da k'ibarsu suna a had'en ya d'agasu sama gaba d'aya aka sa dariya harda su, sauke su yayi ya nufi Mahaifiyarshi wadda sak ita ya biyo daka kalleta zaka gane cewa mahaifiyarshi ce rungume juna sukae a gefen kunnanshi a hankali ta furta "Habibie", d'agowa yay yana Murmushi kafin yace wani abu Hajiya Maryam tace "dayake bani na haife ka ba shiyasa ko kallo ma bazan samu ba ko" k'ayataccen Murmushin gefe ya sakar mata kafin ya yi mata side hug yana fad'in "So sorry lovely Mom", kallon Auntynsu dake gefe yay tanata Murmushi itama Maroon Abaya ce ajikinta murmushi yay mata ya gaidata tare da dan kama hannunta ta amsa mashi,
"What about me Ya haisam" Farha ce tayi Maganar tana jujjuya ido, juyawa yay ya kalleta da Murmushi ya dafa kafad'arta lokacin ya hango Nameer tsaye yana kallonshi da Murmushi akan fuskarshi dama shi sarkin Murmushi ne yafi kowa fara'a a gidansu kullum zaka ga fuskarshi da Murmushi shiyasa ake saurin gane mashi in yana cikin damuwa gashi yana da mugun sauk'in kai suna kama da Haisam sosae saidae shi dimples biyu ne dashi kuma yanayin haskensu ba d'aya ba, tsaye sukae suna kallon juna ba tare da Haisam d'in yace mashi komae ba sanin halin yayan nashi yasa ya nufo shi yana dariya ya rungumeshi, suna cikin haka Senator ya dawo dama yana can wurin Mutanenshi da suka zo tarbarshi da fara'a ya bud'a ma Haisam hannu ya nufeshi suka rungume juna yana fad'in "My Pride...." d'agowa yay yana mashi Murmushi yace "U'r welcome Dad" Senator yace "thanks Son Hope u'r doing gud" kai kawae ya d'aga mashi daga haka kuma suka dunguma suka nufi wurin da Motocinsu suke yana tambayar Hajiya Haisam yace mashi tana gida shi ya hana tazo tunda can zasu yace owk bayan sun shisshiga cikin Motocin suka fita daga cikin Airport d'in Motar Escort na biye dasu, Lokacin da suka isa gidan Hajiya sam ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda tsabar farinciki don sun jima basu zo haka da yawa ba nan aka shiga gaishe gaishe da rungume rungume kan kace mi kopar gidan Hajiyan ya cika da Mutanen Senator wanda yawanci yan siyasa ne wai sunzo yi mashi sannu da zuwa da yake Mutumin kirki ne kuma adalin shugaba fita yayi suka gaisa kafin ya nemi suyi mashi uzuri ya gana da mahaifiyarshi in ya koma Gra duk maison ganinshi sai ya sameshi acan cike da mutuntawa suka yi sallama ya koma, yar kwarya kwaryar liyafa aka shirya musamman dama aka d'aukko kwararrun chefs suka shirya lafiyayyun abinci da abubuwan sha, bayan sun gama cin abincinne aka zauna ana k'ara gaisawa baka jin komae sai turanci da larabci dake tashi daga bakunan yaran jefi jefi kuma wasu sukan yi Hausa...........
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_
Littafin A Sanadin Makwabtaka Kashi na Farko wanda nayi shi a kyauta yazo karshe, Ga mai bukatar cigaba da karanta kashi na biyu wato Book 2 zai biya kudin karatu Naira 300 kacal ta wannan Account din👇
1509618776
Zainab Bature
Access Bank
Za'a turo da shedar biya ta daya daga cikin wadannan Lambobin wayan ko kuma tuntu6a don neman karin bayani, 09013804524 ko 08169856268.
Thanks and i luv u as u patronize🤝🥰
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
6️⃣9️⃣
.........Sai bayan sallar isha Senator da matanshi suka tafi gidansu na G.r.a da tuni an gyara masu shi saboda zuwan nasu cikin Yaran nasu ba wanda ya bisu duk gidan Hajiya suka ce zasu tsaya gwaggo ma ta shigo sun gaisa ta gabatar masu da ita a Matsayin Makwabciyarta mutuniyar kirki mai kulawa da ita duk da wasu sun santa da Hajiyar ba kamar Hajiya Maryam, sosae sukae mata godiya harda Senator d'in tace ai itace da Godiya abun arzikin da ake mata, sosae tayi masu godiya da Addu'oi. Satinsu guda agarin suka koma lokacin kwanansu Fatuu sha ukku wato saura kwana d'aya su dawo saidae ba gaba d'ayansu suka tafi ba an bar wasu daga cikin yaran zasu k'arasa hutunsu dama saida aka jira suka yi hutun sannan aka taho cikin wanda aka barin harda Nameer da jidderh sai twins da suka nace suma sai an barsu wurin granny haka suke ce ma Hajiya sai Farha ma bata tafi ba tare zasu koma Abuja in sun tashi daga can sai ta koma Lagos ita Laila Makaranta zata koma dama bata dad'e da zuwa ba don bata samu zuwa da salla ba ita Fanan ma bata samu zuwa ba duk da taso zuwan Daddy d'inta ya hana yace ta zauna gidan d'an uwanshi wanda likita ne acan india d'in tayi sallar,
A 6angaren Fatuu kuwa tunda sati na biyun ya kama ta kimtsa kayanta tsaf tana jiran ranar tafiya kullum in aka kwana sai tace saura kwana kaza yau da ya rage saura kwana d'aya su cika sati biyu sam ta kasa zaune ta kasa tsaye har bata iya 6oye farincikin da take ciki su kam su yadikko basu son ta tafi ba kamar kannenta tuni sun fara jin kewarta ba kamar Mino duk tafi kowa damuwa har cema Innarta tayi itama abarta ta koma can yadikkon tace a'a abun zaiyi yawa karma ta sake jin ta fadi haka, a ranar da daddare bayan Baffanta ya dawo ne yake sanar da ita tafiyarsu gobe Asabar bazata yuwuwa ba sai jibi in Allah ya kaimu don akwae siyayyar da yake son yi mata kuma sai goben ne Kasuwar da zaije ke ci cikin abunda zai siyo harda sak'on Fatun na tsarabar da zata kaima Haisam ba haka taso ba amman jin harda tsarabar Haisam za'a siyo yasa ta hak'ura hakan kuma ba k'aramin dad'i yayi ma Mino ba, a kwana a tashi ba wuya a wurin Allah duk abunda aka sama rana zai zo harma ya wuce a daren ranar Lahadi baccin Fatuu ragaggene saboda d'oki har k'agara tayi garin ya waye, Asubahin farko ta farka ko jiran yadikko batayi ba taje ta d'aura ruwan wankanta lokacin da yadikkon ta farka saidae ta ganta tana shiryawa da sabbin kayan Fulanin da Baffanta ya siyo mata Navy blue, Murmushi kawae tayi don ta gama fahimtar duk zumudin saboda taje taga Haisam ne, ana gama sallan Asuba suka fito don tafiya dama tun jiya da daddare tayi ma kowa sallama kuma ba laifi sun bata Abubuwa harda kudade haka Mahaifinta ma da Yadikko sun had'a mata sha tara ta arziki, har kopar gida suka rakota dama shi Amadu tuni sun fito shida Kamalu don zai rakasu ne, Mino nata matsar kwalla don itama sam batayi baccin kirki ba saboda tafiyar Fatun da ta saka a ranta gashi an hana tayi masu rakiya zuwa Jimeta inda zasu hau Mota, suna ta d'aga masu hannu bayan sun hau Mota Baffanta yaja suka tafi, Lokacin da suka isa jimeta basu samu Motar da zata kaisu direct Katsina ba hakan yasa suka hau ta Kano har saida suka ga tashinsu suna ta d'aga masu hannu cike da kewa suna masu Fatan Allah ya kiyaye hanya ya kaisu lafiya.
Sam bata jin tafiyar ko bacci ta kasa yi burinta kawai ta ganta a Katsina hakan yasa bata takura ma Amadu ba sosae, sai bayan Azahar suka iso Kano ba 6ata lokaci suka samu Kano line mai zuwa Katsina, tunda suka kamo Hanya take ta sakin Murmushi don har ta fara jiyo kamshin Katsina, akace wai karfen Nasara ba Tabbas kwatsam Mota ta lalace masu a hanya har sunyo nisa sun kusa garin Kankia ta jahar Katsina, tun ana ganin zata gyaru har aka fara fidda ran gyaruwarta duk Mutanen ciki sun fito waje sun zazzauna a gefen hanya ciki harda Fatuu tana a wurin da Mata suke fuskar nan sam ba annuri murna ta koma ciki sai tsoki take bugawa Matar dake kusa da ita tun a Mota mai kirki ko abu zata ci sai ta bata ita ke bata baki tana nuna mata tayi hakuri komi Allah yayi mai kyau ne k'ilan da akansu matsalan zata faru ta faru akan Motar, ita dae jinta kawae take can ta mik'e ta nufi wani gida dake can gefe inda taga ana zuwa yin fitsari taje tayo bayan ta dawo ne ta nufi inda Amadu yake tana ta tura baki tace mashi wai ba'a kusa Katsinar bane su k'arasa ko a k'afa ne, wani kallo yayi mata kafin yace "an kusa baifi awa guda da wani abu ba sai ki taka ki k'arasan" yay Maganar yana harararta tana tura baki tace "ai wllh don bansan hanya ba dana tafiyata",
d'an girgiza kai yay yace" indai hanya ce wannan ba matsala bace mik'ewa zaki