Showing 54001 words to 57000 words out of 212491 words

Chapter 19 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

1004

wawware"Co,co ca,co-la,da fannntah...",
"Wai Gaye yane,mike faruwa ne anan wurin naga ana d'aga lemu ko kawo mana akai mu k'ara ne?" Goga ne yayi maganar wanda tuni suka diro ciki shida dayan suka zauna inda suke da suka ci gaba da bushe-bushensu,Gaye ya waiga yace"baabah ina yarinyar nan wanda muka hadu d'azun da safe na baka labarin ta rotsa ma wani mutum gilashi harma na nuna maka gidansu mutumin?" Goga yace"eah baabah na ganeta wata yar fara mai kumatun nan ko,mi ya faru da ita ne?",

"kaganta nan tazo wai abun mamaki mutumin nan yace ya yafe mata,yanzun nan ta dawo daga wurinshi kaga harda lemunan gora ya bata,shine tazo ta fada man" wata yar iskar dariya gogan yayi yace"yo kai baabah wannan ai ba wani abun mamaki bane,taje ta basa gurasa ba dole ya yafe ba" Gaye ya juyo yana kallon fatuu fuskarsa dauke da yar dariya yace"shegiya Aljanna yar k'arama dake kinsan takan abun,ashe gurasa kika gutsira masa,ahh dole ya yafe kam" cikin rashin fahimtar zancensu da sauri tace"ni wllh ba wata gurasar dana kai masa,yo ni ina naga wata gurasa,dama a bokonmu ake saidawa to kuma yau bama ranar zuwa bace..."

Wata mahaukaciyar dariya gaba dayansu suka kwashe da ita harda gaye,ganin haka yasa fatuu ta d'an tsorata ta juya zata tafi,caraf taji gaye ya ruk'o hannunta,da sauri ta juya tana kallonshi cikin fushi tace"kai Gaye miye haka da Allah sake man hannu ni in tafi gida" kai tabar wiwin dake hannunshi yayi wurin bakinta yace"haba Aljana ya zaki kawo mana ziyara har fadarmu kitafi ba tare da kin ta6a komai ba,kinsan mu akwai karamci,kidan busa kema" da karfi ta buge hannunshi cike da masifa tace"Allah ya tsari kakata Dije,Allah ya kyauta in sha wannan abun,ni ba yar iska bace..." jin hakan yasa Goga da 6aure durowa daga saman windunan da suke zaune suka nufosu a kausashe goga ke fadin"kee,to su waye yan iskan kenan,ai kece ma babbar yar iskar da daren nan fa kika je wurin wani k'ato ya gama dak'una ki,shine don kin raina mu kin d'auke mu masu kawunan kifi zaki wani zo kice wani ya yafe maki hakanan,k'anin gyatumarki ne shi ko na gyatumin ki iyehh??" shuru tayi tana kallon shi ganin yadda yake maganar yasa taji tsoronsu ya kamata gashi sunyi mata rumfa,da sauri ta juya zata fice Goga yasa kafa ya tad'iyota ta yo baya ta fad'i kasa da6ar ass dinta ya daki wani dutsi,da karfi ta saki wata razananniyar kara tace"Wayyo Allah gwaggo!!"

Haisam na komawa falon ya kashe laptop din ya kaita saman desk ya ajiye kafin ya dawo ya dauki cup da can din lemun daya sha ya jefa cikin wastebin din parlon shi kuma cup din ya nufi fridge dashi saida ya dauraye shi a wani d'an madaidaicin basin dake makale a bango gefen fridge din kafin ya maida shi ciki,yaje ya kashe kayan kallo ya rage hasken fitilun wurin baifi guda biyu ya bari a kunne ba,daga haka ya nufi Bedroom hannunshi ruk'e da wayarsa,yana shiga ya jefata saman gado ya wuce cikin laudary,toilet ya shiga yayi brush daga haka ya fito,yaso ya watsa ruwa duk da yayi after ishaa sai dai ya gaji so yake kawai yaji sa a kwance,yadda yake ba tare da yasa sleeping dress ba ya haye gado,saida yayi addu'ar kwanciya kafin ya mika hannunshi yai switching fitilan dakin off daga haka ya kwanta ya lumshe idanunsa alamar bacci.

*** *** ***

Duk'awa Goga yayi inda take zaune tana ta murza wurin da dutsen ya cakar mata yace"kina nufin tafiya zaki batare da muma kin d'an sammana ba,haba ke kuwa,ai ance yaba kyauta tukuici,da gaye bai sanar dake gilashin nada tsada ba ai bazakiyi tunanin kije ki rokesa ya yafe maki ba ta hanyan basa abun dadi" yunkurin mikewa ta fara yi duk da radadin da take ji,hannu yasa ya dannata ta koma kafin yasa duka hannuwansa yana k'okarin kwantar da ita,lokaci guda fatuu ta gane abunda yake kokarin yi mata da sauri ta shiga kiciniyar mikewa tana fadin"ni ka kyaleni,wllh ba abunda naje yayi man saboda Allah ya yafe man,cewa yayi in daina rashin jin magana..." ganin abunda goga ke yi yasa Gaye da sauri ya duk'a gabansa"baabah mi kake kokarin yi haka ne,don Allah rabu da ita ta tafi,zai iya yuwuwa ya yafe mata hakanan kasan suna da kudi sosai fa,miliyan ba wata tsiya bace a wurinsu kyautarta ma sai suba mutum" harara Goga ya dalla ma Gaye yace"koma dai miye yasin bazan ga samu inga rashi ba,abu har gida dama na jima ban k'ara samun irin damar nan ba tunkan yarinyar nan hajara",
juyawa yayi yace ma dayan"kai 6aure zo ka kama man in daure shegen bakin nan nata inba haka ba zata tona mana asiri ne" jin haka yasa fatuu kwara baki tace"Wayyo na shiga ukkuna,a taimaken...bata karasa ba ya buge bakin da karfi,a fusace ya juya yace ma Gaye"dallah kai kuma ka rike man kafafunnan nata" baki na rawa yace"don Allah Goga ka kyale yarinyar nan,abun da fa kake shirin yi ba k'aramin laifi bane wllh,hukuncinsa fa daurin rai ne,kana jin yadda kullum ake sanarwa,kuma kaga ta san mu, ba kamar ni har gidan iyayena ta sani wllh asirinmu tonuwa zaiyi baabah" tsawa ya daka mashi yace"to ni wawa ne da zan bari ta tona mana asiri,dallah zo kaji yanda zamuyi" matsawa Gaye yayi gab da shi,alamu yayi masa na ya kawo kunnansa,ya rad'a masa wata magana,a firgice Gaye ya d'ago yana kallon Goga ta hasken fitilan wayansa dake rike a hannunshi,lokaci guda ya shiga girgiza masa kai alamar a'a,ganin haka yasa fatuu k'ara rudewa duk da bata san miya fada masa ba,kara k'arfin wurga kafan da take tayi saboda Goga da 6aure sun riketa gam,ga gefen bakinta ya fashe saboda bugun da yakai mata........,

A hankali ya bud'e idanunsa cikin duhu yana kallon ceiling,duk yadda yaso ya kwanta don yayi bacci ya kasa baccin,abunda yafi d'aure mashi kai tunanin ina yarinyar taje da ya tsaya masa a rai,bai ga dalilin da hakan zaisa ya zama restless ba,juyawa yayi ya koma yana facing window yayi shiru yana tariyo hiran da sukai da ita cikin ransa kaman maison gano wani abu....,
"_*_uhm nasan gaye sai yayi mamaki sosai idan yaji ka yafe man,shida yace wai ko dan gidanmu ne kai bazaka yafe man ba,dole sai an biya ka,ko kuma akaini gidan yari,aiko sai na fada masa to ka yafen inna ganshi,nasan yanzu haka suna can kangon da suka saba zuwa yin shaye-shayensu,Allah dai ya shirye suu...._" tuno wannan maganar ta fatuu yasa shi tashi zaune da d'an sauri hannu ya kai ya kunna fitila haske ya gauraye d'akin ya jingina bayansa ajikin headboard,a fili yace"kar dae yarinyan can wurin wannan Drug abuser din taje da daren nan don ta fad'a masa I forgive her..."da sauri ya saukko da kafafunsa ya dau wayarsa ya nufi kofar fita a korido ya tsaya ya sanya wasu slippers a kafarsa daga haka ya fice.


Tsawa Goga ya kwatsa ma Gaye"dallah ka rike man kafafunta,in kai baza kai ba mu zamu yi,kasan kuma ba fita zakai ba,gara ma ka bamu hadin kai kawai muyi yadda na fada maka" ba yadda gaye ya iya dole yabi umarnin goga don shine babbansu ko kayan harkar ma shike kawo masu su siya wani lokacin ma kyauta yake basu don shi mutumin manyan mutane ne,d'an bangar siyasa ne na kirki.
Rike kafafuwan fatuu ya fara kokarin yi ta han6arar dashi tana girgiza masa kai,a fusace Goga yace"dalla ka riketa da kyau shegen karfi ne da ita kaman doki" tasowa yayi ya kama kafafun da kyar ya danne su,Goga ya kalli 6aure yace"ina wannan hankacin naka cire sholin ciki ka daure mata baki" ya amsa da toh shikuma goga ya rike ta gam dama duk yafi su girma,bayan ya d'aure bakin,goga yace mashi ya zagayo ya fiddo nashi a cikin aljihun shi ya daure mata hannuwa,6aure ya sake amsawa da toh yayi yadda yabashi umarni,wata yar iskar daria goga yayi yace"yauwa komai ya zama ready,6aure zo ka rike hannuwan don tana iya kwancewa" rike hannuwan 6aure yayi shi kuma ya mike tsaye.....,

Tsaye Haisam yayi cikin center din yana haska gidajen wurin da fitilan wayansa,kokari yake ya gano ko akwai kango a wurin,sai dai a iya haske-hasken da yake baiga wani kango ba yawancin uncompleted buildings din dake layin duk arufe suke da kofofi wasu Gate,dan k'ara gaba yayi yana ci gaba da haskawa har yazo kusan karshen layin baiga kango ba hakan yasa ya fara tunanin ko he was wrong about d girl..."

Daidai saitin kafafun fatuu Goga yazo ya fara kokarin cire belt din tsohon jeans din jikinshi,duk da rirriketan da sukai bai hana ta girgixa kai ba tana dan motsa kafafunta kad'an saboda danne su da Gaye yayi,ga wani gurnani da take,ganin goga na k'okarin cire wandonsa yasa ta k'ara karfin gurnanin da take yi......

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story_


_*BY ZAINAB LALUH📲*_


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


*3️⃣0️⃣*

Juyawa haisam yayi da niyyar barin layin gurnanin da fatuu ke yi ya sauka cikin kunnuwansa abun ka da dare gari yayi tsit da sauri ya juya baya trying to locate inda abun ke fitowa,yana d'an kara taku ya ga kofan shiga wurin wanda take bude ba kofa daidai lokacinne kuma fatuu ta kara k'arfin gurnanin,da sauri ya kutsa kai without second thought ya nufi inda yake jin abun na fitowa,
".....dallah Gaye ka riketa da kyau,wai ya zaka bari k'aramar yarinya tafi karfinka ne,na gaya maka idan kai bazaka yi ba mu wllh sai munyi......."
Wannan maganar ta Goga ita tayi ma Haisam jagora zuwa dakin da suke,yana isa bakin kofan d'akin ya haske su da fitilan wayansa da take da haske sosai lokacin goga na niyyar afka ma fatuu,ai suna ganin an haskesu su duka suka nufi windunan wurin da gudu zasu dire,cikin zafin nama haisam ya bisu yana k'okarin kamo goga wanda ke gudu saman wandonsa rik'e da hannunsa,cakk haisam ya tsaya sakamakon wani rad'adi daya ji tun daga kasan kafarsa har tsakiyan kansa,a hankali ya maido kafansa ta dama baya ya haska kafan hagunsa don a jikinta ne yake jin rad'ad'in,kwalba ce ya taka ta hudo ta k'asan takalminshi ta shige cikin kafan sosai,a hankali ya duk'a yasa hannunsa na dama yana kokarin cire kwalbar,sai dai ba karamin yanka tayi masa ba radadi yake ji sosae,runtse idanunsa ya yi yasa hannu ya cije lip dinsa na k'asa da k'arfi ya fisgo ta,har saida yayi dan sound a hankali"ahhh..." saboda azabar da yaji,aikuwa nan da nan jini ya fara zubowa kaman yana jira...

Ita kam fatuu tana ganin duk sun ruga ta fara kiciniyar kwance hannuwanta cikin sa'a d'aurin ya saki ta samu ta fiddo hannuwanta a gigice ta mike ko tsayawa kwance bakinta bata yi ba ta nufi hanyar fita cikin rashin sani saboda kidimewa da tayi ta kaima bango karo a tunaninta nan ne kofar fita,taga-taga tayi tayo baya gabadaya zata fad'i,ganin haka yasa Haisam da ke haskata tun lokacin data mik'e tarbota cikin zafin nama don ba k'aramin buguwa tayi ba,ba kamar goshinta ji kake wani K'UMM!,
Sosai ya rungumeta ganin tana ta son kwacewa ta gudu a hankali ya dan duk'a yakai bakinsa saitin kunnanta wanda kanta ke saman cikinshi cikin calm and cool voice yace "is okey,u are safe now" lokaci guda ta gane voice dinshi hakan yasa ta lafe ajikinsa ta kankameshi sosae jikinta sai faman rawa yake da gani ta razana sosae,yayin da shi kuma azaba da radadi keta damunsa a tafin kafarsa haka ya daure ya kai hannu ya kwance hanki din dake rufe da bakinta ya jefar cike da kyankyami don k'auri kawae yake,

bayan wani dan lokaci ganin ta daina kermar ya janyeta a hankali gefe guda ya haska mata tasa takalmanta ya duka ya d'aukko gyalenta dake agefensa ya d'an yarfe shi sannan ya mika mata,ta amsa ta yafa shi saman kanta wanda tuni gashinta ya warware yayi kaman fanka don tana da cikar gashi sosai,a hankali yace"mu tafi"yayi maganar yana haska mata hanya,da kyar ya daga kafansa ya fara tafiya duk da zafin da take masa haka ya daure ya rik'a takata a hankali jini naci gaba da zubowa saboda taka tan da yake,
Tana gaba yana bin ta a baya yana haska mata hanya har suka iso bakin kofan fita daga ginin gidan,yana k'okarin sa kafanshi a hankali ya fita yaga ta juyo da sauri zata koma ciki tsayawa yayi yana kallonta ganin haka yasa da sauri tace"lemunana zan daukko" ji yayi kaman ya fizgota ya wawwanka mata mari saboda haushi da ta bashi,tsawa ya kwatsa mata yace"C'mon leave this place...!bakinki ne lemun" da sauri ta juya taci gaba da tafia sumi-sumi.
Tana zuwa k'arshen lungun gidan Hajiya ta juya zata karya kwanar gidansu Haisam dake can bayanta saboda a hankali yake tafiyan ya dan d'aga murya yace"muje gidan hajia" ba musu ta juya ta nufi gidan,ta riga shi isa hakan yasa tayi tsaye a bakin kofan parlonsa,bayan d'an lokaci ya k'araso tana ganin ya shigo part din ta tura kopan falon da sauri ta shige,tsayawa yayi bakin tap din da ake ba flowers ruwa ya wanke kafan da takalmin wanda gaba daya kalansa ta koma ja saboda jinin da kafansa keta fitarwa har lokacin,abunka da dan madara,tana shiga ta nufi can gaban armchairs inda tayi kneel down d'azun ta durkushe,

Shigowa yayi bai ko kalli inda take ba a hankali ya nufi kujera ba tare daya cire takalman kafansa ba ya zauna,hannu ya kai ya dauki tissue box ya 6allo mai d'an yawa ya ninninkata kafin ya tura kasan foot dinsa dake zubar da jini,bayan yayi hakan ya mike ya nufi hanyar bedroom d'insa yana dan jan kafan a hankali,binsa da kallo fatuu tayi ta d'an yamutsa baki alamar tausayi,sai da ya shige sannan ta juyo,fitowa yayi hannunshi rike da dan first aid box na karfe ya tsaya ya kunna fitilan sama don ba haske sosai kafin ya nufo cikin parlon,komawa yayi inda ya tashi ya zauna,ita dai fatuu sai binshi da ido take,
d'age kafan yayi saman table ya bude akwatin ya fiddo d'an scissors ya fara yanke bakin wound din da kwalbar taji masa,ganin haka yasa fatuu cije hakora tayi wani d'an sauti"shuuu! Sai lokacin yayi mata kallon kasan ido hakan yasa da sauri ta sunkuyar da kanta,dressing din ciwon yayi ya nad'e saitin ciwon da bandage,
Bayan ya gama ya d'ago ya kalleta itama kallon shi take,alamu yayi mata da kanshi tazo da sauri ta mike ta matsa gab dashi ta duka cotton ya ciro ya dangwali spirit ya mika mata yace"goge nan" ya fad'a yana nuna mata gefen bakinsa,hannu na rawa ta kar6i audugan ta fara goge inda ya nuna mata sai dai sam ta kasa goge jinin dake a wurin wanda har ya fara bushewa,wata cotton din ya ciro ya dan duk'u yayi mata alamu da hannu ta matso da kanta,goge mata jinin yayi kafin yace"kije wancan room din da kika je d'azun ki wanke face dinki ki ciccire abubuwan dake a kanki ki kulleshi"yadda yayi maganar kaman an masa dole,

Da sauri ta mik'e ta nufi d'akin don yin abunda yace tayi,kaman sabon kamu haka kan ya mayar da ita,a hankali ya cira kai yana kallon bayanta har ta shige d'an guntun tsoki yayi kafin ya mik'e ya daukko dustbin ya kwashe cottons din da sauran abubuwan ya zuba ya maida shi wurinshi ya dawo ya rufe box din bayan ya maida komai ciki,jingina bayansa yayi yad'an kwanta jikin kujeran,

Fitowa tayi bayan duk tayi yadda yace gefen c-table ta durkusa saida ya dau wasu seconds sannan ya d'ago ya kalleta fuskan nan babu yabo ba fallasa hakan yasa tasha jinin jikinta,goshinta ya kalla wurin yayi ja amman bai fashe ba,dawo da kallon yayi cikin idanunta ganin yadda ya d'aure fuska yasa tayi saurin sunkuyar da kanta,can ta d'an d'ago taga har lokacin kallonta yake kasa dauke idanunta tayi itama ta rinka kallonshi tana motsa baki kaman zata ce wani abu sai kyakkyafta idanu take,
yatsansa ya mik'a ya nuna mata fridge"je ki daukko" sumi-sumi ta nufi fridge din ta bude ba tare da ta tsaya za6a ba kawai ta daukko guda ta juyo,kafin ta k'araso inda ta tashi ya mike yana nuna mata hanyar fita,ta juya ta nufi kopan shi kuma ya bi bayanta a hankali yake taka kafar,

Fitowa gwaggo tayi daga d'aki hannunta rike da buta ta nufi band'aki,bayan ta fito har ta nufi dakinta zata shiga sai kuma ta juyo ta nufi dakin fatuu don ta kashe mata hasken wutan da aka maido bada jimawa ba,tana d'aga labulan da niyyar ta sak'a hannunta ta latsa switch ta hango gadonta wayam bata a kwance ajiye butan bakin kopar dakin tayi ta shiga ciki don tabbatar da abunda ta gani aikuwa dai bata a ciki da mamaki cikin ranta tace"to ina fatuun take ne?ko bandaki ta tafi...ai kuma daga can nike tabbas ba can taje ba" rike ha6a tayi tana d'an tunani can ta tuno da d'azun ta tambayeta zata gidan hajiya ai,a fili tace"kar dai wai har yanzu yarinyar nan bata dawo gidan nan ba" tsoki tayi ta juya hanyar fita tana cewa"fatuu ho badai ayi abun arziki da ita ba sai tasa mutum surutu" hanyar zaure ta nufa tana shiga suka hade da Amadu ya shigo hannunsa dauke da kwali ya kwaso kaya aciki ganin gwaggon yasa shi ajiye kwalin a k'asa yana fadin"gwaggo lafia?" tace"lafiya lau fatuu zaka taimaka kaje ka taho da ita kaman yadda aka saba dai"tayi maganar tana yar dariya,shima murmushi yayi yace"wai dama bata gidan ashe" gwaggo tace"eh dazun bayan na dawo tace man wai hajiyar na nemanta shine nace taje amman kar ta bari har ka tashi amman kaga har yanzu bata dawo ba..." daria yayi yace"yanzun haka suna can bacci ya kwashe su,watarana fa haka zaki ga sun hada kawuna sun saki baki suna ta bacci ita da hajiyar sai naje ne nake tashinsu ita hajiyar ta wuce daki" gwaggo dake dariya tace"ina ruwan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login