Showing 198001 words to 201000 words out of 212491 words

Chapter 67 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

1002

wanda tasan ita dae bata taka ta ba suma sauran yan cikin falon kallon suka bita dashi har ta shige Corridor Nameer ne ya matso wurin Fatun ya mik'a mata hannu alamar ta kama ta tashi bin shi da ido tayi kaman zatai kuka ya jinjina mata kai alamar ta tashin, kama hannun nashi tayi ya d'agata ta mik'e suka nufi kujerar da suka zauna da farko ya zauna a kusa da ita yana ce mata sorry suma sauran hak'urin suka shiga bata su twins suka zo gabanta suna tatta6ata suna cewa "Sorry sis Fatuu Aunty Farha is wicked" duk abun nan Haisam na zaune shiru bai ce komae ba saidae daga yanayin fuskarshi zaka fahimci bai ji dadin abunda ya farun ba duk yadda taso kar tayi kuka ta kasa daurewa abun yayi mata ciwo gashi jikinta yayi sanyi don ta fahimci bata samu kar6uwa a wurin farhar ba dama d'azun taga yadda ta kwatsa masu twins tsawa da suna nuna mata ita, sharrrr kwalla suka fara zubo mata da sauri ta duk'ar da kanta Nameer nata bata hakuri yana k'okarin goge mata hawayen saidae ta hana, harda Hajiya da jidderh keta bata hakurin can ta mik'e tsaye cike da nuna damuwa Nameer yace "ina zaki?" a hankali tace "gida" mik'ewa yayi ya kama hannunta yace "muje in raka ki to" suna niyyar tafiya Haisam ya d'aga mashi hannu alamar dakatar dashi ba tare daya ce mashi komae ba, tsayawa yayi yana kallonshi haka ma Fatun, hannu yasa ya cire rigar Fulanin jikinshi ya maida tashi kafin ya mik'e idonshi akan Fatun yayi mata alamar su tafi da kanshi Nameer ya saki hannun nata ta bi bayan Haisam da yayi gaba duk suka bita da kallon rashin jin dadi Hajiya tace "Kiyi hakuri Fateema kinji, taji zafi ne shiyasa har tayi maki hakan" kai kawae ta d'aga mata suka fice, suna Fita Hajiyar ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom rai 6ace duk da ita tayi zaton da gaske takata Fatun tayi amman don mi zata yi mata haka, jiki asanyaye Jidderh ma ta nufi hanyar Bedroom su twins suka bi bayanta suna kunkunin Aunty Farha muguwa ce ya rage Nameer ne kad'ai a falon idonshi akan tv sai dai can k'asan zuciyarshi wani irin takaici ne ya turnuke shi lokaci bayan lokaci yake jan tsoki..............


ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,

ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE๐Ÿ‘ฐ,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWAโญYAR LELE AGUN MIJINTA๐Ÿ˜ SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI๐Ÿค

*๐Ÿ’–A SANADIN MAKWABTAKA๐Ÿ’–*

_A heart touching story of Love and Destiny_ ๐Ÿ’”


*Mallakin*
โฌ‡๏ธ
*๐ŸŒนZAINAB LALUH*๐Ÿ“ฒโœ
_~(Oummu imam)~_

Littafin A Sanadin Makwabtaka Kashi na Farko wanda nayi shi a kyauta yazo karshe, Ga mai bukatar cigaba da karanta kashi na biyu wato Book 2 zai biya kudin karatu Naira 300 kacal ta wannan Account din๐Ÿ‘‡

1509618776
Zainab Bature
Access Bank

Za'a turo da shedar biya ta daya daga cikin wadannan Lambobin wayan ko kuma tuntu6a don neman karin bayani, 09013804524 ko 08169856268.

Thanks and i luv u as u patronize๐Ÿค๐Ÿฅฐ


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

7๏ธโƒฃ0๏ธโƒฃ


........Yana gaba tana biye dashi suka fito Harabar gidan, d'an dakatawa yay ta k'araso inda yake don ya d'an yi mata nisa ganin tana niyyar nufar gate ne yasa yace ta biyo shi part d'inshi, saida ya shiga kafin itama ta shiga ta tsaya gefen kujera shi kuma ya zauna, d'an kallonta yay suka had'a ido ta daina matsar kwallan amman idanunta sun d'an yi ja ba sosae ba, nuna mata armchair yay da hannu alamar ta zauna ta matsa a hankali ta zauna still kallonta yake yama rasa mi zaice mata, d'agowa tay a hankali suka sake had'a ido calmly ya furta "am sorry about what happened" jinjina mashi kai tayi tana d'an motsa baki ya sake cewa "Nagode da tsaraba" nan ma kai ta sake jinjinawa,
"Ko baki yi hakurin bane?" a hankali tace "nayi" yace "Owk smile mana kin d'aure fuska bai maki kyau ba" bata san lokacin data saki Murmushi ba tana kare bakinta da tafin hannu hakan kuma ba k'aramin dad'i yay mashi ba ganin tayi Murmushi, shiru suka d'an yi can tace "kasan ya akai nasan wad'anda zasu yi maka" ta d'age ido, girgiza mata kai yay alamar a'a taci gaba "akwae wani d'an film d'in india mai irin jikinka to a wayan kawu Amadu akwae film d'inshi shine na nuna ma Baffa nace kaman wanda zai mashi zai sai ma yace man ai ya sanka zai gane wanda zasuyi makan" fuskarshi asake da d'an Murmushi cikin cool voice d'inshi yace "Wanda muke kama kenan?" da sauri ta girgiza kai tace "a'a shi wannan a fuska ne kuke kama amman jikinku ba iri d'aya ba wanda na nuna ma baffan shine keda irin jikin ka ni bansan sunanshi ba dae amman yana yawan yin Film d'in india kuma mai k'arfi sosae suke sa shi",
still yay yanata kallonta har ta gama ya jinjina mata kai kafin yace "kina sa man ido sosae kenan har kika san jikinmu d'aya dashi ko" ya d'age mata gira, kyalkyace mashi tayi da dariya tana sunna kai tace "a'a wllh Ya Handsome ba saka maka ido nike bafa ba na sanka ba" d'an ta6e baki yay da d'an Murmushi akan fuskartashi can ya d'aga hannu ya duba wrist watch d'insa dake nuna karfe goma saura yan mintuna hakan yasa ya mik'e yace mata yana zuwa tace mashi to, hanyar Bedroom ya nufa tana ta kallon bayanshi yana kaiwa bakin Corridor ya d'ago mata hannu batare daya juyo ba ya furta "kallon ya isa hakanan" dariya tasa ta kwantar da bayanta a jikin kujeran, bai dad'e ba ya fito ruke da wata babbar leda mai d'auke da tambarin M. ZAKEE's STORE wato store d'in Mamansu Farha Hajiya Maryam, a gabanta ya ajiye ledar yace "nima ga nawa tsaraban" da sauri ta d'ago ta kalleshi tace "ta Lagos da kaje?" kai ya d'aga mata cike da murna ta duk'a zata bud'e yace ta bari sai taje gida yanzu dare yayi ta tashi ya rakata tace to, mikewa tayi tana kokarin d'aukar ledar ya rigata d'auka yace suje ta shige gaba yana biye da ita suka fita, suna akan hanya ta kai hannu tace ya kawo itama ta ruk'e hannu d'aya ba tare daya ce mata komae ba ya sakar mata suka cigaba da tafiya duk da ruk'on jakkar bai mashi dadi ba don bai yi balance ba, tana ta bashi labarin wuyar da suka sha saboda mota data lalace masu a hanya har suka k'araso kopar shiga gidan ya sakar mata Ledan yayi mata saida safe yana shirin juyawa ta kira sunanshi ya waigo tace "Nagode da tsaraba nima" Murmushi kawae yay mata ta d'aga hannu tana mashi bye bye shima ya d'an d'aga mata hannunshi guda kafin ya juya ya tafi.

Lokacin data shiga ciki d'akin gwaggo ta nufa har lokacin Amadu na ciki ya kishingida kan kujera gwaggon na zaune a gefen gado da alama fira suke Fatun ta shigo da sallama ta nufi gwaggo tana washe baki Amadu yace "ai munyi zaton acan zaki kwana keda hankalinki ragaggene" bata tanka mashi ba ta aje ledar gaban gwaggo tana Fad'in tsaraba ce itama Ya Handsome ya bata ta Lagos daya je, fiddo abubuwan dake aciki ta fara yi, Wata hadaddar School Bag ce da takalma cambus guda biyu a cikin jakar akwae littattafai na karatu dana rubutu wato exercise books da textbooks masu yawa don duk manyan Subject d'in da ake a Senior secondary akwae textbook nashi ga uban biroka fensir shafana kilina da sauransu dae abubuwan gwanin burgewa irin na yan gayu don wannan da gani duk Makarantar tasu ba lallae asamu mai irinsu ba ba kaman jakar goyon irin mai trolley din nan ce, saboda tsabar farinciki har ta kasa Magana sai faman d'aga kayan take gwaggo ma dariya ce akan fuskarta, juyawa tayi tana nunnunama Amadu kayan yace "inyee yar gidan Ya Handsome sai nima ki dibar man rabona to" mak'e mashi kafad'a tayi yace wllh bata isa ba wannan uban kayan ya zata yi dasu tace ai tasan harda Haulat shiyasa ya siyo su da yawan yace to shima harda shi ai aka siyon gwaggo dae nata dariya tana girgiza kai, koda ta gwada takalman ba k'aramin kyau suka yi mata ba gashi sunyi mata daidai sai faman washe baki take tana nuna ma gwaggo kafar tata ita kuma tana yin Addu'a, mik'ewa Amadu yay yayi masu sallama dama tun d'azun yake jin bacci daurewa kawai yake yana ma gwaggo firan ruga, bayan ya tafi gwaggo tace "to ki maida su ciki kije kiyi wanka ko kya ji dad'in jikin kinje kin zauna gashi dare ma yayi sosae kije dae kiyi ki rufe kanki kuma ki tabbatar kinyi Addu'a" kai ta d'aga mata bayan ta mayar dasu suka fita tare don ta had'a mata ruwan wankan. Washegari suna gama yin karin kumallo taje tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atampa ta yafa mayafi ta nufi gidan Hajiya don kai mata sauran tsarabar lokacin k'arfe goma da wasu mintuna, lokacin data shiga Falon Hajiyar na zaune kan kujera tana kallon labaru su Jidderh kuma na kan Dining table suna yin breakfast don basu dad'e da tashi ba, da sallama ta shiga Hajiya ta amsa mata tana ganinta ta saki Murmushin jin dad'in ganinta don hakan ya tabbatar mata da bata yi fushi ba kan abunda ya faru jiya su twins ma na ganinta suka taso da gudu suna fad'in "Welcome sis Fatuu" suna k'arasowa suka fad'a jikinta tasa hannu ta dafa bayansu su duka, a kusa da kujerar da Hajiya take suka zauna ta gaidata tana dariya itama dariyar take tace "Yan tafiya ya gajiya?" tace " ba gajiya" aje mata ledar da ta shigo da ita tayi gabanta tace ga sauran tsarabar nan hajiyar tace "kuma dae muna ta shan tsaraba haka da dijen ma ta dawo ta kawo mana fa, to an gode Allah yasaka da Alkhairi" tana rufe baki Jidderh ta k'araso wurin jikinta sanye da doguwar rigar bacci brown mai santsi kanta ta yafa bak'in gyale tana kallon Fatun da Murmushi ta zauna kan Sofa Fatuu ta gaisheta ta amsa cikin muryarta ta yan gayu tace "ya gajiyan tafiya" amsa mata tayi da babu gajiya ta jinjina mata kai, kama hannun Mubeena mubeen yayi yace "zo muje mu gaya ma Ya Nameer Sis Fatuu tazo" suka nufi hanyar Bedroom da gudu, bada jimawa sai gasu sun dawo tare da Nameer d'in ya kamo hannuwansu da gani daga bacci yake don idanunsa sun nuna yana sanye da wando 3 quarter da riga armless da gani shima yana gyming don damtsen hannunsa ya gwada, da Murmushi ya k'arasa kujerar da Fatun take ya haye kan hannun kujerar idonshi akanta itama kallonshi take tana Murmushi cikin muryarshi da bata idasa washewa ba yace " yar fillo kin tashi lpy ya gajiyan tafiya" d'an tura mashi baki tayi tace "nifa ka daina ce man yar fillo ba kasan sunana ba" kawae sai ya dungure mata kai yace "to ke ba yar fillon bace" dariya ya basu gaba d'aya ganin abunda yayi mata, k'ura mata ido yay yana kallonta kafin yace "baki fushi ba kenan?" shiru ta d'anyi kafin ta d'aga mashi kai alamar eh yace "Gud haka ake so mutum ya kasance mai hakuri" Hajiya tace "aikuwa dai Fateema ba dai hakuri ba dama" wani kallo Fatun tayi mata alamar bata yarda da Maganar Hajiyan ba ba kamar da ta ga tana dariya alamar itama da biyu tayi Maganar duk suka yi Murmushi suma don sun san labarin Fatun na bata barin ta kwana duk wannan abun Farha na dining tunda ta juyo lokacin da Fatun ta shigo ta kalleta bata k'ara waigowa ba karshe ma sai ta mik'e ta nufi Bedroom, sai wurin Azahar ta bar gidan su twins na tambayarta zata dawo ko tace masu eh sai da daddare zata zo suyi fira lokacin Nameer har yayi wanka ya canja kaya suka fito atare yace bari ya rakata daga can ya wuce Masallaci, bayan sun fito ta tambayeshi Haisam yace mata yana wurin aiki dama tasani kawae hakanan ta tambayeshi, suna tafe suna fira sai kace sun dad'e da sanin juna har kopar gida ya rakota ya tsaya suka gaisa da Amadu Fatuu na gaya mashi k'anin Ya Handsome ne yace ai ya gane tunda ga kama nan ya gani, yayi mashi anzo lafiya fuska sake Nameer d'in ya ce mashi lafiya lou suma sun dawo lpy, cikin mutuntawa suka gama gaisawar ya kalli Fatuu yace "to yar fillo sai anjima ko" yar harara ta wurga mashi shima ya rama suka sa dariya harda Amadu daga haka ya juya ya tafi, bayan ta shiga gidan tsarabar Haulat ta d'auka ta nufi gidansu don bata san sun dawo ba tun ranar asabar data zo don da sukayi waya da Fatun lokacin suna can ta sanar mata ranar zasu dawo ta iske basu dawo ba Gwaggo tace mata sai washegari hakan yasa jiyan bayan la'asar ta sake zuwa still ta iske basu dawon ba, ba k'aramin farinciki Haulat tayi ba da ganin Fatun sai faman washe baki take kamar zata goyata innarsu ma da kannenta suka yi mata an dawo lafiya, lokacin data bata tsarabar harda ta haisam bayan sun shiga d'aki kasa rufe baki tayi don murna sai faman tatta6a abubuwan da haisam ya siyo masu take cike da zumud'i ta kwashesu taje ta nuno ma innarsu,bayan ta dawo ne innar tasu itama tazo d'akin tayi ma Fatun godiya kafin ta tafi, firan ruga ta shiga bata har akayi la'asar sannan ta baro gidan don tana son zuwa wurin Haisam in ya dawo tayi mashi godiyar tsaraba sosae don ba k'aramin dad'in kayan taji ba, tare da haulat d'in suka taho zata islamiyya tace ma Fatun ita bazata je ba tace eh sai gobe, a daidai kiosk d'in kawu Amadu suka rabu ta wuce, matsawa tayi gaban kiosk d'in ta tambayeshi yaga Ya Handsome ya wuce yace shi bai ganshi ba hakan yasa ta nufi cikin gidan tayi salla bayan ta gama ta fiddo da tsarabar kayan makarantar tana sake dubawa cike da jin dad'i ba komae yafi mata dad'i ba sai sanin cewa duk Makarantar baza'a samu mai irinsu ba, ganin hud'u da rabi ta wuce karfe biyar ta kusa yasa ta maida komae ta mik'e da sauri ta fita waje, wurin kawu Amadu ta sake komawa ta k'ara tambayarshi ko Haisam ya wuce da farko cewa yayi bai sani ba ta aje shi ne yay mata gadi, magiya ta hau yi mashi sannan yace eh ya wuce bada jimawa sosae ba, ko gidan bata koma ba ta nufi gidan Hajiyar ta k'aramar kopa tabi ta shiga part d'inshi tana niyyar hayewa balcony taji daga bayanta da d'an k'arfi ance "Hey!!!" da sauri ta juya don bata tsammaci ganin wani ba, Farha ta gani tsaye bakin fence door tana sanye da skinny fit bak'i wanda iyakarshi gwiwarta sai riga mai dogon hannu bak'a ta kamata sosae gashi daga k'asa bata rufe saman wandon sosae ba ana d'an hango k'asan cikinta da yake fari fat, kanta tasa bakar hula irin mai kama kai yayin da gashinta ash ke zube a gefe da gefen fuskarta hannunta ruke da wayarta wadda keda cover ash haka kafafunta ma na sanye da flat shoe ash ba k'arya tayi kyau sosae ta fito a baturiyarta dama gashi ba ramamma bace tana da yar k'iba sannan a shekaru ta girmewa Fatun sosae don zata kai shekara 18 zuwa 19, da wani irin taku ta nufo Fatun ta tsaya agabanta tana yi mata wani kallon rashin arziki itama Fatun kallonta take ta d'an d'aure fuska saidae jurewa kawae take saboda k'wayar idonta mutum bazai iya jure ma kallonta ba na tsawon lokaci,

"What are u doing here?" ta tambaya, Fatun tai mata banza tana binta da ido ta k'ara cewa "am i not talking to u, why can't u sit in ur House, kullum ke kina gidan mutane ne?" sai lokacin Fatun tace "to ai ba wurin ki nazo ba ko wurin ya...." kafin ta idasa Maganar ta daka mata tsawa "Oh u shut up! Is he ur Father, babanki ne shi ko kin had'a wani abu dashi" ta tambaya ta kumburo baki tana huci haka itama Fatun ta kumburo baki jin abunda tace mata, nuna mata hanyar fita tayi tace "leave here now,mai kwad'ayi kawae baki iya tsayawa gidanku kullum kina gidan Mutane k'wak'wa, i don't wanna see u in dis house again" waro ido Fatun tayi baki bud'e take kallonta jin ta kirata da mai kwad'ayi da kwakwa lokaci guda idanunta suka sauya kala tsantsan bacin rai ne acikinsu sam tama kasa maida mata martani duk da yadda Maganar ta daketa kirjinta har wani d'agawa yake da sauri da sauri,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login