Showing 39001 words to 42000 words out of 212491 words
gira"Not bad"yace, still Abbas d'in daria yake"kace inna maida shi sana'a zanci Abinci dashi kenan?"ya fada,
Haisam wanda har lokacin fuskansa na dauke da murmushi yace"shi kuma lecturing d'in ka kaishi ina?" zama sosae Abbas yayi ya d'an kwantar da bayanshi jikin kujeran yace"baka ga yadda ya zama ba,duk yana neman komawa shiririta,that's why na fara neman wata sana'ar kaga sai yazama inada alternative in ba wanccan sai inci gaba da bin yaran masu kudi ire-irenka ina masu kirari,nasan ba karamin kudi zan rinka samu ba"
Haisam da shima ya dan kwantar da kanshi cike da zolaya yace"wani ke shiriritar da aikin naku baku ba?nan gaba ma in aka biye maku kashe ilimin zaku yi gaba daya,yakamata tun wuri ai taking action akanku" Abbas dake ta daria yace"wani action kuma banda hanamu salary da ake" dage gira haisam yayi"I mean sacking...." da sauri Abbass ya d'ago da kanshi yace"amman kai mugu ne H,zakee,wato kai burinka kenan a kora mu ko" sai lokacin haisam yayi dariyar da hak'oransa suka bayyana,
"in an kora mu sai akawo suwa su koyar? ko su ku za'a maido tunda an fada ma lecturing d'in wasa ne",
"banyi tunanin zaka yi man wannan tambayar ba,seems like ka manta a wace kasa muke ko,kuma nima kasan dae zan iya ai,miye a ciki,all i need to do is Pgde,tunda ba education nayi ba,kai tsaya kaji ko banyi ba zan iya lecturing din,harma in fi wasu da suka dade a fannin" ya karasa maganar cike da tabbacin abunda ya fada.
Abbas yace"aikuwa da kasa mata sun rinka tara c.o"
"Why?" haisam ya tambaye shi.
"Muddin kazama lecturer ai shikenan kuma zaka janye hankalin mata ya dawo kan ka,ba kamar yan matan jami'a da basu shakkar nuna ma malami suna sonsa komae tsaurinsa,basu damu da zai wulakanta su ba,na tabbatar hakance zata faru da kai,ai gaba d'aya nike gaya maka attention dinsu kanka zai dawo,instead of focusing on their studies,kaga ba karamar barna zakai ba kaima,don kasuwa zakayi sosae abokina" ya karasa yanata faman daria.
Shi dae haisam still yayi yana kallon Abbas,tsaf ya fahimci dalilin da yasa abbas din cewa mata zasu maido attention dinsu akansa,don tunda ya taso yana k'arami ake fada masa yana da kyau na musamman har kuma yanxu da ya girma ba'a daina fada masa hakan ba,haka kuma da wuya a kalle shi ba tare da ansake waiwaya wa ba.
Abbas smiling broadly ganin haisam din yayi shiru yace"ko ba daidai na fada ba,I lie? Sauke 6oyayyan ajiyar zuciya haisam yayi kafin yace"in tambayeka Abbas...?"abbas yace"I'm all ears zakee" haisam ya cigaba"have u ever talk completely without mentioning women?na rigada na fahimci is hardly a kare magana da kai baka ambaci mata ba,to ni wannan ba matsalana bane,nothing concern me wit dem,kaima da suke kula ka ai don kana kula su ne,ko bansan ka bane"
Dariya sosae Abbas keyi harda buga kafa yace"to in ban rink'a ambaton mata ba,maza zan rinka ambato H,zakee,ai mata namu ne,muma kuma nasu ne" d'an ta6e baki haisam yayi yana girgiza kai kafin yace"to ya Abuja?"
"sai da ka gama caccaka ta har kana man mummunar fata sannan zaka tambayeni,ashe kaima baka tausayin malamai bayin Allah",
Dan ta6e baki haisam yayi"U know I was just funning u dude,ina tausayin malamai mana,especially primary and secondary skul teachers suna matukar kokari sosae,but their Salary structure is still poor,kawae al'amarin kasan namu ne sai Addu'a,may Almighty Allah give us responsible leaders"
"Ameeen ya Allah" Abbas ya amsa.
"Yaushe ka shigo gari ne?" gyara zama Abbas yayi yace"ban jima da dawowa ba" jinjina kai haisam yayi kafin ya kuma tambayarshi"yasu Nafeesat and my Boy Abdul? Abbas yace"suna nan lafia,ita feenah ma tayi tunanin zuwa kayi ka koma,nace mata kana a gari hajia ta sa an maido mata kai nan,har take cewa shine ko ka leka ku gaisa"
dan murmushin gefe yayi"in sha Allah zan je,am not well settled har yanzu" kai Abbas ya daga yace" Allah ya yarda dama ai sai a hankali komae zai warware tunda wurin aiki ka canja" daga haka suka ci gaba da hira.
*** *** *** ****
Haulat tace"Ina ganin kije ki bashi hakuri tun kafin goben tayi....."cakk fatuu ta tsaya ko kyafta idanunta batayi kamar an dasa mata aya,haulat ta ci gaba"kinga idan ya hakura shikenan waya kawai zai kira yace ya janye inma yakai karar taki",
juyowa fatuu tayi tana kallon haulat da alamun mamaki tace"tabb lalle kema haulat din nan wani lokacin kaman baki da tunani wllh,kina nufin in kai kaina ma kenan,kinga daga nan sai hajia tasan ni ce in dama ya gaya mata"
"ba kince da aka aikeki gidan,kinga 6angarenshi daban ba?"haulat ta tambaya,
Fatuu tace"Eh,amman in naje ya cafke ni ya kaima hajiyar yace ga wadda ta rotsa masa gilashin fa?" girgixa kai haulat tayi"duk da bansan shi ba,nasan da wuya ya aikata haka gaskia,akwae mutumin dana ta6a gani sau biyu kuma ina tunanin shine....."da sauri fatuu tace"wani fari ko?zaki ga kalar farinsa daban" Haulat tace"ni bazan iya ganewa ba don duk a mota nike ganinsa ya wuce kawae dae fari ne"
"shine ma,don duk garin nan ba mai irin kalar farinsa.." da sauri haulat ta katseta"ke ya akai kika sani" tace"tabb yo nida na ganshi a kurkusa har sau biyu,ko kafin ya rabamu fad'a da murja har in fasa masa glass ai ran Alhamis ma da yamma sai da ya rabamu da jamila ina kokarin zubar mata da Awar...tsit fatuu tayi lokaci guda kamar ruwa ya cita,sai faman zare ido take.
Girgiza kai haulat tayi tace"kin bari yama san halinki kenan,Allah yasa ya hakura" a hankali tace "Amin,ai bazan kara ba"ta6e baki kawae haulat tayi tace"kije ki bashi hakurin,kar kiji wani tsoron wai zai cafke ki yakaima hajia,na tabbatar bazai yi haka ba,don sufa yan gayu aji ne dasu,ba don haka ba yadda Gaye yace yasan gidanku ai da yaso hajiyar ta sa ni da tun ranar ya kaita har gidanku tasan kece amman yadda kika je kaimata abinci bata yi maki maganar ba kinga tabbas bata san kece ba,don haka kije kiyi duk yadda zaki ya hakura,ki nuna masa kinyi nadama kar kuma kice wai don gaye yace za'a kai ki gidan yari in ba'a biyasa ba ki ka je bashi hakurin,inta kama kita kuka ma,in bakije ba har gobe tayi indai har yakai k'arar taki to dole Hajia da gwaggo su sani koda ba'a kai ki gidan yarin ba,kuma kinga shikenan na tabbata hajia 6atawa zatai dake duk kuwa yadda take son ki,ga kawu Amadu hmmm...."
Fatuu dai tayi zuru tana saurararta sai zare ido take gabanta na faduwa ta kalli haulat tace"amman kina ganin zai hakuran,ya yafe man haulat,kudin fa da yawa wllh ke baki san yawansu ba ne hmm"ta karasa maganar tana jinjina kai,haulat tace"In sha Allahu ina sa ran zai hakura,tunda na tabbatar yafi karfinsu,kuma ba ita kadaice motarsa ba,ko ni da nace maki na gansa sau biyu duk ba a mota kala daya nake ganinsa ba...."da sauri fatuu ta katseta "nima a mota daban daban nike ganinsa kuma kwalabo yake yi da kayan jikinsa da motar da ya hau" Haulat ta gyada kai"to kingani,kije dai ki bashi hakurin,kinsan wani duk zafin sa idan ka bashi hakuri akan laifin da kayi masa ka nuna kayi nadama bazaka kara ba,yana hakura"
Fatuu tace"ni wllh gabana sai faduwa yake kar inje yasa akamani ko tuwon gwoggo na karshe ban ci ba..." wani irin kallon mamaki haulat tayi mata"ke da baki son tuwon kullum kina k'orafin za'a kashe ki da shi" tace"ai na daina,yanzu nagane ba shine mai kashe mutum ba,gabza ce,in kasamu tuwon kawae ka godema Allah kaci"tasa hannu tayi tagumi,ita dai haulat dan girgiza kai kawae tayi tana murmushi don tasan irin nadamar fatuu.
Shiru sukayi nadan lokaci can fatuu ta kalli haulat tace"don Allah haulat to kizo ki rakani" da sauri tace"in raka ki ina? Fatuu tace"muje mu bashi hakurin....."girgiza kai haulat tayi da sauri"lokacin da kika yi masa 6arnar ai ba tare muke ba,hasali ma ba yadda banyi dake kiyi hakuri ba ki ka kiya,sai yanxu kice wai in raka ki,salon kija man balae" ta k'arashe maganar tana kallon gefen hanya.
Fatuu tace"oh dama kinsan wani abu zai iya faruwa innaje shine kika tura ni don cuta? da sauri haulat ta juyo tana kallonta tace"kindai san ni bazan ta6a cutarki ba ai,kawai ina gudun babana ya ganni tunda kinga limamin masallacin gidanne,kuma kinsan ni ba wani zuwa gidan nike sosae ba sai in na raka ki wani lokacin,dama dai cikin azumi ne shine kullum sai naje kar6ar sadaka da yamma,wani lokacin kuma in raka ki da rana inje insha A.c ko don rage yunwar Azim..." cike da tsiwa fatuu ta katseta"dalla kin cika ni da wani bayani,kawai in zaki raka ni ki rakani,in kuma baki zuwa ki fada man in kama gaba na"
Haulat tace "shikenan muje in raka ki amman iyakata wajen gate gaskia" wata irin harara fatuu ta wurga mata tace"to banso kisha zamanki,zanje ni kadai,kuma insha Allahu zai hakura,d'an bakin ciki sai dai ya mutu"daga haka ta mike ta kakka6e jikinta hadi da zura takalmanta ta juya zata tafi,itama haulat ta mike tana fadin"ai da ni yar bakin ciki ce da ban baki shawara ba ko,amman ba komae gobe ma rana ce,ko godiya bazaki man ba sai ma ki kira ni da yar bakin ciki"
Juyowa fatuu tayi ta k'ara harararta tace"sai ki jira kiga shawarar taki in tayi aiki,kafin kiyi maganar wata godiya" Haulat tayi dan murmushi tace"insha Allahu ma zatayi kawata kuma kanwata,ba inda za'a kai ki muna tare mutu ka raba" wani kallo tayi mata tana turo baki daga haka ta juya fuu ta tafi.
Cike da tsokana Haulat ta dan daga murya tace"kawata bazaki rakani ba,aike na akai in mun dawo sai muje in jira ki a bakin kofan ki shiga ki bashi hakurin" a fusace ta juyo ta kara watsa mata harara had'i da mummurgud'a baki daga haka tayi gaba abunta.
Daria sosae haulat tayi ta juya tabi hanyar da tafara bi d'azun a ranta tana fadin"haka kurum kija man yanzu babanmu yaji wannan abun duk da badani aka aikata ba ai sai ya sa6a man wllh,taje dai ina mata fatan nasara,in ma fushi tayi ma shirya daga baya.
Tafiya take sam hankalinta baya tare da ita,ta tafi duniyar tunanin shawarar da haulat ta bata,gani take anya kuwa zai hakura don a ganin da tayi mashi sau biyu tana ganin kaman ba zaiyi mutunci ba,ranar farko daya rabasu fada da jamila fuskarshi a murtuke take haka ranar da suka yi fada da murja daga magana bata ma idasa fadin abun da zata fadan ba ya gaura mata mari,tunanin hakan ne ke k'ara mata fargabar zuwa wurinshi,amman ba yadda zatayi dole taje kafin gobe tayi.
Daidai shagon kawu Amadu ta tsaya tana jiran ya sallami wani yaro,kallonta yayi bayan yaron ya tafi,fatuu tace"sannu kawu" jinjina mata kai yayi ganinta sukuku yasa yace"har yanzu jikin?" girgiza masa kai tayi"da sauki sosae"ta fada a hankali,d'aura jakar islamiyyarta tayi saman kiosk din tace"kawu jakata zaka aje man,zan dan je gidan Hajia yanzu zan dawo"sanin ba kowa acikin gidansu yasa shi daga mata kai alamar toh,daga haka ta juya ta nufi gidan hajiyar sanata,kirjinta na bugawa damm damm tamkar ana mata luguden ta6are haka ta daure har ta karasa,ta karamar kopa dake a bude ta bi ta shige.
_*Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp message banda phone call,Thanks🤝*
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
*BY ZAINAB LALUH📲*
~(Oummu Imam)~
*page 24⃣*
......Suna cikin fira Abbas ya juya yana kare ma parlour din kallo kafin ya juyo ya kalli haisam"amman dai ya tsaru sosae,order din furnituren kai daga can i guessed" daga yadda haisam din yake ba tare da ya dago ba ya dage masa gira alamar ehh,
"da gani ai,sunyi kyau parlourn ma yayi kyau sosae,amman bai kai na gidana ba tunda ba mata a cikinsa,don inda da mace sai yafi kyau" ya karasa zolayar tashi yana ta daria,
"na lura dae ba zuwa kai mu gaisa ba,iskancin daka saba kazo yi mun...." da sauri Abbas ya katseshi da fad'in"pulling my best friend's leg,Allah zuwa nayi mu gaisa sosae don nayi missing din ka guy irin sosai din nan,kasan kana zuwa nayi tafiya so bamu wani gaisa sosai ba,and we ave'nt spoken like this for long,ko da yaushe sai dai phone and vid call,shiyasa na tara hira da tsokanan da zan maka sosae,Feenah fa har rigima tasa bazan fito ba,wai daga dawowa na zan wani kama fita,sai da nace mata wurin H,zakee zani sannan..." haisam ya katse shi"ai tana da gaskia dama bata barka ka fito ba,for gud 1 week basu saka ka a idonsu ba,kamata yayi yau througout ka zauna gida kafin gobe ka dasa zuwa aiki kuma"
"Hhhh ai ita da kanta take cewa tana da iyaka tsakanina da kai,shiyasa duk abu in ya dangance ka bata jayayya" murmushin jin dadin maganar Haisam yayi,shi kanshi Abbas nada matukar muhimmanci a wurinsa amininsa ne wanda ya zama tamkar dan'uwansa kowa nashi yasan da shi,sun shaku sosae ta yarda zai yi wuya su kwana su wuni ba tare da daya yasa dayan a ido ba indae har suna a gari,in kuwa haisam na Abuja Abbas yaje to a gidansu yake zama koda ma bai a Abujan Abbas din na sauka a gidansu,sai dai ko wani abu da ya danganci aikinsu yaje wanda aka kama masu hotel room shima in yaji bai ra'ayin zama a hotel din sai ya tafi gidan Senator Alee Adamu Zakee,
Hannu Abbas yasa a Aljihun gaban rigarsa ya fiddo wayansa wadda tun suna hira yake jin karan notifications,ganin sakonni nata shigowa har lokacin yasa shi fadin"dadi na da zuwa gidan hajiya kenan",
"What" haisam ya tambaya ba tare da ya dago ba,
"Internet access mana,daga mutum ya kunna wi-fi sai yaita browse and chat for free" dan jinjina kai haisam yayi yace"da alama ma tun kafin kazo kai turning wi-fin on,don tun dazun nike jin notifications tone"
kyalkyacewa da daria Abbas yayi"tun a mota kafin in karaso na kunna" dan d'ago kai haisam yayi ya kalli Abbas yace"lalle ka cika son banza Abbas,amman soon zaka fara biya"
"ah haba dae,nima fa Senator nan babana ne,ya za'ace mutum da abun babansa sai ya biya,
"wannan ba kayan Senator bane na haitham ne" haisam ya bashi amsa,
"Amman da kai da kaya naga dae ai duk mallakar wuya ne ko" Abbas dake ta dariya ya fada,girgiza kai haisam yayi daga haka ya juya yaci gaba da abunda yake cikin computer, shi kuma Abbas ya maida hankali kan wayarsa da sakonni keta faman shigowa.
Tsaye fatuu tayi a bakin Fence Door din part din haisam tsawon wasu mintuna cike da fargabar karasawa wurin shin don ranta ya bata cewa yana nan ganin mota fake a kwanar gate din gidan,ba komae take ma zullumi ba face karfa yasa a kamata daga nan ayi gidan yarin ko kuma hajia tazo ta ganta asirinta ya tonu,hakan yasa ta kasa shiga tuntuni sai faman wasi-wasi take a cikin ranta,can dae tayi shahada ta shige tana tafiya cikin sanda tana waigen bayanta har tazo bakin balcony a hankali ta tattaka ta haye sai kuma tai tsaye anan ta kasa tunkaran kopan don ba karamin bugu kirjinta ke yi ba,matsawa tayi saitin windown parlourn nashi da niyyar ta hango ciki taga ko yana nan sai dae kuma ta kasa hango komae sai ma kanta da take gani a jikin glass din tamkar tana kallon madubi,
Abbas ne ya dago da niyyar yima haisam magana karaf idanunsa suka hango masa fatuu sakamakon blinds din windown dake adan zuge,tayi tsaye ta kasa karasowa sai faman zare ido take tana kallon kanta ta cikin glass din hadi da waige-waigen bayanta tsoronta kar hajia ta shigo sashen,
Abbas ne yace"Zakee wacece wannan?ba tare da ya dago ba yace"wa kenan?
"Ina nufin waccan yarinyar dake tsaye gaban window" sai lokacin ya dago tare da kai dubansa kan window din,kura mata ido yayi yana kokarin tuna inda yasan face din,lokaci guda ya gane yarinyar,"what d hell is she doing here.. ya fada acikin ransa,shikam Abbas sai ya kalli fatuu sai kuma ya kalli haisam ganin yanayin fuskarsa ya dan canja yasa shi cewa"kasanta ne? girgiza masa kai yayi alamar a'a,kafin yace"may be wurin hajia tazo,inba hakan ba,bama za'a barta ta shigo ba" gyada kai Abbas yayi alamar gamsuwa sai kuma yace"kilan irin yan gudun hijira din nan ne dake yawon neman taimako,to amman miya kawota nan gashi kaman bata da gaskia,kasan fa wasun su da sun samu chance sai suyi ma mutum sata,kwanaki haka akayi wani case a estate dinmu na wata yarinya very young daga shiga neman taimako tayi attempting yin sata,da aka kama ta shine tai confessing wai mom dinta ke tura su gidaje bara daga nan in sun gan abu mai amfani su daukko",
Maida idanunsa yayi kan computer kafin yace"Allah ya kyauta" mikewa Abbas yayi yana fadin bari yaje yaga mi take yi a wajen,daidai lokacin kuma fatuu ta bar gaban windown don ta kasa hango ciki kanta kawai take gani,ta nufi kopar shiga falon kirjinta na cigaba da bugawa da karfi, daidai lokacin da ta kai hannu zata kama handle din kopan aka bude,zaro ido tayi cike da razana lokacin da suka hada ido da Abbas,aikuwa da gudun tsiya ta juya saura kadan ta wuntsila wurin sauka,Abbas na fadin"ke,ke,ina ai tuni ta fice daga part din,juyawa yayi ciki yana fadin"dama da ganinta bata da gaskia kaga tana ganina ta tsere,ya kamata ayi ma securityn can magana su bar barin irinsu suna shigowa" ya karasa maganar lokacin da yake kokarin zama,shidae haisam gyada mashi kai kawae yayi alamar toh,
Kan kace mi fatuu ta kai gida ko Amadu dake sallamar yara masu siyayya bai ga sanda ta shige gidan ba,can karshen dan gadonta ta haye tana ta faman sauke numfashi hannunta na dama dafe da saitin zuciyarta don ba karamin gudu