Showing 57001 words to 60000 words out of 212491 words

Chapter 20 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

994

hajjaju" Amadu yace"amman ki barta ta kwana kawai mana" tace"ba kwanan ke banson tayi ba inda kamar yau asabar ne da sai ta kwana to gobe Monday kaga akwai makaranta kuma na daina barinta tana kwana saboda makarar da take yi duk in ta kwanan kaga kwanaki fa akwai ranar da saidai fasa zuwa makaranta tayi saboda bata dawo gidan nan ba sai wurin karfe tara na safe,shiyasa ma in na aika a taho da ita hajiyar bata cewa abarta saboda tasan makara take tunda ita ba da wuri take tashi ba" jinjina kai Amadu yayi yace"Ok zanje in taho da ita,amman bari in k'arasa shigo da kayan in kulle shagon" gwaggo tace"eh kagama,ni bari in koma in kwanta bacci nike ji sosae wllh dama farkawa nayi naga bata dawo ba"tana maganar ta juya ta nufi dakinta.

Fatuu ce gaba Haisam na bin ta a baya sai faman waigawa take tana satar kallonshi don duk ta tsorata da yanayin shi ga ciwon da yaji saboda ita, suna zuwa gab da k'arshen katangar gidan hajiya Amadu ya fito daga gida ya tsaya yana kulle kiosk dinshi,haisam na hango shi yace ma fatuu "hey..." alamar ta tsaya,juyowa tayi ta kalle shi,taku ukku yayi ya k'araso inda take a hankali yace"don't disclose what happaned to anyone" jinjina masa kai kawai tayi,ganin haka yace"kin gane mi nace" da sauri tace"eh,cewa kayi kar na fada ma kowa abunda ya faru" alama yayi mata da hannu ta tafi ta juya ta tunkari Amadu dake tahowa Haisam na niyyar juyawa Amadu ya dan d'aga murya yace"Ina yini" tsayawa haisam yayi ya d'aga masa hannu ba tare daya amsa ba,

Juyawa Amadu yayi tare da fatuun yana cewa"dama baki yi bacci ba shine kika ki kidawo kaman yadda gwaggo tace maki,kawai don kibani wahala" ya kai hannu zai rankwasheta tai saurin janye kan tace"wad muyal kawu(yi hakuri kawu)" Amadu ne ya fara shigewa kafin fatuu saida ta dan juya ta kalli haisam da har lokacin yake tsaye da sauri ta shige ganin sun hada idanu.

______________________

Zama haisam yayi kan kujera bayan ya koma ya shiga cikin contacts din wayarsa yayi dialing wata number mai dauke da sunan SP khamis,wayan na shiga aka daga gaisawa sukai da mutumin wanda daga ji abokinsa ne daga yanayin yadda suka gaisan,Haisam ya sanar dashi game da incident din daya faru yace ya samu rauni ne a k'afarsa shiyasa ba zai iya zuwa station din yayi reporting ba,Sp khamis najin abunda ya faru yace ma Haisam ya bari zaizo yanzu wannan ba maganar waya bace daga haka ya katse, kwanciya yayi saman kujeran gaba daya ma ya nemi baccin da yake ji ya rasa al'amarin ba k'aramin tada masa hankali yayi ba,imagining kawai yake da baije wurin akan lokaci ba abunda zai faru,d'an guntun tsoki kawai yake ja.

Bayan kaman 30 minutes SP khamis ya iso a bakin gate ya parker motarsa ya fito matashi ne da bazai wuce 33yrs ba, jikinsa sanye da uniform din yan sanda riga blue sai black wando su Officer na ganinsa suka sara masa,Officer p ne yayi masa jagora ba tare da 6ata lokaci ba zuwa part d'in haisam bayan ya sanar dasu wurinshi yazo,
Tura kopan yayi bakinsa dauke da sallama,k'okarin tashi zaune haisam yayi bayan ya amsa masa,fuskarsa d'auke da murmushi ya mika ma Haisam hannu yana fadin"H, Zakee the big COE" haisam da shima yake murmushi yace"SP,ya aiki", "Alhamdulillah gamu a cikinsa" ya fad'a yana kokarin zama a daya daga cikin armchairs din dake parlon, haisam yace"am sorry nasa ka baro aikinka..." SP khamis ya katseshi"Oh no,don't say dat, nan ma ai aikin na zo ko,uhum kana fad'a man yadda incident din ya faru ta waya inason k'ara jin cikakken bayanin al'amarin",

Sigh haisam yayi kafin ya sake mashi bayani a takaice,Sp khamis nata jinjina kai,cike da takaici yace"yanzu ina yarinyar take?" haisam yace"tana gidansu and I ave instructed her not to tell anyone about d incident" jinjina kai Sp yayi"hope basu yi nasarar yi mata komai ba dai??" shiru haisam ya d'an yi yana tunano maganar da yaji goga yayi,yace"bana tunani gaskia",
gyara zama SP yayi"Ok yanzu inason statement dinka sannan itama dole zamu bukaci nata" haisam yace"Owk,lokacin da kuke bukata just inform me,ni bari in rubuta maka" ya k'arasa maganar yana kokarin mikewa SP nace mashi yabi a hankali,d'akin da fatuu ta shiga fitsari ya shiga,hannunshi rike da plain sheet da pen ya dawo cikin kankanin lokaci ya rubuta duk bayanin daya sani ya mika ma Sp khamis dubawa yayi kafin yace"gud,yanzu shi guy din da yarinyar ta fada maka baka san gidansu bane?" girgiza kai kawai haisam yayi alamar baisani ba,
SP yace"dole kenan sai wurin yarinyar za'a samu information din da ake bukata gashi yanzu dare yayi gaskia" shiru haisam yayi kaman mai dan tunani can yace"I think u can get that from the security at the gate,tunda kagan sun dan jima suna aiki anan bazasu rasa sanin guy din ba" Sp yace"yauwa bari in tuntu6e su don so nike zuwa gobe su zo hannu in sha Allah" d'aga mashi kai haisam ya yi yayin da SP ya fara kokarin mikewa hannunshi rike da takardar da haisam ya bashi,ganin haisam din na kokarin mikewa don ya raka sa yace"kai zamanka kawai da na samu information din da nike so zan wuce,komai ake ciki I will inform u,amman kafan nan kaje a dubata gaskiya" haisam dake d'an murmushi yace"don't worry nayi mata duk abunda ya dace yanzu" SP dake sauraranshi yace"bafa Hardware ko software bace da zaka ce kayi abunda ya dace,u need to go hospital saboda ba dressing kawai kake bukata ba you also need TT Injection and some drugs like anti-biotics nd pain reliaver"

Komawa yayi ya kwantar da bayansa yana murmushi yace"I have taken d pain reliever,amman dama zanje asibitin first thing tomorrow Morning in sha Allah",
SP yace"better,ko kazo na kai ka wani pharmacy a duba ka" girgiza masa kai yayi"thanks,ba sai kayi wahala ba" ta6e baki yayi jin abunda Haisam d'in yace daga haka ya nufi hanyar fita yana fadin"My regard to hajiya pls" haisam yace"Owk zata ji,sai da safe" SP yace"Allah ya tashe mu lpy" daga haka ya fice.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story_


_*BY ZAINAB LALUH📲*_


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


*3️⃣1️⃣*


Washegari da safe Gwaggo ce acikin kitchen tana ta kwala ma fatuu kira "fatuu,fatuu.." fitowa tayi jikinta sanye da uniform d'in makaranta ta nufi kicin daidai lokacin da ta iso bakin kicin din zata shiga gwaggon ta fito"wai mi kike yi ne nike ta faman kwala maki kira kin k'i fitowa?" fatuu tace"shiryawa fa nike,a gwallijam" gwaggo dake ta kallon fuskarta tace"Jam sumul,kije wurin Amadu ki kar6o madara da milo ki maza kizo ki karya kumallo karki makara" tace "to biredi fa?",

"a'a akwai wani saura zai ishe
ki"gwaggo ta bata amsa,
"To ke bazaki ci ba,ai badai tuwo tunda bakiyi ba jiya?" Gwaggo tace"eh zan bada a siyo man waina gidan ladidi,ke ki ci biredin kawai" gyada kai fatuu tayi har ta juya gwaggon tace"miya same ki a goshi ne naga yayi ja?"
Damm gaban fatuu ya buga, juyowa tayi tana kyakkyafta idanu tana tunanin k'aryar da zata yi ma Gwaggon don dama ko Haisam baice karta fad'a ba,ba fadin zata yi ba,

"Bugewa kikai ne?"gwaggo ta sake tambaya,da sauri tace"eh jiya ne da Hajiya tagan na fara bacci ta tada ni in taho gida shine cikin magagin bacci na bugi bango awurin fitowa, bayan na fito ne na hadu da kawu Amadu" ta k'arasa tana dan kare gefen bakinta da hannunta don kar ta lura da bakin duk da daga ciki ne ya fashe,girgiza kai gwaggo tayi tace"maganin mara jin magana kenan da kin taho da wuri kafin baccin ya kwashe ki ai da ba haka ba,tafi ki amso abunda nace maki lokaci na tafiya" juyawa fatun tayi ta nufi hanyar fita.

Tunda ta fito zata tafi makaranta take kallon gidan hajiya ji take kaman taje sai dai tasan kawu Amadu sai ya tambayi abunda zata je yi tun da safe kuma lokacin tafiya makaranta,hakan yasa ta mik'i hanya kawai don biya ma haulatu,
Tana tafiya tana waiwayen bayanta wai ko zata hango Haisam ya taho a mota amman har ta kawo lungun su haulat bata ga wata mota ta taho ba balle tasa ran shine,lokaci guda gabanta ya fara fad'uwa ta fara tunani a ranta ko dai saboda ciwon da yaji jiya ne yasa bai fito ba,a fili tace"kar fa kuma ya dawo yace bai yafe gilashin ba saboda nasa yaji ciwo,daman naga sai d'aure fuska yake jiyan..." jikinta ne yayi mugun sanyi ta shiga damuwar da har fuskarta ta bayyana,
Tana zuwa kopar gidan haulatun ta fito,fuskarta d'auke da dan murmushi tace"ashe kin taho har inata sauri inje mutaho tare..." kasa karasa maganar tayi saboda yanayin fuskar fatun da ta gani,a hankali tace"miya faru kawata?baki je kin basa hakurin bane ?",
"ba komai,mu tafi karmu makara" daga haka ta wuce gaba,bin bayanta Haulat tayi jiki asanyaye tana ta faman tunane-tunane cikin ranta.

Har akayi masu break fatuu bata saki jikinta ba duk ta shiga damuwa ganin duk yan ajin sun fita yin break fatun na a zaune yasa haulat tace mata"ki taso muje muyi break fatuu" kifa fuskarta tayi saman desk tace"ki tafi kawai bana jin yunwa" jin hakan yasa Haulat da har ta mik'e komawa ta zauna,hannu tasa ta d'an bubbugi bayan fatun tace"wai miyake damunki ne,kodai mutumin cewa yayi bazai yafe bane?kinji ki fada man"
Dagowa tayi fuskarta a d'aure tace"wai bana ce maki ba komai ba,ki kyale ni kije kiyi break dinki" daga haka ta sake maida kanta ta kifa a saman desk din.

Shiru Haulat tayi,sai taji duk zuwa break din ma ya fita ranta dama kuma naira ashirin ce da ita,can ta mike da niyyar zuwa ta siyo ruwa saboda kishin da ta fara ji, "Haulat" taji fatuu ta kira sunanta,a hankali ta juya ta kalleta fuskarta a dan d'aure don bata ji dadin abunda fatun tayi mata ba,kudi fatun ta mik'o mata,kallon kudin tayi kafin ta kalli fatun tace"mi zan siyo maki?",
girgiza kai tayi"ba komai ki had'a kiyi break"shiru Haulat tayi duk da bata da isassun kudi amma tace"a'a ki barshi"daga haka ta juya,

"Fushi kika yi?" fatuu ta jefo mata tambaya,banza ta mata taci gaba da tafiya,ganin hakan yasa da sauri fatuu tace"ki yi hakuri to...."tsayawa da yin tafiyar haulat tayi ta juya ta d'an kalli fatun hakan yasa ta cigaba"banje na bashi hakurin bane shiyasa kika ga duk na damu,tsoro na yau Monday kada maganar Gaye ta tabbata" sai da kirjinta ya buga data ambaci sunan gayen,ita kuwa Haulat jin hakan yasa ta koma inda fatun take ta tsaya a gaban desk din tace"to kuma sai inta faman tambayarki ki k'i gaya man abunda ke damunki",
"to ai nace kiyi hakuri ko" fatun tace,
"Shikenan,in sha Allahu ba abunda zai faru ma,yanzu ki taso muje muyi break din,alabashshi da yamma in aka taso mu islamiyya sai muje tare mu bashi hakurin,nasan in Allah ya yarda zai hakura" mik'ewa fatuu tayi har ta fito daga cikin seat d'in ta koma ta janyo jakarta,bude ciki tayi ta fiddo lemun da Haisam ya bata daga haka suka fuce.

*** *** *** ***

Wuraren karfe 9 na safe Haisam ya farka daga bacci tun bayan da yayi sallan Asuba anan cikin dakinsa,yana farkawa kiran Hajiya ya shigo wayarsa don tana ta kiran telephone bai dauka ba sai tayi tunanin ko bai tashi bane,ganin lokaci nata tafiya yasa ta kira wayarsa,bayan ya d'aga kiran sun gaisa take tambayar ko ya wuce wurin aiki ne,don bata ga yaje sun gaisa ba kaman yadda yake yi kullum kafin ya tafi don bai cika yin breakfast ba a cewarshi yayi safiya da yawa,sai hajiyan ta matsa masa ne ma wani lokacin yake shan tea kawae,sanar mata yayi cewa yana nan bai tafi ba bada wuri zai je bane,in ya gama abunda yake zai shigo.

Toilet ya nufa don yin wanka bayan ya gama ya shirya cikin wata navy blue jallabiya mai gajeran hannu ya fito falo hannunsa rike da wayarsa yana d'an dangyasa kafan mai ciwo ya nufi kujera ya zauna,fara latsa wayan yayi ya kira Tk,yana d'aga kiran yace"t.k are u at home?" da sauri t.k yace "a'a wllh na tafi skul.."kafin ya k'ara cewa wani abu Haisam ya katse kiran,d'an kwantar da kansa yayi yana tunanin yadda zai tafi asibiti, don jiya da tsakan dare kafan ya takura masa da zogi duk da pain reliever din da ya sha,sai wuraran asubahi ya samu yin bacci sosae,duk motocin da zai yi amfani dasu manual ne dole sai yayi amfani da kafan mai ciwo in zai tuka su,gashi a yadda yake jin kafan ba zai iya yin tuki da ita ba.

Bayan wani lokaci ya mik'e, komawa yayi cikin corridor yasa takalma slippers kafin ya dawo cikin parlon ya fuce,wajen gate ya nufa ta k'aramar kopa ya fita,tunkarar Officer CD dake zaune saman benci shi kadai yayi,Officern na ganin haisam din ya tunkaro sa yana d'angyasa kafa ya mike da sauri ya nufo sa yana zuwa wurinsa yace"yalla6ai barka da safiya..."hannu haisam ya mik'a masa suka gaisa kafin yaci gaba"yalla6ai rauni ka ji haka?" d'aga masa kai kawai yayi,cike da jajantawa Officer ya shiga girgiza kai yana fad'in"wai sannu,Allah ya kyauta gaba" "Amin" haisam ya amsa kafin yace"in ba damuwa inason zaka kaini hospital ne,sai dai motan is manual I don't know if u could drive it" ya tambaye shine don yasan ba kowa ya iya tuka mota manual ba,

d'an sosa k'eya Officern yayi yana d'an murmushi yace"wllh yalla6ai kwata kwata ma ni ban iya tukin mota ba.." d'age gira haisam yayi yace"really?" Officer dake ta murmushi ya daga masa kai alamar eh kafin yace"sai dai ko in ma Officer Jamil magana don shi ya iya tuka mota don wani lokacin ma yakan fita da Hajiya in t.k baya nan" jinjina kai Haisam yayi yace"ok bari in koma ciki in yazo sai kayi masa magana..."da sauri Officer ya katseshi"ai yana nan,ya shiga ciki ya kimtsa da yake ba dashi mukai aikin dare ba bai jima da zuwa ba,bari in masa magana" ya k'arasa maganar tare da juyawa ya nufi cikin gidan,
Ba da jimawa ba suka fito atare Officer police ne Jamilun da aka kira ya nufo haisam yana gyara hulansa yana zuwa ya mika mashi hannu suka gaisa yace"yalla6ai ashe tsautsai ka had'u dashi" d'aga masa kai kawai yayi yace"to Allah ya kiyaye gaba" a hankali haisam yace"Amin",
"Yauwa wani motan za'a fiddo ne?Nura yace kana so a kaika asibiti" daga masa kai haisam yayi tare da mika masa makullin mota dake rike a hannunsa na hagu" amsar key d'in Officer jamil yayi ya d'an duba shi kafin ya juya don fiddo motan,Officer Nura kuma ya fara sliding gate din,ba 6ata lokaci ya fito da motan Haisam ya shiga suka tafi.

Wuraren karfe biyu na rana gwaggo na zaune a tsakan gida jikinta sanye da kayan aiki ita da wata mata dukkansu suna zaune a saman kujera yar tsugunno da alama bak'uwa tayi,da gudu fatuu ta shigo daga bakin kopar shigowan ta wurgo jakarta tsakar gida tayi bandaki da gudu,gaba dayansu sai da suka tsorata bakuwar matar ce ta juya ta kalli gwaggon tace"kaman fatima ko?" girgiza kai gwaggo tayi ta d'an ta6e baki tace"itace wllh,haka take don iskanci sai ta tara matsuwa,maimakon tun can makarantar tasan tana ji tayi"
Yar dariya matar tayi tace"ina ruwan fatuu" adaidai lokacin fatun ta fito tana gyara wandonta ta duk'a inda jakarta take ta dauka ta wuce ciki,kallon bakuwar tayi tace"Ladidi mai waina ina yini" amsawa tayi"lafiya lau fatima yan makaranta" kallon Gwaggo tayi tace"sannu da gida gwaggo" yar harararta gwaggon tayi batare da ta amsa mata ba,hakan yasa fatuu yin dariya ta wuce d'aki don tasan hararar ta shigowar da tayi da gudu ce,

"....Oh ladidi kina fadi man wannan al'amari mai cike da tashin hankali" ladidin ta kar6e"wllh bari,ni fa ina cikin tuyan waina da safe naji yara suna cewa wai gashi can an zo kama Gaye nace wane gayen? wai Ashiru d'an gidan Malam Tanimu,shine fa su Bilki suka fita don jin ba'asi nidai bansamu fita ba saboda tuyan wainan da nike,da suka dawo ne suke ban labarin wai yunkurin fyade su kai ma wata jiya da daddare shi da abokanansa Allah baisa sun kaiga yin nasarar aikatawan ba wani mutumi ya gansu,ance ma tun jiya da daddaren yan sanda suka zo neman shi basu same shi agida ba shine suka fad'a ma mahaifinsa mlm tanimun laifin da ake tuhumar d'an nasa,suka kuma bukaci ya basu hadin kai da zarar yaron ya dawo gida ya kira su ya sanar dasu kuma kar ya bari ya fita in ba haka ba zasu dawo su kamashi tare da mahaifiyar Ashirun wato Zulai,aikam yau da safe sai gashi ya dawon don bai kwana a gida ba,yana ko zuwa malam tanimun ya kira yan sandan"

Nannauyar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke cike da takaici tace"kai jama'a duniya dai ta idasa lalacewa yanzu ace kaman Ashiru yasan ya hakkewa mace,yanzu dai indai kana da yaya mata agabanka baka da kwanciyar hankali wllh masifar fyaden nan tayi yawa kullum gargadi ake nasiha ake amman a banza abun sai kara gaba yake na jiki ma sai ya cutar maka da y'a,Allah kai mana maganin wannan masifa ka shiryi al'ummar Annabi..." ladidi ta amsa"S.a.w,ke dai bari Dije Amin ya Allah,ni wllh malam tanimun ma ke bani tausayi shi kuma ta nan Allah ya jarabe shi gashi malami" gwaggo tace"wllh ai abun a tausaya masa ne jarabawar ya'ya ai babbar jarabawa ce mutum baida yadda zaiyi dole ya rungumeta har Allah ya yaye inda rabo,Allah ka shirya mana zuria shirin addinin musulunci",
"Amin" ladidi ta amsa tana kokarin mikewa tace"na tsaida ki zaki tafi aiki ga lokaci nata tafiya" mik'ewa itama Gwaggon tayi tana fadin"to daman dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login