Showing 96001 words to 99000 words out of 212491 words

Chapter 33 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

1694

plate d'in tace mashi gashi nan ya ci,kai ya d'aga mata kafin yasa fork ya dau d'aya ya d'an gutsira yana chewing a hankali yana kallon Tv,itama hajiyar d'auka ta fara tana ci suna d'an yin fira,can ta kai hannu cikin sumar kanshi ta nutsa shi ciki"wai wannan sumar ba'a aske ta ne tayi tsawo da yawa,koda yake dole ai tayi tsawon tunda kud'i ake kashe mata,don ma a nad'e take wannan da ba k'aramin tsawo kitso zai yi ba in akayi maka",

Wani kallo yayi mata da d'an murmushi"ko zaki man kitson ne",
"In kana so ai sai in maka, kasan k'aramin aikina ne,sai dae ba lalle ma kitson ya tsaya akan wannan sumar ba ta cika santsi",ta k'arasa maganar har lokacin hannunta na acikin sumar tana d'an sosa mashi kan,shi dae murmushi kawae yake don abunda take mashin dama ta saba tun yana k'arami haka zata sa hannu cikin sumarshi tana sosa mashi,ba kamar in ranshi ya 6aci ko yayi fushi a haka take rarrashinshi,
cire hannun tayi tace"ya kamata a rik'a rage maka ita, kaima kasha iska",

Sigh yayi"ai ana rage shi,shiyasa kike ganinshi haka da yafi hakan sosae",
jinjina kai tayi suka ci gaba da cin abunda ke gabansu sai dae ita shi yake bata a baki idonta akan tv,

"Motan ki da kika ce zaki bada waye zaki ba?",
maido idonta tayi kanshi"wani abu?,
girgiza mata kai yayi"i just want know in akwae wanda zaki ba",
"Eh,kawunku Mani nike son ba,don kwanaki da suka zo naga tashi ta fara tsufa dama tun wadda Senator ya basu ce,ko za kai wani abu da ita ne?"idasa cinye abunda ke bakinsa yayi kafin yace"No,ki bashi kawae,i thought baki fidda wanda zaki ba bane,da zan ba Abbas ne,amman zansa akawo mashi wani,

"to ka bashin kawae,ai shima d'an gidane wani lokaci aba Manin" lumshe ido yayi yana d'an girgiza kai alamar a'a,shiru tayi tana kallonshi,tasan tunda ta ambaci wanda zata ba,zai yi wuya yayi amfani da ita,
"To ba ni nace ka bashi ba"

"Ki ba wanda kikai niyya rabonshi ne,za'a kawo ma Abbas d'in period",daga haka ya aje fork d'in asaman plate alamar ya k'oshi ya maida kanshi saitin tv,itama hajiyar kallon taci gaba da yi,

"to mi zai hana ka kira Nameer,nasan baza'a rasa motan da basu amfani da ita acan Abujan ba tunda wasu aje suke kawae kaga sai ka tambayeshi in akwae lafiyayya sai aba Abbas d'in kawae",kai ya d'aga mata
alamar toh batare da ya kalleta ba,ta kuma cewa"ko ni in kirashi kawae don nasan ma ba lalle ka kirashin ba",
"Ba sai kin kira ba,zanyi abunda ya kamata",d'an ta6e baki tayi suka ci gaba da yin kallon,

"Wai nikam Fateema ko Lafiya,jiya fa banga tazo gidan nan ba,yau ma gashi har yamma,ko tazo wurinka?"hajiya tayi maganar idonta akan haisam,girgiza mata kai yayi"tun Friday da nayi dropping nata ban k'ara ganinta ba",


"To Allah yasa dae lpy,don in lafiya lafiya baka k'i ganinta agidan nan ba,ba kamar ma weekend",shi dae shiru yayi baice mata komai ba,
can tace"kai bari dai in kira Dijen muji lafiya",juyawa tayi ta d'aukko wayarta akan hannun kujera ta fara k'okarin kiran Gwaggo,tana fara ringing ta d'auka,bayan sun gaisa take tambayarta lafiya bata ga Mutuniyarta ba cikin weekend d'innan,anan gwaggon ke sanar da ita cewa bata lafiya ne tun ranar Juma'a da zazza6i ta kwana,jiya jikin ya d'an yi tsanani don har sai da aka mata allura amman zuwa yau ta samu sauki sosae,salati hajiya tayi tace ai bata sani ba,tace agaida mata ita sai ta shigo dubata in Allah ya yarda,Gwaggon nace mata ai ba sai tazo ba tunda da sauk'i sosae a haka suka yi Sallama,cire wayar tayi daga kunnanta idonta akan haisam da tunda ta saki salati ya juyo yana kallonta,tace"kaji ashe wai bata lpy tun ranar juma'a da zazza6i ta kwana jiya jikin yayi tsanani har saida aka mata allura,amman dai tace da sauki",

"Allah ya bata lafiya",yace still idanunsa akanta,
hajiya taci gaba"aikam zuwa dubiya ya kama ni,ance wai ka gaida mai gaidaka,sam Fateema bata da kyaliya,kar kaso kaga yadda take tashin hankalinta in ban jin dadi,wani ciwo da nayi kwanaki tasani gaba tayi tana kuka wai bata so in Mutu"takai maganar tana dariya,shima d'an Murmushi yayi bai dai ce mata komae ba,

"Ko zaka je ka dubata ne,kaga ma sai ku gaisa da Gwaggonta don ta sanka sosai,kaima nasan zaka santa,matar akwai kirki wllh",shiru ya d'an yi,hajiya ta bishi da ido can ya furta"Ok",
"Yauwa,ka gano ya jikin nata,ko zuwa da daddare ne sai in lek'a",jinjina mata kai yayi daga haka ya mik'e,hajiya tace"in can d'in zaka ko Saude ta zuba abinci ka tafin mata dashi?" Wani kallo ya jefa ma hajiyan kaman harara"ni zaki aika da abinci",

dariya tayi"wai ai naga kaima da baka lpy ta kawo maka abun dubiya ko",
"Ba can zani ba yanzu sai after asr,in zaki bada abu akai mata ki bada"daga haka ya nufi hanyar fita hajiya nata dariya dama tsokana ce kawae tasan bazai ta6a daukar warmer din abinci ba da sunan zuwa dubiya,

Yana isa part d'inshi ya fad'a toilet don yin wanka,after some minutes ya fito jikinsa sanye da Bathrobe ya nufi Closet dinshi,within few minutes ya shirya cikin Red polo shirt da farin Jeans itama rigar daga cikin collar dinta fari ne sai faman sakin daddad'an kamshi yake,a corridor ya tsaya yasa fararen takalma,Masha Allah shigar Red and White nasan ba sai na fad'i kyan da yayi cikin kayan ba,a parlor ya d'au wayarsa da ya aje lokacin da ya shigo daga haka ya nufi Masallaci da aka gama kiran sallan la'asar.

Yana fitowa daga masallacin bayan an gama sallan ya nufi gidansu Fatuu,a bakin shagon Amadu ya tsaya shima bai dad'e da ya dawo daga sallar ba,yana ganin haisam d'in ya shiga washe baki yana gaidashi,hannu ya mik'a masa suka gaisa,cikin cool voice d'inshi yace mashi ya shiga ya sanar yazo duba Zarah ne,da sauri ya amsa mashi da toh kafin ya nufi cikin gidan,bai jima ba ya fito yace mashi ya shigo,atare suka shiga Amadu na gaba shi kuma yana binsa a nutse yake yin tafiyar har suka shiga ciki,suna shiga gwaggo dake abakin kopar d'akinta ta tarbeshi da fara'a"Maraba da d'ana Haisam",fuska a sake ya amsa mata nan take kuma ya ga ya santa da Hajiya,gashi ma har ta kirashi da d'anta,cikin d'akin tace mashi ya shigo wanda ke d'auke da gado six by six da wardrobe d'inshi mai gida biyu da d'an k'aramin Dressing Mirror sai kujera two seater da kuma one seater, d'akin sai k'amshin incense stick da aka kunna ke tashi,a bakin kopar d'akin ya cire takalmansa ya shiga da yar sallama,fuskar gwaggo da fara'a ta nuna masa kujera don ya zauna,bayan ya zauna ita kuma ta koma bakin gadon ta zauna,cikin muryarsa mai sanyi ya fara gaisar da ita ta amsa,shiru ya d'an yi can kuma ya d'ago don tunda ya shigo kanshi na a k'asa,
"Ya mai jiki",

"Ah maijiki da sauk'i sosae,oni Hajiya sai da ta taso ka ai nace mata ta samu sauki da bata wahalar da kai ba wllh", shi dai shiru yayi idonshi na kan floor d'in dakin,ita kam gwaggo idonta na akanshi bata ta6a tunanin zai zo gidan ba don iyakarta dashi su gaisa ne in yazo gidan hajiya,

can tace"Mun ga d'awainiyar abun Arziki,inata son inzo in yi godiya wllh jikin nata ne ya hana,don jiya gaba d'aya bansamu na fita bama saboda jikin nata,yau nike niyyar in shigo da daddare sai kuma ga ka,da nasan zaka zo ai da tunda safe na shigo"fuskarta d'auke da fara'a take yin maganar,
d'an guntun Murmushi yayi ba tare da ya kalleta ba yace"ba wani abu ai",

Godiya ta shiga yi mashi sosae tana shi mashi Albarka,tun yana amsawa kasa kasa har dae yayi shiru yana ci gaba da amsawa acikin ransa,tana cikin yin godiyar Amadu ya shigo dauke da plate ya d'auro ruwa pure water da yan k'ananun robobin lemu guda biyu don irinsu kawae yake saidawa saboda yan makaranta don ba freezer gareshi ba a shagon,a gaban haisam ya aje ya k'ara gaidashi kafin ya fita,shiru sukayi na d'an wani lokaci don Mutumin ba gwanin yin fira bane ba kaman kuma a inda yake bak'o,

"Kasha mana",
d'an d'agowa yayi"Nagode,bana jin kishi",
gwaggo tace"duk da haka ya kamata kasha na zumunci,sai dae kuma kar in matsa ma bansan ko baka shan irinsu ba"da yar zolaya tayi Maganar, sai dae kuma tabbas bai shan ruwan leda da irin lemun da aka kawo masa don ba kowane irin lemu yake sha ba ko a gidansu,daurewa yayi ya cije ya d'auki ledan ruwan gwaggo tai saurin mik'ewa"bari in kawo maka Cup",tsayawa yayi don dama hakanan ya d'auka ba don yana son sha a ledan ba,

dawowa tayi hannunta ruk'e da cup na jug mai kyau,ita ta zuba mashi ruwan kafin ta mik'a mashi ta koma inda ta tashi,kur6a yayi kaman sau ukku ya aje cup d'in,gwaggo dake kallonshi tace"da ina niyyar zubo abinci gashi ruwan ma ka k'i sha sosae",kallonta yayi da d'an Murmushi"a'a Nagode ban jima da naci ba",
dariya gwaggon tayi tace"ai nasanka sarai baka son cin abinci shiyasa ma ban zubo ba",
bai dai ce mata komae ba,can tace"gashi anzo gaida mara lafiyar tana ta bacci,bari in taso ta...."da sauri ya katseta"No a kyaleta,Allah ya bata lafiya"daga haka ya mike zai tafi,

Shi ya fara fitowa yasa takalmanshi kafin Gwaggo ta biyo bayanshi tana ta faman godiyar zuwan da yayi,suna kaiwa tsakiyar gidan yaji an kwala mashi kira,

"Ya Handsome",

atare suka juya shi da gwaggo inda kiran ya fito,Fatuu ce tsaye a bakin kopar dakinta tana sanye da pink riga da skirt d'in da ya siya mata acikin kayannan kanta a bud'e,ba k'aramin kyau suka yi mata ba musamman skirt din box pleated ne irin mai fad'in nan mai tattara daga sama kuma bai kai har can k'asa ba,kayan sun mata cif a jiki ba kamar daba ramamma bace sai ta koma kamar rainon madara da bournvita itama koda yake rainon madarar shanu ce😂,Slowly ya nufi inda take,tsayawa yayi yana kallonta,ta d'an fad'a ba kamar idanunta da ka kallesu zaka gane bata lpy,

"Ya handsome kai ne a gidanmu" ta fad'a tana mashi murmushi,kafin yace wani abu Gwaggo tace"Eh,ke yazo gaidawa da jiki",
kallonshi tayi"to amman shine zaka tafi kuma baka ganni ba",

dan Murmushi yayi calmly yace"kina bacci ne,ya jikin naki?"
"na samu sauk'i",jinjina kai yayi,
"To ka shigo d'akina tunda gaida ni kazo",
still da Murmushi akan fuskarshi"to ba gaki na gan ki ba",
turo baki tayi ta langwa6ar da kae"to ka shigo kaga d'akina",d'an bude mata idanu yayi,tana ganin hakan ta fara mashi magiya harda buga kafafu,shi dae still yayi yana kallon ikon Allah,

"Ina ruwan Fatuu uwar rikici tana lafiya ma ya aka cika balle bata lpy,ka shiga d'ana Haisam"Gwaggo dake jingine da bangon d'akinta ta fad'a,dariya fatuu ta fara"to an dae ce ka shigo ato",
d'an girgiza kai yayi kafin ya fara k'okarin cire takalmanshi gwaggon na cewa ya shiga dasu amman saida ya cire,sai da ya d'an duk'a da zai shiga cikin d'akin,tsaye yayi atsakiyar d'akin bayan ya shiga,ita kuwa sai faman dariyar jin dad'i take yau Yaya Handsome acikin dakinta,

"Ya handsome kaga dakina ni kadai nike kwana acikinshi,wannan kayan fa cikin na Mamata ne da ta rasu aka bani gado"Murmushi yayi yana bin d'akin da kallo,

"gashi ma baki gyarawa"da sauri ta juya tana kallon dakin kafin ta juyo"wllh kuwa ina gyarawa fa",
Yatsanshi ya mik'a yana nuna kayan dake a gefen gadonta"wannan nan yakamata a aje su?" da sauri tace"wanki ne jiya kawu Amadu yayi man,to ban lafiya shiyasa ban ninninke su ba amman gwaggo tace zata ninke man su"ganin yana mata wani kallo tace"wllh Allah ina yin tsafta,ai gwaggo ma bata bari in yi kazanta",nodding kai yayi,

nufar gadon tayi ta ture kayan can k'arshen gado ta kalleshi"kazo ka zauna Ya handsome kana ta tsayuwa",hannu ya d'an daga"No zan tafi ne,Allah ya baki lpy",daga haka ya nufi hanyar fita ta biyo shi,yana niyyar sa hannu ya d'aga labulen d'akin yayi tuntu6e da inda ledan k'asan ta fashe,da sauri Fatuu ta ruko hannunshi tace"kai Ya Handsome kabi a hankali,wllh kada Mutum take yi,rannan fa na shigo da gudu ta tad'iye ni na fad'i baka gan yadda hancina ya bugu ba,ni nama yi tunanin ya ta6e wllh",
he couldn't help it but laugh,Calmly yace"My hand"da sauri ta saki hannun"Yi hakuri,don karka fad'i ne na ruke ka"d'an ta6e baki ya yi wato in ma faduwar zai yi ita a tunaninta zata iya ruke shi ne,daga haka ya fita itama ta fito gwaggo da ta shige d'akinta ta fara kwalama kira,

"Gwaggo!gwaggo..."fitowa tayi tun kafin tace wani abu fatuu ta fara magana,
"Kinga ina ta fama dake ki canja man leda kin k'iya,ai gashi nan sauran kad'an ta kada Ya Handsome wllh"waro ido gwaggo tayi kafin tace wani abu haisam dake kallon fatuu yana Murmushi yace"ko an canja zaki lalata ne,gara abar maki shi ahaka",
Da sauri gwaggo ta kar6e"Wllh kaman kasani,mutum kullum shine shigowa da fita da gudu ba dole ta lalace ba,shiyasa nace ban canja mata ai"tana dariya tayi maganar,ita kam fatuu turo baki tayi"Wayyo don kun ga ban lafiya shine zaku yi man taron dangi ko"gaba d'aya su kae dariya,kallon gwaggo haisam yayi ya k'ara mata sallama daga haka ya nufi hanyar fita fatuu na biye dashi a baya,ita kam gwaggo tana rako shi bakin kitchen ta juya ta koma d'aki,

Yana shiga cikin zauren gidan ya juyo ya kalleta"ki koma,a ina kika ga patient na rakiya"
dariya tayi tace"ai na warke",

shiru yayi yana ta kallonta itama shi take kallo,d'age mata gira yayi"damuwa kika sa aranki shiyasa kike ciwo ko?"
turo baki tayi tace"to fa so sukayi su kashe ni ba dole in damu ba,da shikenan washe garin ranar sai dae a tsinci gawata acikin kangon,wllh nasan gwaggo itama sai ta mutu inta rasa ni kaman mamana,kawu Amadu ma ko bai mutu ba nasan sai ya sume,kai nasan bazaka damu ba ko?"still kallonta yake yace"Why",
"Saboda baka dad'e daka sanni ba",
d'an Murmushin gefen baki yayi"Yanzu dae ai bai faru ba,so stop worrying ur self en" kai ta d'aga mashi kafin tace"ai daman hakanan naji ciwon yazo man aranar da daddare"jinjina mata kai yayi yana niyyar juyawa tace"baka ga kayan dake jikina ba?",

tsayawa yayi"na gani sunyi maki kyau",
ruke ha6a tayi alamar mamaki tace"wai Ya handsome ya akai kasan kayan da zasu yi man ba tare da ka gwada ni ba,kasan fa duka kayan sunyi man daidai wllh",
fuskarshi a sake yace"Ke in naje dake wurin siyan kaya bazaki iya za6ar man daidai dani ba?"kallonshi ta fara yi from head to toe can tace"gaskiya sai dae in kanga maka kayan inga in sunyi maka,kuma ma sai dai inyi d'agyal,ko nayi ma ba lalle in kamo ka ba don tsawo gare ka nikuma yar gudul ce"ta k'arasa tana ta dariya shima yar dariyar ya yi,abunda fatuu bata sani ba shine tsananin lissafin dake akan haisam yasa daya kalli Mutum zai iya estimating abunda zai mashi daidai saboda karatun da yayi ya kunshi lissafi sosae,

"Go back Zarah"ya fad'a yana niyyar fita,maimakon ta koma d'in sai ta biyoshi tana fad'in"bari in raka ka waje sai in dawo,tun ranar juma'a da muka dawo ban sake lek'o waje ba"shiru baice mata komae ba har suka fita,adaidai gefen kiosk d'in Amadu ya juyo yace to ta koma,murmushi tayi mashi tace"Nagode Ya Handsome mai kirki"kai kawae ya d'aga mata,da baya baya ta fara komawa ciki tana mashi bye bye,yana dae tsaye yanata kallonta da d'an murmushi akan fuskarshi,cikin rashin sani ta tafi zata bugi bangon kopar shiga cikin gidan,da d'an k'arfi ya furta"Zarah!be careful"juyawa tayi ta kalli bayanta sai kuma ta juyo tana ta dariya,girgiza mata kai yai yayi mata alamar ta shige daga haka ya juya ya tafi.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_


_*BY ZAINAB LALUH*_



*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


*4️⃣5️⃣*


Misalin karfe takwas da wani abu na dare Haisam ya parker motarsa abakin shagon Amadu,fitowa yayi ya zagaya d'aya bangaren ya bud'e back door,wata k'atuwar farar leda ya fiddo ya nufi kiosk d'in bayan ya rufe kopar Motar,yara guda biyu ne ke yin siyayya,saida ya d'an jira a gefe aka sallamesu kafin ya matsa,Amadu na ganinshi ya fara washe baki ya shiga gaisar dashi,hannu ya bashi suka gaisa kafin ya d'aura ledan agaban kiosk d'in yace ya kai ciki,juyawa yayi ya nufi motarshi Amadu sai faman godiya yake mashi,hannu kawai ya d'aga mashi daga haka ya bud'e Motar ya shige ya jata,

Lokacin da ya shiga gidan,gwaggo na zaune saman darduma dake shimfide'e akan tabarma a can k'arshen bangon dake tsakankanin d'akunansu da alama salla tayi gashi ba wutan Nepa amman tsakar gidan akwai hasken globe mai caji,Fatuu na kwance agabanta ta d'aura kanta saman cinyar Gwaggon suna fira tana d'an shafa mata kai,wurinsu ya nufa ya aje ledan agabansu,

"gashi Yaya Haisam yace in kawo",

zumbur fatuu ta d'ago jin ance haisam,ita kuwa gwaggo da mamaki ta bud'e ledan tana fad'in"yace ka kawo...",
d'agowa tayi ido waje ta kalli Amadu bayan ta duba abunda ke a ciki tace"shi bai gajiya ne,wannan hidima ai tayi yawa",

Amadu yace"wllh yanzun nan ina shago ya tsaya da Mota yazo har bakin shagon yace in kawo ciki....",
katseshi fatuu tayi"gwaggo miye aciki?",
fiddo kayan cikin ledan ta fara yi tana fad'in"abubuwan ciye ciye ne",
zaro ido fatuu tayi ganin kayan da aka kawo,Manyan gasassun kaji guda biyu,manyan robobin yoghourt da ice cream guda ukku ukku sai wata leda shak'e da kayan Marmari ba abunda babu su kankana,Apple,Abarba,lemu, Ayaba,shamman,pear da sauransu dae wasu ma bata san su ba,fatuu na ganin fruit d'in tasa hannu ta rufe bakinta,

"Wannan dai da gani kayan mara lpy ne" gwaggo ce tayi maganar,
"To gwaggo wake da lpy,ai yanzu kowa kika gani ba lafiya ne dashi ba,in d'aukko Plate ki zuba man kasona na baro shago ba kowa",
kallonshi gwaggo tayi tace"Oh ni bansan wane kalan uba bane kai,yarinya bata lafiya baka siyo mata ba,an kawo mata kuma kana niyyar cinye mata",

"amman dai ai kinsan wannan kayan sunyi mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login