Showing 99001 words to 102000 words out of 212491 words
yawa ko,dama can harda mu aka kawo shiyasa ma wasu abubuwan aka sako ukku ukku",
dariya gwaggo tayi tana girgiza kai tace"Wannan dae da sunanta aka kawo don haka nata ne",tana kai Maganar ta tura ma fatuu ledan kayan,da sauri Amadu yace"Gwaggo ya da haka,kinsan fa Yarinyar nan ba hankali ta cika ba kin tura mata ledan kuma gaba d'aya",ita dai dariya kawai take ganin yadda ya harzuka,
Hannu fatuu ta kai cikin ledan kayan ta fiddo duka ice cream d'in ta aje agabanta daga haka ta tura ma gwaggo ledan tace"ni su nike so",
kallon Amadu gwaggo tayi"to kaga ita abunda ma ya dameta nan,sai ka d'aukko plate a kicin in zuba maka ko ka koma shagon,juyawa yayi ya nufi kicin d'in yana fad'in"atoh yanzu naji bayani,amman kyace wai kayan mara lafiya ne",
Bayan ya kawo plate d'in ta yagar mashi naman mai d'an yawa,ta bashi robar Yoghourt d'aya tana niyyar dibar mashi fruit d'in yace ta barshi ba yanzu ba sai ya gama da wad'annan tukun,daga haka ya nufi hanyar fita kopar gida gwaggo nata mashi tsiya,ita kam fatuu tasa ice cream d'in tayi gaba taita sha gwaggo na ce mata kada sanyi ya kamata fa,har saida ta shanye roba biyu sannan ta fara cin naman,gaba dayansu ba wanda yaci abincin dare don ba k'aramin k'oshi sukai ba,d'ayar robar Yoghourt d'in data rage gwaggo tace ma fatuu ta k'ara da ita tace to saidai ta tafi da ita Makaranta gobe,acikin d'an tsohon fridge d'insu dake acikin kicin suka saka sauran abubuwan da suka rage harda fruit masu yawa don basu sha su sosae ba,naman ma sun rage,daga haka gwaggo tasata ta d'aukko magunguna ta sha suka ci gaba da yin hira har aka maido da wuta suka nufi d'akin gwaggon gaba d'aya don su kwanta dama tunda ta fara ciwo anan take kwana.
MONDAY
Wuraren k'arfe 7:00 na safe Haisam tsaye agaban Dressing Mirror d'in bedroom d'inshi ya gama shiryawa cikin tsadaddun suit black color,yar cikin fara ce sai Bow tie red color,daga gaban aljihun ta saman anyi adon red harda wata yar sarka mai walwali,k'afafunshi na sanye da dakakkun takalma penny loafer na zallar bak'ar fata wad'anda sababbi ne fil yau ya fara saka su harma da suit d'in,ba k'aramin had'uwa yayi ba acikin kayan,da ka kalle shi zaka yanke cewa ba d'an Nigeria bane sai kaji yayi magana sannan zaka iya gasgata hakan,bayan ya gama gyara sumarshi ya kai hannu ya d'auki kwalbar turare ya shiga feshe jikinshi dashi,aje shi yayi ya d'aukko wata kwalbar ya k'ara fesawa sai da ya fesa kala ukku kana ya dakata ya feshe sumarshi da hair spray mai daddad'an kamshi,agogon Diamond d'inshi dake a ajiye ya d'auka ya sanya a wrist d'insa daga haka ya nufi kopar fita,
Bayan ya fita kopar d'akin da Fatuu taje fitsari ya bud'e ya shiga,bai jima ba ya fito hannunshi ruk'e da wata yar babbar bak'ar jaka irin ta ma'aikata,cikin parlon ya fito daga haka ya nufi kopa ya fice,
A nutse yake tafiya cikin harabar gidan bayan ya fito ya nufi part d'in hajiya,tunda ya fito Tk dake tattara busassun ganyayyakin da suka fad'o a harabar ya dakata da aikin da yakeyi gaba d'aya ya zuba ma Haisam na mujiya,ba k'aramin tafiya yayi dashi ba,yadda Haisam ke d'aukar wanka in zaije aiki yasa tk k'agara yaga ya fara aikin shima don ya rink'a daukar wankan kamar yadda yake yi,lokacin da yazo saitin tk d'in da hannu yayi mashi alamar yazo aikuwa da sauri ya wurgar da tsintsiyar kwakwar ya nufe shi,gaidashi ya shiga yi bayan ya isa,amsa mashi yayi fuska asake ya mik'a mashi jakarshi had'i da bashi Umarnin ya k'ara goge masa Mercedes Benz kafin ya fito daga haka ya wuce,juyawa tk yayi hannunsa ruk'e da jakar ya tunkari parking space d'in bakinshi a washe kaman gonar auduga,a fili yake fad'in"Yau shegiyar za'a hau..",
yana isa ya bud'e d'ayan side d'in driver ya aje jakar ya maida kopar ya rufe,lallausan farin yadin da yake goge motoci dashi ya d'aukko acikin wurin ya fara goge jikin Motar wadda dama tuni agoge take sai faman kyalli take don kullum ne sai Tk ya gogeta duk da ba hawanta Haisam d'in ke yi ba tun bayan da ya zo da ita.
Bakinshi d'auke da Sallama ya shiga cikin parlon,Hajiya dake zaune saman Sofa 2 seater jikinta nad'e da lifaya Milk Color mai Manyan fulawoyi light blue idanunta sanye cikin glasses ta amsa mashi had'i da kai idanunta gareshi,suna had'a ido ya sakar mata k'ayataccen Murmushinshi itama Murmushin takeyi,nufar inda take zaune yayi yana fad'in"Gud Morning My Sweethrt ",
Hannu ta mik'o mashi" Morning a Shining Star,How was ur nyt?",
"Alhamdulillah"ya fad'a yayin da ya kai hannu yana tattara takardun dake gefenta ya zauna,
"Yau zaki fita kenan",
"Eh,muna da bak'in turawane, shiyasa zan fita da wuri don mu tar6esu",jinjina mata kai yayi,
"Bari akawo maka ko tea ne ka sha", hannu ya kai Saman Sofa table dake gabanta ya d'aukko tea cup dake d'auke da kakkauran tea mai zafi yana d'an tiriri yace"let me take this" kai ta d'aga masa ya fara sipping tea d'in,yana cikin sha Saude ta k'araso inda suke hannunta d'auke da d'an babban plate an rufeshi ta aje asaman table din,kallonshi tayi tace"Barka da Safiya Yalla6ai",
"Barka"ya amsa mata,juyawa tayi gun hajiya"Hajiya gashi nan,za'a zubo masa ne?" kafin ta bata amsa Haisam ya girgiza mata kai alamar a'a,hajiya tace ta tafi kawae,
Hannu hajiya tasa ta bud'e plate din,kallon haisam tayi"ka d'an had'a da wad'annan kafi jin nauyin cikinka",
kallon plate d'in yayi,sliced bread ne da wainar kwai,ganin bai ce komai ba yasa hajiya kai hannu ta d'aukko yankan biredi d'aya ta yago wainar tasa aciki ta fara k'okarin bashi a baki,a hankali yake gatsar bread d'in yana sipping tea d'in har ya cinye ahaka yaci guda biyu ganin tana kokarin d'aukko wani yasashi mik'ewa da sauri yace"am Ok Sweethrt",k'yaleshi tayi don tasan baison cin abinci da sassafe wannan bread d'in ma da ya ci sa'a aka ci,duk'awa ya yi saitin fuskarta ya manna mata kiss a gefen fuskar wanda hakan yake mata kullum in zai tafi aiki,mik'ewa ya yi ya tunkari Corridor d'in dakinta bayan d'an wani lokaci ya fito da alama bakinshi ya wanko,hanyar fita daga falon ya nufa yana fad'in"Till i come back",
Hajiya dake Murmushi ta fara yi mashi Addu'ar da ta saba yi mashi kullum"Allah Ubangiji Ya tsare,Ya baka ikon yin abunda kaje yi,ya kuma maido man da kai lafiya",
Hannu ya d'ago mata"wish u same Sweethrt",daga haka ya fuce,hajiya dake kallon bayanshi tana ta murmushi ta d'an girgiza kai,tana matuk'ar kaunar Haisam ba kamar kuma da ya kasance akwae yanayin Mijinta da ya d'aukko wato Gen. Adamu Zakee.
__________________
Mik'ewa tayi bayan ta gama sanya igiyoyin Sandals dinta ta goya yar jakarta ta makaranta, kallon gwaggo tayi dake tsaye abakin kopar d'akinta,
"Zan tafi Gwaggo",
"kindai matsa sai kinje Makarantar nan,da kin bari kin k'ara samun sauki sosae", turo baki tayi tace"ai na samu sauk'in zan iya zuwa,kuma in na zauna ma ai ni kad'ai za'a bari tunda kema aiki zaki ko",
"Ai shikenan,dama ina gudun kar jikin ya dawo maki ne a Makarantar...." katseta Fatuu tayi"in ma ciwon ya dawo ba ga Haulatu ba ai sai ta rakani clinic ko akan dae in zauna ni kadai a gida",
gyad'a kai gwaggo tayi kawae dama ita niyyarta ta tura Fatun gidan hajiya in zata aikin to ta matsa sai taje makarantar,kud'i gwaggo ta mik'o mata ta amsa daga haka ta juya ta nufi hanyar fita,
"ba kin ajiye abu ba a fridge jiya kince dashi zaki makarantar",Gwaggo ce tayi Maganar,da sauri ta juyo ta nufi kicin tana fad'in"Yauwa kakus nagode da kika tuna man don har na manta",d'aukko robar youghout d'in tayi ta hado da fruit a bakin kicin ta saukko da jakar ta zuba su ciki kafin ta maidata bayan,nufar kopar fita tayi tana fad'in"na tafi kakus",
"A dawo lpy,Allah ya tsare", juyowa tayi ta kalli gwaggo,"yau baki cewa banda rigima don Allah Fatuu?",
Yar dariya gwaggon tayi tace"ai na lura dae kaman da gaske kin daina rashin ji,da alama Allah ya kar6i Addu'ata",dariya kawai tayi ta d'aga mata hannu tana mata bye bye itama gwaggon hakan tayi mata har ta fuce,girgiza kai Gwaggon tayi,tana Matuk'ar jin Fatuu cikin ranta,tamkar Aysha d'inta take kallonta,juyawa tayi ta shige cikin d'aki don ta idasa shiryawa itama ta tafi wurin aiki.
Parking Space ya nufa bayan ya fito,a tsaye ya iske tk yana d'an k'ara kakka6e jikin Motar, yana ganin haisam ya dakata da abunda yake yana mashi dariya,yana isowa kusa dashi yasa hannu da sauri ya bud'e mashi Motar,har zai shiga ya juyo ya kalli tk dake ta faman bin sa da ido,
"Any problem?"ya tambaya fuskarshi a sake,maimakon ya bashi amsa sai yasa hannu yana d'an sosa k'eya,a zahiri tabbas yana da buk'ata,sai dae bazai iya fad'i mashi ba don gani yake buk'atar tashi tana da d'an girma,wani mashin ne da ake yayi yake so ya mallaka sai yaba kaninshi nashi da yake da,tuntuni yake rok'onshi ya bashi mashin d'in yace mashi ya bari sai ya siya wani to kuma yanzu baida kudin da zai siya wanccan din don ba wata sana'a yake ba illa kud'in da hajiya ke saka mashi a Account a duk k'arshen wata saboda Karatunshi da yan hidindimun kanshi,duk da yana balaen son mashin d'in bai ta6a tunanin tambayarta ba don dama tk yana da hangen nesa sam baida had'ama ya iya bin komai a hankali kuma hada hakan yasa yake zaune lafiya da hajiya,
Jin yayi shiru yasa Haisam gane akwae wani abu,
"tell me,kana da matsala ne?",
Haisam da ya rik'e murfin motar ya sake tambaya,d'an Murmushin yak'e Tk yayi yace" ba wani abu Yaya haisam",
shigewa yayi cikin Motar tk ya matsa don ya rufe masa kopar,
"U can send me a message",
Haisam ya fad'a ba tare da ya kalli tk d'in ba,rufe masa kopar yayi bayan ya amsa mashi da toh,sai da yayi Warming d'in Motar kafin ya fita daga cikin parking space din,shima tk fitowa ya yi ya tsaya gefe guda yana kallon Motar,da gudu ya ja Motar ya fice daga gidan su officer na d'aga mashi hannu ya sakar masu Horn.
************,
Tafe take ta raba hanya biyu tana ta tafiya sai dai yau tafiyar tata da yar natsuwa ba kaman yadda ta saba wurga k'afafu ba in tana tafiya,horn d'in da aka yi mata da k'arfi ne yasa ta koma gefen hanyar da sauri ba tare data waigo ba,cigaba da tafiya tayi aka k'ara yi mata horn d'in aikuwa a fusace ta juyo cike da tsiwa ta bud'e baki zata yi magana,tana yin arba da Bak'ar Motar dake a bayantan ta kasa magana,bin ta kawae tayi da ido ba tare data san ko waye a ciki ba,slowly glass d'in kopar gaban ya fara sauka k'asa,tana yin arba da fuskar Haisam tasa duka tafukan hannayenta ta rufe baki alamar mamaki,jingina kanshi yayi ajikin headrest d'in seat yana kallonta fuskarshi a sake,
"Ya Handsome ashe kaine kake ta man horn" fatuu ta fad'a bayan ta cire hannun,
"Yea,ni ne za'ai ma masifa" ya bata amsa,
Tura baki tayi"ni fa ba masifa zanyi ba,da naji an k'ara yi man horn dinne shine na juyo ince ai na kauce",d'an ta6e baki yayi don yasan ba gaskiya ta fad'a ba,
"Kin samu sauki ne zaki school?"
"Eh,kuma ma in ban je ba ni kad'ai za'a bari agidan",
jinjina kai yayi"Ok,get into d car",
hannu ta d'aga tana nuna motar tace"in shigo kace?" kai ya d'aga mata alamar eh,matsawa tayi ta kai hannu zata bud'e kopar baya taji ta a rufe,komawa tayi saitin haisam tace"Ya handsome tak'i bud'ewa ko ba ta nan ake shiga bane?",daga yadda ya kwantar da kanshi ya daga mata kai alamar eh,
"To ta ina ake shiga?",ta tambaya,
yatsanshi guda ya d'aga sama,zaro ido tayi"kenan ta sama ake hawa?",gyad'a kai yayi,cike da mamaki take kallon saman Motar can tace"itama kaman jirgi ce kenan ta,to mi zan taka in hau,ko itama tsani ke gareta?" Still yayi yana kallonta ganin da gaske ta d'auka ta saman ake hawa,tunanin ranar da zata daina wauta ya shiga yi tana ganin handle ajikin kopan bayan amman take tambayan ko bata nan ake shiga ba,ganin tana ta kallonshi tana jiran amsa yasashi cewa"ke zaki hau da kanki",
hannu tasa ta ruke ha6arta ta fara tunanin yadda zata hau saman Motar,kallonshi tayi tace"Ya Handsome kodae ka idasa sauke glass d'in sai ka matsa man in shigo ta nan inda kake",wani kallo ya bita dashi kafin ya kai hannu ya bud'e k'ofofin ta gaba,juyawa yayi yace"ki shigo",
"Ta ina?"ta tambaya,
"Ta ina kika san ana shiga Mota?" hannu ta d'aga ta nuna mashi k'opa,kai ya gyad'a mata alamar tanan zata shigo,da sauri ta kama handle din ta ja sai gashi ta bud'e,shigewa tayi ta rufe kopar da karfi don kar yace bata rufu ba irin rannan,tsakiyar backseat d'in ta zauna ta kame wuri guda,wani irin ni'imtaccen sanyin Ac had'e da kamshi suka fara ratsata sai faman sakin Murmushi take,d'aga kai tayi suka had'a ido da Haisam ta cikin madubin gaban Motar,dariya tayi mashi tace"ashe wasa kake man kace ta sama ake shigowa",
shi dae kallonta kawae yake bai ce komai ba,
"to na shigo Ya Handsome mu tafi",
D'age mata gira yayi ta cikin madubin"ina?"
zaro ido tayi"ba kai kace in shigo ba,ai nayi zaton Makarantar zaka kai ni fa",
K'ara gyara kanshi yayi a jikin headrest,
"yeah can zan kaiki amman in kin zauna a inda ya dace",cikin rashin fahimta tace"to a ina zan zauna?"hannu ya kai ya d'auke jakarshi da yatsanshi ya nuna mata kujerar dake a gefenshin tace toh,maimakon ta bud'e Motar ta fita ta zagaya sai ta kutsa ta tsakankanin kujerun gaban,har saida haisam yaja gefe guda,zaunawa tayi a kujeran gefen nashi ta kalleshi,
"to na dawo",
kai ya d'aga mata ya maida jakar baya daga haka ya ja Motar suka fara tafiya,
"Ki sauko bag d'in mana"yace mata ganin ta takure don da jakar a bayanta ta zauna,curo jakar tayi ta aje ak'asan seat din,
"wllh sanyin ya fi yawa anan gaban"ta fad'a tana lullu6e jikinta da hijab dinta,hannu ya kai ya rage mata Ac din ba tare da yace komai ba,curo hannuwanta tayi daga cikin hijabin jin sanyin ya rage ta kalli haisam da idonsa na akan hanya cikin natsuwa yake driving din,
"Ya Handsome"ta kira Sunanshi,d'age mata gira yayi alamar amsawa ba tare da ya kalleta ba,
"Wai kaima abun dubiya ne ka kawo man jiya?"shiru ya d'an yi kaman ba zaice komai ba, ganin tayi kasak'e tana jiran amsarshi yasa shi cewa"ko nayi laifi ne?",
Da sauri ta girgiza kai"a'a ba kai laifi ba,kawae dae naga kayan da yawa nasan ka kashe uban kud'i amman naji dadinsu wllh,kasan mi?" kai ya girgiza still idanunsa na a kan hanya,
"Duka fa ice cream d'innan roba ukkun ni kadae na shanye su,na bar masu Yoghourt din,amman su d'aya d'aya suka d'auka aka bani sauran roba d'ayan ka ganshi ma nan a jakata zani Makaranta dashi harda ma fruit na d'ebo,naso ma in aje ice cream d'in shima roba d'aya amman na kasa saida na shanye shi duka tun jiyan sannan hankalina ya kwanta"ta k'arasa tana ta dariya,
sai lokacin ya d'an kalleta yace"kina shan sanyi da yawa zaki ciwo fa",
langa6ar da kai tayi cike da shagwa6a"to ai bakina ne bai man dad'i shiyasa da nasha naji yana da d'an banzan dadi na kasa hakuri saida na shanye shi duka"d'an Murmushi yayi ya cigaba da driving,
"Thank u so much Ya Handsome mai kirki,May Allah give u more Money"yadda tayi turancin gwanin dad'i ba kaman da yake Muryarta har yanzu akwae d'an sautin fulani dama kuma in bafullatana tayi turanci sound d'in ba dai dadi ba,
Juyowa yayi ya kalleta"Ameen yar fillo" fuskarshi d'auke da Murmushi yayi maganar,turo baki tayi sai kuma tayi dariya tace"ai kai Yayana ne ko kace man hakan bazan ji haushi ba",
cigaba yayi da driving fuskarshi a sake,can tace"Wai Yaya Handsome kasan makarantarmu ne?naga muna ta tafiya kuma baka tambayeni inda take ba,
"Kaman haka"ya bata amsa,
"to ya akai kasan Makarantarmu?ko ka ta6a kai wata ne?ko kana da Budurwa acan ne?"
"bani da ita",
"Budurwar?"kai ya daga mata alamar eh,
"To ya akai baka da ita?baka ta6a cewa kana son wata bane?",yace"yea",
"kuma wata bata ta6a cewa tana sonka ba Ya Handsome?kai ya daga mata alamar eh,jinjina kai tayi"nasan akwae masu son ka kawai tsoronka suke ji balle su gaya maka kasan fa ko Ya Handsome,wllh in Mutum bai sanka ba da ya ganka zai yi tunanin kai masifaffe ne mara kirki,nima da farko nayi tunanin hakan"shiru ta d'an yi kafin taci gaba,
"Don dae ni k'arama ce da sai ka so ni,kuma ma ni ko na gama Secondary Skul ba zan yi aure ba sai na zama likita na fara aiki ma",
Wani kallo ya juyo ya yi mata kafin ya maida idon kan hanya yace"to ko in jira ki ne?",
zare ido tayi"ka jirani har in zama likitan?"
"Yeah,
"tabb lokacin ai ka fara zama tsoho",d'an jinjina kai yayi da d'an Murmushi yace"ba zaki so tsoho ba kenan",
"Gaskiya lokacin fa ni nazama babbar Budurwa kuma sai in auri tsoho,kuma kai ai yanzu yakamata kayi budurwa ko kayi aure kaima kaman abokinka,in kana so sai in yi ma Budurwa a Makarantarmu, a Ajinmu akwae wata Sofiya Moussa tana da kyau,kasan mi?" Haisam da yayi still yana saurararta ya girgiza mata kai alamar a'a,
"Itafa Safiyar buzuwa ce yar Nijar baka ganta ba fara ce sosae tana da gashi,kuma doguwa ce,nasan in ta ganka da gudu zata amince don yan Makarantarmu ko Malami suka gani mai kyau mai yin gayu sai su fara sonshi kaga sunata rububinshi balle kai,in gaya mata kana sonta?"
D'age gira yayi ya d'an kalleta itama shi take kallo tana jiran amsarshi yace"wa kenan?"
"Safiyar",
girgiza mata kai yayi"bansa ki ba",
gyad'a