Showing 27001 words to 30000 words out of 212491 words

Chapter 10 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

953

fara kiran Saude,daga cikin corridorn da bedrooms suke Saude ta fito tana yafa kallabinta,hajiya ta bata umarnin ta kawo masu Abinci cikin parlor,ta juya ta fara kawo masu,kafin ta gama jerawa Kawu Mani ya juya yana tambayar hajiya"hajjaju ya wajen mutanen Lagos,hajiya Maryam da k'waran mijinta kwana biyu bamu gaisa ba? Daria hajiya tayi tace "suna nan lafiya lau",a lokacin Saude ta gama serving abincin saman lallausan Carpet d'in parlon bayan ta gaishe su tace masu"Bismillah" suka amsa da "to" had'i da yi mata godia,ta juya ta koma ciki Hajiya ma tace masu zata d'an shiga ciki kafin su gama.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

*Mallakin*
⬇️
*ZAINAB LALUH*🌹
*(Oummu imam)*

*Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp banda phone call,Thanks🤝*


*Free page1️⃣6️⃣&1️⃣7️⃣*


Haisam na fitowa daga part d'in Hajiya ya nufi Part d'insa yana amsa wayan da aka kira shi,a daidai stairs din balcony ya gama wayan,tura kofa yayi ya shiga cikin parlon ya zauna kan kujera hadi da daukar Remote yayi powering tv On,ya d'an kishingida yaci gaba da kallon American film d'in da yake kallo a MBCMAX, bayan wani d'an lokaci ya dau wayarsa ya duba time,sake d'aukan remote yayi yai Offing tv sannan ya mik'e ya nufi bedroom.
Sanye cikin Sportswear ya fito,red t-shirt da wandonta black daga gefen hagu na rigan na dauke da tambarin ADIDAS wanda akayi da bakar sak'a haka wandon ma adai dai gefen da akayi rubutun rigan shima akayi da jar sak'a daga k'asa yad'an matse,ba k'aramin kyau yayi cikin shigan kayan ba,kuma da ganin laushin kayan tabbas zasu yi kudi,saida ya tsaya yasa takalma a corridor kafin ya iso cikin parlon ya dau wayansa ya fice zuwa masallaci wanda liman ke ta kwalla kiran sallah,
Tare da su Uncle Mani ya fito bayan angama sallan la'asar d'in ya nufi cikin parking space don fiddo da Bike d'insa bayan yayi ma T.k da ya fito daga masallaci bayan sun fito umarnin ya daukko masa jakarsa kaman jiya,

Uncle Mani ya nufi part d'in Hajia don yi mata sallama su kuma su Alhaji Sa'idu suka tsaya gefen motar da suka zo da ita suna jiran ya dawo gaba daya hankalinsu na kan Haisam daya fiddo bike d'in cikin harabar ya haye yana kokarin sa helmet,adai dai lokacin da t.k ya kusa k'arasowa da jakar,
Hajiya da Kawu Mani suka fito suka nufo parking space din,Kawu Mani dake ta kallon Haisam tunda suka fito ya fara magana"Yanzu Hajjaju shima Haisam na hawa irin mashin d'in nan? Hajia ta ta6e baki tace " Unn" adaidai lokacin da suka k'araso wurin su Alhaji Sa'idu ya kunna mashin d'in gaba daya suka toshe kunnuwansu da hannayensu da sauri,haisam ya d'an juyo ya d'aga ma Uncle Mani hannu alamar yana masa sallama bai jira ya maido masa ba yaja mashin din da gudu ya tunkari gate d'in da tuni an wangale masa shi.
Uncle Mani ya sauke ajiyar zuciya bayan Haisam ya fice yace"I don't know what's wrong with our Youths,abu mai had'ari shi suke mayarwa abun adon su,and what really baffle me with them shine duk irin mummunan had'arin da mashin d'innan ke haddasawa hakan bai serving dinsu misali su daina hawan...Alhaji Sa'idu ya kar6e"Sam basu bi dashi yadda yadace ne,haka zaka ga suna ta falla uban gudu kai kace zasu kiyama..."Mutumin na karshe ya katse shi da cewa"Ai wasu kam kiyaman suke tafiya wllh sam basu la'akari da irin titinan mu ba kaman na waje bane,su yi ta tuk'in ganganci,gashi naji ance mashin d'in tsada ne dashi sosae..."Hajiya dake tsaye hannuwanta goye a bayanta ta amsa "tsada kam! Miliyan biyar ya zuba kafin ya mallaki wannan nasan..."gaba daya suka zaro ido a tare suka maimaita kudin da hajiyan ta fad'a,ita kam kai ta jinjina masu Uncle Mani yace "to Allah ya kyauta,Allah ya k'ara tsarewa,gaba d'aya suka amsa da Amin" daga haka ya kalli hajia da d'an murmushi yace "to hajjaju mu zamu wuce sai wani lokaci kuma in Allah yasa rayuwarmu ta kai" hajia tayi murmushi tace"To Allah yasa rayuwar tamu ta kai" ta fiddo hannayenta dake goye a bayanta ta mik'a ma Alhaji Sa'idu kud'i dake cikin hannunta na dama da fara'a tace"gashi ayi ma iyali tsaraba nagode da ziyara,Allah yabar zumunci" hannu biyu yasa ya kar6a harda d'an russunawa suna ta godiya shida dayan,Uncle Mani yace"To ni hajjaju ba'a sallame ni ba" dariya tayi tace banda kai ai sune bak'i na, kai na gida ne" shima dariyar yake ya bud'e mota yace"ba wani abu nasan tawa sallamar babba ce tafi karfin hannu k'ilan,zan turo Account details" daga haka ya shige Abokan tafiyarma suka shiga suna ta kara godiar rafar 50k da hajia ta basu cike da farinciki hannu ta d'aga masu bayan sun fita daga cikin parking space din tace"Agaida Iyali",daga haka ta juya ta koma ciki.

Tunda ta shige gida take kunshe a daki,bayan tayi sallar Azahar bacci yayi awon gaba da ita,ko Uniform d'in bata cire ba,bugun kofar da ake tayi ne ya farkar da ita a tsorace ta fito daga d'akin tana tafiya cikin sand'a har Lokacin kuma ana ta buga kofar da k'arfi,tsayawa tayi cikin zauren tana tunanin waye ke buga kofan haka? kodai mai Motar ne ya kawo k'ara,ji tayi gabanta yayi mugun fad'uwa nan take tsoro ya kama ta tace a ranta "to ya akai yasan gidanmu bayan lokacin da na jefi motan ba kowa wurin..." wani bugu aka yima k'ofar wanda daji mai buga kofan ya k'ule yasa ta tunkari kofar da sauri ta d'an leka idonta d'aya ta ramin makulli nan take ta gane waye da sauri takai hannu sama ta cire sakatan sannan ta d'an ja baya,aikam da karfi aka bugo kofan don da bata matsa ba daba k'aramin buguwa zatai ba,rai a6ace yake kallonta Kawu Amadu ne hannunshi daya rungume da kwali d'ayan kuma katuwar leda ce,Fatuu dake ta faman zare ido tace "sannu da zuwa Kawu Amadu...."da sauri ya katseta da fad'in "sannu da zuwan uwarwa,don iskanci daman kina cikin gidan kika barni inata bugun k'ofa tsawon lokaci,to waima uban me kike a cikin gidan daba zaki zo ki budan ba? d'an turo baki tayi tace "ba komai,bacci ne ya d'auke ni fa" a harzuk'e yace"to miye na kulle kofa don zaki yi bacci" da sauri tace "ina gudun kar a shigo ayi sata ne ina baccin...." "k'arya kike" yace yana k'are mata kallo kafin yaci gaba "fad'a kika jawo ko? Da sauri ta girgiza kai alamar a'a,kwafa yayi yace "ai na dawo gidan inma rigima ki ka jawo zan gani,kuma uban miye na zama da Uniform har yanxu a jiki da alama ma ko wanka baki yi ba,bare kiyi sallah" ya k'arasa maganar yana kokarin aje kayan hannunsa a bakin kofa,d'agowa yayi ya daka mata tsawa"wuce kije ki wanka kafin na buge ki a wurin" juyawa tayi ta nufi cikin gida tana d'an k'unk'uni har ta nufi d'aki taji yace"bakiji mi nace kiyi bane? Da sauri tace "naji.." yace"to wuce ki dau bokiti ki d'ibi ruwa" ta wuce ta xuba ruwan ta shige band'aki,shima yana shiga wankan yayi a d'an band'akin cikin d'akin nasa ya shirya ya kwashi kayan da ya siyo ya nufi shago don jera su.

Sai can bayan Issha gwaggo ta dawo,fatuu dai na k'unk'ume a d'aki cike da zullumin kar akawo k'ararta, koda ta fito tayi ma gwaggon sannu da zuwa dakin ta koma ita kam gwaggo a gajiye take hakan yasa ko ta kan Fatuu bata bi ba balle har ta fahimci wani abu,sai can dare gwaggo tayi bacci sannan ta fito taci abinci tayi sallah ta koma ta kwanta tare da yankewa ranta cewa baza'a kawo k'arar tata ba tunda har aka kai wannan lokacin.

Washe gari asabar da safe Fatuu ce da Haulat zaune cikin ajin su na islamiyya,Haulat ta kalli Fatuu da murmushi tace"sannu hajiyar fad'a" wata yar dariyar iskanci fatuu tayi tace "waya ce maki nayi fada" d'an ta6e baki Haulat tayi tace "har gida akazo aka fad'a mana irin fadan da kuka yi, wai har kin fasa ma Murja baki da hanci" murmura idanu Fatuu tayi tace"Yessss,gobe ma ta k'ara gaya man banzan maganganu harta kirani da yar kauye" girgiza kai haulat tayi tace"ni wllh don kince Gwaggo bata nan amman a lokacin da sai na kai k'arar ki tunda ke dai baki da hakuri" harararta Fatuu tayi tace "aida da ta dawo kinzo kin kawo k'arartawa sarkin masu hakurin duniya" haulat tace "tunda ya rigada ya wuce miye na inzo,Amman ai naji ance wani mutum ne yayi maganinki da ki ka k'i barin fadan ya wanka maki mari" ta kai maganar tana tik'ar daria,wata yar iskar dariya Fatuu ta sake yi tace"hehehe ashe yai maganina,muka dai yi maganin juna don shima yayi asara ehe" haulat ta dakata da dariyar da take tace "what do you mean da ku kai maganin juna?wace irin asara kuma? Fatuu ta gyad'a kai da turancin ta na yar sakandire tace "what u hear" Still haulat tayi tana ta kallonta can tace "don Allah Fatuu fad'a man abunda kika yi masa" fatun na shirin yin magana Malaminsu ya shigo hakan yasata yin shiru daga nan kuma basu sake samun daman yin magana ba don yana fita wani ma ya shigo a haka har aka tashi,akan hanyar su ta komawa gida Haulat tace "d'azun na tambaye ki mi kika yiwa Mutumin baki gaya man ba" banza fatuu tayi mata,haulat ta sake cewa "kinji,mi kika yi masa ne" ba tare data kalleta ba tace"ke dalla bafa komai,wasa nike,ba abunda nayi masa kawai don kar kiyi tunanin yayi nasara akaina ne" haulat tace "kawai dai bazaki fadan bane Amman ko nayi rantsuwa ba zanyi kaffara ba tunda kika ce yayi asara da akwai abunda kika yi masa...." cikin tsiwa tace "ehh d'in nayi, tunda ba ki yarda ba abunda nayi masa ba" shiru haulat tayi amman ba don ta yardan ba,can tace "to ki kar6i jakar ki ko,kince in taho maki da ita kuma kin barni inata kayanta" juyowa Fatuu tayi ta figi jakar ba ko nagode tayi gaba abunta sai wurga kafa take da alama dai ta saba da yin tafiya haka,girgiza kai haulat tayi tace daga abun arziki,tabi bayanta har suka zo bakin lungun da suke rabuwa,haulat ta d'an daga murya tace "sai munhade Anjima hajia Fatuu ikon Allah" Fatuu ta juyo tayi mata kallon up and down ta k'ara gaba,Haulat dai dariya tayi a fili tace"Allah ya shirye ki" daga haka ta nufi hanyar gidansu, adai dai kofar shiga gida fatuu ta waiga tana kallon hanyar da haulat ta bi a fili tace "don ina sakarya Allah ya rufa man asiri in tona ma kaina,don na tabbata na fad'i mata sai ta fad'a ma gwaggo ko kuma tayi ta ma mutane nasihar banza ita ga mai hakuri yen-yen-yen" ta d'age baki daga haka ta shige gida.

Haulat ce keta faman sauri da yamma zata islamiyya don ta makara sakamakon aikenta siyen gero da Innarsu tayi,tana k'okarin shiga lungun da zai kaita har islamiyyar taji daga gefenta ana magana "Ke,ke yar liman wait" da sauri ta juya tana kallon mai maganan,ya nufota yana wata irin tafiya irin ta nigas,da mamaki haulat ke kallonsa tana tunanin ita miye had'inta da Gaye da zai tsaida ta,yana k'arasowa yace"Ke dalla tambayanki zanyi kike ta faman zare ido uwa mujiya" ita dai haulat shiru tayi tana jiran jin abunda zai ce,ya ci gaba "dama tambayanki zanyi k'awarnan taki an kamata tana can cikin cell ne ko har anyi gaba da ita? cikin rashin fahimtar zancen shi haulat tace "wace kawar tawa kuma? Wata yar iskar daria yayi yace "kina da wata k'awa ne bayan Aljanar yarinyar nan mara jin magana, kullum ba tare nike ganinku ba" nan take ta gane Fatuu yake nufi don duk in suna tare suka had'u dashi Aljana yake cema fatun,da sauri haulat tace "to mitayi da za'a kai ta cell kuma? tayi maganar cike da fargaba tana ta zare ido, rik'e ha6a gaye yayi yace "wai kina nufin baki san aika-aikar da aljanar nan ta aikata ba...? da sauri haulat ta girgiza masa kai alamar a'a, jinjina kai yayi yace"tabb,to wllh ruwa ta 6allo ma kanta don ina tabbatar maki sai taje gidan yari..." da sauri haulat ta dafe k'irji tana salati tace"don Allah Gaye ka gaya man abunda tayi,ni sam wllh bansani ba" sai da ya gyara tsayuwa ya karkace baki yace "to bari kiji wani mutum ne jiya hakanan Aljanar nan ta jefar masa glass d'in bayan mota,gaba daya ta dagargaza glass din don wannan glass din yayi konden..." cikin tsananin tashin hankali haulat tasa hannuwanta duka biyu ta rufe bakinta ya ci gaba "atoh kima fad'a mata ta shirya don comfat (confirm) in ba'a biya shi ba har yakai k'ara na rantse da Assamadu sai taje fursun,yo motar fa ba k'aramar mota bace,to tsaya ma kiji,mai motar dan gidan Hajiyar Sanata ne kinsan kuwa ba'a k'aramar harka a gidan nan......" daga haka ya kad'a kai yayi gaba abunshi,

kasa motsawa haulat tayi na tsawon lokaci da k'yar ta juya taci gaba da tafiya a hankali gabanta sai fad'uwa yake tamkar itace akace zata gidan yarin,cikin zuciyarta kam mamaki kawai take na abunda fatun ta aikata,ashe asarar da take nufin mutumin yayi kenan,"tabb lallai Fatuu bata da hankali!" ta fad'a a fili tana jinjina kai.
A daidai bakin ajinsu ta tsaya tana tunanin shiga don tasan ta makara gashi akwae malami cikin ajin,can dai tayi shahada ta kutsa kai tare da yin yar sallama,d'an kallonta malamin yayi yaci gaba da bayanin da yake hakan yasa haulat yin saurin shigewa ta nufi wurin zamansu sai dai ga mamakinta Fatuu bata a wurin,tunani ta fara yi a ranta bayan ta zauna"to Fatuu bata zo bane? Kodai anje an kamata...wani irin bugu gabanta yayi da sauri ta d'ago da kanta a lokacin kuma ta hango fatun acan dayan bangaren,tunda haulat ta shigo ta wuce Fatuu ta ganta a ranta tace "da nice na makara da ya buge ni,ni da kowa ya tsana"ta saci kallon malamin ta d'an hararesa kafin ta juya inda haulat take nan take suka had'a ido don tunda ta hango fatuu take ta kallonta cike da al'ajabin abunda gaye yace zai sameta,murgude fatuu tayi mata ta juya,haulat ta girgiza kai cike da tausayinta,ta kuma fahimci dalilin da yasa fatun ta canja wurin zama don ta saba hakan da d'an abu ya hada su wanda bai kai ya kawo ba sai ta canja wurin zama sai tagadama ta dawo ko haulat taje ta bata hakuri sannan ta dawo,haulat ce kad'ai ke iya jure halin fatuu don ta karanci halayenta tsab shiyasa ma bata biye ta.

Haulat ce keta sauri ta isko Fatuu don da aka tashi ta tsaya copying rubutun da malam yayi bata nan daga littafin wata kawarta da suke zama tare,ita kuwa Fatuu ana tashi tayi gaba abunta don guje ma haulat din take karta k'ara tambayarta game da asaran da tace Mutumin daya raba su fad'a yayi don tasan halinta wani lokacin nacin tambaya ne da ita kuma karshe inta gano tana iya zuwa ta fadi ma gwaggo "Fatuu!fatuu ki tsaya" haulat dake biye da ita a baya tace,ganin bata da niyyar tsayawa yasa haulat yin dan gudu tasha gabanta,cak fatuu ta tsaya fuska ad'aure tace "miye haka zaki wani shage gaba na" kasa magana haulat tayi don k'arfin halin fatun mugun mamaki yake bata ta aikata irin wannan babbar ta'asar amman hankalinta akwance,tsoki fatuu taja tana kokarin bin ta gefen haulat din,taji tace "To ai yanzu nasan abunda kike 6oyewa hajia" da sauri fatuu ta kalleta sama da k'asa tace "ni mi nike 6oyewa? Haulat ta jinjina kai cike da takaici tace "asarar da kika ce mutumin nan yayi na tambayeki wace asara ce kika k'i fad'a man to yanzu nasan komai,ke yanzu fatuu abunda kika yi kin kyauta?hakanan ki jefar ma mutum mota har ki lalata masa glass....."katse ta Fatuu tayi da fad'in "naje na fasa d'in,dama nasan ai sai kin bi diddigi don kin saba sa man ido,to na fasan kuma ko gobe ya k'ara shiga harkata har ya d'aga hannu ya mareni sai na kara ja masa asara don ni ba ai man na kyale ehe" daga haka ta kad'a kai tayi gaba,cikin d'aga murya haulat tace "to kinsan wanene kika fasa ma gilashin mota.....? a fusace ta juyo tace"ina ruwana da ko waye,Allah yasa d'an sarkin makkah ne" ta juya taci gaba da tafiya abunta don ita tayi tunanin tambayarta haulat d'in tayi,cike da takaici haulat tai tsaye tana kallon bayanta a fili tace "lallai Fatuu bata da hankali wllh bata san bala'en da ta jawo ma kanta bane,tama k'i ta tsaya ta saurare ni...." girgiza kai tayi ta fara tafiya tana ta sak'e sak'e a ranta "ko dai inje in sanarma gwaggo don tasan halin da ake aciki..." girgiza kai ta sake yi da sauri a fili tace "kai a'a,bai kamata ta fara jin wannan mummunan labarin daga baki na ba gaskia" can kuma tace "to wai ma ni ina ruwana da zan damu,ita wadda ta aikata laifin ma ko a jikinta,kawai dai ba dad'i ne kana tare da mutum wani mummunan abu ya same shi,to amman tunda ita taja ma kanta ai ita ta sani" ta watsa hannuwa,daina bin bayan fatun tayi,ta canza hanya,lokacin da fatuu zata sha kwana ta juya bata ga haulat d'in ba ta6e baki tayi a ranta tace gwara da nayi mata haka inba haka ba sai tace zata zo ta gaya ma gwaggo,a fili tace "inma tazo ta fadan sai in k'aryata ta tunda dai ba a gabanta akayi ba kuma bata da shaida" tayi k'wafa tace "ta sake ta gaya ma gwaggo wllh 6atawa zamu yi ba ruwana da ita" tayi maganar tana mummurgud'a baki,To hajia Fatuu ba dai yau kika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login