Showing 42001 words to 45000 words out of 212491 words
tayi ba ta tsorata sosae lokacin da Abbas ya bude kopan,dama a d'arare take.
Abbas ya dan dago daga jinginar da yayi jikin kujera yana duba agogon wrist dinsa kafin yace"I think i will take my leave now zakee" dagowa haisam yayi ya jingina bayansa da kujera yana kallon Abbas "nayi tunanin za kai magrib anan it's almost time" sigh Abbas ya yi yace"anya kuwa, nayi ma feenah alkawarin ina gida za'ai magrib duk da yanzu ma time ya kure,banso tayi fushi" ya karasa maganar yana murmushi,
shikam haisam dan waro idanu yayi cike da mamaki"yaushe kenan ka fara tsoron fushin Nafeesat? tuntsirewa da daria Abbas yayi"A yau din nan,kasan mata sun iya tsiya ba kamar in ka 6ata masu rai sun san ta yadda zasu rama,yadda na dawo daga tafiyar nan ai kaga bazan so in 6ata mata rai ba kar sai anjima in zama kamar d'an maraya tunda nidae ba yan tsallake tsallake nike ba,a iya ta halalin na tsaya...."tun kafin ya karasa Haisam ya d'aure fuska hadi da juyar da kansa gefe guda yana girgiza shi,ganin yadda yayi yasa Abbas kara tuntsirewa da wata yar iskar daria,dama yasan haisam din kunyar irin wadannan maganganun yake,shi kuma gashi bakinshi a sake yake wurin yin irin maganganun ya cigaba da cewa"ko da yake kaifa ba sanin yadda abun yake kai ba balle ka fahim....." da sauri haisam ya rarumi throw pillow ya jefa ma Abbas yana fadin"Go Abbas,Just go pls" sosai Abbas keta daria ya fara kokarin mikewa tsaye yana fadin"komai ka nuna kai mai kunya ne,bari kai auren mugani" shi dai still yayi yana kallonshi ganin ya mike yace"ba zaka shiga ku gaisa da hajia ba?" Abbas yace"next time",
gyada kai ya yi"in tace ta ganka baka shiga kun gaisa ba zan fada mata saboda kar matarka tayi fushi ne ka ki zuwa ka gaida ta",
"ah ai sai dae in kaine zaka fada mata nazo,tunda bata ganni ba ko ride dina na a wajen gate" dan murmushi haisam yayi yace"I don't have to..da kanta tana zaune zata gan kazo gidan" haisam na fadin hakan Abbas ya fahimci abunda yake nufi hannu yasa ya dafe forehead dinshi"Oh namanta da CCTV fa,tabb dole kam inje in gaidata kar nayi babban laifi,amman fa in na koma gida feenah bata saurare ni ba wllh kiranka zanyi kamata bayanin kai ka rike ni" harararsa kawae haisam yayi ya yunkura ya mike don kiran magrib da aka fara,patting shoulder dinshi Abbas yayi yana ci gaba da tabbatar mashi da zai kirashi indai feenah bata saurareshi ba a haka suka fice zuwa masallacin gidan.
Atare suka shigo falon hajia bayan gama sallar magrib,kujera 2 seater haisam ya nufa ya fada samanta ya dan kwanta yayin da Abbas ya zauna saman one seater yana facing din haisam,ganin hajiyan bata a falon yasa Abbas cewa"ina hajiyan ne? watsa hannuwa haisam yayi alamar oho,sai kuma yace"kilan bata gama sallan ba kasan tana dan dadewa" Abbas yace"pls to ka kira ta mana kasan fa ina sauri ne" kura masa ido haisam yayi kaman bazai tanka sa ba sai kuma yace"badai matsalanka feenah bace,to ka kira nin if she denies u..." da sauri Abbas ya katseshi"akwae abunda nike so zan siya a hanya ne" haisam dake ta kallon shi yace"harda bribe kenan zaka bayar,nasan bai wuce chicken karka damu nasan inda zaka samu wannan koda tsakiyan dare ne" ya karasa maganar yana wani irin murmushin rainin wayo,shikam Abbas dan buga kafa yayi a kule yace"pls zakee do call her" hannu haisam yasa yana shafa beard dinsa kafin calmly yace"anya Abbas..." da sauri Abbas ya katseshi"halan ni jarababbe ne zaka ce,mu barshi a hakan idan kayi aure mayi wannan maganar ni dai pls ka kira man ita,
Waya haisam ya ciro daga cikin aljihun jeans din jikinsa ya shiga kiran hajiyan tana d'agawa yace"U have a guest" yana fadin hakan ya cire wayan ya ajeta a gefensa, dagowa yayi yaci gaba da kallon Abbas yana wani murmushi hadi da dan girgiza kai,dan guntun tsoki abbas yaja yace"irin ka ne in kukayi aure kunfi kowa jaraba wllh zaka rinka man wani kallon iskanci"cike da rainin wayo haisam ya dage gira yace"haba" kafin Abbas yace wani abu hajiya ta shigo falon tana sanye da dogon hijab har kasa hannunta rike da cazbaha nufo inda suke zaune tayi tana fadin"bako daga ina..."bata karasa ba suka hada ido da Abbas dake kallonta yana murmushi,hannu hajiya tasa ta rike ha6arta"Abbas,dama kaine bakon?aikuwa da nasan kaine ma ba zan fito ba,yanzun ma komawa ta zanyi"ta kai maganar tana kokarin juyawa,da sauri Abbas ya mike yaje yasha gabanta yana daria,ruko hannayenta yayi yana fadin"afuwan hajjaju ta,tuba nike" harararsa tayi tace"ni bawani dadin bakin da zakayi man,yaushe rabon da ka tako kafafunka gidan nan da sunan kazo gaidani?sai yanzu da abokinka ya dawo shine zan ganka wato dai dama saboda shi kadae kake zuwa ko?" da sauri Abbas yace"No hajjaju aikin san dae ina zuwa ko da baya nan,kawae kwana biyu wllh abubuwa ne sukai yawa bansamu na leko ba,amman dama yanzu zuwa nayi don in gaidaki in kuma bada hakuri,dawowa ta gari kenan..."hajiya dake d'an harararsa ta katseshi"dawowarka gari kenan kazo ganin abokinka ko",
"a'a ke nazo gaidawa ai shi tun kafin na tafi ma mun hadu,pls tuba nike muje ciki ki zauna sai mu gaisa sosae" uhm tace kafin ta juya suka nufi wurin kujeru,haisam dake ta latsa waya amman yana jin abunda suke cewa ya dago yana kallon Abbas da har lokacin yake rike da hannun hajia guda yace"da girman ka..."da sauri Abbas ya daga masa hannu alamar yayi shiru don Allah,karaf sukaji hajia tace"yake karya ba"gaba daya suka sa dariya,
saman 3 seater suka zauna Abbas ya shiga gaida ta,tace"ya iyali,suma dai ka hanamu zumunci kiri kiri Abbas" da sauri yace"ni na isa hajjaju ai in kullum kika ce kina son ganinsu indai ina gari zan kawo maki su",
"haka dae kace amman yaushe rabon da ka kawo su tun can kwanaki da kuka zo"
"in sha Allahu cikin satin nan zan kawo su hajjaju afuwan nasan nayi laifi",
"Shikenan zan hakura amman in baka kawo mun su anyi zumunci ba banga mai sasanta mu ba" da sauri yace"zanma kawo su ai" juyawa hajiya tayi side din da kitchen yake tana fadin"Saude ko ta gama sallan tazo ta kawo maka lemu" tana niyyar kwala ma sauden kira Abbas yace"bari inje in daukko ai ni ba bako bane dama kishi nike ji" ya mike ya nufi hanyar dining yana fadin"ke kin damu dani hajiata,shi wannan gwauron ko tayin ruwanma baiyi munba balle ma ya daukko man" haisam dake a kishingid'e yace"baka san inda ruwan yake bane,ko ni yaron ka ne da zan daukko ma"
Bayan Abbas ya daukko lemun bai zauna ba suka yi sallama da hajia,tace ya jira zata bada sako akai ma d'anta,Saude ce ta kawo masa ledar biscuits dasu sweets din da ta siyo ma hajiyar dazun da rana da taje siyayya kasuwa,suka nufi wajen gate inda ya parker motarsa,bayan Abbas ya tafi komawa haisam yayi part din hajiya ya ci gaba da kallo har aka kira sallan isha ya fito ya nufi masallaci.
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
*BY ZAINAB LALUH📲*
~(Oummu Imam)~
Free page 25
.......Bayan angama sallan komawa haisam yayi part d'insa ya shiga wanka,bai jima sosae ba ya fito daga cikin bedroom dinsa ashirye cikin riga da wando marasa nauyi rigan sleeveless hoodie ce army green,irin rigan nan mara hannuwa mai dauke da hula mak'ale a wuya igiyoyinta sun zubo saman kirjinshi sannan gaban rigan anyi wani design din rubutu baki mai walwali, wandon kuwa baki ne 3 quarter ya wuce gwiwarsa ya d'an matse,ba karamin kyau yayi cikin shigan ba,kirarsa ta kakkarfa ta bayyana,baisa hulan rigan ba tana kwance a bayansa sai da ya yi shut down laptop din dake ajiye a falon kafin ya fice ya koma part din hajia,don gaba d'aya yau he's busy working on his laptop dama kuma bai zuwa Gym ranar lahadi,tunda rana hajiya keta kiranshi tana korafin yana gida amman bazai zo suyi hira ba,ya sanar da ita yana wani aikine,tace to ya dawo falonta yayi aikin mana yace mata yafi samun network a part dinsa tayi hakuri da dare zai zo suyi firan.
*** *** ****
Tun bayan da ta shige d'akin bata fito ba saida aka kira magriba ta fito yin alwala anan suka had'e da Amadu yana ganinta yace"ke,yaushe ki ka dawo gidan?ba dazun da ki ka dawo daga islamiyya kince man zaki gidan hajia ba?" fatuu dake ta zare idanu tace"ai..ai hajiyan batanan ne shine na dawo" gyada kai yai ya wuce yayi alwalarsa ya nufi masallaci,itama alwalar tayi ta koma daki tayi salla,gaba daya ranta bai mata dadi sai tufka da warwara take zulluminta kada gobe tayi bataje ta bashi hakuri kaman yadda haulat ta bata shawara ba,gashi ita dae harga Allah tsoron zuwa take don batasan abunda zai biyo baya ba,kuma tana ganin mutumin kaman baida kirki,tana ta zaune har aka kira sallan isha'e,anan ta yanke shawarar komawa bashi hakurin bayan ta gama sallan isha din,
tana gama sallan ta shiga yin addu'a tana rok'on Allah da ya taimaketa mutumin yayi hakuri in taje,ta tuba bazata kara ba,tana cikin shafa addu'an ta jiyo sallamar gwaggo ta dawo,gabanta ne ya fadi rass ta shiga tunanin yadda zata fita daga gidan don tasan sai gwaggon ta tambayi abunda zata je yi gidan hajia yanzu,
d'aga labulen dakinta da gwaggo tayi yasata juyawa da sauri tana kallonta da yake akwae wutan Nepa,shigowa ciki gwaggo tayi jikinta sanye da uniform din aiki fatuu dake kallonta tace"Dja66ama bé wargo gwaggo",
"yauwa,ya gidan? "Lafiya lou" ta bata amsa,
"ashe bakiji dadi ba?yanzun nan Amadu ke gaya man a kopar gida" fatuu tace"eh amman nasamu sauki sosai,ya bani magani nasha har islamiyya ma naje" jinjina kai gwaggo tayi"kin kuwa ci abinci?" Girgiza mata kai fatuu tayi alamar a'a,ganinta sukuku gashi idanunta kaman tayi kuka yasa gwaggo cewa"kodae wani abun ke damunki?ince ba fitina kika jawo mana ba dae,dama inata mamaki kwana biyu da ba'a kawo man k'ararki ba,fada man gaskia minene fatuu? gabanta ne ya fadi rasss da sauri ta sunkuyar da kanta kasa tace"a'a gwaggo ba wani abu fa,kawai har yanzu ban dan jin dadi ne"ta karasa gabanta nata faduwa,
Jinjina kai gwaggo tayi ta nufi hanyar fita tana fad'in"ki tashi ki ci abincin sai ki k'ara shan magani,Allah ya sawaka,ni bari inje in watsa ruwa insamu na kwanta na kwaso gajiya sosai,kizo ki kar6i abincin gama abun biki can cikin jakata da aka ban in zaki ci su cin-cin ne da dublan" daga haka ta fice,sosai gaban fatuu yaci gaba da faduwa jin maganar da gwaggo ta mata,tabbas dole ta tafi taba mutumin nan hakuri tun gobe batayi ba asirinta ya tonu,
*** *** *** ***
Hajiya zaune a falo tana kallon sabon shirin kwana cas'in na tashar arewa 24, haisam ya shigo da yar sallamar da ba lalle ma in taji ba ya nufi kujera ya zauna yana facing din hajiyar,juyowa tayi ta kalle shi da d'an murmushi"sannu,yau kasha aiki,yini guda mutum na latse-latse,basu hakuri gobe kaje office din" hannu yasa ya shafo forehead dinsa kafin yace"ba aikin office bane" gyada kai tayi sai kuma tace"halan turawan ne,suda basu ganin mutum mai hazaka su kyale,in sunyi hakuri ba tattarawa za kai duka ka koma wurinsu ba"
d'an kwantar da kai yayi baice mata komae ba saima wani lumshe ido da yayi,da sauri ta juya tana kallon t.v jin muryar yawale yana magana,ba karamin cin dariyar acting dinsa take ba yana burgeta,tana ta daria tace"in baya ga ma film,ai ni a zahiri bazan iya d'aukan irin wannan matsayin direba ba,sai kata maimaita mashi magana sannan ya fahimta ina dalili" juyowa tayi tace ma haisam"wai nan direba ne fa ahaka" A hankali haisam ya ware idanunsa kan tv d'in yana kallon abunda hajiyan ke magana akai,dan murmushi yayi ya juya ya dauki wayansa dake aje a hannun kujera yana fadin"in driver dinki ne har marinsa zaki one day",
"in naga zai man wasa da rayuwa ba dole na maresa ba,ai wannan kyansa yaron gida ba abu mai mahimmaci kaman tuki ba" shi dai bai ce mata komai ba ya cigaba da latsa wayarsa,ita kuma hajiya taci gaba da kallon su yawale da rayya tana daria,jefi-jefi take waigowa tana ma haisam magana kan shirin don dama haka take bata iya shiru in tana kallo shidai sai dae yayi d'an murmushi ko ya daga mata kai don ba kallon shirin yake ba,so ba abunda yake fahimta.
Hajiya ta sake juyowa tace"akawo maka abinci ko?" Kai ya daga mata alamar eh,ta juya tana kwala ma Saude kira,bayan ta fito ta bata umarnin ta kawo ma haisam abinci tace mata basai ta zubo a warmer ba tunda yanzu zai ci ta amsa da to,ta shige kicin don zubo masa abincin,a tray ta d'auro kayan abincin ta nufo inda haisam d'in yake don ta fahimci indai shi kad'ai zaici abinci baison akai masa saman dining table,saman sofa table ta daura tray din tana gaishe shi ya amsa,tana kokarin zuba masa zo6o cikin cup ya dakatar da ita alamar ta barshi zai zuba da kansa,daga haka tace "aci lpy" sannan ta juya,
cire plate din da aka rufe abincin yayi ya tsaya yana kallon shi wanda spaghetti ce tasha vegetables da busasshen kifi sai kamshi ke tashi,da sauri ya d'ago yana niyyar tsaida Saude dake k'okarin shigewa cikin corridor"hey...." Hajia ta juya da sauri tace"je ki abunki" kafin ta juyo tana dan harararsa"in ma zaka cinye ka cinye don ba abunda za'a rage,wato dazun don kaga can aka bika dashi shine ka tsakura kace azo a dauke ai dama nace zamu hade da daddare ne" haisam dake ta kallonta yana dan cizon lip d'insa na k'asa had'i da dan murmushi yace "did i say anything?" A tsiwace tace"But u'r about to....haka kurum don ka jaman sharri iyayenka su zo su ga ka rame suce hakanan na matsa ka dawo wurina ashe bana baka abinci" Haisam couldn't help it but laugh,sai kace ta daukko wani k'aramin yaro wanda baisan ciwon kansa ba,itama dariyar take taci gaba da kallonta da har yanzu ake shirin da take kallo,shi kuma ya fara cin abincin.
Tunda ta amso abincin ta dawo d'aki ta kasa cin wani na kirki yan lomomi ne tayi taji duk ya fita ranta ba kuma don bata jin yunwar ba,sai don hankalinta daba a kwance ba,tunaninta yadda zata fita yanzu ba tare da gwaggo ta hanata ba don dole fa taje taba mutumin nan hakuri da daren nan,tsam ta mik'e hannunta dauke da plate din abincin ta maida kicin ta rufe a tsakar gida tayi tsaye tana zullumin zuwa tambayar gwaggon daga baya dai ta nufi d'akin gabanta nata faduwa,d'aga labulan d'akin tayi ta shiga da yar sallama gwaggo da har ta kwanta amman bata yi bacci ba ta d'ago da kanta tana k'okarin kunna fitilan wayanta "fatuu,djam? ta tambayeta,Matsawa tayi kusa da gadon tana kallon gwaggon tace"d..dama gidan hajia zanje" cike da mamaki gwaggo tace"gidan hajiya da daren nan,me zaki je yi?",
"Un..dama jiya ne dana je tace in koma yau zata bani sako,to dana dawo islamiyyar safe ban lafiya sai d'azun dana dawo ta yamma naje sai na iske bata nan ta fita ita da t.k amman Aunty Saude tace man in koma in ta dawo don kafin ta fitan saida ta aikota tazo ta kira ni ta iske ban dawo daga islamiyyar ba" ta k'arasa maganar sai faman zare ido take gabanta naci gaba da bugawa da k'arfi,ba don ba haske sosai ad'akin ba da tuni gwaggo ta gane k'arya take shirga mata don har yar zufa tayi,
sanin dama hajiyar na aikowa kiran fatuu wani lokacin yasa gwaggo cewa"to miyasa tun dazun baki je kinga ko ta dawon ba,kika bari dare yayi har haka tara fa ta kusa inma bata yi ba..." da sauri ta katseta "ai ina niyyar dana gama sallah in koma sai kuma kika dawo" gwaggon tace"to ki maza kije ki dawo karfa ki zauna har Amadu ya tashi" cike da farin ciki tace"ah bazan zauna bama" daga haka ta fice ta nufi hanyar fita ko hijab bata yi tunanin taje tasa ba iya d'an bakin gyalenta na gado ne a saman kanta ga kan yayi wani tum saboda gashinta dake a kwance ba kitso yayin da jikinta ke sanye da riga da skirt na material da alama tana son sa riga da skirt,gidan hajiya ta nufa duk da fargabar da take ji hakan bai hanata tunkarar gidan ba don tasha alwashin a daren nan sai taba mutumin nan hakuri.
Sauran kad'an haisam ya k'arasa cinye abincin wayarsa ta hau yin wata kara alamar notification,sanin karar ko ta miye yasa da dan sauri yakai hannu kan hannun kujerar yadau wayan yana dubawa lokaci guda yanayinsa ya canza da wani irin expression mai kaman mamaki kaman bacin rai yake kallon videon fatuu dake sand'a tana tunkarar falonsa,lokaci guda ya furta"Again...! jin haka yasa hajiya juyowa tana kallonsa "ince dai lafiya ko?"ta tambaya,"Yea,nothing" ya bata amsa yana k'okarin mik'ewa don ya yanke a ransa sai yaje yaji mike kawo ta part dinsa,ganin yana kokarin tashi Hajia tace"wai mike faruwa,gashi nan yanayin fuskar ka ya canja kuma ka ki ka sanar dani" d'an murmushi yayi"nace ba komae Sweethrt,just wani sako ne na tura shine aka sanar dani bai shiga ba zanje nai resending" ya fadi mata hakanne don ta kwantar da hankalinta,
tace"to baka sha zo6on ba", "kar ki damu zan sha lemu inna koma can" dan 6ata rai tayi ta fara korafi "shikenan baza'a bar mutum ya huta ba,yini guda mutum nata faman latse,latse haba" yar daria yayi yace"to dama mai nema ina yaga hutu sweethrt" yana gab da fita daga falon tace"zaka dawo muyi hira ko? d'aga mata hannu yayi yana juya shi alamar a'a yace"ki ci gaba da kallon ki saida safe tomorrow is Monday and early to bed early to rise.." daga haka ya fice hajiya na fadin"Allah ya tashe mu lpy toh".
Da sauri ya nufi part dinsa don baison ta fice kafin ya isa,
A hankali fatuu ta kama handle din